Showing 18001 words to 21000 words out of 60716 words
Chapter 7 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt
amma idan ta bi Jabirun suka tafi tun da bai san ko ina ba kamar yadda ita ko Kanon ma bata taɓa zuwa ba tana dai jin labarinta kuma haka mala'ikan ya bata umarni a kan su tafi birni tare.
Jabiru kuwa ransa fari tas yana jinjinawa kaifin ƙwaƙwalwarsa da ta sama masa mafita a kan cikar burinsa cikin sauƙi.
*DA ASUBA*
Iya a kiɗime ta sakko daga saman gadon nata, tana ƙanƙame da jakar kuɗin dan ko kaɗan bata cikin kwanciyar hankali, gani ma take kamar dai ɓarayi za su zo su burma mata wuƙa su ƙwace kuɗi a haka ta kwana cikin taraddadi. A hankali ta shiga tashin Jabiru tana masa magana raɗa-raɗa.
"Kai Jaburu tashi mu san inda dare ya mana, kar gari ya waye asiri ya tono a samu matsala" Ta faɗa masa lokacin da ya tashi zaune.
"Dan aradu ban shirya mutuwa ba yanzu duk da daman mutuwar ba wai ana mata shiri bane, amma gwara dai in zauna in yi istigfari sauran laifukana su wanku" Ta faɗa a zuciyarta lokacin da tunanin mala'ikan mutuwar da ya ziyarce ta jiya ya faɗo mata bata san cewa Jabiru ne ya mata iya shege irin na yaran zamani ba. Jakar kuɗin ta zazzage ta yi wani ɗauri da wani ƙaton ɗankwali a ƙugunta ta kwashi kuɗin ta ɗura a ciki da yake kuɗaɗen suna ɗaɗɗaure da kyaure sai ya zamana saitin mararta ya yi tozo kamar mai ciki saboda kuɗin da kuma tudun ɗankwalin da ta loda.
"Iya ya kika cire su daga jakar?"
"Kai tun kafin a haifi uwar mai sabulu barbela take da farinta, yo har a nunawa na rigingine farin wata ai ka san an ce mugu shi ya san makwancin mugu, yanzu idan muka tafi da su a jaka ɓarayi za su iya tare motar mu amma idan na saka a cikina na yi dibarar mu ta manya Allah za su yi tunanin ko juna biyu ne"
"Haba Iya tsofe-tsofe da ke za a ga wani juna biyu"
"Kai Jaburu bar ni in mutu maza su kai ni ba mata ba, wannan dibarar da ita za mu tafi dan haka mu lallaɓa mu bar gidan nan Allah zai kai mu lafiya ka san bahaushe ya ce dogaro ga Allah jari ne" Ta faɗa tana kallon ɗakin nata ta cikin hasken farin wata.
"Allah sarki ɗakina saduwar alkairi sai na dawo na san lokacin da za mu dawo da kuɗi dumu-dumu a jikinmu wataƙila ma sai dai a gina mini ɗakin siminta amma kai ba zan sa a rusheka ba zan barka ko dan tarihi" Ta faɗa a ranta tana leƙo waje dan tabbatar da ba kowa, haka suka lallaɓa suka bar gidan Jabiru yana riƙe da wata babbar leda mai ɗauke da kayansu kala bibbiyu.
Tun da suka fito suka nufi bakin kasuwar ƙauyen sai dai babu wata mota da za ta tashi tun da lokacin da duku-duku ne ko sallar asuba ba a shiga ba. Jabiru ne ya je ya tado wani abokinsa mai hayar machine dan dama ko da sun hau motar ma a tashar garin nasu babu wacce za ta kai su Kano kawai dai za ta kai su garin da za su samu motar ne. Su duka biyun suka hau machine ɗin da yake abokin Jabirun ya ji kuɗi da za a bashi mai tsoka da yake Iya ta ɗauka musu kuɗi a cikin kuɗin gonar, lokacin da suka je garin Ɗirani an fito daga sallar asuba dan haka a tashar ya sauke su, Iya ta bashi kuɗinsa yana murna ta kuma bashi saƙon wajen su Baba Umaru a kan ya sanar musu tana cikin ƙoshin lafiya kuma duk abin da Alhaji Audu zai faɗa musu dangane da gona gaskiya ne sai dai ta nannage shi a kan cewa ba zai faɗi saƙon ba sai da yamma, ita ta yi hakan ne dan jar su daɗe basu dawo ba su kuma su Baba su ƙaryata Alhajin duk da tana da yaƙinin dawowar su da wuri saboda bahaushe ya ce fata na gari lamiri. A tashar suka yi sallar asuba gari na wayewa aka fara lodi su Iya ne farkon shiga motar amma tun kan su shiga ta sanar da direba cewa ba za a ta biya wa Jabiru kuɗin mota ba mai mota kuwa ya ce ba zai ɗauke shi a kyauta ba. Ko da Jabirun ma ya ce ta biya sai ta ce
"Kai Jabiru baka da hankali ka san dai kuɗin arincaɓa ne idan muka taɓa kuɗin nan da yawa aka zo bai isa ba fa? Daga ni har kai babu wanda ya san kuɗin arincaɓar" Ta faɗa masa cikin raɗa dan haka shi ma sai ya yarda. Da mota ta cika Iya ta garƙama Jabiru a kan cinya ko da mutane suke ce mata ya yi girma ta riƙe shi a cinyarta sai ta ce
"Ni Ansai na ga ɓatan nono a ƙirjin budurwa, ku dai ƴan adam bakwa mutuwar ɗakin ku sai ta wani, ai dama na san a rina wai an saci zanin mahaukaciya to Jaburu dai jikana ne kuma da kuke batun na ɗora shi a cinya nawa ma Jabirun yake yaron da ba a daɗe da yaye shi ba" Ta faɗa tana sababi babu wanda ya ƙara cewa komai a haka mota ta tashi ta kama hanyar Kano ta dabo tumbin giwa. Tun da tafiya ta yi nisa sai idanun Iya suka raina fata saboda ƙagewa da ƙafafunta suka yi domin Jabiru ya yi bacci duk jikinsa ya saki, amma a haka ta daure duk da iskar da ake yi ta haɗa guɓi sharkaf ga yunwa babu abin da suka ci.
*KANO*
Tun da motar su ta shigo garin Kano bakin Iya yake a sake kamar layar mai tafiya, ganin garin cike da motoci da machina ga adaidaita sahu sai kuma jama'a kamar me.
"Na shiga aljanna na maƙale ni Ansai, haƙiƙa bahaushe ya yi gaskiya da yake cewa zo mu ci tuwo ya fi tuwon daɗi, dan Allah haka dama Kanon take wallahi yadda ake bada labarinta ta wuce nan, kai jama'a ji yadda motoci suke tari-tari babu adadi" Ta faɗa a fili tana riƙe da haɓa mamaki ya cika ta duk abin nan da ake Jabiru bacci yake bai san wainar da ake toyawa ba ƴan cikin motar kuwa sai dariya suke jin kalaman Iya.
"Jaburu, kai Jaburu kai tashi da Allah can kai sai bacci kamar kasa" Ta faɗa tana ɗaka masa duka dan ya tashi kar take kallo ita kaɗai. Ƙaran horn na motoci da machine da hayaniyar jama'a su ne suka sanya Jabiru wartsakewa ya saki baki da jajayen idanunsa na masu bacci yana bin garin da kallon mamaki.
"Laaaaaaaaa Iya kin ga adaidaita sahu wallahi sak yadda aka bani labarinta kuma iri ɗaya da ta hoton littafin nan" Ya faɗa da ƙarfi yana nunawa ta window bakin nan a washe kamar gonar auduga.
"Dan Allah Jaburu ka ce har ka hangi arincaɓar a ina take?" Iya ta faɗa tana ɗaga suya dan ta ha ga tun da ita duk wannan faɗi tashin da take bata san ma ya adadidaita sahun yake ba dan bata ma taɓa gani ba ko da hoto kuwa.
"Haba Iya duk gasu nan sun cika garin ko ina, su ne fa waɗannan ruwan ɗorawar (Yellow) Masu kamar mota" Ya faɗa daidai lokacin da direba ya faka motar a bakin tasha dan ba cikin tasha zai shiga da su ba, wajen kuma iya ganinka masu adaidata sahu ne sun lallaya adaidaitan. Tun da aka buɗe motar kowa ya shiga fitowa amma Iya gaba ɗaya sai jikinta ya yi sanya ga sanyin da ƙafafunta suka yi saboda zaan da Jabiru ya yi a kanta ga shi har lokacin mamaki ya ya mamaye mata zuciya na ganin adaidaitan a haka ta fito.
"Baba adaidaita sahun ne?" Wani matashi mai neman fasinja ya tambayi Iya.
"Hajiya ina za a kai ki?" Wani ma daga gefe ɗayan ya zo yana tambayar Iya, ita kuma ta saka hannu biyu ta dafe cikinta dan ita ganin jama'ar garin ma duk sai hankalinta ya tashi a nata ganin mutane sun yi yawa garin ma ya yi girma.
"Jaburu yanzu dama a kan wannan abun ne ka sanya na ɗaga hankalina, na rinƙa tada zaune tsaye duk dan ganin ka mallake shi, Jaburu a kan wannan abun ka sanya na siyar da gonar gadon da muka gada wajen Malam ni da su Umaru...
"Wai mai ya kawo wannan maganar ne Iya? Kin manta ni da kaina na ce ki bari sai ta sakko ke da kan ki kika ce mini mu je jiya wajen Alhaji? Kuma dama ai haka adaidaitan take"
"Yo mene ne ma bai kawo ba yanzu a ce saboda wannan abun mai ƙafafu uku ne na siyar da gonar gado, ka san yadda gonar gado take kuwa, wannan abu riɗimɗim a kife kamar wani kunkuru sai wani shegen labule da ake sakawa kamar ana munafurci a ciki, kana ganin masu hayar arincaɓar ma yadda ka san san almajirai sai suna bi jama'a suna fadanci kafin su samo fasinja, ni ba na ɗauka wani abin kirki ne, abin arziƙi duk tunanina zai yi shige da jirgin sama ni wannan abun ko birge ni bai yi ba shi ya sa ma ko farkon shigowarmu garin nan idanuna suna maƙale a kan motoci da machina, sai kuma mutane da nake kallo dan ni wannan abin ma da na gansu wallahi a tunanina motar lodar agwagi da talo-talo ce" Ta faɗa tana rushewa da kukan takaicin an rabo ta da gida ga takaicin ganin adaidaita sahu ba yadda ta tsammata ba.
"Haba Hajiya ya za ki zo nan ki cika mana kunne da kuka kamar dai ana zaman makoki?" Wani matsashi ya faɗa yana kallon Iya da take tsaye da Jabiru yana bata baki.
"Kai ina ruwan biri da kada?" Iya ta jefa masa tambayar tana harararsa.
"Dama babu amma kuma ki sani nan wajen ba wajen kuka bane gwara ku je gida ki samu wuri ki zauna, kowa dai ya san wajen nan ba ya rasa ƴan daba da ɓarayi masu ƙwace...
Dididimdim gaban Iya ya bada wani sauti dan ta tsorata sosai da ya ce ƴan daba ne da masu ƙwace dan bata manta da karon su da wanda suka raba ta da sarƙar murjaninta ba bare kuma yanzu da take ɗauke da maƙudan kuɗi in aka ƙwace mata an taƙaice ta.
"Dan Allah yaro ka yi haƙuri da kalamina dama mu baƙi ne a garin nan babu inda muka sani babu kuma wanda muka sani ka taimaka mana edan Allah"
"Iyeee taɓ sai dai ku biya mu je gidan da nake kwana amma fa gaba ɗaya maza ne a gidan sai mata maza "
"Zan biya yaro kuma batun maza ma ka ajiye a gefe na san duk basu fi jikokina ba, mata maza kuma ai su ma halittar Allah ne zan biya na sati guda kafin in samu in fara wanke wanke da shara sai in ke biya duk wata...
"Haba Iya wane wanke wanke kuma?" Jabiru da bai san manufar Iya ba da ta faɗi hakan ya tambaya.
"To ina ruwanka ita ma ai sana'a ce kuma ma ke samun abin zubawa a bakin salati" Iya ta faɗa jin Jabiru zai mata ɓaran ɓarama dan ta san zai iya nuna wa akwai kuɗi a jikinta aje a murƙusheta a ƙwace cikin dare.
"To kya samu kike kwanan dai amma batun wajen aiki sai dai ki fita ki nemo da kan ki"
"Wannan ba abin damuwa bane" Ta faɗa a fili a zuciyarta kuma sai ta ce
"Mun kawo kan mu ni Ansai yanzu muna zaune a cikin mutunci da sutura amma mun zo wajen kwana ma zai ke gagararmu, ni ban san mai ya ɗauki hankalina ba ma ban yi tunanin mazauni ba" Ta faɗa a zuciyarta tana ɗan jin da na sanin tahowar amma kaɗan dan har yanzu bata saduda ba dan ta ci alwashin cikawa Jabiru burinsa duk da dai ta ga adaidaita sahun ba kamar yadda ta tsammata ba.
Yana gaba suna biye da shi, Iya kuwa sai aikawa Jabiru harara take tana masa kashedi da idon wanda shi ko kaɗan bai gane manufar hakan ba ita kuma tana masa hakan ne dan ar ya yi suɓul da baka wajan bayyana dalilin zuwansu Kanon da kuma abin da suka riƙo dan ta san ba ƙaramin aikinsa bane.
Ɗan sahu ya kira ya faɗa masa inda zai kai su suka shiga amma Iya dakyar ta shiga. Sun zauna shi abokin tafiyar tasu a aljihu ya zauna wato can kusa da direban a bayan kuma Iya da Jabiru.
"Oh inda ranka ka sha kallo, taɓ dama in ka ji makaho yana cewa a yi wasan jifa to ya taka dutse ne" Cewar Iya cikin al'ajabin idanunta ƙurrr a saman adaidaitan daga ciki bayan ta kama ƙarafan jiki da hannu biyu ta rirriƙe tamkar mai tsoron faɗuwa.
"Ke tsohuwa kar fa ki zage mu muna zaune ah to na ji sai yada magana kike" Abokin tafiyar ya faɗa cikin muryar gagararre.
"Allah ka rufi bakina ka.ɓoyi muryata ni shegiya in ji kaza haba ɗan nan ni ina na ga ƙarfin halin zaginku wallahi karin magana ne dai na yi, ka san ban taa shiga arincaɓar nan ba hasali ma ban taɓa ganinsa ba sai yau wallahi ko a falsafar hoto ban taɓa gani ba shi ne fa nake ta al'ajabi lallai Allah buwayi ne gagara misali" Iya ta faɗa cikin sanyaya murya dan ita tsoron Kanon ma duka ya kama ta bare kuma shi wannan mai zubin ƴan sara sukan
"Ah ko da na ji ai na ɗakko da ni kike ne"
"Ah wallahi" Jabiru kuwa sai dariya yake dannewa ganin Iya tana kaffa-kaffa da saurayin tamkar wani ubanta.
Sai da mai adaidaitan ya tsaya a daidai gidan da saurayin ya nuna masa, baki sake Iya take ganin wani wawakeken gidan ƙasa wanda kamar saukar damina yake jira ya ruguje saboda yadda ya tsufa duk ya rufta.
"Ba dai a wannan ruɓaɓɓan gidan za mu sauka ba kamar wasu masu gudun hijira ai da wannan gida gwara gadar da ake cewa ana kwana a ƙasanta a garin legas duk tsiya dai ita babu alamar rugujewa a tare da ita amma wannan gida daga ganinsa kabari salama alaikum ne ko kuma a kira shi shiga da likkafaninka" Iya ta faɗa a ranta lokacin da take ƙoƙarin fitowa.
"Nawa ne kuɗinka?" Saurayin nan ya tambayi mai napep ɗin dan saboda ƙarfin hali ma ko ciniki bai yi da mai napep ɗin ba kan cewa a nawa zai kawo su.
"Dubu ɗaya ne"
Iya kuwa tun lokacin da ta ji yana tambayar kuɗin sai ranta ya cika da murna ganin banza ta faɗi sun zo a ɓagas za a biya musu kuɗi kyauta tana shirin buɗe baki ta fara jero masa godiya ta ji ya ce
"Iya sai gare ki na tambaya miki kuɗin sai ki biya shi" Baki sake Iya take kallonsa jin abin da ya yi kallon Jabiru ta yu da ya yi saurin ɗauke kai yana danne dariyarsa dan tuni ya hango jirginta ya san ta ɗauka banza ce ta faɗi sai kuma ta ji wani batun da ban.
"Na ji abu bambarakwai wai namiji da suna hajara, wannan ai shi ae kira hajaran majaran, ashe dai da ya yi gwargwaɗan a gaban araincaɓar ba shi zai biya kuɗin ba" Ta faɗa a zuciyarta tana ɗakko kuɗin ko ragi bata da damar nema ta miƙa. Har ya tada napep ɗin zai tafi Iya ta ce
"Dan Allah tsaya ɗana zan maka tambaya" Dakatawa ya yi yana kallonta sai da ta ƙarasa wajen kamar mai raɗa ta ce
"Ka yi haƙuri da tambayata, ni baƙuwa ce a garin nan, dan Allah duk waɗannan arincaɓar da na gani a can bakin tasha bila adadin kamar jamfa a jos dukansu akwai masu su?"
"Mene ne arincaɓa?"
"Irin wannan kunkurun da kake tuƙawa"
"Taɓ lallai tsohuwa an gaishe ki wallahi kin ci gaisuwar ban girma"
"Dama girman ne ya kama ni ɗan nan amma ka san an ce matambayi ba ya ɓata"
"To nan da kika gani kowa da nashi kuma kowa ya san wannne ne nasa a wajen nan wani abu ne aka yi?"
"Ikon Allah na zaune ya faɗi, babu abin da aka yi kawai dai cewa na yi Allah ƙara muku kaifin basira da kowa daga cikin ku yake iya gane wanne ne nasa duk kuwa da yawansu kuma kaloli ɗaya ne"
"To mun gode" Ya faɗa yana jan napep ɗin a guje ya bar wajen. Tsayawa ta yi tana bin sa da kallo tana ta mamaki wai a kan wannan kunkurun abun suka baro gida ita bata taɓa kawowa cewa haka adaidaita sahun ma yake.
"Amma kuma ana samu wallahi, ji fa yadda sawu ɗaya ya yi aka bashi naira dubu guda ko canji babu kuma ko ragi ban ji an nema ba duk da unguwar tasu akwai nisa kuma lungu ce, yanzu mu idan muka fita tun safe ai ina ga kafin dare mun yi cinikin da ba lallai mu iya lissafa su ba" Ta faɗa a ranta.
"Iya ki zo mu shiga mana" Jabiru da ya ga abin nata ba na ƙare bane ya faɗa yana kallonta sai lokacin ta dawo daga tunanin, tana ɗagowa ta ga saurayin nan ya zubawa cikinta da ya yi tudun kuɗin nan idanu. Ganin ta gan shi sai ya wayance yana kauda kai gefe, gaban Iya ne ya faɗi a take ta shiga tunanin ko dai maye ne shi wanda suke gani har hanji.
"Duk wanda zai ga hanjin da yake cikin ka kuwa ganin kuɗi ba zai masa wahala ba tun da an ce suna ganin kayan cikin mutum kamar suna ganin abin da aka rufe da rariyae rankaɗe" Wani sashe na zuciyarta ya bata amsa. Gaba ɗaya sai ta diririce.
"Iya gaki kin tsufa amma kuma juna biyu gare ki tsoho kika baro gida?" Saurayin ya tambaya yana ɗan basarwa.
"Ayya yaro ba juna biyu bane ƙaba ne ya fito mini, to ko an yanke haka