Showing 66001 words to 69000 words out of 135756 words

Chapter 23 - Bibiyata Akeyi book Complete 1 to end..txt

25 Nov 2024

7568

kano road can tahango motarsa atsaye, yana kallonta yafito daga motar yak'araso zuwa wajan ta."
Tun daga nesa yake kallonta yanajii wani zuciyarsa ba bugawa da saurii da saurii tunda yake bai ta6a jin wani abuu haka akan wata y'a mace ba sai akan *hanna* wanda ayanzu ya kawarda hakan, sai gashi kuma yanajiin hakan akan k'awarta. "
Wani irin kallo yake mata Tun daga nesa wanda ita kanta takasa jurewa kallonda yake mata." k'ananun kayane ajikin sa sun bala'in yimasa kyau. "dan ita kanta yamata kwarjini."
Ta sunkuyarda kanta har ta isa wajansa. "
Tana zuwa tad'an rusuna ta gaidashi ya amsa yana mai binta da kallo."
Wata irin murya yayi amfanii wajen cewa kinzo k'ar6awa k'awarki aika ko. "
Gabanta ne yafara fad'i dan Wani yanayi ta tsincii kanta dashi ga Wani irin kunyarsa data lullu6eta,"
D'aga masa kai kawai tayi. "
Ta mika hannu da niyar kar6ar laidain hannunsa yayi saurin zanjeyawa da'agowa tayi ta marairaice idanu tace ana jirana na nefa,
Shima irin muryarta yayi yace to muje in rakaki dan baza ki d'auki kaya ba."
Shagwabe fuska tayi tace wannan har Wani kaya ne dazakace wai kaya. "
Inuwa yananema yazauna sannna ya nuna mata itama tazauna bbu musu tazauna dan tafarajin dad'in hirar tasu,"
Haka ta zauna sukayita hira gasu dukanku masusan barkwancii, nan da nan suka saba. " basusan lokacii yayi nisaba sai kiran hameeda taganii."
Tana dubawa taga har 3 tasan komadai menene yanzu anfara shirin tafiya walima tashi tayi da saurii ya kalleta ina zakije muna tad'i? " yaya ka kalli lokacin tafiya yayi ni bansaniba, dan tsaki yaja yace kibari zan kaiki, marairaice fuska tayi kamar zatayi kuka tace" *hanna* bazatajii dad'ii ba, "Tashi yayi
Sanda yarakata har bakin gate kafin yajuya."
Tana shiga tasamu kusan duka sungama shiri saura amarya da ake mata makeup kamar munafuka tashigo tashige toilet tafara wanka kafin tashigo tafara shiri."
Zuwa hud'u sungama shiri sai wajan 4:20.suka isa *awala hotel* malama juwairiyya ne tayi wa'azii, zuwa 6pm.an tashi koda, suka koma gida abinda yadamu *hanna* har yanzu bataga anty maman amal awajen walimar ba kuma ta tabbata fushi takeyi dalilin dayasata kuka awajen walimar kenan, mutane dayawa sukayi zaton cewa wa'azine yaratsa ta."
Tadawo takira wayarta kuma ba'ad'aga ba. " ba'awuce ko ina dasuba sai gidan babanta dan gobe yakama d'aurin aure kenan."
Ahaka ta kwana bbu kuzari gawani irin fad'uwar gaba dan tasan daga gobe zata bar gida kuma saidai tazao yawo ko hutu kukakam awannan daren tayishi bbu iyaka. "
Washe gari da safe yakama asabar ranar d'aurin aure kenan."












_Kuyi hakuri ku kar6i uzurina wallhy, nima kaina banso hakanba_






To be continued










Ur's
*z33yyb3rw3r*


*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_




_
Writting by



© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )


Yaban gwani yazama dole gaskiya action kinyi k'okarii a littafinki na *saiful maleek* Allah yak'ara basira da zaqin hannu, "
Muna biyeda ke abuk dinki nagaba."
Kinyi k'ok'arii wajan kammala buk dinki dawurii Allah yqtqimaka. "
Ina tayakii murnar kammalawa."




Page 55


*
Dasafe haka tatashi duk jikinta bbu k'arfii dan kukan datasha jiya da daddadre, "
Tun sassafe bak'i suka k'ara cika gidan tamm bbu masaka tsinke danma Allah yataimaka gidan yanada d'an girmansa."
Auren za'a d'aura shine a masallacin a babban masallacin fahda dake bauchin yakubu."
Can kano kuwa su MG sai shirin tafowa d'aurin aure akeyi, "
MG kuwa yana shashinsa tareda abokanan sa wanda sukazo daga k'asashe daban daban."
Shahid mahmud abbas, dakuma hamood bn abid ne kusa dashi suna zaune, " banda tsokanarsa bbu abunda sukeyi gabaki d'aya tare sukayi passing out,"
Idan baku manta ba ashekarar dasu MG sukayi passing out a rusia nafad'a muku su uku ne."
Kuma dukansu musulmai ne, so sun zo bikinne, dan sukam sunyi aure. "
Yayinda Shahid yaransa biyu shi kuma hamood d'ansa d'aya,
Alokacinda sukayi aure bbu irin takurawa wanda basuyiwa MG ba Amma yak'ii,"
Shi yasa yanzu suka sashi agaba suna tsokana, "
Shiru yamusu kawai yana murmushi dan wani irin nishad'i da farinciki yake ciki."
Ko bbu komai yasan ayau zai mallaki *hanna* yauce ranarda yayi shekara goma ciff yana jira, "
To dan maiyasa bazaiyi farinciki ba."
Murmushi kawai yakeyi yana shafa gashin kansa, "
Baice musu komai kawai da ido yake binsu."
Hamood ne yatashi ya kalli MG yace" soldier nifa tun jiya bansa matata a ido naba dan haka katashi kaje ka kainii wajanta na ganta."
Murmushin rainin hankali MG yayi sannan yace ai Idan kaga nafita anan to katabbata cewa nafita ne da nufiin tafiya aje a d'aureni da sweery ne,"
Idan bahaka ba kam ina nan yanzu ma barina tashii plzz katashi ku shirya karkumuyi latti dan, "
Sake baki sukeyi suna kallonsa tunda suke basu ta6a tunanin cewa MG zaiyiwa wani abu zumud'i hakaba,"
Ganin haka yasa kowa fara shiri kafin k'arfe tara 9:00.am duka abokanan ango sungama shiri,".
MG kuwa farar shadda yasa karrr babbar riga gara." tasha bak'in aikii, "
Da bak'in hula gashinsa yakwanta yayi luff luff,"
Da bak'in takalmii sau ciki sai shek'ii yakeyi. "
Sai link dayasa a hannun rigarsa ta ciki, links d'in black diamon ne,"
Kai alikacin kaga MG sai numfashinka yad'auke bak'aramun kyau yayiba Idan ana fad'in kyau to ina nufin kyau Kai ni aganina kalmar kyau tayi ka d'an ta fasaltashi. "
Koda yafito abokanansa tsayawa sukayi suna kallonsa,"
Dan sunsan yanada kyau Amma kuma nayau dabanne dakuma yahad'u da fara'a da kuma yanayin farinciki dayake ciki, "
Sai kyawunsa yak'ara bayyana,"
Futa yayi ya nufii shashin Unmii yayinda abokanan sa suka take masa baya har zuwa sashin Unmii Koda yashiga yasameta itama tayi shiga ta alfarma tayi wani masifar kyau. "
Sai annashuwa yakeyi tako ina hakwaranta awaje yake ga y'an uwanta sunsata agaba sai hira mai dad'ii suke yi,"
Alokacin MG yayi sallama yashigo tundaga nesa Unmii ke kollon d'an nata wani irin kyau dayamata da wani k'ayataccen murmushi afuskarsa, "
Kana kallonsa kasan yana cikin farinciki marar misaltuwa."
Koda yak'araso zuwa yayi ya zube guiwowinsa agabanta, "
Saurin sa hannuwanta tayi ta rige k'qfafunsa Tana magana tanacewa mai son katashi kada ka 6ata wannna kwalliyar dan banso ko kwayar zarra ta kura ta sauka ajikinka harsai wanda akayi kwalliyar dominta taganii."
Mai son ina matuk'ar farinciki yau in sha Allah burinka zai cika yau in sha Allah zan kalli ranarda nadad'e ina jiranta. "
Allah yamaka albarka yabaka zaman lpy arayuwar aurenka,"
Allah yarabaka da duk wani sharrii da fitintunuu da zasu taso cikin aurenku. "
Ahaka tayita masa addu'a masu matuk'ar mahimmancii har sanda yaji hawaye na k'ok'arin zubowa a idanuwansa,"
Ganin yanda idanuwansa suka cika da hawaye najin dad'iin addu'arda mahaifiyarsa take masa. "
Girgiza masa Kai Unmii tayi tace a'a mai son ko ka manta yau ranar meyece?"
Dakake shirin yin kuka."
A'a karka fara katashi kaje ku tafii kar Kuyi latti. "
Had'a hannuwanta biyu yayi ya sumbata sannan yace ba kuka zanyiba ummiina,"
Ummiina kokin manta waye d'ankii. ne."
Ummiina na d'ankii fa jarimii ne,"
Kawai dai najii dad'iin addu'ooiinkii ne. "
Inasonkii ummiina," Inasonkii fiyeda kowa aduniyar nan,"
Kinfii min kowa da komai mahimmancii. "
Allah yabanii ikon yimiki biyayya,"
Sa hannu tayi alips d'inta tamasa alamun yayi shiru shhhh tashi katafii Allah yamaka albarka amsawa yayi da amin, "
Mutanen d'akin duk sun zuba musu ido gabakii d'aya sai d'a da uwar suka burgeshi sai rayuwarsu tabasu sha'awa."
Yatashi haka sanda ya sunbacii umminsa agoshi kafinnan ya gaida mutanen wajen yajuya zai fita, "
Yak'ara juyowa yakalli amminsa yace Inasonkii ummiina,"
Murmushin ta mayar masa tace nima inasonka d'ana sosai Ahaka yafice yanufii shashin kilishi, "
Koda ya isa yayi sallama ya jira akamasa isoo ya shiga, ta na kallonsa afili tanuna tana farinciki a zuciyarta kuwa ba haka bane." bak'in cikin Auren bare dazaiyiibe makill. "
Koda intisar tajii muryarsa saita futo ganinsa haka da wani irin kyau dayayi ga annashuwa da farinciki afuskarsa,"
Ba k'aramin kishi bane ya turnuk'eta,"
Tasan wannnan farinciki da annashuwa duk dan zai aurii watane take idanuwanta suka cike da kwalla. "
Dkayr ta iya gaidashi ya amsa da fara'a sosai haryana tambayarta yatakwana hakan kuwa bak'aramun dad'ii yamata ba ko bbu komai yau tasamu dariya da kuma kulawarsa."
Daganan yafice kilishi namasa addu'ooiin zaman lafiyanda ko zuciyarta bata kaiba. " Daganan wajan mai marataba yanufa yaje yasamu harya gama shiri su ake jira. "
K'arfe goma dai-dai suka tashi damai martaba da iyalansa dakuma y'an uwa da abokanai zuwa wajan d'aurin aure."
Dake ajirgi ne basu dad'ee ba suka isa, "
Agidan mai martaba sarkin bauchi suka yada zango k'arfe shad'aya masallacii da wajan sun cikin bbu masaka tsinke."
Jama'akam fad'ansu 6ata baki ne sojoji birjikk ta ko inaa, "
Fararen fata sunfii kowa yawa awajen bikin,"
Dan idan kaga taron wajen zakace taron k'asa da k'asa akeyi k'arfe shad'aya da rabii 11:30 dai-dai aranar asabar ranar rana mai dum6in tarihi aka d' aura auren *Abudullahi abdul'aziz lameed'o da hannatu muhammad dambam* akan sadakii naira dubu hamsin ka call."
A dai-dai wannnan lokacii gaban *hanna* yayi wata irin mummunan fad'uwa. "
Jitakryi kamar tasa hannunta akayi ta kwala ihuu."
Yayinda shikuma MG alokacin wani abuu daya tokare masa makoshi tsawon shekara goma sai alokacin ya fad'a. "







To be countinued






Ur's
*z33yyb3rw3r*


*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_


_
Writting by



© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )


Page 56


*
Abinda yatokarewa MG kirjii samada shekara goma, "
Sai alokacin da yajii and'aura aurensa da *hanna* kafin yajii abin ya fad'a masa sai wani irin sanyii yaringa jii zuciyarsa namasa,"
Fara'a kawai yakeyi bakinsa kamar gonar auduga, "
Sai gaisawa da y'an uwa da abokan arziki yakeyi tako ina,"
Yayinda ita kuwa *hanna* tun lokacin da taga 11:30 dai-dai yayi ga wani irin fad'uwar gaba dake damunta tasan cewa aikin gama yarigada yagama, "
Kawai ta tsincii kanta da hawaye dan ko k'arfin kukan batadashi dake ta dad'e tanayi."
Kuma tanajii ana tad'ii ta window cewa k'arfe d'aya bayan anyii reception zasu kama hanya."
Cikin ranta tanajin wani zafii da rad'ad'ii sai kace wanda suka gajii da ita zasu bada ita k'arfe d'aya. "
Ahaka ta zauna bbu yanda Ammah batayi da ita tayi wanka ba Amma firr tak'ii yii babu irin lallashin da batayi mata ba Amma tak'ii,"
Ganin lokacii yawuce yasa Amma taje tafad'awa mama, "
Duk da mama itama najin zafinn rabuwar ta da d'iyarta tadaure ta shiga tafarayi mata fad'a."
Sai alokacin *hanna* tasamu bakin yiin kuka tajuya takalli mama tace,"
Hava mama kumin dasauk'i mana tafad'a tana wani matsanancin kuka,"
Hava mama tafiya fa zanyi na barku Amma bazaku barnii naji da d'aya ba? "
Mama yazanyi nashiga uku tafad'a tanamai fashewa da kuka."
Nan da nan idanuwan mama itama yaciko sosai, tausayin y'ar tata yayi bala'iin kamata," Tashi tayi da sauri tafice daga d'akin dan idan bahqka ba zuciyarta na iya tsinkewa tafashe da kuka."
Mama bata wuce ko ina ba sai dak'in ta tana zuwa ta zube tana sauke ajiyar zuciya, "
Ganin haka yasa umma matsowa kusa da ita tana tamvayar maiyafaru duk da tasan cewa yau Mama sai ahankali rabuwa da d'iya yanada matuk'ar ciwo."
Matsowa tayi kusa da ita ta dafa ta. "
Sannan tace hava aisha yanzu idan ke baki dauree ba tayaya kike tunanin yarinyar zata daure?"
Nasan da ciwo Amma hakuri zakiyi bayau fa kika fara aurar da d'iya ba dan haka kiyi hakuri ko itama yarinyar zata samu ta kwantar da hankalinta."
Girgiza Kai Mama tayi Sannan tace kayyah yaya wallhy wannnan ba irin way'ancan bane kada ki manta, "
Auren hajja nayi tunani Akwai wata agabana sannan auren hindu shima ta barmin *hanna* yaya kike tunani zanjii yanzu idan aka d'aukemin ita?."
Banida wani mai taimakamin kinsan kulawar y'ay'a maza ba kamar na y'ay'a mata ba."
Goge kwallar data zubo mata tayi Sannan tace yaya kije ki rarrasheta dan tak'iyin wanka,"
Jikin umma ne yayi sanyi liqis Sannan ta tashi ta nufii d'akin Ammah bata reda tak'ara maganaba, "
Azaune tasamu *hanna* tana sheshekar kuka,"
K'arasawa kusada ita tayi ta dafa ta, cikin muryar lallashi tace, "
Hava *hanna* mekikeyi hakan?"
*Hanna* kiyita kuka sai kace wanda aka miki auren dole? "
Hava *hanna* kada ki kasance marowaciya mana kada ki kasance wanda bata sowa mahaifinta rahamar ubangiji."
Ke kanki shaida ne wannnan ingan taccen hadisi ne cewa duk mahaifinda ya aurar da y'ay'ansa samada biyu zuwa gidan mazajensu lpy,
Suka kare mutumcinsu Allah namasa albishir da gidan aljanna. "
Kukan *hanna* ne yatsagaita Sannan umma tacigaba da cewa,"
*Hanna* kisowa mahaifinku wannnan rahma, "
Kiyiwa mahaifinku biyayya dan samun wannnan rahama."
Ahaka umma tayi ta conviceing nata ta tashi tashiga wanka, "
Tana fitowa tayi umma ta bata mayuka kala kala ta shafa,"
Sannan ta bata turaruka samada kala shabiyar ta shafa, "
Kuma duka masu sanyiin kamshi."
Sanda tagama shafawa Sannan umma tace tazauna ayi mata makeup Amma firr tak'ii, "
Haka umma takyaleta bata matsa ba, dan tasan ko anyii zuwa jimawa idan taga anzo tafiya da ita zata 6ata da kuka."
Haka tad'uko mata wata bak'ar exclusive mai ratsin farii dinkin riga da zani anyi plain na zanin. "
Yazauna ajikinta d'an kwalin kuma tad'aurashi kawai batareda tayi wani style ba tazauna kawai tana tunani sai alokacin umma takawo mata tea da masa akan tacii,"
Dkayr tad'an tsakula dan d'acin abincin takeji, "
Tea d'inma dakyar ta kurba d'an kadan Sannan tace ta koshi."
Su kuwa can suna *faria suite limited* suna reception, "
K'arfe 12:30 zasu gama,"
Dazaran sungama za'atafii da amarya, "
K'arfe 12:40 suka gama reception alokacin motocii suka nufii gidansu dan d'aukan amare,"
Alokacin aka kira *hanna* zuwa d'akin baba anan tasamu duk y'an uwanta aciki Nasiha kowa yake mata sosai daga wannnan yagama wannnan yake kar6a, "
Itakuwa Mama takasa cewa komai duk jkinta yayi sanyi sosai."
Hawayene yake ambaliya afuskarta,"
Tanajin k'aran isowan motocii tayi saurin rarrrafawa gaban baba tana kuka tana cewa baba kamin rai natuba nabi Allah kayafemun baba karka bari su tafii danii. "
Wallhy baba idan wani abuu namaka nadaina baba bazan sake ba."
Baba bansan baka sona ba wallhy dakana sona bazaka bari su tafii danii ba,"
Ganin baba ya sunkuyar da kansa yasa ta rarrafa wajen abba tariqo kafarsa tana kuka abba kumin rai natuba nabii Allah nabiku abba kutaimakenii. "
Wani irin tausayin ta cikin matan kuwa d'ai-d'ai wayanda basu fara hawaye ba."
Ganin abba bai kulata ba yasa ta rarrafa gaban anty maamn amal, "
Tana kuka tana anty dan Allah kiyafemun, kiyi wa su abba magana."
Anty maman amal ce ta rungumota tana cewa baki min komaiba kanwata, "
Wallhy ban kutace kiba,"
Ba kawai inaso ki fahimcii Abinda yakamata kiyi ne."
Amma kiyi hakuri *hanna* gata ake maki ba wani abun ba. "
Aure gatane agareki, aure shine martabarkii."
Kiyi hakuri Ahaka matanda sukazo dauk'anta, sukayi sallama, "
Tana jinsu k'arfin kukan ta ya k'aru,"
Ahaka suka shigo aka gama duk wani abuu daza'ayii, "
Aka rufa mata abaya aka nufe waje da ita."


To be countinued


Ur's
*z33yyb3rw3r*


*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_


_
Writting by



© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )


Page 57


* A dai-dai wannan lokacii *hanna* kuka takeyi kamar ranta zai fita, "
Kuka takeyi kamar wanda akace har abada bazata zo gidanba."
Kuka takeyi tamkar wanda akace mata mahaifiyarta ta rasu. "
Fulani ce riqe da ita d'ayan gefen kuma umma,"
Sai baki umma ke bata, "
Alokacin aka shigar da ita wata mota k'irar *marcedeze benz* E350,
Yayinda duk sauran motocin corolla s ne wanda *hanna* kad'ai zata shigane ya banbanta,"
Haka *hanna* tanajii tana ganii aka turata cikin mota aikuwa saleem na gefen ta shima idanuwansa taff hawaye caff ta cafke hannunsa bbu yadda ba'ayi tasakeshiba amma fir tak'i duk da mabiyi da mabiyi bbu shiri amma akwai soyayya a cikin zuciyya ganin Haka yasa amma tace yashiga gaba,"
Yana shiga sannan umma ta shiga d'ayan gefen fulanii ta shiga d'aya, sukasa *hanna* atsakiya suka d'auki hanya."
Amota Sai lallashin ta umma keyi, Fulani tace rabu da ita tayi abunta ai girman kenan, "
Yanzu idan batayiba Sai ace tayi rashin kunya,"
Tafiyar mintii 25minute ce tasadasu da airport."
Dan acikinsu akwai wanda zasu tafii Amota amma Sai sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login