Showing 90001 words to 93000 words out of 135756 words

Chapter 31 - Bibiyata Akeyi book Complete 1 to end..txt

25 Nov 2024

7584

ita bazata sakaba."
Kamar yanda ya lura da *hanna* kullum Sai anyii rikici da ita akan pink d'in abuu."
Ahaka bayanda suka iya suka barta dan idanda saboo yakamata su saba da halin *hanna*."
Washe garii MG yakoma kano."
Bayan yaje bai b'oyewa mahaifiyarsa abunda yake faruwa dashiba duk da dai bai shaida mata cewa wacece Yarinyar ba?"
Kuma bai fad'a mata shekrunta ba."
Alokacin ummii ta shaida masa cewa sonta yakeyi."
Bbu yanda batayi akan yafad'a mata gidansu da adress d'insu ba."
Amma firr yak'ii yace mata dasauran lokaci."


Zuwa sunday Sanda yakoma bauchii dan kwana biyu dayayi baiganta ba jiyakeyi Kamar ya shekara duk yavii ya susuce."
Yana isa mai makarntarsu yafara nqima yashaida masa komai kan yanaso acanja uniform zuwa pink, mai makarantar ganin kud'ii nan danan ya amince."
Monday dake student kowa yazo za'a bashi unifor kyauta."
Pink colour *hanna* tayi murna sosai."
A''inda iyayen yara sukayi mamakin ganin yanda mai makarntar yakeda son kud'ii amma harya iya kyautan uniform."
Ahaka *hanna* tacigaba da karantawa har zuwa lokacinda suka shiga secoundry na dariya tayi dariya na kuka ma tayishi."
Kukantane ya tsananta Alokacin da taga MG yarubuta sojojina sun dawo masu saida rake dan ta dalilinki, sojojina sun zamq masu shago ta dalilinki."
Sojojina sun zama y'an taxi ta dalilinki."
Duk wani taxi takika shiga iya tsayon girmanki, ina tsare dake, wannan abuun nayi shine dan kar ki had'u da wanda zai sayemun zuciyarki."
*Hanna* sojojina har kwasan kwata na layinku sunyi dan tsaron lafiyarki."
Aduk yanda kike sojojina *BIBIYARKI SUKEYI*."
Aduk lokacinda da kike wani abuu idan kin cire mutanen gidanku tom ina *BIBIYE DAKE* k'arfin da kukan *hanna* yayinee yasata barin karatun Sanda tayi kukanta t koshi sannan kuma afili ta furta tabbas banyii laifii ba danace *BIBIYATA AKEYI* Share hawayenta tayi sannan tacigaba da karatun."


To be continued


Ur's
z33iiyyb3rw3r


*BIBIYATA AKEYI*


_Bismillahirrahmanirrahim_


Writing by
© _Zaynab Bawa_
( _z33iiyyb3rw3r_ )


_Like my page on Facebook :::Zaynab BAWA novels_


Followed me on instagram ::::mhiz_z33iiyyb3rw3r


*Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata agareshi yace." Duk wanda yakaranta wannan addu'a, la'ila ha illallahu wahdahu la sharika lahu, lahul hamdu wa lahul mulku yuhyi ayumitu ahuwa hayyul layamutu wahuwa ala kulli shai'in k'adir." Allah zai rubuta masa lada dubu sau dubu sannan zai yaye masa zunubi dubu sau dubu."*


*Yanada kyau karanta addu'ar nan bayan tashi daga bacci." Alhmdllhillazii ahyana ba'ada ma amatana wa'ilaihinnushur."*


================


Page 71


*
Share hawayen fuskarta tayi sannan tacigaba da karatun."
Page na gaba da bud'e, Alokacin da tafara girma, alokacinne fargaba yadad'u wa MG yanda yaga dare haka yake ganin rana haka yake kallon dare, Koda bacci yakeyi mafarkinsa bai wuce na *hanna* ba, akwai lokacinda wani malamin su yadaketa akan batayi note ba sanadiyar korarasa daga aikii kenan."
Tsayawa *hanna* tayi da karatun tarufe bakinta da hannunta tabbas tasan lokacinda wannan abun yafaru kuma tundaga wannan lokacii bbu wanda yak'ara dukanta tabbas abun har mamaki yake bata, tarasa dalili sai yanzu tasamu dalili."
Cigaba tayi da karatun, quarter na teacher's dinku sojojinane, narasa wani irin so nakeyiwa *hanna* ko alabarii banta6ajin Labarin makaman ciyar soyayaya irin wanda nake mataba."
Ko a film banta6a ganiiba balle azahiri."
Hak'ika wannan jarabawa ta ubangiji ne, wanda ke jarabtar bayinsa Aduk yanda yaso kuma Aduk lokacinda yayi niyya."
Hak'ika wannan jarabawa ta fad'a kan MG, duk lokacin birthday d'in ta, Aduk k'asarda MG yake saiya dawo yayi wshng d'inta birthday ya ajiye mata gift da Hannunsa, har yakawo lokacinda *hanna* tafara mensturation, ana farko harsanda suka dangana da asibiti, ganin bayan ansallametane sukayi baincike abunda yakwantarda ita, aikawa MG details na komai sukayii."
Awatan yasa aka canjawa likitan asibiti zuwa wani babban hospital, sannan yad'auko wata female doctor wanda takware afannin mata, yasata a asibitin, wani month da *hanna* suka dawo bayan tagama yimata treatment saita buk'aci data runga zuwa tun kafin date yacika."
Ahakanne yad'an samu relief, shikuma MG yananan yana bibiyar rayuwarta, Ahaka abubuwa sukayita tafiya dan har zuwa gama schooll ne secoundry,"
Tayi jamb ta samu admissn, tun daga ranarda tafara zuwa makaranta tun wannnan rana MG ke cikin fargaba, dan yasan yanayin jami'a dole za'asamu wanda zaija hankalinta."
Yanda yaci sa'a *hanna* bata kasance d'aya daga cikin masu rawar kan samarii ba."
Kodan batada farin jikinsu ne ohow🤷‍♀, Yad'aura da cewa, nasha wahala sosai na rashin yin aure da wuri sannan na fuskanci matsaloli da dama tafuskan hakan." Amma har indai akan jiran *hanna* ne zan iya komai zan iya jira ko hakan yana nufiin zan iya had'uwa da wata matsalar, banjin arayuwa, banda ta fannin iyaye akwai wani abunda yafimun ita mahimmancii aduniya, banjin ko rayuwarda nakeyi takaimun tata,"
Bansan maiyasaba amma nasandai haka kawai nayanke shawarar barinki harsaikinkai 19 kafin naasanar dake, Sai gashi, zuciya ta tana taraddadin hakan, Kuma amma nakasa sanardake ko mahaifanki."
Akowani lokacii nakan rasa wani abune ke tsayarda nii daga yin hakan."
Sau dayawa naso sanarda mahaifina amma kuma konaje gabansa ban iyace komai, Hakanne yasa na tattara lamurana na miqasu ga Allah."
Ina addu'a kawai dannasan Allah zaijii kaina tun dashi yad'auramun wannan lalurar kuma zai yayr mun."
Wani page ta bud'e dasabon rubutu kamar haka, Ayau na kasance cikin bak'in ciki, marar misaltuwa shine ranarda d'aya daga cikin soldier's d'ina yasanar dani cewa, *hanna* tafito daga lecture's har taje siyan abun shago, yabige wani mutum taje fad'uwa har yakamata, aranar nashiga rud'ani dan hankalina yakasa kwanciya, nakasa yarda da wannan mutum, K'arfe tara dai-dai na dare, tracer na wayar *hanna* ta nunamin kan call yashigo wayarta."
Ya tsincii kansa da son Jin wayan, bud'e wa yayi ya fara jii, kafin yagama duk yabii yashiga tashin hankali."
Suna gama wayar akayi tracing na wayar sa."
Alokacin yasamu duk wani impormation dayakeso akan sa."
Ya nemo kuma yasanii, amma bai yi Tunaniin zai iya rabashi da *hanna* ba, dan alamu masu yawa sun nuna tana sonsa."
Ahaka MG yacigaba da rayuwar k'uncii amma hakan baisa yakaraya ko Sau d'aya daga sonta da kuma burin auranta ba."
Shidai kawai yabata lokacii ne itada saurayin nata."dan kokad'an jikinsa bai bashi cewa wancan zai aurii *hanna* ba, yana yawan yin mafarkai akan cewa ya aurii *hanna* dayarnsu, Koda mafarkai ba gaskiya bane amma kuma yanajin dad'ii da wannan mafarki."
Ranarda labarii yazomin cewa *hanna* sun rabu da najeeb, narasa awani halii na tsincii kaina, ina tsananin tausayin *hanna*. "
Bayan karanta page dadama ne, yabud'e page d'in da MG ke cewa."
Yau ne takasance ranar farin ciki agareni, *hanna* ta yarda zata aureni, Koda nasan batasona amma inada yak'inin wataran zata sonii."
Labarai ta runga karantawa kala-kala duk randa suka had'u da MG ko Murmushi tayi sayya rubuta."
Balle yakaiga dariya."
Har zuwa ranar d'aurin aure su, har diner da aka yi sanda ya rubuta."
Har zuwa tafiyarsa."
Rufe littafin tayi tana kuka sosai wanda har zuciyarta zafii take mata, tana cewa Allah natuba, natuba Allah wayyo Allah na, mijina kayafeni, wallhy nima inasonka, Allah wani irin soyayya ta ka jarabcii wannan Bawa naka da ita wanda komai nayi baya ganin laifiina."
Allah natuba, tanayii tana riqe cikinta, dan zuciyarta tana mata suya gabaki d'aya haushin kanta takejii."
Ga wani irin son MG dayaa kamata wanda ita kanta batasan akwaishi tun daba, ko kuma lokacin yashiga ba."
Tafii 30 minute Ahaka amma kuma bbu sauk'i zazza6ine ma yafara rufeta." Tashi tayi ta niyar gyara akwatin, tana d'agashi yafad'o yazube, pics d'intane ne acike da k'atuwar trolly d'in tun tana yarinya har izuwa girmanta, abundai bbu yadda za'a fassarashi."
Bata k'ara kaiwa awaa d'aya ba zazza6ine mai zafii yarufeta, ko iya d'aga hannunta batayi, Ahaka matar abid tashigo tasameta, kiran doctor tayi amma shima soldier ne, yaduba ta yakawo mata maganganuwa, batafii kwana 2 ba zazza6in yasauka zai kuma azabar sonjin muryar MG takeyi tanasonjin awani halii yake ciki?." takira wayarsa hatta gashi baya shiga gashi 2 weeks kenan bbu wanda yajii Labarin su."
Itakam *hanna* Idan kaganta tayi rama sosai, kullum ararrashinta matan abokansa sukeyi, dakyar takecin abincii."


Ummii ne zaune tasa afeeya agaba, fad'a takeyi kawai akan itadai aje ad'auko mata y'arta bazata iya da rashin abu biyu ba bbu yareema kuma bbu matarsa *hanna* dan kimanin 5day's kenan kota kira wayar *hanna* ba'a d'agawa."
Duk yanda sukayi su shawo kan ummii abun yagagara."
Suma kansu Suna cikin tashin hankali.". Awashe garii afeeya tashirya da tatafii rushia da niyar dauko *hanna*."


To be continued


Ur's
Z33iiyyb3rw3r


*BIBIYATA AKEYI*


_Bismillahirrahmanirrahim_


Writing by
© _Zaynab Bawa_
( _z33iiyyb3rw3r_ )


_Like my page on Facebook :::Zaynab BAWA novels_


Followed me on instagram ::::mhiz_z33iiyyb3rw3r


*Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata agareshi yace, (Hajaral muslimu akhahu.") wato musulmi ta k'aurace d'an uwansa." Manzon Allah SAW, yace (kasafki damihi) wato kamar yazubarda jinin jikinsa ne. Hak'ik'a mai yanke zumunta yana cikin tashin hankali, Allah ka k'ara mana son y'an uwanmu acikin zuk'atanmu." Ameen ya Allah."*





*Manzon Allah SAW yace, ita wannan duniya da kuke ganii, (alsijnil muminun) wato takasance kurkuku wajen mumini." Yayinda tazama aljannah wa kafirii." Ya Allah ina rok'onka kada kasa dad'in duniya ya rud'emu, mukasa aiwatar da abunda zai fisshemu aranar alqiyama, Ya rabb, kabamu ikon bauta maka akowani hali muka tsincii kanmu, sannan Aduk abunda muka mallaka muyi amfanii dashi wajan bautata maka." Ameen ya rabbil izzatt."*


================


Page 72


*
K'arfe had'u na yamma jirginsu afeeya yasauk'a arussia, taxii tatsara ya kaita har zuwa estate na manyan sojoji."
Tun daga farkon layin sojojina azube, ako ina, shiga wajan yayiwa afeeya matuk'ar wahala dakyar suka barta tashiga izuwa estate d'in."
Koda ta isa bakin gate d'in bbu yanda batayiba anhanata shiga dan wajen manyan sojojine, acikin sojoinma sai kanada appointment kake shiga, ko kuma yakasance kana d'aya daga cikin masu tsaron wajen."
Har magrib afeeya na wajen, takira wayan *hanna* ba'a picking." har ranta ya6aci sosai dan tayi kusan 3hour's tana kira."
Wani tunani tayi nan danan hankalinta yatashi, batasan Kowani abune yafaru da *hanna* ba yasa bata picking."
Gashi Duk wani shaida dazai nuna cewa ita y'ar uwar MG ne batazo dashiba balle tasamu tadubata ko lpy, dan tasan hakan ba halin *hanna* bane."
Itakuwa *hanna* nacan ko breakfast batayiba dake yau cikin matan abid da shahid bbu wanda yaahigo."
Dakyar tasamu tashiga tayi wanka dan yunwa tacii jikinta sosai." Koda bayan tafito wayarta tad'auka taci gaba d kiran MG kamar kullum."
Abinda tasabaji shi akace wayar akashe take,"
Kukane ya kufcemata batasan awani hali MG ke ciki ba, ta tabbata da yana lpy zai nemeta, maiyasa zaimata haka?" maiyasa sai lokacin da take matuk'ar sonsa zai tafii ya barta."
Dakyar ta tsagaita kukan ganin magrib tana neman wucewa, ta tashi jirii ne yafara ebarta, dasauri tazauna."
Sallarma sai azaune tayita."
Bayan *hanna* ta idarda sallan tana kan pray mat, tana kuka tana yiwa mijinta addu'a, dan tasan a halin yanzu abunda yafii buk'ata kenan."
wayarta dake can gefe ne ta k'arayin ring dan dama tadad'e tanajii tak'asa picking."
Cikin kasala tatashi amma yanzu jirin ba sosai ba tanufii phone d'in, dushi dushi take ganin wayar, picking tayi sannan takara a kunnenta, afeeya ne tasauk'e ajiyan zuciya Jin anyii picking."
Tana d'agawa bata jira amsa sallama ko gaiasiwa ba tace *hanna* ina gate, sunk'i su barnii nashiga."
To kawai *hanna* tace ta ajiye wayan." dakyar tafuta ad'akin zuwa falo nanma sanda tazauna tahuta tukunna, ta isa zuwa bakin k'ofa, d'aya daga cikin soldier's din dake tsaronta taaika dan bazata iya futaba."
Tana fad'a masa aikar tazube awajen ta kwanta tana numfashii sama-sama."
Shikuwa yana zuwa baisamu matsala wajen shigoda itaba."
Sanda yabud'e mata k'ofa yana riqe da trollyn d'inta sannan tashiga."
Adab k'ofa taga *hanna* kwance cikin saurii taqarasa ta riqota tana cewa, *hanna* *hanna* tanajii ana kiranta tayi k'okarin bud'e idanuwanta amma tana bud'e wa saiya koma luuu yarufe, dan wani irin jiri takeji wanda ko idanuwanta bazata iya bud'ewa ba."
Riqe ta afeeya tayi, Jin tana numfashi sama-sama yasata fita ariikice tayiwa soldier's magana nan danan akayi asibiti da ita." Asibitin dake cikin estate d'in suka wuce da ita, ana zuwa doctor yafara dubata, bai dad'e ba akayi admitiing d'insu."
Afeeya duk atunaninta ciki *hanna* kedashi, Allah Allah takeyi likita yazo ya tabbatar mata takira ummii tafad'a mata, dan tasan hakan zai kwantar da hankalin ta."
Bayan doctor yashigo, afeeya tace doctor meyake damunta?"
Nisawa yayi sannan yace batacin abincii ulcer takamata har tayi chronic sannan tanqsaka damuwa sosai hakan har yana shirin sanya mata hawan jini."
Afeeya bata iya cewa komai ba gabaki d'aya tqusayin *hanna* ne yakamata tasan damuwarta bazai wuce akan mijinta ba."
Doctor ganin hankalinta baya jikinta yanakan *hanna* yasa yayi gyran murya."
Tana juyowa yace karki damu nan da safiya za'ayi discharging naku."
Daxaran drip d'in sun k'are zata farka."
Idan tatashi asamamata wani abunda zataci."
Y'ar karamar drawer yanuna mata yace," Duk wani abunda zaku buk'ata yana cikin nan."
Sannan yace bayan tacii abincii Idan tatashi tashige office na nurse akwai injections da madicines da zatayi taking."
Godiya afeeya tamasa yafita sannan kuma ta k'urawa *hanna* ido tana Mamakin irin ramar da tayi."
K'arfe 10:00 drip na *hanna* yak'are."
Sai, 10:25pm kafin ta farfad'o, waige waige tafara yi dan sanin inane yanda take."
Ganin afeeya tayi dake kan sallaya tana sallah batasan farkawarta ba."
Shiru *hanna* tayi tak'ura mata idanuwa har ta idar tajuyo da niyyar duba *hanna* ganin idanuwanta abud'e yasa afeeya tataso dasaurii ta isa wajen ta, sannu tafara yi mata itakuma banda Murmushi bbu abunda takeyi."
Tea tahad'a mata tabata dakyar tasha."
Sannan tad'anji k'arfii." Juyawa tayi ta kalli afeeya tace Anty afeeya zanyi sallah." d'agata tayi ta taimaka mata zuwa toilet tayi alwala." Sannan kuma tafito azaune tayi sallah." Tana sallah afeeya tafita taje takira nurse, dakyar akayiwa *hanna* allura sanda tahad'a da kuka." har sanda tasaka Anty afeeya dariya. " wajen shan maganii kuma ba'asha wahala sosai ba." riqeta afeeya tayi ta kwanta ajikinta tacii gaba da kuka." dakyar tasamu ta sakata tayi bacci."
K'arfe 7:00am akayi discharging nasu."


_Kuyi hakuri da wannan wallhy Yau sai ahankali."_


To be continued


Ur's
Z33iiyyb3rw3r


*BIBIYATA AKEYI*


_Bismillahirrahmanirrahim_


Writing by
© _Zaynab Bawa_
( _z33iiyyb3rw3r_ )


_Like my page on Facebook :::Zaynab BAWA novels_


Followed me on instagram ::::mhiz_z33iiyyb3rw3r





*Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace, kalmomi masu k'arfii akan harshe."* ```thaqilatan fil mizan``` *way'anda suka kasance masu nauyi akan mizani." kuma habibtan fir rahman." way'anda suka kasance mafii soyuwa awajan, Allah subhanahu wata alah." sune SUBHANNALLAHI WABI HAMDIHI, SUBHANALLAHIL AZIM."*


*wani mutumi yasamu Manzon Allah SAW ya tambayashi." yace* ```ya rasulillah man haqqan masu bihusnii sahabatihi````
*Waye ya wajaba akan mutane sufii kyautatawa."*
*Sai Manzon Allah yace mahaifiyarka, Sai wannan mutumii yak'ara cewa Sai kuma wa?" Sai Manzon Allah yak'ara cewa mahaifiyarka, Sai wannan mutumii yak'ara cewa thumma man, fa qala rasulillah thumma ummuk." sannan Sai Manzon Allah yace thumma abuk." yanada kyau ka kayautatawa mahaifiiya dan sanda Allah ya ambaceta sau uku kafin ya ambacii mahaifii." Allah kabamu ikon kyautatawa mahaifanmu."*


================


Page 73


*
Gida suka nufa, suna shiga afeeya tataimakawa *hanna* ta shiga wanka itakuma tafita dan shirya musu breakfast."
*Hanna* bata d'auki lokacii wajen wankan ba tafito dan ba k'arfiin jikinta takejii sosai ba." abakin bed ta zauna ta had'a kai da gwuiwa hawaye na zubo mata, tunaninta d'aya awani hali MG yake ciki." sallama afeeya rayi aqofar d'akin jin ba'a amsaba yasata shiga dan atunaninta bata futo awanka ba." ganin *hanna* tayi tahad'e kai da gwuiwa alamun kuka takeyi, dasaurii tak'arasa wajenta, ta ta6a kafad'unta *hanna* tayi saurin d'agowa cikin muryar damuwa afeeya tace *hanna* wai meke damunki ne? Kinsan kuwa mai doctor yace? Plz kidena saka tunani acikin ranki, jin haka yasa *hanna* fashewa da kuka tace anty ya zanyii wallhy wayarsa bata shiga tunda yatafii ko sau d'aya bamuyi waya ba kuma haryanzu bbu wanda yasan halinda suke ciki, k'ara wani kukan take tana anty nashiga uku wallhy idan wani abu yasameshi bazan iya rayuwa bbu shiba, anty kitaimakenii yadawo." wallhy inasaonsa anty duk abunda nafad'a k'aryane ban ta6a k'in saba, tasaka hannu akayi tana cewa nashiga ukuna." idon afeeya tabb yacika da kwalla tausayin *hanna* dakuma tausayin kansu narashin sanin halinda d'an uwansu yake ciki yakamata, tabbas tasan aranda akace sun rasa MG tashin hankali yashigesu har iya k'arshen rayuwarsu, mutumne wanda yafii kowa soyuwa aran dangii." bawai dan kud'insa ko mulkinsa ba a'a saidan kawai Allah yayishi dashiga ran alummah." zama tayi abakin gadon ta rungume *hanna* tana tana bubbuga bayanta dan duk wani abunda zaifito abakinta yanzu kuka ne shiyasata yin shiru kawai." hwaye tabb a'iidonta."
D'iga hawayen idonta yafarayi abayaan *hanna* aikuwa *hanna* ta k'ank'ameta tsam taqara sake wani kukan." shafa bayanta kawai afeeya takeyi dan bbu wata kalma dazatayi amfani da ita wajen nusarda ita, tasan dolene hanna ta damu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login