Showing 42001 words to 45000 words out of 60716 words

Chapter 15 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt

27 Dec 2024

3516

kuma tamu ta ƙare wallahi in suka kama mu kashin mu ya bushe sai dai rayuwar gidan kaso(Gidan yari) Daga can kuma a bindige mu har ƙiyama" Cewar Iya tana sakin kuka irin nasu na tsofaffi gaba ɗaya ido ya raina fata tsoro ya bayyana ƙarara daga ita har dodon ƴan arincaɓar.


"Aradu yau mun ɗakko ruwan dafa kanmu, ni kuwa suna kama mu zan ce kece kika saka ni in kaɗe shi da na kaɗe shi kika ga adaidaitan ya warce shi sai kika ce in hau gidan sama kike mini kirari" Ya faɗa lokacin shi ma hawaye sun cika idanun sai yana runtsa idanun yake ganin gabansa.




*ƳAN KAROTA*


Tun da suka fahimci abin da yake faruwa a take aka sanar da shugabansu sai ya basu umarnin a bi bayan adaidaitan dan su a nasu tunanin ma mahaukaci ne dan in ba mahaukaci ba waye zai kaɗe mutum kuma ya tafi da mutum ɗin a saman abin hawa ko tsayawa babu kuma ma sun lura tuƙin ganganci yake kamar a bai iya tuƙa adaidaitar ba. Lokacin da suke bin su akwai tazara tsakanin su, dan haka ma ko da suka zo inda suka ga abokin aikin nasu ya faɗi a take suka tsaya suka ɗauke shi a sume tamkar matacce, shi ne kuma suka bi bayansu dan suna ganin idan suka tarki tafiya kai shi asibiti adaidaitan zai ɓace musu.


*IYA DA JABIRU*


Kuka suke wiwi a tare tamkar wanda aka musu mutuwa babu mai lallashin wani, layin da suka bi kwalta ce dan haka sun zo daidai wata bishiyar dalbejiya(Maina) Mai ya ƙare adaidaita ya tsaya cak! Kallon Jabiru Iya ta yi ta ce


"To Jaburu mu yafi juna ko ta Allah za ta kasance" Ta faɗa tana masa kallon ƙarshe dan ta fara tunanin wataƙila su harbe su nan take. Da farko bai ce mata komai ba sai kuma ya ce


"Ni dai fita zan yi in gudu a ƙafa... Tun kan ya kai ƙarshen maganar ta kalle shi wannan karon kuka mai sauti take yi hawaye nan kamar an kunna lalataccen famfo ta ce


"Haba Jaburu arincaɓar fa(Adaidaita sahun)?"Wani kallo ya mata irin na ana ta kai wa yake ta kaya ya ce


"Sai ki ɗauka ki ɗora a kan ki ki tafi da shi, in sun zo sai su haɗa da ke da adaidaita sahun su harbe" Ya faɗa yana saka ƙafa zai fice ta riƙo rigarsa ta ce


"Yanzu Jaburu... Tun kan ta faɗa ya katse ta da cewa


"Iya ki fito mu yi ta kan mu mutanen birnin nan babu tausayi ko imani a lamarinsu"


"Amma Jabiru mu ɓoye arincaɓar mana kar mu tsira su tafi da ita" Fitowa ya yi da sauri ganin duk babu mutane ya ce ta fito suka shiga tura adaidaitar suka ganganra da ita daga kan kwalta wata kwana suka shiga da ita cikin sa a suka samu wani ƙaton bahu irin wanda ake ɗinka buhun simintin nan danyawa suka rufawa adaidaitar sai suka fito daga layin a guje suka nufi ɗaya layin na hannun damar su, ƙaran motar da suka jiyo ya basu tabbacin ƴan karotar ne, hanya biyu ce a layin dan haka cikin rikita Iya ta yi hagu Jabiru ya yi dama.




*IYA*

Miƙewa ta yi zimbet tana gudu amma dan kar a gane ta ita kaɗai a zargi wani abu ganin layin da jama'a maza da mata kowa yana sabgar gabansa sai ta ce.


"Jama'a kowa ya yi ta kansa ƴan garkuwa da mutane ne a wancan layin suna tafiya d wanda tsautsayi ya rufta... Mutane jin haka sai kowa ya bazama dan dama ko sati ba a yi ba da ɗauke ƴar me unguwar har gida suka zo suka tafi da ita kuma har yau basu maido da ita ba. Gaba ɗaya sai layin ya hargitse aka shiga rafka gudun famfalaƙin ceton rai. Wani mai shago a guje ya fito daga shagonsa shagon da yake wa mutane tijara ga babu alfarmar bashi ko na naira biyar yana ta ƙafafa da shagon amma tau sai ga shi ko shagon bai rufe ba ya bazamo a guje, mai awarar da take soyawa a gaban shagon ta sauke ta juye man amma kaskon bai gama hucewa ba jin abin da Iya ta faɗa sai ta kinkimi mazubin kuɗinta man kuwa bata san ta tuntsurar da shi ba ta bi ta kan kwanon ta wuce a guje ko waiwaye babu. Mai shago na zuwa shi bai san ma ya aka yi ya sunkuya ya suri kaskin suyar awarar ba shi dai kawai ya ga ya kifa kaskon a suɗaɗaɗan kansa da ya sha askin ƙwal kwabo, duk da zafin da ya ziyarce shi amma a haka yake gudu ɗauke da kasko a kife a kansa.




Wani mai baro da ya zo ɗaukan buhhunan gawayi da suke ajiye a jikin bishiyar maina (Dalbejiya) Sai wata tsohuwa makauniya tana gefe a zaune da kwanon silba a gabanta tana bara kwanon da ƴan canjinta a ciki, jin abin da Iya ta ce sai mai ɗaukan gawayin ya rikice dan ya san idan ƴan garkuwar suka ɗauke shi sun ɗauki banza dan daga shi har iyayensa basu da kulin da za a iyo famsarsa, hannu da ya miƙa a maimakon ya sauke a kan buhun gawayi sai ya sauke a kan makauniyar wannan ta zaune a kusa da bahhunan, wacce ta rikice da jin abin da aka ce ta suri kwanon bararta ya maƙala a hamata tana lalumen sandarta sai ji ta yi an sure ta an yi sama da ita har za ta yi ihun firgita da tsurewa sai ta ji an ajiye ta a cikin baro an shiga tura baron da ƙarfi. Ɗif ta yi da bakinta.


"Allah na gode maka, da ka bani wanda zai tuƙani dan dama ni da nake makauniyar nan kafin in kai gida ma an ɗauke ni" Ta faɗa a zuciyarta tana jin daɗi tare da ƙanƙame kwanon bararta dan ta san dai cikin rashin sani Isa mai dako ya ɗora ta a baro ya tura a tunaninsa buhun gawayi ne bai damu da nauyin da ya ji ba ya wuce misali burinsa kawai ya je inda zai samu mafaka ba tare da ya yi arangama da masu garkuwa da mutane ba.




Mai siyar da manja manjansa a cikin bokitin fanti babba a kan, yana rumfarsa sai kwalabe masu manjan wani yaro ya bashi ɗari biyu zai zuba masa a leda amma ji an ce masu garkuwa d mutane sun iyowa unguwar tsinke sai ya shiga cika kofin awon manjan yana sauyewa yaron a kansa, sai da ya zuba masa kofin wajen kofi goma sannan a rikice ya suri bokitin manjan maimakon ya ɗora ƙasan bokitin a kansa sai kawai ya kifa bokitin gaba ɗaya ya juye manjan a kansa da jikinsa a haka ya sheƙa gidansa a guje jiki jaɓa-jaɓa da manja. Yaron nan ma ganin an masa wanka da manja kuma mai manjan ya gudu sai ya juya ya tafi gida yana kuka.




Iya kuwa da ita ake gudun mata sai tseren shiga gidaje suke da yaran su, wani tsoho yana zaune a kan tabarma zabgegen carbinsa yana maƙale a hannunsa sai sandarsa a gefe guda, da kwanon silbar da aka kawo masa ruwa sai hularsa danya cire ya ajiye . Yana ta mismis da baki. Babu abin da tsohon nan ya tsana sama da ƴan boko haram da duk wani abu da ya danganci bindiga da yake ƴan asalin garin maiduguri ne can Borno state tun da aka tsiri saka bama -bamai Allah ya kuɓuto da su suka yi hijira suka dawo Kano, hankalinsa yana tashi in ya ji ana batun masu garkuwa da mutane musamman da ya san shi talaka ne fitik babu cin yau babu na gobe, ya san muddin aka tafi da shi sai dai a kashe shi domin ba za a samu mai fanso sa ba.


"Jama'ar musulmi, al'ummar annabi kowa ya yi ta kansa masu garkuwa da mutane sun wa wannan unguwa kutse suna wartar wanda tsautsayi ya rufta da shi" Tsohon yana zaune ya jiyo muryar Iya ta wawake baki tana faɗa, a kiɗime ya tashi ƙirjinsa yana bugawa da ƙarfi cike da tsoro ya wawuri silbar da ya shanye ruwa a tunaninsa hularsa ce haka ya kifa kwanon silbar a kansa ya miƙe yana ambaton Allah a ransa, carbin da ya ajiye ne ya yi wa ƙafarsa dabaibaiyi domin harɗe shi ya yi, da sauri ya tsugunna yana ambaton Lahaula wala ƙuwwata a zuciyarsa dan gaba ɗaya ta ɗafa hankalinsa ga shi ba gani yake ba, yana gama ware carbin daga ƙafarsa ya yi wurgi da shi gefe gabansa yana dukan tara-tara Iya ganin tsohon nan duk ya diririce dakyar ta danne dariyarta ta nufi wajensa tana faɗin


"Malam ka taimaka mini da wajen fakewa hanya ce ta kawo wannan abu yake neman rutsawa da ni ga shi gidana da nisa kar a je su kwashe ni in shiga uku" Duk jawabin da take ko saurarenta bai yi ba burinsa shi ma ya shige gidan dan ba ya ma gane mau take faɗa. Ƙofar shiga gidan ya yi wa kutse kansa kife da ƙatuwar silbar da ya kifa a matsayin hula, har ya kusa shigewa ya tuna da tabarmar da yake zaune wacce ta amaryarsa ce ga ta masifaffiya dakyar dama ta ba shi ya san kuwa ko da a ce bom ne ya tashi ba zuwan pan garkuwa da mutane ba to tabbas idan ya shiga gidan nan babu tabarmar sai ya dawo ya ɗauka dan ya san halinta ba kanwar lasa bace ga shi ba ta da uzuri a kan komai.


"Na rasa dalilin da ya saka ni auren Gajegala masifar matarnan da tada turnuƙinta ko lokacin muna gabas(Mai duguri) Bata saurara mini bare kuma yanzu na rasa ranar da za ta saduda" Ya faɗa a fili yana dawowa da ɗan gudu-gudu ya warci tabarmar bujukura wacce ko naɗewa bai yi ba saboda rashin nutsuwa ga shi yana jin tashin ƙaran takalman jama'a da suke gudu domin tsira daga tarkon ƴan bindiga masu garkuwa da mutane.


"Yanzu a kan tabarmar nan babu tausayi babu tsoron Allah, sai ta dawo da ni " Ya faɗa lokacin da ya yayumo tsohuwar tabarmar da ta fara zazzarewa saboda tsufa amma a hakan gani take tamkar sabon kafet ta bashi. Iya da take tsaye daga gefe haushinsa ya ƙular da ita na banza da ya baiwa ajiyarta a kan neman taimakon mafaka da ta yi a wajensa saboda ta tsira kar Ƴan karota su ganta duk da ta san ba lallai ne ma sun ganta ba lokacin da take cikin adaidaita sahun bare har su shaidata sai dai shi marar gaskiya ko a cikin ruwa gumi yake, kuma dai tana ganin binciken su zai iya sawa su gano ta dan haka ta fi gane ta shige gidan mutane ta ɓuya idan ƙurar da ta ɗakko su ta lafa sai ta fito ta san na yi duk da tana ta tunanin Jabirunta amma ta san shi ma zai yi ƙoƙarin tserewa tun da dai maƙasudin abin da zai saka a gano su sun masa maɓoya babbar maɓoya ma kuwa wato adaidaita sahun su.




Sai da ya kusa shigewa zaure gidan ta riga shi shigewa, yana zuwa zai wuce ta saka ƙafa ta danne tabarmar da ya yayumo ya ja ya ƙara ja amma ya ji an danne tabarmar ga shi da yake tsohuwa ce yana tsoron ya figeta ta yage a banza ya shiga uku ta ce sai ya biya ta tabarmar ga shi a wannan zamanin da ake ciki na Tinubu bashi da kuɗin tabarmar ba shi da dalilinsu dan haka sai ya fara ja a hankali tare da dawowa da baya ya ɗan sunkuya zai taɓa da hannunsa domin gano a inda matsalar da ta riƙe, sunkuyawar da ya yi Iya ta yi amfani da hannunta ƙwanƙwasa kwanon silbar kansa tamkar mai ƙwanƙwasa ƙofa, a kiɗime Malam ya tashi bai ma san lokacin da ya saki tabarmar ba dan shi a iya saninsa babu komai a kansa sai hula amma jin ƙaran silbar sai ya gigita shi dan a nasa tunanin masu garkuwa da mutanen ne suka ƙaraso za su tafi da shi. Har ya fara alamun bazama zai cikawa rigarsa iska tabarmar da ya saki ta faɗo masa da sauri cikin damuwa ya sake durƙusawa yana cewa


"Dan Allah ko za ku tafi da ni ku mini lamuni in kai wa Gajegala tabarmarta dan na san in kun tafi da ni babu mai biyan kuɗin fansa idan kun gaji da ajiyata kun kashe ni Gajegala ba za ta yafe mini tabarmar nan ba dan a al'amuranta babu imani" Ya faɗa lokacin da ya tsugunna ya saki wani marayan kuka marar sauti jin an sake dukan wani abu a kansa ƙwal wanda a nasa tunanin ma ko bakin bindiga ne.


"Ai babu lamuni tsakaninmu da kai tun da ka zo hannu har tabarmar ma za mu haɗa mu tafi... Cewar Iya cikin yin muryar gardi amma kuma ganin wulgawar motar Ƴan karota shi ne abin da ya dakatar da ita daga maganar da ta fara, shi kuma Malam tuni ya rikice jin abin da ta fara faɗa.


"Malam mutanen ɓoyena ne suke son su ɗaga mana hankali, ni ma neman mafaka na zo zauren gidan naka amma ga tabarmar ka shige gida kar tsautsayi ya rufta da mu, dan na ji gaba ɗaya unguwar ta rukice sai kayya-kayya ake" Ta faɗa cikin daidaita asalin muryartar tare da yayumar tsahuwar tabarmar ta miƙa masa hannu yana karkarwa ya karɓa ko halin godiya bai samu yi mata ba, ya shige.


"Ba dan na hangi wucewar motar da take farautar mu ba wallahi da sai ka gwammace kiɗa da karatu dan sai na baka wuju-wuju" Ta faɗa a ranta tana ɗan yin dogon kai ta hangi layin babu kowa sai motar da yake ta faman bilayi da alama ma basu fahimci abin da yake faruwa ba.




*JABIRU*


Tun da ya durfafi layin da ya bi babu abin da yake sai zabgar gudu dan hatta takalmansa ya watsar da su saboda haƙarsa ta cimma ruwa. Mutane ana ta masa kallon mahaukaci.


"Da sannu za mu dawo kamar mahaukatan daga ni har ku" Ya faɗa a ransa lokacin da ya zo gifta wasu ƴan mata guda uku da suke tsayawa a saitin wata haɗaɗɗiyar mota wani mai camera yana ɗaukansu hoto sun raja'a an sha mayafi sai juyi ake. Takalmin su Jabiru ta kalla lokacin da ya tsagaita gudu, ganin tsinin takalmin ya yi yawa kowacce ɗogo-ɗogo kamar za ta kere katanga a tsayi su a dole an sha wankan an yi gayu sai wani ɗaga waya ake da ganin su ka san ƴan ƙarya ne kawai.


"Kai wai lafiya za ka shigowa mutane unguwa kana gudu ko dai mahaukaci ne kai kowa ya yi ta kansa" Wani matashi da ya tara wata uwar suma suna zaune su huɗu a kan benci kowa yana danna waya kamar an musu wahayi da danna wayar ya faɗa yana aikawa Jabiru harara yana masa kallon ɗan ƙauye kidahumi, ganin sai da ya zo saitin su ya sunkuya yana haku tare da mayar da numfashi. Hannu Jabiru ya ɗaga yana nuna bayansa hanyar da ya biyo yana huci.


"Wai uban meye ne kake nuna wa ko angamo ka yi?" Ɗayan ya faɗa yana tashi tsaye yana wani gyara wandonsa tiri kwata.


"Yanzu ne na zo wucewa ta ɗaya kayin can wasu da suka mini kama da ƴan bindiga kasancewar suna kan machina kuma da bindigu rataye a jikin su fuskokin su a rufe na ji ɗaya yana waya yana cewa.


"Oga bom uku aka saka a mabanbantan wurare, saura ƙiris su tashi fa zarar sun tashi za su iya tada unguwar nan gaba ɗaya har ma da wanda suke maƙotaka da su yana gama faɗar hakan suka gudu a machina ni kuna na fito daga maɓoya... Tun kan ya kai ƙarshen maganar samarin nan huɗu sun zabga a guje har ɗaya yana tuntuɓe, guda biyu suka yi karo da duka gabzu da junansu wajen yin gudun famfalaƙi, ɗaya kuwa kambas ɗin da yake ƙafarsa ya cire ɗaya, ɗayan kuma ya ga dai ba zai iya tsayawa cirewa ba dan jar ya ɓata lokacin dan ya san ba ƙaramin gudu bane a gabansa kafin ya bar unguwar dan gudu da tsira da ransa kar bom ya tashi. Mai tiri kwatan nan ashe dai dama wandon nr babu belt shi ya sa yake gyarawa ai yana fara gudun wandon ya silliɓe har sai da Jabiru ya hango baƙaƙen mazaunansa amma shi bai damu da mazaunansa da suke tangararai a bainar titi ba ya fi damuwa da ya gudu kar ya mutu a tashin bom.


Da yake Jabirun ba a hankali ya yi maganar ba, ƴan matan nan ƴan ƙarya a kan kunnuwan su aka faɗa, mai ɗaukan hoto wurgi ya yi da camerar ɗaukan hoton ya cire takalama falfalfal sai ga shi ya zo ya gifta Jabiru ko neman ba a si da ƙarin bayani babu wanda ya yi kowa burinsa ya tsira da ransa da yake ƙasar ta zama sai addu'a koyaushe komai yana iya faruwa sai dai fatan Allah ya karemu da kariyarsa amin. Kallon sa Jabiru ya yi dan a yadda ya falfalo a guje ya fi kama da mahaukaci sabon kamu wanda ana kama wa sai dai a masa masauki a Dawanau. Ƴan matan nan kuwa su uku suna jin abin da Jabiru ya faɗa wa samarin nan sai su ma suka fara neman hanyar tsira dan dama su duka ƴaƴan gidan mutunci ne ƴaƴan malamai waɗanda ko mayafi iyayen su basa barinsu su yafa amma kuma sai su fito da hijabi daga gida idan sub fito sai su yafa mayafi ba tare da iyayen sun san wainar da suke toyawa ba, wacce take riƙe da ledar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login