Showing 39001 words to 42000 words out of 60716 words
Chapter 14 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt
fa duk tsaruwar gidan wannan amma babu abinci da za a ci da safe ma sai garin kwaki muka ci muka fita, ni dai yanzu ba zan ci gari ba" Ya faɗa yana wani kumbura baki.
Salati Iyar ta kwasa tamkar wanda aka yi wani gagarumin abu har tana tafa hannuwa ta ce
" Au Allah Jaburu ni Ansai yau na ga samun wuri tusar asuba, yanzu garin kwakin ne kake cewa ba za ka ci sau biyu ba, da a can gida ne ma kana can kana fama da ɗanyen tuwon Aliya da Maimuna amma yanzu shi ne har kake cewa baka ci garin da safe ba yanzu ka ƙara to ai sai ka bari sai ka fara cinikin arincaɓar tukunna mutumin da tun almuru muka fita amma muka ringa bilayi bamu samu fasinja ba daga ƙarshe muka ɗauki aljani ya bamu wuju-wuju sai yanzu muka dawo gida ba azahar ba la'asar ga magriba ta kawo kai amma maimakon ka ɗaura alwala ka kalli gabas ka gabatar da salloli sai ta abinci kake wato kai sarki ci kamar gara ko?" Ta gama rattabo maganar tana kallonsa da mamaki. Shi ma kallon nata yake dan ya ga sai ka ce wanda ya yi saɓo.
"Yo Iya a can gida kika ce amma nan ai ba gida bane birni ne a birni wa yake cin abinci ƙasƙantacce da ban ce miki ba ma shinkafa da miyar dage-dage(Jar miya) Shi ne har kike ganin wautata.
"Wannan kuma sai dai in kaina za ka kai a yanke sai ka auni shinkafar da miyar dage-dagen ka ci" Ta faɗa tana shigewa ta bar shi da baki a sake.
Bayan sallar magriba suna zaune zugum babu mai cewa komai, Iya ta ce
"Oh Allah ka tashi ƴar mai allo jikar mai siyar da tawada" Ta faɗa tana tashi ta fice daga falon Jabiru ya bi ta da kallo, ta jima sai gata ta dawo da kwano ta zauna ta ce
"Bismillah ga marar imani na annabi ya ce ya ƙoshi" Ta faɗa tana kallon Jabiru da ya turɓune fuska tamkar ya saki kuka.
"Wai ba da kai nake ba Jaburu baka zo mu ci garin nan ba sai ka je ulsa(Olsa) Ta kama ka in shiga uku, yo idan kana fama da cutar yunwa ni ina na kama na riƙe wa zai nemo kuɗin da za mu sauke wancan uban bashin jinginar gonar da muka libgawa kanmu" Ta faɗa lokacin da ta cika luday da garin ta shanye.
"Ni fa ba shan garin nan zan yi ba, daga can wajen baki shigowa layin nan na ga wani mai siyar da gurasa ki bani in siyo kawai" Banza ta masa ta cigaba da shan garin sai da ta ji ta ƙoshi ta saki wata gyatsa tare da hamdala sannan ta zaro ɗari biyu ta miƙa masa.
"Ai sai ka je ka siya ɗan baiwa haihuwar sa'a wallahi Jaburu ba dan son da nake maka ba kuma ina tsoron ɓatawa marayan Allah rai da wani abun bana yarda in maka shi ba" Shi bai tanka mata ba ya fita ya siyo ya zauna ya cinye dan cewa ta yi ba za ta ci ba.
"Kai Jaburu kalli gidan na wutar tar-tar kamar da rana ga kayan kallo girke a falo amma muna zaune zugum kamar masu ciwon baki ko kuma masu zaman makokin mutuwa, bayan yanzu ko gidan makoki kowa sha'aninsa yake, ka tashi ka jona mana kallon mu ga su Ali Nuhu da Adamu Zango mana"
"Wa ai in kin ganni a lahira kaini aka yi sai dai ke ki jona amma ni ba zan je garin kunnawa ba wuta ta jani in mutu a banza"
"Au Allah wato ga Ansan mahaukata sai in yarda in taɓa wutar nepa in jona kallo bayan kaima mai jini a jika baka yarda ba sai ni da duk jinina ya zama tsohon jini kuma sauran-saura zan taɓa in je ta tsotse ɗan sauran da ya rage mini in baƙunci lahira ban shirya ba, to su sha zaman su kayan kallon"
*WASHE GARI*
Iya bakam ta yi babu wani baccin kirki da ya ga idanunta tana ta tunanin wayewar gari su fita nema, dan yanzu ji take duk duniya babu abin da take so da ƙauna fiye da adaidaita sahun nan saboda in ta tuna ɗinbin dukiyar da ta kashe kuma ma kuɗin jinginar gonar gado sai ta ji ko ƙuda yanzu ba ta ƙaunar ya taɓa. Sallah ta tashi ta yi da asuba ta zauna tana lazimi dan ta san k me za a yi ba zai tashi ba dan haka sai da gari ya yi shaaaa sanan Jabiru ya yi sallah abin da ya bashi mamaki shi ne yadda ya ga Iya da sanyin safiyar nan tana riƙe da tsumma mai lema tana ta faman goge adaidaitar.
"Iya yau dai ko mafarki kika yi mai daɗi har kike mini aikin goge adaidaita...
Wani kallo ta masa da ga sa ya kasa ƙarasa maganar da ya yi niyya ya tsaya yana jiran abin da za ta ce.
"Jaburu kake gyara maganarka wallahi, arincaɓarmu dai ni yanzu baka ji yadda arincaɓar nan ya shiga raina ba bana ƙaunar ko ƙuda ya taɓa shi ka san kayan kuɗi, dan haka ma nake roƙon ka kake masa tuƙi na tsanaki ban da tuƙin ganganci dan bana so ko ƙwarzane ya same shi,"
"To shikenn tun da haka kika ce ko abin tsoro muka haɗu da shi a hankali zan ke tafiya"
"Ka jika kai kuma da wani abu yo ai ina ana dara fidda uwa ake, ina maganar idan ba a ga komai ba kuma ma babu abin da zai ƙara hala mu da abin tsoro" Bai tanka mata ba ta ci gaba da gogewa tas suka shirya suka fito.
"Yau kam mun yi sakko Iya"
"Jaburu da sanyin safiya ake kama fara, na ga alama a garin nan idan muna tsayawa kallon ruwa kwaɗo ƙafa zai mana"
Sun zo daidai wata bishiya sun tsaya za su sayi pure water sai suka ji wasu samari masu adaidaita sahu suna hirar cewa yanzu sun gaji da abubuwan da hukumar ƴan karota take fitowa da shi duk sun bi sun addabi ƴan adaidaita sahu. Wannan magana da suka ji shi Jabiru bai kawo komai ba sai bayan sun fara tafiya Iya ta ce
"Wai ni Jaburu su waye ƴan farautar da na ji suna faɗar sun damu mutane ƴan arincaɓa? Kar fa mu je a yi watanda da kan mu dan ni sai na ji duk zaman garin ma ya fara gundurata ka san dama duk wani abu daga birni yake farawa kar a je a yi wuff da kanmu"
"Iya ba wasu bane fa illa masu bada hannu a kan hanya, kuma ba ƴan farauta aka ce ba ƴan karota"
"Yo ni ina na sani, kuma Allah na tuba amma su har a kan wani an basu aikin tare hanya sai su takura jama'a ai ni da zarar mun haɗa hanya da su indai ba bindiga gare su ba sai na musu tsiya" Ta faɗa tana gatsinan gefen hanci. Dariya Jabiru ya yi.
"Iya Ansai nan fa ba gida bane"
"Daji ne? Na ce daji ne"
"A'ah wai kar ki taro abin da bashi bane ba hukuma wa zai ja da su"
Baki ta taɓe bata ce komai ba a haka har suka hayo kan kwalta.
"Iya kin ga fa wanda ake magana a kan su, baki ji ranar da muka zo garin nn ba mai adaidaita sahun yana cewa ƴan karota sun ƙaro wulaƙanci to ni ma a nan na gane su"
"Ikon Allah wai dama waɗancan ne"
"Eh"
"Yo ce mini za ka yi masu ƙoƙarin haɗa mutane haɗari"
"Kamar yaya Iya masu ƙoƙarin hanawa dai"
"Yo tsakani da Allah, sai ka ga sun tara motoci da arincaɓa dodo-dodo har sai lokacin da suka ga dama za su ce a tafi ka ga kuwa yadda ake tafiya riiii ɗin wannan ai sai a samu haɗari"
Banza ya mata, da yake an dakatar da su ne amma daga haka suna hango wani tsoho mai adaidaita da basu san mai ya yi ba an dakatar da shi a gefe wani ɗan karota sai masifa yake masa shi kuma yana ta hala hannu da alama haƙuri yake bayarwa.
"Ka ga abin da nake faɗa maka mutanen nan basu da imani"
"Na gani aradu Iya amma sai mun ramawa mutumin nan bari ki ga" Ya faɗa yana cije baki. Da yake su ne a ƙarshe a kan layin dan haka ana bada hannu sai ababen hawa suka tafi riiiii amma Jabiru sai ya tafi a hankali sai da suka wuce kawai wannan ɗayan da yake wa tsohon nan masifa Ya tsaye ya kafa wani ƙwamemen gulashi baƙi dama shi ma baƙin ne.
"Allahu akbar kabiran kamar kumbo kamar kayanta, ji shi baƙi ya saka baƙin tabarau (Gilashi) Sai faman hura hanci yake da waninwuya kamar mariƙin lema, ga wani gemu ziyat kamar jelar tsatso" Cewar Iya a zuciyarta
Jabiru ganin tamkar an sanar da jama'a abin da zai yi dan sai ya ga titin kamar an yi shara da yake ababen hawan duk sun yi gaba, yana zuwa a guje ya yi ciki da mutumin nan, Ɗan karota bai lura ba shi ala dole yana bakin aiki zai ita taka kowa son ransa kuma dama shi yana cikin waɗanda basani ba sabo, yana wannan tsayen ƙiƙam sai jin wani abu ya yi ya kwashe shi kafin ya ankara sai ya ji tamkar an yi sama da shi sai da ya yi da gaske ya zo da rubda ciki a saman gaban adaidaita sahun, da hannu biyu a dafe yana ciccira idanu amma shi bai san cewa adaidaita bane duk a tunaninsa ma tirela ce ta haɗu da tirela shi ne tsautsayi ya haɗa da shi babu wanda ya ankara da abin da ya faru daga cikin abokanan aikinsa hankalinsu yana wani waje sai dai mutane da suke can gefe suke hangowa daga cikin abokan aikin kuwa mutum ɗaya ne ya gani shi kuma abokin faɗansa ne basa jituwa dan haka da ya hangi abin da yake faruwa sai ya shiga dariya har da riƙe ciki a zuciyarsa yana fatan Allah ƙara.
"Ya yi Jaburu rumfa sha shirgi, Jaburu dodon ƴan arincaɓa na Umaru bada kan ka a sare ka je gida ka ce ya faɗi, ɗan gidan Mamman jikan Ansatu ƙwararran mai tuƙi ku wanda suka riga ka koyar tuƙin tsoronka suke" Iya da abin da Jabiru ya yi ya birgeta ta shiga rattabo masa kiraru tamkar ta ari baki har wani sako ƙafa waje take irin na samari idan suna aljihun adaidaita da suke yi. Jabiru a take ya sake jin kansa ya masa wani gingiringim domin kirarin da Iyar ta masa ba ƙaramin zuga shi ta yi ba dan haka sai ya ƙara wutar gudun.
"Jaburu bi da mu ta gidan sama dama bamu taɓa hawa ba" Cewar Iya tana nuna masa gada, Jabiru kallon gadar ya yi shi tsoro ma yake dan yana ganinta ta yi wani tudu da gangare kamar wani sirnane amma kuma dan kar ya bada kansa a wajen kakar tasa musamman da ya ji tana masa kirari. Gadar ya nufa gadan-gadan ya hau, ɗan karota kuwa yana kan gaban adaidatar santsin gilas ɗin jiki na gaban sai zamo da shi yake yana ƙara ƙanƙamewa ya damƙe bakin nan sai faman jan salati yake ga ruwan hawaye suna ta sintiri a kumatunsa tamkar babu gobe. Shi duk a tunaninsa tirela ce ta yi sama da shi ya faɗa samanta dan haka ma idanunsa a rufe suke ruff dan ya san muddin tirelar ta jefo da shi kwankwatsewa zai yi ba lallai ya shura da rai ba ma wataƙila sai an harhaɗa ƙasusuwansa waje ɗaya a binne ba tare da an masa wankan gawa ba sai dai a yayyafa ruwa dan a take ma tunanin wani abokinsu ko arba'in ba a masa ba da mutuwarsa kuma irin haka ce ta faru da shi wannan tunanin ya sanya hankalinsa ya ƙara kai wa ƙololuwa wajen tashi ya sare matuƙa yana jin bankwana da duniya baki ɗaya yana hailala da salatin annabi istigfari yana neman gafarar Allah yana jin ina ma a bashi dama ya koma gida kafin ya mutu ya nemi gafarar matarsa dan ko yau kafin ya fito sai da ya mata shegen duka ba tare da ta masa laifin komai ba ya san zaluntarta yake.
"Ki yafe mini Falmata na san da alhakin ki ma ni kuma ga irin mutuwar da zan yi ta faɗowa daga saman tirela Allah sa ma a yayin faɗowata kar ta take ni ta murtsuke" Ya faɗa cikin tausayin kansa tare da tunanin makomarsa kasancewarsa namiji mai cin zalin iyalinsa, haka ya mayar da kansa ya kwantar yana ji ina ma ina ma.
Jabiru kuwa gudu ya ƙurewa adaidaitar musamman da ya gan su ɗare-ɗare a saman gada sai ya ƙara jin kansa ya masa girma domin ya tabbatar yanzu ya ƙware a tuƙi tun da har yana tuƙi a kan gada wacce bai taɓa hawa ba. Iya wani daɗi ne ya lulluɓe ta musamman idan ta hango ababen hawan d suke can ƙasa suna warici sai ta ji tamkar a jirgin saman da yake yawo a sararin samaniya take. Haba Jaburu tamkar ka manta yadda ƴan ɗakko amarya suke kwabo a mashina a garinmu ai kama ta ya yi kake kwabo da mutumin nan mai ɗamara(Ɗan karota) Amma in bai jijjigu ba ba zai san darajar mutame ba ka ga an yi ba a yi ba rufin ƙofa da ɓarawo" Iya tana gama faɗin haka sai Jabiru ya fara kwana -kwana da adaidaitar, ɗa karota a take ya ji tamkar ana tirelar ce ta fara tashi dama a lokacin ne ya ci gaba da bankwana da duniya. Har lokacin idanunsa a rufe ruf sai da aka zo wajen round da yake Jabiru ba wani ƙwarewa ya yi ba sai kawai napep ɗin ya yi gajaf a take ɗan karota ya ji tamkar an fisgo shi an warɓar gefe a nanya faɗi da reran jama'a aka shiga kayya -kayya kafin a zo Jabiru ya ɗauki hanya a guje ya kwatse da sauran napep ɗin amma sai ya banbanta da su saboda kana ganinsa ka san tuƙin gamganci yake, motar ƴan karota da ya hango cike fal da ahalin karota shi ne abin da ya ɗaga masa hankali da shi da Iya, hanya suka ɗauka ɗoɗar yana gudu ya kutsa wata hanyar da ta sada shi da wata unguwar masu ƙaramin ƙarfi sai dai har lokacin yana hango motar karotan tana biye da su duk da akwai tazara sosai a tsakanin su.
Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay
TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃
Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada.
Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi.
Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa.
Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰
Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari.
Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851
[12/23, 15:52] Mom mashkur & Afrah: https://youtu.be/SmW933P9SlI?si=v8wQ0i6QtglW1gAG
ƳAN ADAIDAITA SAHU
(Masu keken napep)
NA
MAMAN AFRAH
*SHIN KIN TURA NAKI SCREEN SHORT ƊIN NAKI NA SUBSCRIBE? GARAƁASA CE FA DA SUBSCRIBE KAWAI ZA KI MORE DA KARATU A ƁAGAS, NA KUSA GAMA FREE PAGES 5OO NE IN BA ZA KI YI SUBSCRIBE NA YOUTUBE CHANEL BA* 😂😂😂😂😂
Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.
ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳
kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu.
a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳
Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA.
09013181851
Page1️⃣1️⃣
"Mun shiga uku Jaburu wannan rundunar da aka ciko mota da su tamkar mun yi kisan kan mutane ɗari, shikenan na san