Showing 27001 words to 30000 words out of 60716 words

Chapter 10 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt

27 Dec 2024

3510

ƙarasa wajensa ta faɗa cike da mamaki.


"Nan ne gidan mana"


"Kai jama'a daɗi kashe ni wahala ta huta tabbas na yarda idan ajali ya kira ko ba ciwo sai an je, yau ni Ansai ce zan mallaki wannan danƙareran gida a cikin binne?" Ta faɗa cike da mamaki tana saka hannu daga cikin rigarta ta fara wajen ɗaurin nan da ta yi ta saka kuɗi, dan har ranta yanzu tana ganin ko da a ce ba a basu komai ba daga cikin kuɗin ai sun samu kadarar da har sai jikokin jikoki sun mora.


Jabiru tsalle yake yi kawai saboda farinciki dan shi yana ganin zuwa birni ya musu rana. Dan haka Ɗan harƙalla yana wangame get har rige-rige ake na shiga tsakanin Iya da Jabiru, Ɗan harƙalla kuwa da sauri ya shiga napep ɗin ya tada ya shigo da shi cikin gidan ya mayar da get ɗin ya rufe, a nan inda ya faka napep ɗin a gefe da yake filin wajen yana da girma sosai dan ba ƙaramin gida bane, su Iya kuwa suna nan suna ta kalle-kalle dan tuni sun doshi can cikin gidan ma. Sai dai yana zuwa da ya buɗe babban falon da yake part ɗin Yayan nasu sai Iya da Jabiru suka dakata da shiga.


"Kai Haƙilu ya za a yi ka ce mu taka ruwan mudubi mu yi tafiya ni tun da uwata ta haife ni ma ina na taɓa jin an yi daddaɓe tsakar ɗaki da mudubi wannan da gani salon mugunta ne wallahi, duk da na san kyauta ba ta hana arziƙi amma garin son banzana ba zan yarda in yi abin da zan zo ina daman ban yi ba Allah fishshe ni aikin dana sani yadda na tsufa da ƙafafuna haka zan mutu da su ba zan mutu da gundulallun ƙafafu ba wallahi" Ta faɗa tana ƙara ja da baya tamkar ta ga zakin da yake neman abinci.


"Wallahi Iya kar ki taka haka kawai mu zame a banza" Jabiru da ya koma can gefe kamar ya ga wuta ya faɗa yana wani kumbura baki.


"Na shiga aljanna na maƙale ƙauyawan nan sai sun saka asirina ya tono, ina so in yi in fece amma suna neman zuwa da matsala haka kawai bayan ko ina na gidan tayis ɗin ne" Ɗan harƙalla ya faɗa a zuciyarsa yana danne ɓacin ransa dan ya san idan ransa ya ɓaci abin ba zai yi kyau ba.


"Allah sarki wannan ai tayis ake kiransa ko wane gidan ƴan gayu shi ake sakawa a ɗaki baya karya mutane hasali ma daɗin takawa gare shi sai mutum ya ji siiiii idan ya taka" Ya faɗa cikin sanyin murya yana fara takawa suka ga ya shige ya yi zagaye amma ko alamar faɗuwa, a haka suka fara takawa kamar masu koyon tafiya har suka ƙware ya nuna musu ko ina na gidan suna ta san barka.


"Taɓa wannan sai mun gama haɗa kuɗin gonar nan za mu je mu kaiwa Alhaji Audu mu taho da su Umaru amma sai kowanne ya saki juyar matarsa dan yanzu gidan nan sai dai su auri matan birni amma ba su Aliya ba dan wannan gidan aka kawo su dauɗa zai yi" Iya ta faɗa tana zaunawa a wata luntsumemiyar kujera.


"Kai jama'a garin daɗi ba kusa ba in ji kyankyaso da ys leƙa masa, luntsumi irin wannan kujera mai laushi kamar ba a duniya ba" Cewar Iya tana gyara zama.


"Ga mukullin adaidaita sahun ni zan tafi a sallame ni" Ɗan harƙalla ya faɗa yana kallon kuɗin da Iya ta fito da su dan ya matsu ya tafi kar asiri ya tonu"


"Yaro ka tafi ina? Ai baka ƙarasa laifinka ba dan wannan da kake gani hotiho ne babu abin da ya sani a jikin arincaɓa sai ka koya masa" Ta faɗa tana nuna Jabiru. Da sauri Ɗan harƙalla ya kalli Jabirun yana jin wani haushinsa.


"Kai kuwa mene ne abin wahala a tuƙa adaidaita sahu, mukulli kawai za ka kunna fa kake tuƙawa kamar dai yadda ake tuƙa machine"


"Kai raba kan ka da Jaburu marayan Allah ne ko amalanken shanu ba ya hawa bare machine, wannan ma dan shi ya ambata cewa yana so ni kuma kaf duniya Jaburu ne ƙaddarar soyayata shi ya sa ma na cika masa burinsa" Ta faɗa tana kafe Ɗan harƙalla da ido wanda tashin hankali da damuwa suka bayyana ƙarara a tare da shi dan shi niyyarsa dama yana karɓar kuɗin ya gudu amma kuma suna neman ɓallo masa ruwa.


"To babu damuwa zan koya masa amma dai a cikin gidan nan dan bana so mu fita waje mutane za su ce abin kunyane duk girmansa bai iya tuƙa adaidaita sahu ba sai an koya masa"


"Kai Haƙilu ba shi kaɗai za ka koya wa ba har da ni, ka san tare za muke fita sana'ar hayar to ko da wata ran ma idan shi ba zai fita ba sai ni na fita, kuma batun fita ma a bar shi duk da abin kunya gaba muka bashi ba baya ba, wannan gidan ai ko jirgin sama ya isa a koyawa mutum ba arincaɓa ba" Ta faɗa tana tashi ta miƙa masa kuɗin, ya saka cikin wata jaka da ya zo da ita, shi dai bai ce komai ba jin wai har ita za a koyawa.


Ɗan harƙalla a mazaunin direba, sai ya ce Jabiru ya zauna a hannun adaidaitar kusa da shi, Iya tana baya ta tashi tsaye duk da a duƙe take dan ba zai iyu ta miƙe tsaye ba, ta daddafe ƙarfen nan ta yi dogon wuya tana kallon abubuwan da ake nuna wa Jabiru dan bata so a barta a baya.




Haka ya wuni yana koya wa Jabiru adaidaita sahun amma dai bai wani ƙware ba sai dai ya ɗan fara iya ja, dan da aka bashi ya gwada tuƙawa Iya har da rawa da juyi ganin Jabiru yana tuƙa adaidaita sai jinjina masa take tana masa kirari shi kuma yana jin kansa ya masa gingiringim. Dan yanzu sai ta ji tana mugun ƙaunar adaidaitan sahun. Bayan ya gama da su ya musu sallama ya basu dubu goma a cikin kuɗin, Iya godiya kamar ta ari baki dan tana ganin ya musu komai haka ya musu sallama dan shi har lokacin ba a nutse yake ba duk da ya san da wuya wani zo gidan amma dai an ce marar gaskiya ko cikin ruwa sai ya yi gumi. Haka ya fito ya dan har da gari da sugar Iya ta bashi ya siyo musu a wani shago, yana basu ya kama gabansa dan lokacin ma la'asar lis. Iya da Jabiru kuwa sai kewaya gida suke suna wadaƙar su ga nepa ga ruwa a famfo sun rasa inda za su saka kan su dan murna.


WASHE GARI


Sai da suka sha garin nan da Iya ta haɗa dan sai wajen ƙarfe goma ma suka shirya domin tafiya hayar adaidaitan.


"Kai Jaburu nawa ce da kai komai baka yi da karazana ka dai ga yadda garin nan yake da arincaɓa kaca-kaca gasu nan maimakon mu fita tun da sanyin safiya mu samu rabon mu amma har rana ta ƙwalle muna gida"


"Haba Iya ai rabonka ba ya wuce ka kuma ko su masu hawan za su so su hau adaidaita wanda ake wuta ba wanda ba ya gudu ba ni kwa nan idan na ringa falfala wuta sai kowa ya san na ƙware" Ya faɗa yana fashewa da dariya dan gaba ɗaya daɗi ya mamaye masa zuciya sai ɗaga mukullin adaidaitar yake.


"Ya yi rinfa sha shirgi Jaburi, dodon ƴan arincaɓa, na Umaru ɗan gidan Mamman jikan Ansatu bada kan ka a sare ka je gida ka ce ya faɗi" Iya ta faɗa tana wani ɗaga hannu sama tana jinjina masa shi kuma sai wani kaɗa kai yake kamar ƙadangare jin irin kirarin da Iyar take masa ji yake kamar ya zama tsuntsu kan gudu saboda yana son ake zuga shi.




*ƘAUYEN ƊANMOƊI*




Tun da su Iya suka tafi babu wanda ya lura, sai da gari ya waye Baba Umaru ya je gaisheta amma sai ya tarar wayam, bayan da suka gano cewar Iya da Jabiru basa nan sai suka shiga gari yawon cigiya da sanarwa. Labarin da mai machine ɗin nan da ya kai su Iya wajen hawa mota da ya zo musu da shi na saƙon da Iyar ta bayar sun shiga tashin hankali dan sun san mahaifiyarsu babu inda ta sani a binni bare kuma Jabiru da kansa dusa ce kawai babbar damuwar ma samun labarin kuɗin jinginar gonar gadon da suka karɓa. Haka suka dangana tare da bin su Iya da addu'a domin babu wanda ya san inda za a same su ma, ga damuwar bada jinginar gonar gadon da Iyar ta yi gonar da suka dogara ita.



*KANO*




Jabiru Iya ce ta taimaka masa suka buɗe get ɗin gidan, sai da suka wangame shi tas tamkar dai ba adaidaita sahu za a fito da ita daga ciki ba sai ka ce wanda za a fito da tirela. Bayan sun fito da adaidaitan Iya tana turo shi dakyar.


"Kai Jaburu anya kuwa za a yi abin arziƙi yo ni ai duk ƙarfina da kuma garin da na sha ya ƙare a turo maka arincaɓan, anya wannan ba sai ina siyan maganin ciwo tara ba na ciwon jiki" Iya ta faɗa lokacin da ta kama tsantsa tana kallonsa yadda ya shiga ya yi wani zama na gagararru ya wani wawwangale ƙafafu tamkar mai karyayyun cinyoyi.


"Rufe gida Iya nafi so mu fantama cikin gari yin abin da ya kawo mu" Ya faɗa yana gyara zama tamkar wani wanda zai tuƙa jirgin sama. Bata tanka masa ba ta saka mukullin ta kulle get ɗin ta taho ta kama ƙarfen ƙofar gaban napep ɗin ta ɗare, ta zauna a gaban wajen aljihu.


"Iya ke da za ki shiga baya kya zauna a nan kar fa ki faɗo"


"Kai Jaburu na sha tabara na sha lahaula ni nan da kake gani nan gani nan bari ce farar tumfafiya, yo mu da zamu zuba fasinja a baya ya za a yi in zauna a yi asarar wajen mutun guda ai a nan zan zauna ni ce nan kalbus sayyara (Karen mota) " Ta faɗa tana tuntsurewa da dariya, kallonta Jabiru ya yi ya girgiza kai tare da tada adaidaita sahun. Burrrr ya bada wani ƙara kafin Iya ta tambaya dalilin ƙaran Jabiru ya fusgi adaidaitar sun fita da gudu, sosai Iya ta kama ƙarafan ta riƙe saboda shirin ko ta kwana dan ta lura da lamarin tuƙin Jabirun sai da shiri. Gajab-gajab yake shiga ta ƙananan ramukan kwatocin layi dan haka sai napep ɗin ya kasance yana sama yana ƙasa yana yin gefe da gefe.


"Jaburu anya kuwa ka nuna koyar tuƙin nan sai in ke ganin kamar dai hannun naka bai gama faɗawa ba, ga shi ban san inda za a samu ɗan harƙal... Kafin ta kai ƙarshen maganar sun canɓala wata kwata wacce bata da wani zurfi irin hanya ce aka yi wa wata makwararan wani gida, Iya a gigice ta yi sauri fitowa daga gaban ta koma baya kasancewar da suka yi gajab sai adaidaita sahun ya mutu ya tsaya cak.


"Iya ya kika bar mazauninki?"


"Kai Jaburu duk ƙaunata da arincaɓa (Adaidaita sahu) Da kuma ƙaunarka gare ni ba zan bari in mutu a banza ba" Ta faɗa tana gyara zamanta dakaka. Shi dai bai ce komai ba ya cije leɓe ya ƙara tada napep ɗin ya saki wata wuta, Jabiru da yake tuƙi sai jin hannayen Iya ya yi duka biyu ta ƙanƙamo wuyansa tamkar wanda ta shaƙe biri da igiya. Da hannu ɗaya ya riƙe adaidaitan ya saka ɗaya ya ƙwaci kansa dakyar wanda sanadin hakan adaidiitan ya ƙwace kaɗan ya rage su bugu da bishiya dakyar ya karkatar da shi ya kashe.


"Wallahi ko dai ki sauka ki dawo gaba ko kuma ki koma gida ki jira in dawo...


"In ka isa in nutse a wurin nan Jaburu a sayi arincaɓar da kuɗin gonar gadona da na ƴaƴa ka zo mini da maganar banza wallahi ƙafata ƙafarka" Ta katse masa maganar


"To dawo wajen zamanki wannan kina shaƙo mini wuya ai sai ki kashe mana kasuwa babu wanda zai shiga"


"Ko da na ji amma ni babu gidan da zan koma aradu Jaburu nan gani nan bari farar tumfafiya" Ta faɗa tana dawowa gaban ya ja suka cigaba da tafiya.


Haka suka rinƙa yawo a cikin gari, babu inda suka sani sai mai da suke ƙonewa a banza, a haka har suka zo ƙofar ɗin asibitin Aminu Kano. Wani tsoho da furfura ta gama baibaye masa fuska ƙafarsa babu takalmi sai wani ƙullin kayansa a cikin rigar filo, da net (Gidan sauro) Riƙe a ɗaya hannun yana ɗan gudu-gudu yana waiwaye da gani ma ba lafiya ce ta ishe shi ba, tun kafin ya ƙaraso yake ɗagawa Jabiru hannu alamun Jabirun ya je da napep ɗin.


"Iya kin ga mun samu fasinja" Jabiru ya faɗa cike da zumuɗi dan dama babu wanda ya tare su dan ko suna tafiya idan suka ga mutum har ɗan tsayawa suke amma babu wanda ya shiga sai su ga an tsayar da wanda yake gabansu ko bayansu sun kasa gane ko dai mutane sun lura da Jabirun ɗanyen direba ne Allah ne masani.


"Alhamdulillahi! Ai fa dama mahaƙurci mawadaci, duk mai haƙuri ya kan dafa dutsenhar ya sha romonsa yanzu ba gashi ba an tsayar da mu, ni wallahi dama tafiyar nan dan babu shiri muka taho binnin Kanon nan da sai na karɓa maka maganin kasuwa yadda ida muka fito hutun kirki ba za mu yi ba mun rinƙa jidar mutane kamar dabobi ko kamar kyauta muke ɗaukansu" Iya ta faɗa tana jijjiga kai alamar Allah ne ya san halin jaki da bai bashi ƙoho ba.


Tsohon nan yana haki haɗe da ɗan tari ya faɗo cikin adaidaita sahun cikin ƴar muryarsa da bata fita ya buɗe baki ya ce


"Mu je yaro, mu je kar su biyo sawuna suna kama ni kwanana ya ƙare ban gaji da duniya ba" Baki sake Iya ta bi bakin tsohon da kallo ganin haƙorin kirki ma babu a ciki duk sun zube sabo da tsufa sai jefi-jefi.


"Jaburu wannan fa da alama mun yi babbn kamu ina tunanin kakarmu ta yanke saƙa, miliyoyin da muka kashe jiya ne za mu mayar da gurbinsu" Iya da ta kai bakinta kusa da kunne Jabiru ta faɗa cikin raɗa.


"Kamar ya Iya? A ina ne kakar tamu za ta yanke saƙa to ai ina ganin ko zare kakar mu ba za ta samu ba bare ta yanke saƙa indai a jikin wannan ne"


"Baka da hankali Jaburu ta yaro kyau take ba ta ƙarko, wannan da kake gani daga gani ba ƙaramin kuɗi gare shi ba kasan akwai masu kuɗin da suke saka maƙudan kuɗi a leda su libga tsumma to shi ma wannan daga gani kuɗi ne shaƙe a cikin rigar filon nan dan haka kawai mu yi wuff da shi" Ta faɗa tana cikin raɗa kannewa Jabiru ido. Gyaɗa kai Jabiru ya yi alamar gamsuwa da maganarta.


"Mu tafi yaro, mu tafi unguwa uku za ka kai ni"


"In ce dai ka tanadi kuɗi yo zuwa unguwanni uku a garin nan ai ba ƙaramin abu bane, ana tafiya ana samun goluso(Goslow) Haka na ji ana faɗa ɗazu" Iya da bata san sunan unguwa bane unguwa ukun ta faɗa tun da su ba sanin sunayen unguwannin suka yi ba.


"Kai yaro ja mu tafi wannan tsuhuwar bata san ma unguwa ce unguwa ukun ba kai da yake aikin ka ne mu je dan Allah zan ke nuna maka hanya" Ya faɗa hankali tashe yana waiwaiye. Haka Jabiru ya tada nape ɗin suka tafi ruuuu. Iya da Jabiru dai sai daɗi suke ji domin suna ganin rigar filon nan ƙwace goruba a hannun kuturu ba zai yi wuya ba duk da tun da ya zauna a napep ɗin ya ƙanƙame net (Gidan sauro) Da rigar filon nan.


"Yaro adaidaitan naka dai ko yana buƙatar juyen baƙin mai ne yo abu sai ruguguu yake kamar tashi cidar ruwan sama" Cewar tsohon nan da yake yi wa Jabiru kwatance dakyar sanadin yadda yake jin adaidatan sahun tamkar jujjuya shi ake yi saboda gaba ɗaya ya kasa fahimtar mene ne matsalar, bai san cewa ɗanyen direba ya hayo ba ɗanyen ma ɗanye sharaf.


"Ba arincaɓar bane yake buƙatar juye, mai arincaɓar ne yake buƙatar ya yi juye, juyen ma na rigar filon hannunka amma da sannu za ka gane shayi ruwa ne" Iya ta faɗa a zuciyarta rana wani murmushi.


"Baba yana da ɗan matsala ne amma ba babbar matsala ba"


"Kai jama'a " Tshohon ya faɗa a fili yana ƙara ƙanƙame filon da net ɗin.


Tun fa suka fara tafiya tsohon ne yake kwatanta inda za a bi har dai aka kusa layin da gudan nasa take, dai faman ajiyar zuciya yake tamkar yaron da ya sha kuka ya ƙoshi.


'Yaro kan kwanar can da taya take nan ne gidan nawa yake" Ya faɗa cike da ɗan zumunɗin ganin an kusa zuwa a sauke shi ya huta daga tunanin rayuwa ko mutuwa da yake ta faman yi da fargaba tun da ya shiga adaidaitan ganu yake kamar dai ma direban bai san hannunsa ba ma. Tsoho ganin dai kamar ma Jabiru bai ji abin da yake nufi ba sai dai ya ji Iya ta ce


'Kai dai wannan tsoho da kwanzantu kake aradu, to ka buɗe kunnuwanka rass ka san ma wannan arincaɓar da ka shigo direbanta ɗanye ne sharaf kamar alayyahun fa aka tsunko yanzu dan haka faɗar a yi kwanar gidanka ma mara ɓata baki ne kawai ka yi fatan saukarmu lafiya dan yanzu a halin da ake ciki yanzu arincaɓar nan ki kwana ba zai sha ba" Iya ta faɗa hankali kwance dan ta ga duk babu jama'a hakan ya nuna za su ci duniyar su da tsinken tsire.


"Ɗanye!!!" mutumin tsantar tashin hankali ya a bayyana a tare da shi ya fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login