Showing 21001 words to 24000 words out of 60716 words
Chapter 8 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt
yake ƙara fitowa amma ba ciki bane ni yanzu idan ina da juna biyu ai har a mini waƙar soriye a garinmu" Ta faɗa gabanta yana faɗuwa tana fatan ya yarda da maganar ta. Kai kawai ya kaɗa alamar gamsuwa ya yi gaba suka bishi a baya. Tin da suka fara tunkarar cikin gidan suke jin hayaniya, amma abin mamaki sai Iya take jiyo muryar mata bayan ya ce mata duka gidan maza ne. Suna shiga idanun su suka sauka a kan ƙartan maza suna sanye da riga da zani har da gwaggwaro suka yi da ɗankwali.
"Ƴan daudu" Shi ne abin da Iya ta faɗa a zuciyarta, ita da ba abin da ta tsana irin ƴan daudu.
"Ni Ansatu yau kuma arangama muka yi fa shigowa gidan waɗanda Allah ya tsinewa, yo ai Allah ya tsinewa mai kamanceciniya da jinsin da ba nasa ba wato maza masu shigar mata ko mata masu shigar maza to ko dama su ne wanda yaron nan ya ce mata maza?" Ta sake faɗa a zuciyarta cike da mamaki kafin ta gama tantancewa wani garsameman ƙato wanda ya saka riga da da zani ya sha ɗaurin ɗankwali yana rataye da wata shegiyar jaka mai kamar zabira fuskarsa da jagira har da janbaki ya taho wajen Iya yana tafiya yana yanga hannun nan nasa a maƙale yana wani mere baki ya zo ya ce
"Oyoyo ni dai ga ƙawata na samu, tare da muke haƙawa muna binnewa ba tare da kowa ya sani ba ko ya ji kan mu ai dama daidai ruwa daidai tsaki" Ya faɗa yana ɗaga hannunsa bai sauke a ko ina ba sai a kan kafaɗar Iya.
Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay
TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃
Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada.
Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi.
Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa.
Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰
Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari.
Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851
[12/23, 15:51] Mom mashkur & Afrah: https://www.youtube.com/@MAMANAFRAHNOVEL
ƳAN ADAIDAITA SAHU
(Masu keken napep)
NA
MAMAN AFRAH
GARAƁASA💃💃💃💃💃💃💃💃💃
Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.
ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳
kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu.
a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳
Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA.
09013181851
.
Page6️⃣
"A'uzubillahi minashshaiɗanir rajim, haba wannan ai sai ka sa a kife mu garsameme da kai ka taɓa mini kafaɗa, haka kawai ka ɗora mini jakar tsaba kaji su bini" Iya ta faɗa tana doke hannunsa tare da matsawa gefe ta riƙe haɓa da hannu ɗaya ɗayan kuma yana dafe da cikinta inda kuɗin nan suke.
"Haba ƙawas ya kike batun garsamemen ƙato, kina ganina ƴar suwulwular yarinya shafalfal son kowa ƙin wanda bai samu ba ko ƙawancen ne bakya so ki yi dani, ai ƙawance ba sai da sa'anka ba in kina ganin kin mini tsufa" Ɗan daudun ya faɗa cikin karya muryar mata irin ta ƴan daudu. Ko amsa Iya bata bashi ba ta tsaya kallon gidan da ɗakuna ne birjik gasu nan a laye daga gani kasan gidan haya ne hayar ma da ya amsa sunan haya dan gidan ya tara mutane kala da ban da ban.
"Hajiya ga gida an kawo ki sai kuma mu je wajen mai gayya mai aiki ki yi signing" Saurayin nan ya faɗa yana kallon Iya. Iya jin ya ce ta yi signing kuma ita bata ma san mai yake nufi ba sai ta ji abin wani banbarakwai wai namiji da suna hajara dan haka kallonsa ta yi cike da neman ƙarin bayani ta ce.
"Haba ɗan nan ni fa hayar ɗaki na nema na sati guda amma kana maganar in yi sijin(Gidan kaso) Mai ya yi zafi shi ba wuta ba mai na muku da za a danƙara ni a sijin fisabilillahi wa rasulihi?" Ta faɗa cike da jimanta abin da yake ƙoƙarin samunta fuskar nan ta nuna alamar damuwa ƙarara. Gaba ɗaya sai wurin ya kaure da dariya, saurayin ne ma ya tsayar da tasa dariyar dakyar ya ce
"A haba madam ba fa sijin ake nufi ba wai ki saka hannu ma'ana ki bayar da matsabban shaidar zamanki a cikin gidan "
"Ayyooo ɗan nan yanzu na ji batu ai mu da yake ba jin yaren nasarar nan nake ba, ka san ni ɗiyar mai allo jikar mai siyar da tawada ina zan san wannan abu ni Ansai in dai kuɗi ne ba a rasa wanda za a bayar ba duk da ina tsoron rasa abin sakawa a bakin salati dan wannan kuɗin shi kaɗai ya rage mini shi nake kira sama da ƙasa yake amsawa ga shi haka muka baro garin mu (Ɗan moɗi) Babu abin da muka saka a hanjin mu da yake asubanci muka yi tun da duku-duku muka fito saboda kar mu yi saɓani da mota ta tafi ta bar mu" Ta faɗa tana kallon kaskon da wani ɗan daudu ya zage yana soya awara ga kuma doya a gefe. Bai tanka mata ba illa taɓe baki da ya yi, gaba ya shiga suka bi bayansa wani ɗaki ya shiga na biyun ƙarshe. Wani dangajejen namiji ne a zaune a tabarma ya sha ɗauri ɗankwali ture ka ga tsiya. Baki sake Iya take kallonsa.
"Oh jama'ar annabi na ga annabi in na yi hali na gari ni Ansai, su gidan nan gaba ki ɗayansu ƴan daudu sun fi yawa ya zaman namu zai kasance?" Iya ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta ce
"Gafaran mu dai"
"Ah, ah marhabin lale da manyan mata maganin ƙanana ƙanana ai ni dama na fi son ake samun jinsin mu idan za a samo ƴan haya, yo ina dalili a kan mai za a ke kawo mana jinsin maza wallahi ba na jin daɗin zaman nan gida ɗaya da maza duk sai mutum yake kasa sakewa, dan dai babu yadda za ka yi yo gidan haya ai ba sai yadda kake so za ka samu ba gida ne na kazo na zo" Ya faɗa yana wani karkarya murya yana fari da idanu.
"Dama mana ai haka abin yake sai haƙuri" Iya ta faɗa ba dan ranta ya so ba ita bata son ko da haɗa hanya da ƴan daudu ne saboda suna kamanceceniya da maza kuma ta san hakan babu kyau amma tun da zama ya haɗa babu yadd za ta yi, sun zauna ɗan daudun ya kalle su ya ce
"Daga gani kun sha hanya amma sai dai haƙuri yau babu komai na afawa a bakin salati a ɗakin nan saboda azumi nake na ramuwa yau, kin san idan al'ada(Priod) Ta same ka cikin watan azumi babu yadda ka iya sai dai ka ajiye azumi yo dama ai jinin al'adar ma ibada ne" Ya faɗa yana wani sinne kai alamar jin kunya.
"Kai jama'a mu kuma da haka muka fara wai kuturu ya ga mai ƙyasbi" Iya ta faɗa a ranta
.
"Yo ka sunkuyar da kai mana ƙato da kai ka zage ka sha azumi cikin azumi da nufin jinin al'ada saboda rashin tsoron Allah" Ta sake faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce
"Ai dama mu mata azumin mu ya gaji haka yanzu za ka ga mace tana azumi in an jima sai ya karye dole dama sai dai ramakon mu da yake ma girma ta kama mu yanzu al'adarma sai dai mu ga ana yi" Iya ta faɗa dan ganin an zauna lafiya dan ta lura ƴan daudun su ne ƙarfin gidan kar su je a kore su suke neman inda za su fake.
"Zaman dindindin za ki yi a gidan?" Ɗan daudun ya jefawa Iya tambayar.
"Taɓ yo ai da rashin sani karen gwauro ya kori bazawara, wa ya aike ni bare ya ga na daɗe ku zama da ku a gidan nan ai ba zan lamunta ba ma samu mafaka dai kafin mu samu mu kufce" Ta ce a zuciyarta a fili kuma ta ce
"Sati guda zamu yi"
"Dubu goma"
"Kai malam ka ji tsoron Allah ka ji tsoron ranar mutuwarka yanzu sati gudan ne zan biya jaka hamsin(10000)? Kamar wacce za ta kwana a ɗaki goma"
"Haba ki saka minjaye a maganar ki mana, da ƴar uwarki mace fa kike magana ba da namiji ba, ki ce dai haba malama ko kuma haba mai gayya mai aiki" Ya faɗa cikin karairaya.
"Ashsha mantawa na yi ashe dai duk mu ne ai kuɗin hayar sati gudan ne na ji babu sauƙi wai ciwon arne"
"Za ki iya yin gaba ki nema dan ni ma ba gidana bane hayar nake mai gidan ne ya bani dillanci"
"A mini sauƙi dan Allah, idan muka bar nan ina muka kama muka riƙe ai da hanau gwara mannau"
"Haka za ki ce amma ba wai ki tsaya gardama ba kamar dai kin kawo turɓaya(Ƙasa) Lokacin da za a gina gidan"
"Yo ba dole na ce a mini sauƙi ba ai na ji ana jaka ɗari ai kuwa a lamarin babu sauƙi sai na Allah, kuma faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar dashi, dan dai ma tunani baiwa ne in ma ba dan wauta da take sa biri ganin ayaba kamar takobi ni da ba gidana ba"
"Babu wani dogon batu ki bayar da dubu bakwai"
Haka ya ta bayar da kuɗin ba dan ranta ya so ba amma ta san kawai an cuceta, haka suka fito tana hangar lokacin da aka ba saurayin nan kuɗi da alama cin hancin ya kawo customer ne, ta san kuwa kawai sun ci tuwo ne a kan Iyar. Wani tangamemen ɗaki aka nuna musu wanda ko tabarma babu.
"Wannan mutane sama da hamsin ne suke kwana a ciki k...
"Hamsin fa ka ce ɗan nan kuma a ciki mu ma za mu kwatsu? " Iya ta katse saurayin nan.
"Eh mana a dubu bakwai ɗin kike so a baki ɗaki guda ku biyu"
"A'a amma dai duka mata ne a ciki ko?"
"Ke wannan ba garƙameman ƙato bane kika taho da shi, kuma ki ce ke a ware miki wasu jinsi, to gidan haya kamar motar haya yake ko ina ka samu ka zauna babu banbancin jinsi tun da kowa kuɗi ya biya" Saurayin ya faɗa yana juyawa ya fice daga gidan yana wani boƙara.
"Ah idan ka haɗu da ƴan duniya sai haƙuri, in ban da abin ka ka haɗa su da ƙaramin yaro Jaburu da babu abin da ya sani " Ta faɗa a zuciyarta.
*DARE*
Bayan su Iya sun ɗan miƙawa cikinsu ɗan abin da ba a rasa ba, duk da ba wani ƙoshi suka yi ba sun dai ragewa yunwa ƙarfi ne, dama abincin siyarwa ba wani albarka gare shi ba. Bayan ɗakin ya cika maƙil da maza da mata maza wato ƴan daudu kowa yana sabgarsa saɓanin Iya da take jin ta a damuwa saboda tana ganin daga kwana ɗaya ba za ta iya cigaba da kwana a gidan ba. Shi kuwa Jabiru kwanciya ya yi lokaci ƙanƙani ya fara sakin munshari haka ma Iya ta totsu daga can ƙarshen bango ya zamana Jabiru ne a kusa d ita dan gaba ɗaya jeruwa aka yi aka hau layi sai ya zamana idan wannan ya sanya kansa a nan sai wancam ya saka ƙafarsa a wurin wato suka yi kai da ƙafafuwa.
"Kai jama'a gamu ga Allah ɓarawo a hannun mata, ni dama na san a rina wai an saci zanin mahaukaciya, ya za a yi a kwamutsa mutane a ɗaki sama da mutum hamsin kamar akuyoyi a karar siyar da dabbobi, haba ni Ansai in ba dalili mai sa a leƙa gaban sirika ba ina zan zo in kwanta cikin gardawa haka ga shi nan sai sakin tusa ake ko ta ina tamkar ana sakin bom a filin yaƙi na rasa ma ta wane ɓangare tusar take fitowa abinka da manyan ƙartai sai ji kake ƙara yana fita booottttt" Cewar Iya a zuciyarta lokacin da dare ya tsala warin tusa ya hana ta sakat har wani ɗaci-ɗaci take mata a maƙoshi ga munshari da ya cika ɗakin tamkar an dannewa raƙumi wuya da igiya. Jin matsin ya yi yawa saboda an takure ta a jikin bango, gashi duk sanyin da ake ɗan yi amma saboda numfashi ya yi yawa a ɗakin.
"Haba garda'u fisabilillahi dan kun gan ni tsohuwa babu ƙarfin kirkin da zan turo ku shi ya sa kuke turarreniya, wato ga Ansai karkatacciyar kuka mai daɗin hawa ba dan ba dan ba, amma ba komai zama lafiya ya fi zama ɗan sarki" Ta faɗa tana nishi dakyar jin an matse Jabiru ya matse ta tamkar wanda gini ya ruguzowa haka ta ji matsin. "Tabbas tun ba a je ko in ba tusa ta fara ƙarewa bodari, kuma ruwa ya ƙarewa ɗa kada, tun ba a kwana ba ga shi yunwa tana neman mini lahani babu abincin kirki ga shi har ina neman kasa banbnce alif da ambaki bare in ware lam, Allah sarki Maimuna da Aliya matan arziƙi bayin Allah koyaushe su kawo mini abinci amma ina musu ikon irin namu na sirikai ga shin yanzu ɗanyen tuwon nasu ma nake nema amma ban smu bare ma na san ba ɗanyen bane, amma ba komai ai sana'a muka fito domin sana'a tafi ka je maula" Ta faɗa a zuciyarta amma har lokacin bata karaya ba. A haka bacci ɓarawo ya ɗan so sace ta ga gajiya, amma hannunta rufe a hancinta dan har lokacin tana jin ƙaran fitar tusar nan tamkar wanda suka wuni suna cin alala daga ta ji darrrr daga can ɓarin sai ta ji buttttbottt daga wancan gefen. Ji ta yi an dafa ta kamar a cikin bacci da yake dama rufda ciki ta yi saboda kuɗin da yake ƙunshe a cikinta, sai ya zamana hannun ɗaya yana hanci ɗaya a cikinta. Ji take kamar a mafarki aka ƙara dafa bayanta, kafin ta gama tantancewa dan da farko ma ta ɗauka Jabiru ne.
"Jaburu ko fitsari zan raka ka? Ai da kake iya baccin ma ka yi ƙoƙari a cikin wannan ɗakin da ya gama ɗumama da tusar garada dan ma kai yaro ne taka tusar ko ka yi ma ba a ji ƙaran fitowarta sosai ba bare warinta " Ta faɗa tana murtsuke fuska da hannun da ta toshe hanci. Cidak ta ji an ɗaga ta kafin ta samu zarafin ƙwatar kanta ko yin magana an saka hannu an danne mata baki, Sai haura ƙafafu take tana zare idanu lokaci guda hankalinta ya tashi dan ba komai bane ya faɗo mata irin kuɗin da yake jikinta za a mata fashi a ƙwace, amma daga jin yanayin ruƙon da aka mata ya tabbatar mata da cewa wanda ya riƙe ta ba ƙaramin ƙato bane kuma majiyi ƙarfi. Hannu biyu ta saka ta danne cikinta. Gidan sai tashin munshari babu alamar mai ido biyu ma a gidan hankalin Iya ya yi matuƙar tashi ganin an nufi wata ƴar hanya da ita baj zame da ita ba sai wani ɗaki yana shiga ya rufe ƙofar ya maƙala sakata.
"Allah sarki Jaburu ga Iyar ka a nan za a raba ta da kuɗin arincaɓar da kuka ci buri tare, shikenan mafarkin ka ba zai zama gaskiya ba na siyan arincaɓa, ni kuma mala'ila zai dawo ya ɗauki raina, su kuma iyayenka gonar ta salwanta tun da babu inda za au samu kuɗi su biya Alhaji Audu kuɗin da muka bada jinginar goma shikenan ni Ansai zan tafin in bar ƴaƴana da yunwa basu da gonar nomawa, ga Jaburu na bar shi a garin Kano a gidan ƴan daudu ba lallai ya iya komawa gida ba, ni kar ma in je su rinjaye shi ya faɗa daudun, dan na san suna ƙwace kuɗin nan ba lallai na fito daga ɗakin ba mala'ikan mutuwa zai