Showing 24001 words to 27000 words out of 60716 words
Chapter 9 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt
ɗauki raina"Ta faɗa a zuciyarta.
"Ni Ansai wai ni aka yi wa ɗaukan baibai(Baby) Da girmana a mini ɗaukan jarirai... Jin an ɗora ta a kan wata shimfiɗa daga nan akalar tunanin nata ya sauya sai yanzu ta gane ashe ba neman kuɗi ya zo ba.
"Allah ƙadiran wa maridan yo ai ta kwana gidan sauƙi ashe ma ka ce ma'adanar ɗan tofi (HQ) kake nema ai bana hana ka ba da tun a can ma ka mini raɗa a kunne da ba sai ka ba kan ka wahalar kinkimoni ba, da ƙafafuna zan biyo ka ka san dama an daɗe ba a haɗu ba tun da mijina Malam da ya fara tsufa aka bar wannan harka ta gabatar da sunna" Iya ta faɗa masa cikin raɗa-raɗa a zuciyarta kuma sai ta ce
"Ba kai ɗan duniya hayaƙin taba ba, ai ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali wanka, ban da tijara ta ƴaƴan zamani na yi jika da kai ka zo neman lalata da ni bari na yi ta maka bariki sai in ga ƙaryarka na san dai ai ƙarshen alewa ƙasa"
. Cak ya dakata daga jan zanin Iyan da yake mamaki fal ransa ganin ma ita take neman ɗage zanin da kan ta, saurin saka hannu ya yi ya dafe zanin nata baki sake yake binta da kallo ta cikin hasken farin watan da ya ratsa ɗakin, wani farrrr ya ga ta yi da idanunta har sai da baƙin idanun ya ɗauke sai farin tsabar farfarin da take yi.
"Wannan tsohuwar da ganinta ƴar duniya ce tun tana budurwa ta yi dumiyanci, wataƙila ma tana ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki, in ba tsohuwar ƴar duniya ba wacce ta taɓa duniyanci a baya a ce tsofe-tsofe da ita amma ko a jikinta wato bata ma tsoron komai wallahi ko da kuɗi ba zan tara da ke ba dama asirin yin arziƙi aka mini malamin ya ce idan na tara da tsohuwa burina zai cika amma tun da haka kike ba zan kwasawa kaina jangwam ba in zo in samu dukiyar ta ƙi ciyuwa da daɗin rai yo ina ɗauke da ƙanjamau kabari salama alaikum ai tunanin mutuwa ma ba zai bari na ci kuɗin cikin kwanciyar hankali ba" Ya faɗa a zuciyarsa yana ja mata zanin ya rufe mata a fili ya ce.
"Tashi ki koma makwancinki"
"Haba baibai(Baby) Wannan kalmar Iya tana jin ta ne a bakin samari a garinsu da suke cewa ƴan matansu baby shi ne ta kama ta riƙe. Ai ma yi abin da ya sa ka kawo ni ko da zan tafi...
"Ki tashi ki bar ɗakin nan" Ya faɗa cikin tsawa dan shi zuwa yanzu ma tsoron Iyar ya shige shi, shi da aka ce ya tara da tsohuwa ma tunnin diramar da za a yi da ita yake ya ɗauka sai ta ƙarfi sai ga shi ma ko a jikinta.
"Ai kaɗan ma ka gani wallahi ba kai ɗan duniya ba" Ta faɗa a zuciyarta ganin ya tsorata da lamarin.
"Ba zan Iya tafiya ba baibai(Baby) Ka ɗauke ni dai ka kai ni irin ɗaukan da ka mini na indiyawa" Takaici ne ya sa ya kama gefen rigar Iyar ya fara ja ƙiiiii sai ga ta a tsaye yana janta kamar wata akuyar da aka sakawa igiya ita kuwa ta kama saitin cikinta ta damƙe da hannu biyu dan dama ita ta yi tunanin Ko sauraronta bai yi ba ya buɗe ƙofar ya turo ta waje ya mayar ya rufe yana jin wani tashin hankali da faɗuwar gaba.
"Shegen sama wai kura ta hangi biri, wato wa ya faɗa maka barno gabas take ai dama ta yaro kyau take ba ta ƙarko" Cewar Iya a zuciyarta lokacin da ta baro ɗakin tana zuwa ɗakin ta nemi wuri ta zauna dan ɗosanawa ma kawai ta yi dan wurin ma bai ishe ta kwanciya ba, a haka akankira assalatu tana zaune jingine da bango tana gyangyaɗi.
*DA YAMMA*
Suka yi wa mai gayya mai aiki sallama a kan cewa za su je Iya ta samo gidan aikin wanke-wanke da shara, haka suka ɗauki kayansu fakaice suka bar gidan dan Iya ta ce su da zaman gidan ƴan daudu haihata -haihata duk da basu san ina za su je ba.
"Wai Iya sai yaushe za ki siya mini adaidaitan ne? Kin kama kuɗi kin ƙunshe sai yawo kike da shi a cikin riga sai wani ya bibbige ki ya ƙwace...
"A bakin ka Jaburu wallahi bakinka ya sari kashi ehe wannan kuɗi babu wanda ya isa ya karɓa, kuma da kake batun arincaɓa ai za a siya daga ni har kai babu wanda ya san inda ake siyarwa kuma wannan gidan da muka kwana kana gani dai babu wani na kirki kai gaba ɗaya duniya ma yanzu na kirki wuya suke kar aje mu damƙa maƙudan kuɗin nan da suke tattalin arziƙina da na iyayenka a gudu a barmu da gwale idanu" Ta faɗa idanunta kafe a kan wani mata shi da yake tsaye a layin, shi kaɗai da yake layin tamkar an yi shara. Sanye yake da riga da wando pencil sai gashin kansa da ya tara an masa aski mai layin kitso.
"Jaburu ina ganin wancan saurayin mu tambaye shi inda ake siyar da arincaɓar ka san an ce matambayi ba ya ɓata"
Shi dai Jabiru da to ya amsa.
"Ɗan nan dan Allah tambaya muke"
"Tsoho da ya yanka rago ba ɗan nan ya saka mini ba Haƙilu ya saka mini ana kirana ƊAN HARƘALLA" Shiru Iya ta yi jin ya ce wai Ɗan harƙalla. "Anya akwai abin arziƙi a nan kuwa ɗan harzaƙalla sai ka ce wani mai ƙwacen wayoyi" Ta faɗa a ranta tare da sakin murmushin ƙarfin hali ta ce
"Allah sarki Haƙilu rashin sani ne da ya fi dare duhu"
"Tambayi abin da kike son sani" Ya faɗa yana wani ɗaga kai sama yana fito, alamar gagara.
"Dama gidan haya muke tambaya inda za mu samu da kuma inda ake siyar da arincaɓa... Tun kan ta kai ƙarshen maganar sai kawai ta ga ɗan harƙalla ya sauke kansa daga kallon saman da yake kuma ya dakata da fiton, a take ya saka hannu a aljihu ya fito da wani carbi ya fara ja cikin girmamawa ya ce
"Baba ina wuni ya wajen manyan fatan kowa lafiya, amma Baba gonaki kika siyar ne?" Ya faɗa yana ƙarewa Iya kallo tamkar dai yana son gano inda kuɗin yake a jikinta.
"Wayyo tsuntsu daga sama gashashshe, lallai yau na yi baban kamu a ɓagas" Ya faɗa a zuciyarsa yana jii tamkar ya taka rawa.
Mamaki ne ya cika Iya jin ya ce ta siyar da gonaki a take ta fara tunanin ko dai aljani ne in ba haka ba ya aka yi ya san gona ta siyar.
"Ya aka yi ka san gona na siyar?"
"Allah sarki Iya kinsan yawanci iyayenmu na karkara gona ita ce kadara, amma mene ne ɗayan abin da kika ce arincaɓa"
"Allah sarki haka ne, ina nufin kunkurun da ake hayarsa wanda za kake ganinsa ko ina a cikin garin nan naku kamar an yi asakon barbela"
"Adaidaira sahu" Jabiru ya faɗa yana washe baki dan yadda ya ji ana batun siyan adaidaitar sai ya ji wani daɗi ya mamaye masa zuciya.
"Allahu akbar kabiran, ai gidan kuka zo, ai ni nan dillalin siyar da gida ne m ba wai haya ba, kuma a kuɗi ƙalilan, sannan adaidaita sahu ma ina siyar da shi" Ya faɗa a fili yana washe bakin jin kuɗaɗen da suke neman shigowa hannunsa, a take wani tunani ya faɗo masa ɗazu yana tahowa a ƙasan wata bishiya ya wuce wani mai napep shi da wani yana cewa mai napep ɗin
" Kai ai da kai da kasa duk ɗaya ne, mutum a ce bashi da aiki sai bacci kai da ka fito nema amma ka nemi bishiya ta kafa bacci sai magriba ta ƙarato ka kwashi jiki ka koma gida bayan ka san matarka dan ku rufawa juna asiri ta saya adaidatan, amma saboda nauyin baccinka sai a haɗa da kai da adaidaita sahun a ɗauke baka sani ba kana bacci" Wannan maganar ce take yi wa Ɗan harƙalla amsa kuwwa a kunne a take ya gano abin da zai yi.
"Mu fa ba siyan gida za mu yi ba haya muke nema"
"Ai da haya da siyan duk kusan kuɗinsu ɗaya, akwai wani wanda nake da shi har hawan bene akwai a kuɗi mai sauƙi zan siyar muku da shi" Ya faɗa yana tuno gidan Babban Yayansu Aminu wanda soja ne babba ma kuwa a Legos yake aiki shi ne ya gina gidansa mai mugun kyau an kusa bikinsa to gidan babu kowa a ciki shi ne Ɗan harƙalla ya hango yadda zai siyarwa su Iya gidan ya amshe kuɗin ya arce in ya so komai ta fanjama fanjam.
"Gidan bene fa ɗan nan? Yanzu har muna da kuɗin da za a siyar mana da gidan bene? Ko dai haya kke nufi, amma a siyar mana adaidaita a siyar mana gidan bene duka kuɗin fa bai ƙarasa miliyan huɗu ba dan mun taɓa kuɗin" Cewar Iya cike da mamaki hannunta a kan cikinta tana tattaɓa kuɗaɗan dan gani take ashe ita muguwar mai dukiya ce tun da tana da kuɗin siyan gida da napep.
"Kai jama'a faɗuwa ta zo daidai da zama, mu wallahi gaba ta kai mu gobarar titi, ashe dai gwara da muka mayar da faɗan da ya fi ƙarfinmu wasa wato muka bar gidan ƴan daudun nan ashe dai rabo ne auren budurwa da ciki, ga shi yanzu zan mallaki gida mai hawan bene a birni,
wannan ai dole ma idan muka samu dama mu tafi mu taho da su Umaru mu ƙauro garin nan " Ta faɗa a zuciyarta tana jin tamkar ta taka rawa.
"Taɓ miliyan huɗu lallai lallai gaba ta kai ni gobarar Jos" Ya faɗa a zuciyarsa yana raya cewa garin zai bari ko dai ya yi nisan kiwon da sai an kai ruwa rana kafin ma a ji labarin inda yake dama wata rana sai ya yi wata guda ma ba ya zuwa gida saboda ya gagari kowa.
"Ai a miliyan huɗun har canji zan baku saboda cefane kin san mu a islamiya an koya mana yadda ake taimako"
"Allahu akbar ɗan nan Allah baka lada"
"Yanzu ku jirani a nan yanzu zan dawo, amma kar fa ku tafi yanzu zan dawo" Ya faɗa yana tuno yadda zai yi ya sato mukullin gidan Yayan nasa a ɗakin Hajiya.
"A haba mu kam ai ba gudu ba ja da baya, ko nan da can ba za mu matsa ba, muna nan ai mun ga wurin zama yo Allah na tuba gidan bene wasa ne, yo ko cewa ka yi mu shekara guda a tsaye a wajen nan ai mu babu tafiya sai dai mu zubawa sarautar Allah ido mu ga har ka dawo" Iya ta faɗa tana kallonsa.
"To babu komai, ai akwai mukullin wani gida wanda nake ganin ya fi daceqa da ku to na bauar ajiya ne shi ne zan karɓo"
"A dawo lafiya" Iya da Jabiru suka haɗa baki wajen faɗa da sauri ya juya ya bar waje da sauri.
Ya sha wuya kafin ya samu sato mukullin gidan Yayan nasu, da take babu wani nisa duka unguwa ɗaya ne da gidan nasu sai dai akwai nisa tsakanin da gidan Yayan nasu, yana ɗakkowa ya wuce layin da ya biyo ɗazu cikin sa'a kuwa babu kowa a layin sannan adaidaitan yana nan kamar yadda ya gani ɗazu sai dai yanzu abokin mai napep ɗin ba ya nan. Tin kan ya ƙaraso wajen napep ɗin yake jiyo ƙaran munsharin mutumin wani murmushi ya saki, sai da ya ƙare masa kallo abin mamaki kan nan ya karkace har da su yawun bacci saboda nauyin bacci sai da ya tabbatar babu mai kallonsa sannan ya ɗakko wani filo ƙarami irin na kujera a can boot ɗin napep ɗin ya ajiye a ƙasan bishiyar, cikin sauri ya saka ƙarfinsa ya kinkimo mai napep ɗin da ya langaɓar kai kamar matacce dakyar ya kai shi ya kwantar tare da ɗora masa kai a kan filon haba wa mutumin ka mai napep ya gyara kwanciya tare da cigaba da sakin munshari.
"Taɓ wannan ai kai ne sauna kira mana shashasha in ka ga sakarai ku taho tare, in ban da sakarci jiran jirgi a tashar mota ta yaya za kake bacci kamar an zare maka rai" Ya faɗa a ransa tare da kunna napep ɗin ya zuba aguje. Amma mai napep ɗin ko motsi bai yi ba.
Su Iya suna nan zaune sai ganin Ɗan harƙalla suka yi ya zo a adaidata sahu gaba ɗaya daga Iya har Jabiru tsaye suka miƙe daga tsugunnun zaman jiran gawon shanun da suke baki sake suna al'ajabi.
"Kai, kai, kai kai, kyankyatsi wannan ne arincaɓar Jaburun?" Iya ta faɗa cike da mamaki.
"Cancaɗi lallai kuwa zan sha zabga gudu aradu" Cewar Jabiru baki kamar gonar auduga.
"Yo ba dole ba ka yi gudu Jaburu ai sai mun lale kuɗinmu sab...
"Ku shigo mu tafi saboda ana jirana a kasuwar adaidaita sahuna mutane sama da hamsin za su siya wannan ma dakyar na karɓo muku shi dan ana ta rububun shi saboda kyan tayoyinsa" Ya faɗa tana ta waige waige irin na marar gaskiya amma da yake su Iya a ruɗe suke da ganin napep ɗin babu wanda ya lura a cikin su.
Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay
TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃
Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada.
Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi.
Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa.
Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰
Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari.
Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851
[12/14, 13:01] Mom mashkur & Afrah: https://youtu.be/nRgkQ4KXcGM?si=YXzOdqPbrjwtLizS
ƳAN ADAIDAITA SAHU
(Masu keken napep)
NA
MAMAN AFRAH
GARAƁASA💃💃💃
akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.
ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳
kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu.
a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳
Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA.
09013181851
Page 7️⃣
Iya sai washe baki take shi kuma Jabiru yana tattaɓa jikin napep ɗin yana ji cewa wannan nasa ne. Shi kuma Ɗan harƙalla gaba ɗaya ma ba ya cikin nutsuwa saboda kayan satar da ya ɗakko dan haka ma zagaye ya yi ko ta layin gidan nasu bai bi ba ga shi yana ta zulumin cewa shi bai ma ga kuɗin da tsohuwar take ta faman cewa tana da shi ba kar ya je ya jefa kansa a rijiyar kasada, sai dai ya kissima a ransa cewa matsawar suka je gidan ya samu babu miliyoyin kuɗin nan a wajen su sai sun gwammace kiɗa da karatu domin kuwa sai ya sa sun banbance tsakanin aya da tsakuwa.
Da hanzari ya fito daga napep ɗin, ya tsaya waige-waige dan ya tabbatar babu mai ganinsa duk da unguwar babu mutane kamar sabuwar unguwa ce tun da sai an shiga ciki sosai daga gidan su ɗan harƙallar unguwa ce da kowa yana gidansa a rufe. Su Iya da suka fito suna ta kewaya napep ɗin suna tattaɓawa basu lura da cewar Ɗan harƙalla ba a nutse yake ba domin kuwa shi marar gaskiya ko a cikin ruwa sai ya yi gumi. Su Iya hankalinsu bai kai ga cewa a ƙofar gidan da za a siyar musu suke ba sai da suka ga Ɗan harƙalla yana ƙoƙarin buɗewa baki sake suke kallonsa ganin yana buɗe wani haɗaɗɗan gida mai ƙaton get.
"Kai yaro kana cikin hankalinka kuwa ko dai ka yi makuwa ne? Ka lura da gidan da kake buɗewa kuwa?" Iya da ta