Showing 15001 words to 18000 words out of 60716 words
Chapter 6 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt
ta tinkari su Baban da maganar.
"Kar ka damu Jaburu zan musu magana a siyar da kasona a bani in saya maka"Ta faɗa dan ta faranta masa, fa gudu ya ƙarasa yana ƙanƙame ta yana ta murna da sanya mata albarka ita dai sai amin take cewa dan babu yadda za ta yi bata son ɓatawa maraya rai ne kawai amma da kaf duniya babu mai sakata ta siyar da kason gonarta da take ji da shi wanda mijinta ya bar mata.
*MAGRIBA*
Su Baba ta tara domin sanar da su munimmiyar maganar sayar da gonar dan ba za ta juri ganin Jabiru cikin ɓacin rai ba gwara ko ma mai za su ce su faɗa.
"Mamman" Iya ta kira shi da wata murya mai kamar lallashi
"Umaru" Shi ma ta kira shi
"Na'am Iya" Suka haɗa baki wajen amsawa.
"Dama wata magana ce nake so na faɗa muku amma a matsayin umarni take ba shawara ba, ina so ku samu Alhaji Audu ya saya yankin gasona na gonar mahaifinku"
"Gona kuma Iya?"
"Haka kuka ji na ce"
"Iya mai za ki yi da kuɗin gona kuma? Bayan kin san gonar nan ita ce rufin asirinmu gaba da baya kuma ko ranar nan da Alhaji Audu ya zo da maganar sai da kika faɗa da bakinki amma kuma ynzu ki zo da wata maganar da ban" Baba Umaru ya faɗa yana bin ta da kallo mai cike da ayar tambaya.
"Sake shawara na yi, so nake a yanka mini ɓangarena tun da mallakina ne ba na wani ba kuma da kake maganar mai zan yi da kuɗi ni har wata buƙata nake da ita wacce ta wuce siyan arincaɓar Jaburu" Kallon kallo aka shiga tsakanin Baba Mamman da Baba Umaru.
"Iya wai kin taɓa ganin adaidaitar a gari nan?"
"Yo ni tun da uwata ma ta haife ni ina na taɓa ganinta"
"To yanzu idan ya kawo nan qaye zai hau? Kuma kina ganin ƙauyan nan kaf sai mutum ya zagaye shi bai gaji ba wuye zai hau adaidatar a kai mutum ina ko gona za a kai mutum, garin nan duk rairayi ne ta yaya wata adaidaita za ta tuƙu, sannan zamanin tsadar man nan ya zai ke da siyan mai, uwa uba ma bai iya tuƙawa ba amma har kina cewa a siyar da gona a siya masa kin manta gonar nan ce kaɗai muke da ita, mu ma ba wani aiki muke ba da ita muka dogara a cikinta muke noma amfanin gonar da za mu ci idan aka yamke ta aka siyar shin sauran zai iya muke noma amfanin da zai ke kai mu shekara?..
"Kai umaru ba a koti kake ba da za kake jero tambayoyi kamar ka kama ɓarawo ko marar gaskiya, in bai iya ba ba sai a koya masa ba kuma sana'a ai sai an gwada a kan san na ƙwarai kuma in ma gonakin zai ke kai mutane ai babu laifi tun da ba gidan giya zai kai su ba, kuma da kake maganar noma amfani duka nawa muke matayen naku da ba haihuwa suke ba ko ni ɗan cikin nan nawa da a wani abincin kirki nake ci ba shi ne sai ana nomawa da ɓangarena ni dai ga abin da na ce" Ta katse Baba Umaru cikin kaushin murya.
"Shikenan Iya za mu je wajen Alhajin mu masa maganar yadda muka yi za ki ji" Cewar Baba Mamman cikin lallashi.
"Yawwa ko da na ji ko ku fa ai hakan ya fi amma kuke musu da ni ai duk ɗan da yake musawa uwarsa ba zai wanye ƙalaw ba, ku je to Allah muku albarka"
Da amin suka amsa suka fito daga ɗakin nata waje suka nufa suka kira Jabiru sula sanya shi a gaba da faɗa da kuma kashedin kar ya sake ya ce su suka masa magana dan haka ya nuna ya ji zai faɗa wa Iyar cewa ya fasa siyan adaidaitar kamar yadda suka buƙata amma kuma a zuciyarsa yana tunanin yadda zai shirya wata gadar zaren da zai bi ya hau a sannu ba tare da kowa ya gane ba.
"Sha kuruminka Jaburuna za a siyar da gonata a siya maka arincaɓar da kake so" Ta faɗa tana washe baki kamar gonar auduga.
"Iya ni fa na fasa siyan adaidatar nan kawai kar ki siyar da gonarki ki bari idan Allah ya hore kya siya mini" Ya faɗa muryarsa tana rawa alamar maganar ba daga zuciyarsa take ba turasasa shi aka yi.
"Jaburu anya ba aljannu suka shige ka ba, kai da bakin ka kake cewa kar a siya maka arincaɓa? Ko dai makuwa ka yi ne, anya ba matan babannin nan naka bane suka shiga suka fita suka cire maka son arincaɓar saboda suna baƙin cikin za ka samu sana'ar yi" Ta faɗa cikin ɓaɓatun faɗa irin na tsofaffi tana sakin kukan tausayinsa dan tana ganin asiri aka masa.
"Ras nake Iya kawai dai na bari ne an ce adaidaitar yanzu yana tsada idan ya sakko sai a siya"
"Allah sarki Jaburu ashe dai kana da hankali da dogon tunani, wallahi har na ji sanyi a raina da na fahimci ba asiri aka maka ba yin kan ka ne"
"Allah sarki Iya Ansai ta" Ya faɗa yana murmusawa.
"Allah sarki Jaburuna" Ita ma ta faɗa tana ƴar dariya. Fita ya yi ita kuma ta ce da daddare ta samu su Baba da maganar ba sai an siyar da gonar ba a bari tukunna.
Jabiru yana ta tunanin yadda abubuwa za su kasance yadda zai yi abu cikin ruwan sanyi ba tare da kowa ya gane ba.
Lokacin da Iya ta shiga bayi domin yin tsarki za ta yi sallar isha'i a sannan Jabiru ya fakaici ido ya shige ɗakin nata, kayan da ya shigo da su a leda ya buɗe ya saka bankaɗeɗiyar babbar rigar farin boyel da ya aro bayan ya saka ya ɗauki farin hirami ya naɗa a kan masa, ya ɗauke ledar ya saka a aljihu ya koma bayan ƙofa ya rakuɓe. Sai da ta gama alwala ta shigo ɗakin tana ɗan zancen ta ita kaɗai hijabi ta saka ta shimfiɗa sallaya, sai da ta yi kabbara ya lallaɓo ya fito daga bayan ƙofar takalminsa yana cikin aljihunsa, a hankali ya lallaɓa ya je bayan Iya ya tsaya, sai da ta yi raka'a biyu ta zauna ta yi zaman tahiya ta sake tashi ta yi raka'a ɗaya lokacin da ta kai sujada a lokacjn cikin sanɗa ya yi saurin komawa gabanta ya zauna, ya naɗe ƙafafunsa yana fuskantar ta.
"Allahu akbar!" Ta faɗa lokacin da ta ɗago daga sujadar, ganin mutum zaune a gabanta sanye da farin kaya har da rawani ga shi ɗakin dama babu haske sai na fitilar da ba wani fitowa hasken ya yi ba dan ba za ka gane fuskar mutum ba. Gabanta ne ya yanke ya faɗi lokaci guda ta shiga tunanin aljani ne ko kuwa mala'ikan mutuwa ne ya zo ɗaukan ranta.
Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay
TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃
Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada.
Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi.
Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa.
Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰
Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari.
Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851
[12/23, 15:51] Mom mashkur & Afrah: https://www.youtube.com/@MAMANAFRAHNOVEL
*ƳAN ADAIDAITA SAHU*
(Masu keken napep)
NA
MAMAN AFRAH
BABBAR GARAƁASA💃💃💃💃💃💃💃💃
Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.
ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳
kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu.
a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳
Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA.
09013181851
Page5️⃣
Idanu ta runtse tana jin yadda bugun zuciyarta yake bugawa da sauri-sauri dakyar tsamu ƙarfin gwiwar tashi tsayen ta kawo ɗaya raka'ar, idanunta har lokacin a rufe, gabanta yana faɗuwa.
"Allahu akbar" Ta faɗa lokacin da ta kai sujada ta biyu tun da ta yi sujadar take ta faman cewa
"Allah ka yafe mini kura kuraina, Allah ka jinkirta mini mutuwata ba yanzu ba sai na aurar da marayan nan Jaburu Allah ka sa mala'ikan nan ya tafi ba tare da ya ɗau raina ba" Ta faɗa tana son ɗagowa amma tana tsoro ta buɗe idanu ta gan shi, har sai da ta zo yin sallama sannan ta buɗe idanun ta kalli hagu da dama ta yi sallamar a hankali kamar mai raɗa. Yana nan zaune kansa a sunkuye bai ɗago ba.
Karkarwa jikinta yake tun ƙarfi ta kasa jin ƙarfin da za ta iya barin wajen da take ma.
"Ansatu" Ta ji ya kira sunanta da wata murya kamar ta larabawa dan ya yi muryar uztazai sai hakan ya ƙara bata tabbacin mala'ikan mutuwa ne, musamma da ya kira sunanta na gskiya bai ce Ansai ba kamar yadda ake kiranta da shi ba. So take ta amsa amma kuwwar da cikinta yake yi ga shi bakin nata ya ƙi ko da ba laɓɓanta ne damar su buɗu bare har ta kai ga yin magana.
"Ansatu a yau ne wa'adinki ya cika, yau za ki koma ga ubangijinki, dama kwanakin ki suna ƙaruwa ne saboda yawan zumunci kin san idan ɗan adam yana yawan zumunci Allah yana ƙara masa kwanaki, to kuma kina taimakon maraya amma yanzu kin kasa masa abin da yake so" Ya faɗa cikin muryar nan ta ustazanci yana wani maƙale muryar.
"Wallahi ban daina zumunci ba wajen kawu Ribaɗo ma ina yawan zuwa kafin Allah ya masa rasuwa, wallahi maganar Jaburu kuma ɗazun nan ya ce a bar siyen arincaɓar sai ta sakko saboda ta yi tsada" Ta faɗa cikin rawar murya tana fatan Allah sa kar ya ɗauki ran nata.
"Ai yanzu ma bata ɓaci ba za ki iya zuwa ki siyar da gonar gaba ɗaya ma ba sai kin bi ta kan ƴaƴanki ba, ko garin ne ku bari ke da marayan da kuɗaɗen sai ki siyar cikin sirri ku tafi birni a saya masa farin cikin maraya ba ƙaramin abu bane"
"Wallahi zan siyar a yau ba sai gobe ba zan je wajen Alhaji Audu gobe za mu daka sakko mu tafi" Ta faɗa cikin tsoro da karkarwar baki dan tsoron tana magana da mala'ikan mutuwa har da sakin fitsari a zaunen. Sai da ya tsorata ta sosai ya tabbatar ta tsorata sannan ya ce
"Ki rufe idanunki ki yi sujada saboda kar guguwar ɓacewata ta tafi da ke... Tun kan ya ƙarasa faɗa Iya ta durƙushe ta yi sujadar idanunta ɓam a rufe, laɓɓanta kaɗai sun fahimci halin da take ciki saboda karkarwar da suje suna haluwa da haƙoranta, ta saman bayanta ya lallaɓa ya tsallaka ya silale ya fice daga gidan baki ɗaya. Kayan ya je ya mayar wa mai su.
Tun da ta yi sujadar take ta faman istigfari har Jabiru ya dawo har zuwa lokacin bata ta shi daga sujadar ba. Da sallama ya shigo yana ƙwala mata kira, yana cewa ga batir ɗin da ta bashi kuɗi ya siyo. A kiɗime ta ɗago ta sauke numfashi batir ɗin ya saka ya kunna fitilar haske ya gauyaraye ɗakin. Ta haɗa gumi jargaf tamkar an sheƙa mata ruwa har jikin hijabin nata.
"Iya lafiya dai kika ɗago baki salance ba ke da kike sallah?"
"Jaburu baka ga kowa ba?"
"A ina Iya"
"A'a shikenan a bar kaza a cikin gashinta, maza ina so za mu fita da kai fita cikin sirri"
"To Iya ai dama da ke muke sirri babu wanda zai ji "Jaburu za mu tafi gidan Alhaji Audu"
"Mai za mu yi a can Iya"
"Bakin ka alekum Jaburu" Da to ya amsa mata, dan ba ya son jan maganar tun da ya san mai za su je yi. Babu wanda ya lura Iya da Jabiru suka bar gidan sai gidan Alhaji Audu bayan ta sanar da su Baba kar su je ta fasa siyar da gonar. Sun tarar da Alhajin a falonsa bayan matarsa ta musu iso aka fita aka bar Iya da Alhaji sai kuma Jabiru da yake zaune a gefe, bayan an gaisa Iya ta ce
"Alhaji na zo da wata magana ne dama, amma ina fatan ka amince mini ka taimaka ina cikin matsuwa"
"An zo wajen da nake son a zo" Cewar Alhajin a zuciyarsa a fili kuma sai ya ce.
"Babu komai Ansai ai indai ina da hali zan miki" Ya faɗa cikin kwantar da murya dan ya gama gano lagwanta. Jabiru kuwa sai dariya yake a zuciyarsa ganin cikin ruwan sanyi burinsa zai cika.
"Dama magana nake so na maka a kan gonar gadon nan da ka je da maganarta ranar nan...
"Haba ai babu komai tun da noma ta kuke ki bari wata rana idan kuka tashi siyarwa sai a siyar...
"Ban tari numfashinka ba amma na zo ka karɓi jinginar ɓangarena a cikin gonar, ka bani kuɗin sai kake noma ɓangaren nawa, amma kuma idan na mayar maka da kuɗin sai ka mayar mini da gonar ina cikin buƙatuwa kuma kar wanda ya ji maganar nan a sirri nake so a yi kar wanda ya sani. Dan gobe asubanci zan yi mu bar garin nan ni da Jaburu ba tare da kowa ya sani ba"
"Gaskiya hakan ba zai iyu ba"
"Na shiga uku ni Ansai shikenan mala'ikan mutuwa zai zo ya ɗauki raina in har ban cikawa marayan nan buri ba wayyo Allah ka kawo mini ɗauki" Ta faɗa a zuciyarta tana jin faɗuwar gaba dan bata son ta mutu yanzu.
"Lahaula wala ƙuwwata illah billah, haƙata ba za ta cim ma ruwa ba kenan duk abin da na yi ya tashi a banza kenan?" Jabiru ya faɗa a zuciyarsa kamar ya yi kuka.
Tun da Iya ta dage tana ta bashi haƙuri dan ganin bai hana ba dan bata son ko kaɗan ta mutu, shi kuwa Jabiru ya san dalilin da Iyar ta nace a kan cewa sai an karɓi jinginar gonar.
"Sai dai na karɓi jinginar duka gona amma ba wani ɓangare na gona ba, idan har kin dawo da kuɗi a mayar muku gona idan baku kawo ba gona ta zama mallakina" Shiru Iyar ta yi tana nazari ganin in ta bada gonar duka da mai za suke noma suna cin abinci amma tsoron kar mala'ikan mutuwa ya zo ya tafi sa ranta sai ta amince babu musu dan tana ganin idan har suka bar garin da kuɗin hayar adaidaitar za su tara su kawo a biya kuɗin gonar. Naira miliyan uku, basu dan dama ya gama sanin wurin dan ranar nan har cewa su Baba mamman ya yi zai ƙara a kan naira miliyan ukun ɗin amma suka ƙi. Hannun Iya har karkarwa yake ta saka ta riƙo jakar miliyoyin kuɗin dan dama shi ɗan kasuwa ne kuma bai fiya ajiye kuɗi a banki ba. Babu wanda ya san sun dawo gidan haka suka lallaɓa suka koma gida babu wanda ya san wainar da suka toya da za su tafi ne ma ya kirawo matarsa dan ta zama sheda sai takarda da ya ba Iya ta saka hannu alamar ta karɓi kuɗi. Da dare Iya a kan jakar ta yi rufda ciki a kai daga ita har Jabiru babu wanda ya yi baccin kirki dan Iya ko bacci ɓarawo ya ɗauketa a tsorace take farkawa hannunta damƙe da jakar, amma a ranta ko da na sani bata yi ba na bayar da jinginar gonar, sai dai tana da yaƙinin Jabiru zai tara fiye da kuɗin a sana'ar adaidaitan wanda za su dawo da shi su mayarwa sa Alhaji Audu ya mayar musu da gonar tun kafin ma damuna ta yi hakan ya sanya ta ce za su yi asubanci domin zuwa birnin Kano a can za a siya adaidaitan a nemi kuɗi a can ta san muddin ta zauna dole ƴaƴan za su samu labarin abin da ta yi