Showing 57001 words to 60000 words out of 60716 words
Chapter 20 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt
wa iyayenka kar ka ɗauki arincaɓar nan, wallahi wata badaƙalar ce a kan arincaɓar da kuɗin bashi aka siya kuɗin bashin ma gonar gado aka bayar jingina...
"Kar ki sake kirana da namiji baki ga shigata bane za ki sauya mini suna da siffa?" Ya faɗa yana karkarya muryarsa.
"Allah baki haƙuri, dan Allah kar ki tafi da arincaɓar nan"
"Sunana Ma'ishsha, dan haka ki kirani da sunana in ya so ko ma menene sai ki faɗa.
"Daga baya kenan wai an yi sadaka da karuwa" Cewar Iya a zuciyarta a fili kuma sai ta ce
"Ma'isha...
"Ma'ishsha aka ce"
"Dan Allah ka barni in yi wanda na iya saboda bakin ne bakin tsufa sai abin da ya fito ne ake ganewa.
Ko saurarenta bai tsaya yi ba ya tafi yana yangarsa kamar yadda yake lokacin da suka haɗu, takalminsa ya saka a ƙofar ɗakin Iya da take masa magiya ta je za ta bi bayansa ta yi tuntuɓe da ƙafar Jabiru da yake kwance yaɓar a wajen. Girif ta niƙu da ƙasa amma saboda hankalinta ya yi gaba tana faɗuwa ta tashi zaune ta saka hannu ta ɗaɗawa Jabiru duka a ƙafar ji kake ɗal, da sauri ya runtse idanu.
"Allah wadaran naka ya lalace in ji jaki dawa da ya ga an ɗorawa jakin gida kaya" Cewar Iya a zuciyarta ta tashi ta yi waje. Tun daga ƙofar ɗaki take masa magiya shi kuma har ta taddo shi yana tafiya da hannu a maƙale ko kallonta bai yi ba ya buɗe get ɗin, yana fita sai Iya ma za ta rufa masa baya amma me? Sai lokacin ta tuna da halin da take ciki na shigar da take jikinta duk da cewar magriba ta yi amma ba za ta iya fita waje a haka ba. Kuka take wiwi tana roƙonsa amma sai da ya je wurin adaidaitar ya shiga mazaunin direba ga mukulli a jiki Allah da ya sa ma babu wanda ya je wurin, hannu biyu Iya ta ɗora a ka tana girka kuka. Murmushi ya yi ya fito ya ɗakko jakarsa da take bayan adaidaitar tare da ɗagawa Iya hannu ya juya ya tafi abinsa ko waiwaye babu.
"Allah miki albarka Ma'isha, da kin ɗauki arincaɓar nan da kin mana ƙanƙanci" Cewar Ita a fili tana sauke ajiyar zuciya
Gida ta koma da sauri ta sako kaya ta fito ta buɗe get ɗin ta zo take tura napep ɗin da iya ƙarfinta, dakyar ta samu yake gangarawa, da haka ta samu ta shigo da shi gidan ta ƙulle sai ta rungume adaidaitar ta kwantar da kanta a jikin adaidaitar ta sauke wata ajiyar zuciya.
"Oh ni Ansai tsautsayi dai ba ya wuce baƙo ko ɗan gari" Ta faɗa a fili tana juyawa ta koma cikin falon inda Jabiru yake kallonsa ta yi sheƙeƙe ta saki wani tsaki mai sauti ta ce
"Ai yau dai na ga asara yawun bacci da safe, kai yanzu dama she sangamemen ƙato ne shi ne ka zauna ya naɗa maka duka ka ringa kuka kamar matar marigayi, duk ka cika gidan nan ni na ɗauka ma sunnar kake aikatawa, ashe dai kai ake jaɓa tamkar an samu jaki, to ai shikenan gobe ma rana ce ka ƙwallafa rai a matar da ba taka ba yanzu ai ga shi nan an mayar maka da baki kamar na jaɓa" Ta faɗa tana harararsa tun da tana ganin duk shi ne ummul aba'isin faruwar komai.
💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
*ZAN CIKAWA KOWANNE MUTUM ƊAYA 1Ok*
*PROMO PROMO PROMO Ina *neman mutum 20 wayanda suke da 25k za mu yi team work na 52U,*zan cika wa kowanne mutum ɗaya 1Ok*zanna basu 1Ok in account ya bude, na tsawon wata 6, in sha Allah in dai kun bada hadin kai kowa za'a ba shi kudin sa, ke dai* *kawai kudin ki ki ka sani In sha Allah, wacce ta yarda dani kuma tana da kudin tayi magana in sakata a list*
1_
2_
3_
4_
5_
6_
7_
8_
9_
10_
11_
12_
13_
14_
15_
16_
17_
18_
19_
20_
*Wacce take da kudin in ba ki da pls kar ki shiga*🧏🏻♀️
*Za ki iya yin hannu da yawa, amma lissafin zai fara ne in mutum 20 din sun hadu Ga Karin bayani*
*Zamu yi Team Work na 52u ga wanda suke da 25k a hannu zan cikawa kowanne mutum ɗaya 1OK ta yanda a cikin wata daya kacal zaka fara morar kudin 52u da yardar Allah. Duk wanda ya shirya zai iya yimin magana _ 👇*
09013181851
*MAMAN AFRAH TEAM*
Duk Wanda zai yi sai ya min magana insa shi a list ya tura kudin activation dinshi 25k, a maimakon 36k duk wata zan dinga bashi 15k har wata 3 in account dinshi ya bude an sallame shi sai ya koma yaci gaba girbe abinda account ke ba shi👌 Allah ya bamu sa'a ya 🤲ha damu da mutanen kwarai ya bar Mana 52u🤲
💃💃💃💃💃💃
SAURA PAGE 1 MU GAMA FREE PAGES WANDA ZAI KARE, WANDA BAI YI SUBSCRIBE BA YA YI WANDA ZAI BIYA 5OO to.
Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.
ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳
kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu.
a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳
Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA.
09013181851
[12/23, 17:22] Mom mashkur & Afrah: ƳAN ADAIDAITA SAHU
(Masu keken napep)
NA
MAMAN AFRAH
Page1️⃣6️⃣
Sai da ta yi ta masa masifa sannan ta samo wani man zafi a kan mudubin ɗakin ta lallafta masa a zototon bakin haka ya sha zunduma ihun zafin man a ciwon har jikinsa sai da ta shashshafa masa, haka dai suka kwanta ranar da takaicin kuɗin da matashin nan ya gudu da shi, babu abin da suka ci,da safe ne ma Iya ta samu ragowar garin nan sigan ma ya ƙare amma a haka ta jiƙa ta sha. Da yake zuwa safe jikin Jabiru ma ya warware bakin ma ya sace sai kumburi kaɗan haka suka shirya wajen goma na safe domin zuwa nema saboda ko biyar basu da ita ga babu abinci.
Sun shirya suka fito Iya ta rufe gidan suka hau suka tafi, Jabiru sai tuƙi akei a sannu ga rashin karyawa da bai yi ba ga kuma bai gama dawowa daidai ba.
"Jaburu ka ga wata tsaleliya can daga gani mace ce sak ba mata maza ba, ina nufin mace ce ba irin na jiya ba mai suna Ma'isha yake ko wa" Ta faɗa cike da zolaya ganin ko sun ga mace a hanya sai yake kauda kai ko kallon su ba ya son yi. Bai tankawa Iya ba har ta gaji ta ƙyale shi.
"Iya Allah sa dai yau mu samu fasinja amma wallahi in ba haka ba za mu banu bamu da abinci gaskiya mu dage da neman fasinja"
"Wallahi Jaburu abin ne sai du'ai"
Wata mata ce haka bata fi shekaru sittin ba tana tafiya a wani layi da suka shawo kwana, da yake layin babu kowa tana tafiya kai da ganinta ka san hutu ya zauna ma'ana kana ganinta ka san akwai masu gidan rana. Riƙe take da wata jaka irin jakar da ma'aikata suke zuwa office kana kallon jakar a cike take da wani abu.
"Iya ji yadda matar can ta riƙo jaka kamar ma dakyar take tafiya saboda nauyin jakar da alama ma kuɗi ne masu yawa a ciki"
"Na gani Jaburu dama wannan zamani wasu ne suka san babu amma wasu basu san ma mene ne babun ba, ina ma mu ne da kuɗin nan da mun warke kakar mu ta yanke saƙa"
"Wallahi kuwa ai kuɗi sun yi, to Iya ko dai tun da ba kowa jakar za mu warce mu gudu?"
"Wallahi kamar ka shiga raina Jaburu amma ina tsoro"
"Babu wani tsoro ai a guje za mu bar layin tun da dai ba kowa"
"To bari na fita na warto mana sai mu gudu ai yanzu sai dai Allah gafarta mana ƙasar ce sai a hankali kuma mu ma dai jiya ka ga ai saurayin nan ne ya yi ciki da faɗi da kuɗinmu ina ga ma Allah ne ya maido mana da mafi alkairinsu" Ta faɗa lokacin da Jabiru ya rage tafiya ganin sun zo dab da matar. Matar ta sakankance tana tafiya sai ji ta yi an warce jaka tana waiwayowa sai ganin ta yi wacce ta warta ta shige napep kafin ta yi ihun a kawo mata ɗauki har sun bar wajen a guje ga ba kowa a layin. Su Iya kuwa afujajan suka ƙarasa gida suna zuwa Iya ta buɗe get suka shige suka kulle da yake unguwar dama kamar ta munafukai babu kowa a layin nasu kowa yana gidansa bai damu da wani ba, dan tun zuwansu har yau basu taɓa ganin yara ma a unguwar ba bare manyan.
"Kai kakanninmu sun yanke saƙa ba ma kakar mu ba" Jabiru ya faɗa lokacin da ya ji nauyin jakar.
"Ai sai mun sati bama fita sai dai mu je mu siyo nama da nonon roba, sai mun murmure sannan"Iya ta faɗa tana ƴar dariyarsu ta manya ta saka mukulli ta kulle ƙofar falon.
"Ya kike rufewa?"
"Saboda tsaro ba dan tsoro ba, gwara mu irga kuɗin a tsanake ka san su kuma al'aura ne suna son a suturte su" Ta faɗa tana zama a tsakiyae falon ta barbaje Jabiru ma ya zauna suka saka jakar a tsakiya. Jabiru ne mai buɗe gaba ɗayan su sai da suka miƙe tsaye saboda tsananin kaɗuwa da suka yi ganin kuɗi na mamaki wanda ya shallake tunanin su.
Da sauri suka koma suka zaune a tare idanunsu ƙurrr a kan kuɗin da gaba ɗaya ƴan dubu-dubu ne rafa-rafa har rige-rigen kai hannu ake tsakanin Iya da Jabiru kowa sai ɗauka yake yana ajiyewa a gabansa sai da suka fito da gaba ɗaya rafofin daga cikin jakar har lokacin suna mamakin yawan kuɗin
"Ita kuwa matar nan ina za ta je da himin kuɗi haka? Kuɗi dami-dami, wannan kuɗin ai ya wuce misali" Jabiru ya faɗa yana kallon Iya hannunsa hagu da dama riƙe da rafa ɗai-ɗai
"Kai dai bari Jaburu wannan ai shashanci ne faɗa da sirika ranar biki, in ba sakarci jiran jirgi a tashar mota ba wane tsautsayi ni zai sa ta fito da kuɗi haka?"
"Rabon mu ne ya rantse"
"Tabbas dama an ce rabo rawani, yanzu dai mu wari wanda za mu je mu siyo kayan abinci kai har da gawayi in ke mana girkin mu sauran kuɗin kuma mu adana muna cin kaji da kayan daɗi kafin mu saka rana mu je mu kaiwa Alhaji Audu kuɗinsa dan na san kuɗi har ƙara siyan wata gonar ya isa a yi"
"Gaskiya Iya kuɗi sun yi a rayuwa ni ko gajiya bana yi da kallon su" Ya faɗa yana washe haƙora.
"Yo ba dole ba ai ni da ake cewa kallon korayen ganye yana saka ƙwarin ido to ban yarda ba, ni dai kallon kuɗi ne yake ƙaramin ƙwarin ido" Ta faɗa tana dariya
Suna cikin jin daɗin ganin tsagwaron kuɗin sai kawai kuɗi ya fara sawaya yana komawa hatsi(Gero) A tsorace suka tashi tsaye dan gaba ɗaya sai suka tsorata. Rige rigen gudu cikin bedroom domin su tsira amma sai ƙofar beroom ɗin ta ƙi buɗuwa suna rarraba idanu sai kawai suka ga wannan matar mai jaka ta fito zaune a wajen jakar sai dai wannan karon har da farin gemu a duka kuncinan ta a maimakon a haɓarta. Jikin su Iya ne ya shiga tsuma kowanne yake karkarwa kamar mazari, Iya ta fara waiwayen neman mafaka sai kawai ta ji goyo a bayanta ko da ta ɗan juya sai ta hango jarirai har uku ta cikin mudubin falon, goye a bayanta amma babu zani haka kawai suke maƙale da ita a'uziyya ta shiga ambato a zuciyarta amma kafin ta kai ƙarshen a'uziyyar sai ta ga wasu jariran guda biyu a hannunta kallon Jabiru ta yi irin kallon ka ga wata masifar da muka jefa kanmu Jabiru ya rasa bakin magana kafin ƙiftawar idanu sai ga cikin wata tara a ɓullo a jikin Jabiru.
"Labbaika lahumma labbaik, labbaika la sharikala labbaik" Cewar Iya a zuciyarta wannan karon hatta laɓɓan bakinta karkarwa suke yi.
"Iyyaka na'abudu wa iyyaka nasta'in" Cewar Jabiru a zuciyarsa jin hatta bayansa ma an banƙara masa shi ga wannan rututun ciki tamkar naƙuda za ta tashi a lokacin.
Iya idan ta kalli jariran hannunta sai ta hango na bayanta a madubi, sai ta kalli cikin jikin Jabiru basu gama dawowa daga duniyar shan mamaki ba, sai kawai suka ga matar nan da jakar sun ɓace. Suna ɓacewa jariran Iya gaba ɗaya suka saki kuka kowanne yi yake inya-inya.
"Jarirai biyar Allahumma ajirni fi musibati" Cewar Iya a zuciyata tana lallaɓawa ta yi zaman ƴan bori a wajen tare da sakin kukan ita ma.
"Haka jiya aka lakaɗa mini na jaki yanzu kuma ga shi na tashi ta cikin haihuwa ina matsayin namiji"
"Yo wane irin kana namiji ni yanzu da nake mace ma ina zan kai jarirai har rai biyar, ko da kukan su aka barni ai an gama saka ni a tsantsar masifa da tashin hankali aradu ni Ansai mun haɗu da jarabawoyi dai a lamarin mu na tahowa birni hayar arincaɓar nan, abin takaicin ma da har yau bamu mori kuɗin arincaɓar ba ko naira biyar sai baƙaƙen azabobi da muke karɓa daga wannan sai wancan... Jan wuyan rigarta da aka fara yi daga baya shi ne ya dakatar da ita daga maganar da take yi hango mudubi ta yi daga nan inda take zaune da yake mudubin dogo ne daga sama har ƙasa kana gani idan mutum kwa yana tsaye daga kansa har ƙagarsa yana hangowa a ciki, baki sake take ganin jariran kowanne ya jan rigarta kuma bayan jarirai duka daga gani sabuwar haihuwa ne in ba kwanan su ɗay ba to basu fi kwana biyu ba a duniya amma har suka iya jan riga suna jan suna kuka. Bata gama dawowa daga shan ruwan mamakin da suka shayar da ita ba sai ta ga na hannunta ma sun miƙa hannu kowanne yana fisgar rigarta, hakan ya ƙara tabbatar mata da cewa mama suke nema.
"Ba zan iya ganin wannan ɗanyan aiki ba abu kamar almara a ce ɗan jariri ya san yake jan riga? Dan dai dama ba jariran mutane bane komai ma suka yi babu mamaki" Iya ta faɗa a zuciyarta tana ɗagowa ta kalli Jabiru domin ta ga shin shi ma yana kallon abin mamakin da take kallo ko kuwa, amma tana ɗagowa sai ta ga ya kifa kai a bango yana rera kuka tamkar wanda aka ce an masa mutuwa. Kafin ta maido idanunta kan jariran sai jin hannun ɗaya ta yi ya sako ta ƙasan rigarta yana lalumar mashayarta. Da sauri ta ɗaga na hannun nata za ta yi wurgi da su amma sai ta ji su tamkar an saka mayen ƙarfe an haɗa ta da jikin su ko ɓanɓaruwa ba za su yi ba.
"Na ga annabi in na yi hali na gari ni Ansai yau kuma wace kitumurmura aka shirya mana" Ta faɗa a zuciyarta ita ma tana sakin kukan takaici.
"Ansai ki basu mama su sha, wato ki shayar da su su duka, kuma ina so in sanar da ke cewa basa ƙoshi wannan sai su wuni suna tsotsa basu san ƙoshi ba" Ta ji murya an ata magana amma bta ga mai maganar ba.
"Kam bala'i na shiga talatin ba ɗaya ni Ansai, wato har sunana ma ake kira to ni da ba shayarwa nake ba ina ni ina shayar da jarirai kuma ma yaushe rabon duniya da aiyaraye ina ruwan ma yake a mamar to ko akwai ruwan ma ai ba zan shayar da ƴaƴan aljannu ba" Ta faɗa a zuciyarta lokacin da ta ji an kira sunanta kuma sai kukan nata ya tsaya cak hatta Jabiru da yake kukan sai ya dakata cike da tsoro dan ya san dai tun da aka ba Iya umarnin shayar da jariran to ana dab da bashi umarnin ya shayar ɗin shi ma tun da aka saka masa tsohon cikin haihuwa.
"Ba, ba, babu ruwa ko ɗigo a ciki alqur'an aradu rabona da shayarwa tun shekaru aru-aru yanzu maman nawa ko na basu maɗas yake babu komai" Ta faɗa cike da tsoro tana wurwurga idanu a falon.
"Ki basu su mamula ruwan zai zo" Ta ji an faɗa.
"Duka fa maman guda biyu ne ya zan yi da sauran yaran" Ta faɗa hawaye yana zubowa tamkar wanda ta shekara bata yi kukan ba, saboda yawan hawayen da yake kwaranyowa kana kallonta ka san tana cikon tashin hankali.
"Wayyo bayana wayyo cikina" Ta ji Jabiru ya faɗa yana riƙe ciki da baya. Idanunta masu cike da hawaye ta zaro su cikin sanyin murya da ƙarfin hali ta ce
"Ba dai haihuwa za ka yi ba Jaburiu ni Ansai na ga ta kaina namiji da ciki da kuma naƙuda" Ta faɗa tana kallonsa.
"Iya kamar cikina zai fashe"
"Jaburu ba cikinka bane mararka ce dama haka mata suke jin ciwon mara idan suna naƙuda" Ta faɗa tana kallon jariran cinyarta da ta ji kowa ya kamo mamanta guda ɗaya ta ƙasan rigarta, sai kuwa ta gan shi jalele suna ƙoƙarin kaiwa baki, ga shi babu