Showing 51001 words to 54000 words out of 60716 words
Chapter 18 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt
mini tsaba(Hatsi, gero) Kaji su bini a kan mai ido zai ci wuta haka kawai kana maraya ka sa a ƙona ni a kan ban cika maka burinka ba, ka yi haƙuri bari ta dawo mu san yadda za a yi mu je gidan tana shigowa ka ɗauki hanyar gida d... Shigowarta napep ɗin ne ya dakatar da Iya daga maganar da take son ƙarasawa shi kuma da sauri ya goge hawayen murna fal cikinsa ya ja suka cigaba da tafiya. Hanyar unguwar su ya ɗauka ita dai ta ƙwame a baya bata ce komai ba.
"Baiwar Allah zan ɗakko saƙo a cikin gida tun da Allah ya sa mun biyo ta hanyar" Cewar Iya cikin sanyin murya.
"Ikon Allah wannan gidan ne gidan matar nan? Ko dai ɗanta ne ya mutu ya bar musu gado wannan haɗaɗɗan gida" Budurwar ta faɗa a zuciyarta
"Ba damuwa" Ta faɗa idanunta kafe a kan gidan. Iya kuwa fita ta yi ta fito da mukullin daga ɗan tofi ta buɗe get ɗin ta shige dama ta ƙiftawa Jabiru ido, jim kaɗan sai ga ta ta fito.
"Baiwar Allah dan Allah ki shigo ki taimaka mini in kamo kaya" Cewar Iya da ta zo har gaban napep ɗin. Shiru Budurwar ta yi tana mamakin mai ya sa bata ce shi ya je ya kamo mata kayan ba, ko dai basu yarda da ita bane, saurin kawar da zancen zucin ta yi ta ajiye jakarta ta fito tana ƙarewwa unguwar kallo, sai da suka shige cikin gidan Iya tana gaba budurwar tana bin ta a baya har cikin ɗaki kawai sai Iya ta shammace ta ta fita ta banke ƙofar ta saka mukulli da sauri budurwar ta fara buga ƙofar tana faɗin a buɗe amma Iya lokacin har ta kusa bakin get tun daga bakin get take ƙwallawa Jabiru kira, shi kuma ya fito da sauri yana washe baki ko mukullin napep ɗin bai cire ba ya shigo.
"Maza tana ɗaki ka san ni indai a kan abin da zan faranta maka rai ne Jaburu to babu abin da ba zan yi ba haka kawai yo tsuntsu daga sama gasasshe" Ta faɗa tana garƙamawa get ɗin mukulli ta bi bayan Jabirun dan ta je ta masa gadin ƙofar ɗakin.
09013181851
[12/23, 15:52] Mom mashkur & Afrah: ƳAN ADAIDAITA SAHU
(Masu keken napep)
NA
MAMAN AFRAH
Page 1️⃣4️⃣
"Na san Allah zai yafe mini, Allah mai yafiya ne ko shi ma Jaburun ai Allah sai ya gafarta masa, ni kaina na san ba abin kirki bane in taimaka masa ya ƙwamushe ƴar mutane, kuma ma va a son ka aikata saɓo batan ka san saɓi ne ka ce ka tuba daga baya to amma dai ya na iya bana son ɓacin ran Jaburu marayan Allah, in ban da ma dai saka rai a abu ina shi ina wannan sangamemiyar mata, a toh tun magriba ta gabato sai mu haɗa ta mu kore ta mu kulle gidan mu shiga gari ai ba lallai ta shaida gidan bama" Cewar Iya da take tsaye, ganin tsayuwar ba za ta yi ba sai ta juya ta kalli get ɗin ta jijjiga kai irin ko an jiyo ihu babu wanda zai shigo kawowa budurwar ɗauki ta juya domin zuwa can ta yi wa Jabiru gadin ƙofar.
"Jaburu mazan fama kenan na Iya mai gaza mai rikicin gangan" Ta faɗa tana murmudawa tare da samun kujera ta zauna tare da harɗe ƙafa ɗaya a kan ɗaya.
*JABIRU*
A can cikin ɗaki kuwa tun lokacin da Jabiru ya je ya buɗe ƙofar da kasancewar Iya a jiki ta bar mukullin, dan haka yana buɗewa ya shige ya kulle ya cire mukullin ya kefa saman drower ɗakin. Budurwar ya tunkara da take ta raɓewa a jikin bango domin yanzu ta gane ta kuma fahimci abin da ake so a aiwatar a kanta.
"Ka yi haƙuri dan Allah kar ka aiwatar da ƙudurinka a kaina"
"Babu zancen haƙuri ƴar yarinya kawai ki bada kai bori ya hau, bar ganin kina da jiki to ƙarfin namiji da mace ba ɗaya bane bare ni nan Jabiru"
"Dan Allah ka yi haƙuri" Ta faɗa hawaye suna sintiri a fuskarta.
"Ai da kin adana hawayenki da haƙurinki wataƙila anjima su miki amfani amma yanzu babu tasirin da za su yi, kin san wanda ya yi nisa ba ya jin kira" Ya faɗa yana tunkararta ganin ya cire riga ya wurgar sai suka fara ƴar tsere a ɗakin har ya yi nasarar kamota aka shiga kokawa, haka Jabiru ya jefa a gadon ya shiga cire mata riga tana ja yana ja sai dai bai lura da komai ba sai da ya farɗi rigar mamanta sai ga famfas (Pampers) Ta yara duƙunƙune guda biyu suna tseren faɗowa da mamaki sosai Jabiru ya bi famfas ɗin da kallo yana tashi zimbet daga kan gadon hankalinsa a tashe domin kuwa ya gane ba mace bace namiji ne ya yi shigar mata, dan ba komai ne ya ƙara ɗaga masa hankali ba sai yadda dantsen namijin yake a murɗe ashe rigar mata ce da ta rufe shi ya sa ba a lura ba sai yanzu ya gani muraran da idanunsa.
Gefe can ya rakuɓe jikinsa yana karkarwa idanunsa kafe a kan famfas ɗin nan guda biyu wanda suka zubo wanda yake yi wa kallon mama(Breast) Ashe dai ciko ne aka yi aka mayar da shi banzar bazara. Matashin nan kuwa dan ba a kira shi budurwa ba yanzu dan ya tashi daga wannan jinsin dama a rashin sani karen bebe ya ɓata. Tsaye ya tashi fuska a murtuke ya nufi gaban mudubi ya ɗauki toilet paper ya goge kwalliyar fuskarsa da jambakin gaba ɗaya, hannu ya sanya ya cire ɗaurin ɗankwalin da Jabiru bai cire ba dan shi Jabiru zip ɗon rigar ya cire shi ya sa abin bai kai ga cire ɗankwali ba. Yana cirewa sai ya ciro hular gashin da take ɗauke da kitso yaraf-yaraf sai ga gashin kansa mai cibiri-cibiri irin na matasan zamani, siket ɗin atamfar jikinsa ya zame sai ga tiri kwata na jeans a ciki wurgi ya yi da su tare da nufar inda Jabiru yake yana muzurai kana kallon fuskarsa ka san taƙadari ne babu wani alamar imani ko tausayi a tare da shi. Kallon fuskarsa kawai Jabiru yake tun bai san mai zai faru ba har gumi ya gama jiƙa shi ga wani fitsari da yake neman kufce masa dan ya san dai yau babu zama an ɗaurawa karya zani dan yau sai ta Allah, an kama kwarto a turakar mai gida. Sosai Jabiru yake jin tsoro musamman da ya san ƙofar ya kulle ta da mukulli dan ƙarfin hali ɓarawo da sallama ma sai ya jefa mukullin saman drower ga shi yanzu baya ta haihu.
"Wayyo Allah ni Jabiru faɗan da ya fi ƙarfunka maida shi wasa, ni kaza garin tone-tone na na tono wuƙar yankana" Ya faɗa a ransa yana ƙoƙarin haɗa laɓɓansa a fili ko Allah zai bashi ikon haɗa kalmomin da zai famshi kansa da su a wajen mutumin da ya ɗauka mace ce ashe dai ƙaron gardi ya kawo ɗaki ya garƙame.
"Wallahi ba halina bane ka mini rai in sha Allahu an yi na farko an yi na ƙarshe nan gaba mace ko ta kare ce (Karya macen kare) Na gani a hanya babu ni babu ita bare macen mutum" Ya faɗa hawaye suna zubowa ratata yana ƙare mannewa da jikin bango tamkar dai bangon ya tsage ya shige ciki.
"Ka dana kalamanka da sannu za su maka amfani amma ba yanzu b a dan wanda ya yi nisa ba ya jin kira" Matashin ya faɗa da wata kakkausar murya ta ƙaton namiji, muryar da ta ƙara razana Jabiru tare da saka shi a kogin da na sani tsumu-tsumu, a take ya ji duka jarabar da yake ji a kan budurwar da har ya kasa haƙuri ta yi gabas ya yi yamma.
"Na rantse da Allah na tuba, ni daga yau ma na zama mata maza bana sha'awar mata ma baki ɗaya ni ko aure ma ba zan yi ba bare na ƙara tarkar haikewa wata mace ka rufa mini kwandon asiri" Cewar Jabiru murya tana rawa domin ganin matashin nan ya dunƙule hannu ya nufo fuskarsa gadan-gadan. Tun kafin ƙwaƙwalwarsa ta gama tantance masa abin da za a masa ya ji saukar wani naushi mai ha'ula'i wanda a take ji da ganin Jabiru suka yi ƙaura daga gare shi na wasu daƙiƙai kafin ya saki wani ƙara mai gunna sai ga shi yaraf ya zube saman silin ɗin ɗakin yan juya masa tamkar yadda famka take juyawa.
Iya tana zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya ta jiyo ihun Jabiru wata dariya ce mai sauti ta kufce mata, da sauri ta saka hannu ta danne bakinta tana ɗan kallon ƙofar da za ta sada ta da tsakar gidan irin kamar kar wani ya ganta a zuciyarta ta ce
"Oh ni Ansai zan je garin wutar tawa in yi suɓutar baki, ah lallai Jaburu an samu abin da ake so ki jo yadda ya saki ihu tamkar wani zaki a tsakiyar daji" Ta faɗa tana ƙara tuntsurewa da dariya marar sauti, dan ita a nata tunanin Jabiru yana can yana haikewa ƴar mutane ne bata san cewa ido ya daɗe da juyewa da mujiya ba.
"Wannan ce ƙaddararki yarinya sai ki ɗau halin annabawa (Haƙuri) Dan aikin gama ya gama sai dai a bi wani sarkin ba wannan ba lallai Jaburu jarumi ne "
"Wayyo Allah!" Jabiru ya ƙara fasa ƙara jin an kifa masa wani naushin a gadon baya, dan ɗago shi saurayin ya yi tsaye daga kwanciyar reran ɗin da ya yi a tsakiyar ɗakin.
Iya kuwa jin ihun Jabiru a karo na biyu har da kiran wayyo Allah, sai ta ƙara cika da farin ciki a take ma sai ta tashi tsaye ta gyara ɗaurin zani ta shiga rausaya kai kamar ƙadangaruwa tana waƙar
"Fati fatima mai zogale" Tana yi tana juyi abin ta tamkar sallah. Tana ta rawa shi kuwa Jabiru ana haɗa masa jini da majina a ɗaki a nata tunanin ihun daɗi yake bata san baƙar azaba ake gana masa ba. Sai da ta yi rawar ta gaji dan kanta ta zauna har lokacin tana jin ihun Jabiru dan daga ƙarshe sai ma ta daina jin ihun sai kuka.
"Yi kukan ka Jaburu ai dama a rayuwa ana kukan wahala ko damuwa sannan ana kukan daɗi to kai dai yau kukan daɗi kake, ita yarinyar ba a ma jin kukan ta sai nashi ake jiyowa ko kunya ba ya ji ya zage yana ihu da kuka, wannan in muka koma ƙauye in za a masa aure ai sai dai a masa gidansa da ban dan ba za a kawo shi cikin gida irin na wanda ake kawo su gidan iyaye su zauna a musu kewayen su a nan amma shi wannan tun da haka yake ɓaran ɓarama yo wannan ai sai ya cika gida da iface-iface amma in aka ware masa gidansa sai ya je can in hamimiyar doki zai ke yi ma gidansa ne" Ta faɗa a ranta lokacin da rake jin kukan nasa ya fara yawa.
"Uhm in ji ami ciwon haƙori bari dai in tashi in ke kar yaron nan ya yi wa ƴar mutane ɓarna, yo ai abin ya wuce hankali kai da za ka yi abu saisa-saisa ka kashe ƙishirwarka amma sai ka nannage a ɗaki kamar wata matarka ta sunna" Ta faɗa lokacin da ta je jikin ƙofar ta kara kunnuwanta ko za ta ji kukan macen amma shiru wai malam ya ci shirwa.
"Kai wannan ɗiya ko dai ba budurwa bace? Ko kuma dama ƴar hannu ce , amma in ba haka ba ana haike miki ko ɗan kukan ƙwatar kan nan naki ba za ki yi ba kai zamani sai a bar shi" Ta faɗa a ranta tana taɓe baki.
"Jaburu, Jaburu, Jaburu haba kai da baka iya cin ƙwan makauniya ba yanzu fisabilillahi dan dai baka mutuwar tsakar ɗakinka sai ta wani ya za a yi ka daɗe kana abu ɗaya har na gaji da maka gadin ƙofa haka kawai ka cika gida da iface-iface da kuka da kururuwa, so kake sai an yi abin kunya wai uwa ta cinye sirika ranar aure, kai da na maka gwaninta za ka watsa mini ƙasa a ido ko dan abin kirki bai gaji kare ba in ya yi ma dukansa ake yi, ai yarinyar ma ta maida faɗan da ya fi ƙardinka wasa kake mayar da shi amma ai ka wuce gona da iri" Ta faɗa cikin ɗaga murya yadda zai ji dan ta ga abin na sa ba buɗe ƙofar zai yi ya fito a tun da babu niyya wai ango ya kwana da wando. Duk wannan maganar da takw inu take bayan hari domin kuwa lokacin Jabiru ya ci dukan da ko hannunsa ba ya iya ɗagawa saboda jigata bakin nan an fasa masa shi ya kumbura ya yi tsawo ya yi zototo.
"Au ƙyale ni ma ka yi to ai gobe ma rana ce ta jibi har tafi yawa, ai wauta take sanya biri ya ga ayaba kamar takobi, wato ga Ansai ƙaramar danga mai... Tun kan ta ƙarasa maganar sai ta ji alamar saka mukulli a jikin ƙofar da ta jingina ta kara kunnenta, matsawa ta yi daga jikin ƙofar domin ta basu wuri su fito.
"Hab ko kai fa a ce baka san annabi ya faku a tun daɗewa sai abu ɗaya kake ga shi mun bar arincaɓa a waje duk hankalina ba a kwance yake ba" Ta faɗa tana juyawa za ta koma tsakiyar falon. Bata san cewa ba Jabiru ne yake buɗe ƙofar ba matashin ne ya ɗakko mukullin tun da a gabansa ya ɗora a saman drower. Yana buɗe ƙofar ya koma ya kama ƙafar Jawo ƙafafun Jabiru.
"Ai gwara dai ka fito kar ka mayar musu da ƙafar ƴa kamar ta agwagwa, in kuma abin ya wuce aiki ya zama aika-aika ne sai mu nemo ruwan zafi ta gasa jikinta ta kama gabant... Juyowar da ta yi ta sauke idanunta a kan wani namiji mai wando tiri kwata ko riga babu sai gabanta ya bada wani rassss, kafin ta mayar da idanunta kan Jabiru da ake janyowa wanda yake kwance magashiyyan tamkar wanda ba ya lumfashi, kallon rashin fahimta take gaba ɗaya sai kanta ya juye ta ma kasa samun ƙwaƙƙwaran tunanin da za ta yi, saboda ita dai bata san ta inda aka samu ƙaton namiji wanda ya tuɓe yake musu yawo zagadam-zagadam a gida ba, abin tambayar ma shi ne ina yarinyar budurwa? Matashin da fuskarsa take a haɗe tamkar baƙin hadarin gabas. Yana jan Jabiru a ƙasa sai da ya kawo shi tsakiyar falon ya warɓar da shi tamkar wani tabarmar leda, Jabiru da babu abin da yake iya faɗa ko ya aikata sai kallo da idanu sai kuma zubar da hawayen azaba da idanunsa suke yi sai ya ji ya yi da na sanin fita hayar adaidaita sahun ma yau gaba ɗaya bare har ya haɗu da wata ya ɗakko ta.
"Jaburuuuu" Iya ta yi ƙarfin halin faɗa jikinta yana karkarwa ta kasa gane mafarki take ko idanunta biyu tana wasi-wasin cewar ko dai sun sake wani gamon ne.
"Ai kuwa in dai wani gamon muka yi a gobe ba sai jibi ba za mu bar wannan Kanon ina dalili sai baƙar azaba muke sha har yau ko cinikin ƙwandala bamu yi ba sai ɓarnar kuɗin siyan abinci " Ta faɗa a zuciyarta tana kallon ƙafafin matashin sai dai ganin farce kamar nata ba kofaton aljannu ba sai abin ya ƙara ɗaure mata kai. Jabiru sai ƙoƙarin magana yake yana son ambatar sunan Iya amma yadda bakinsa ya yi tsawo kamar shantu ko bututu sai ya ji ko I ɗin farkon sunan Iyar va zai iya faɗa ba bare har ya ƙarasa da faɗin YA.
Yana jaɓar da Jabiru sai ya nufi wajen da Iya take tsaye tun kafin ya ƙarasa sai jikin Iya ya kama rawa kamar mazari tana jin dama ta iya layar zana da tuni ta ɓace a kan wannan tsoron da take ciki da bata san takamaimai dalinlin damuwar ƙato a ɗakin a bare kuma har ya nakaɗawa Jabiru duka ita kuma da ya nufo ta sai ma ta rasa mai zai mata tabbas ta tabbatar idan ya mata duka irin dukan da ya yi wa Jabiru to kuwa sai gawarta!. Yana zuwa bai yi wata-wata ba ya sanya hannu ya finciki hannun Iya ya juya zai koma ɗakin da ya fito da Jabiru daga ciki.
"Na yi imani da Allah da ranar lahira kuma aradu na yi alwala da kabbarar harama" Cewar Iya cikin tsoro tana turjewa dan ta san yana shiga da ita ɗakin sai gawarta tun da jikinta ba zai ɗauki jigilar da jikin Jabiru ya ɗauka ba. Ganin ko saurarenta bai yi sai ta ƙara kaimi wajen faɗin
"Ka yi wa iyayenka ka rabu da ni, tsohuwa ce ni idan kuma gidan kuke so mu bari to har garin nan za mu tafi mu bar muku" Ta faɗa da sauya akalar maganar ko mutanen ɓoye ne.
"Idan gemun ɗan uwanka ya kama da wuta sai ka shafawa naka ruwa" Ta faɗa a zuciyarta hankalinta ya kai ƙololuwar tashi ganin gadan-gadan ya nufi ɗakin da ita, ga shi babu wani mai ceton ta hatta Jabirun da take ganin zai kawo mata ɗauki gashi nan tana gani magashiyyan a kwance ko uhum ba ya iya cewa bare ta sa ran zai taimake ta, shi kansa yana halin da yake buƙatar taimakon.
"Tabbas faɗan da ya fi ƙarfinka kai bawa wasa kake mayar da shi ina kaza ina faɗa da giwa ana zaune ƙalaw gwara dai na lallaɓa na rabu lafiya da wannan mutumi, amma ni abin tambayar ban san lokacin da