Showing 48001 words to 51000 words out of 60716 words

Chapter 17 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt

27 Dec 2024

3517

dusa biyar haka nake jin yana ciwo ko ina amsawa yake, kawai dan takaici sai da muka je inda aka yada zangon nan zan sakko jakata sai na ji tana min sannu goɗai-goɗai ta sakko ni mamaki da al'ajabi ya hana ni maganaa nan na tabbatar cewa tsoro da firgita babu abin da ba ya sakawa kalli bayana fa, Allah sa kar ya yi kanta" Ya faɗa yana juya masa bayansa.


"Yo da wane idon zan gani, haba dai sai ka ce wanda ya goyi raƙuma ko goɗiya? Tabarakallah yo ai ka samu lada ga ladan tseratar da iyalinka ga ladan goyo" Malam makaho ya faɗa yana ƴar dariya. Takaici ne ya hana shi magana wai ya samu lada, haka Jabiru ya zo sumi-sumi ya fice ta gabansu babu wanda ya lura da shi dan ko ina ma sai hayaniya suke tun da a ransu basu taɓa saka cewa wanda ya yi abin zai iya dawowa unguwar ba ma, tun fa sun gano ƙarya ya shirga musu tun da dai ko hayaƙin toyin ƙone shara babu bare wani hayaƙin tashin bom. Iya ma ganin duhun magriba ta saɗaɗo ta buɗe ƙofar gidan ta fito dan tun da Malam ya shige gidan nan ko ƙwaƙƙwaran motsi bata ji ba bare ta sanya rai za su fito ta tabbatar yau ko sallah sai dai su harhaɗa. Wajen napep ɗin ta nufa tana ta addu'ar Allah sa Jabiru bai yi wauta sun kama shi ba ko su tafi da napep ɗin nasu baki ɗaya. Dan haka tana dosar wajen sai ta ga napep ɗin yana nan yadda suka bar shi. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta lallaɓa ta shige bayan adaidaitar ta zauna sai da ya zauna a fili ta ce


"Ni ƴar nan ina zan gano Jabiru?"


"Gani" Cewar Jabiru da yake zaune a mazaunin direba sai dai ya sunkuya shi ya sa Iya bata lura da shi ba da ta shigo, da farko sai da ta tsorata i dai jin muryarsa sai ta ji wani sanyi da daɗi, haka suka yace buhun suka ka bar wajen tare da bin kwaltar suka koma ta inda suka biyo dan in suka luluƙa Jabiru ba zai gane hanyar gida ba, dan haka suka saddaƙar suna addu'ar Allah ya sanya saɓani da su da ƴan karota a haka suka samu Allah ya taimake su suka koma gida. Nan Jabiru ya bata cincin da lemo tana sha suna hira suna dariya kowa yana bada labarin abubuwan da suka faru Iya kan dariya har da runtsirawa.


"Gaskiya Jaburu ka cika jikana aradu" Ta faɗa tana ƙara yin dariyar sai da ta cinye cincin da lemon suka yi sallah kowa ya watsa ruwa.


"Oh ni Ansai yau ma haka muka ƙare gallafirin mu babu cinikin ko kwabo sai mai da muka sheƙe sai dai tun da mun kuɓuta daga hannun mutanen can ai shikenan" Ta faɗa a zuciyarta lokacin da ta kwanta bacci.


*ƳAN KAROTA*


Tun da suka bi bayan su Iya haka suka sha walgigi amma basu ga ko mai kama da su ba dama Allah bai sa ko lambar jikin napep ɗin sun gani ba bare har su samu wata hujja wajen neman su ga shi kuma basu gan su da idanunsu ba shi kansa wanda suka kaɗe ɗin da ya farfaɗo bai gane komai ba dan sai ya zama kamar wani zautacce ce ma dakyar dai ya dawo daidai.




09013181851
[12/23, 15:52] Mom mashkur & Afrah: ƳAN ADAIDAITA SAHU
(Masu keken napep)



NA








MAMAN AFRAH






Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.


ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳


kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu.


a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳


Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA.


09013181851




Page1️⃣3️⃣




Washe gari ko da Iya ta shirya Jabiru sai cewa ya yi jikinsa duk ciwo yake na gudun da ya sha yi jiya dan haka yau sai dai su huta.


"Qur'ani baka isa ba Jaburu wanda ya fito nema ina shi ina hutu abin ma ya zama rashin hankali wallahi, haka kawai ka san bashi na ciwo muka taho birnin nan dan ganin na cika maka burinka amma maimakon ka zage dantse ka nema sai ka ce wai jikinka yana ciwo ni ma ai in gudun ne na yi ko dan ni jikin ƙarfe gare ni ba na tsoka ba" Cewar Iya tana tsaye riƙe da tsantsa shi kuma yana kwance ya yi ɗai-ɗai a kan gado.


"Ni dai ban ce ba amma dai ai kya bari mu huta ko yau da gobe ne jibi sai mu fita m...


"Wallahi ka yi tsalala kamar shayi ana zaune ƙalaw har za mu kwana biyu bamu fita nema ba kamar wasu wanda aka yi wa baki wato kai gaka ɗan daɗi gida ka samu kuntsumemiyar katifa a gado in aka barka sai ka wuni kana baccin asara, to ka tashi fita babu fashi" Ta faɗa tana ɗaka masa duka a ƙwabri da sauri ya tashi yana kumbura baki ya fito haka ya yi alwala ya yi sallarsa.


"Wai nan sallah ce aka yi gari ya waye rangararai ai wannan sallar ƙadangari ce ai su ne suke ɗaga kai da hantsi" Ta faɗa tana taɓe baki.


"Wai ya za a yi da abinci ne Iya?"


"Ban sani ba wato kai ka fi so muke ƙwamushe ɗan kuɗin hannun namu da Allah ya sanya yaron nan Ɗan harƙalla ya bamu sai mun kashe mu zo mu tsugunna bayan kasuwar arincaɓar har yau bamu san ta ina take ci ba, ko ficika bamu yi ba wataƙila ma yau sai an saka mata mai"


"Haba Iya ci ai ya zama dole kin san dai ciki manta kyautar jiya gare shi, ki siya mana ko waina ce in mun fita "


To na ji, amma garin masara zan auno yau ake tuƙa tuwo ina dalili ina ɗan mafari zan ke cacar kuɗi ni ba gwabnati ba" Ta faɗa tana shigewa bayi ta yi wanka ta fito.


Tun da ta shirya take fama fa Jabiru a kan ya yi wanka amma ya ƙi, haka ya ɗauki mai ya lallafka sai sheƙi yake tamkar an zuwar da man gyaɗa kwalba guda a kansa. Haka suka fita ta kulle gidan tana ta mitar zai ke kashe musu kasuwa in ba ya wanka saboda za a ke ji yana warin dauɗa. Bayan sun ci waina da ƙosai a wajen wata mata da take soyawa suka tafi suka ringa bilayi






Gidan mai suka je suka sha mai na dubu ɗaya, Iya tana ta faman mita a kan kuɗin da ta bayar amma Jabiru ya yi kunnen uwar shegu da ita haka ta gaji da mitar ta yi shiru. Ranar ma haka suka wuni amma babu fasinjan da suka samu ga suna ɗan tsoro duk inda za su kutsa saboda kar a je ƴan karota su gano su, ganin dai babu ciniki gudun shanyewar mai a banza sai Iya ta ce su samu inuwa su zauna ai rabon mutum ba ya wuce shi indai suna da rabo to fasinja zai zo har inda suke. Har la'asar babu wanda ya ɗaga musu hannu ga shi tun wainar safe basu ci komai ba sallah ma a wajen Iya ta yi Jabiru ne ya je masallacin unguwar ya yi sallah ya ɗakko mata ruwan ita ma ta yi. Suna zaune a cikin napep ɗin bacci ya yi awongaba da Iya ta jingina sai sakin munshari take. Jabiru da yake zaune kansa sunkuye kamar an ce ta ɗago kai ya hango wata budurwa tsaleliya ƴar duma duma, tana tafiya hannun nan a maƙale tamkar lauje sai wani hura hanci take. Tun da ya kafe ta da ido daga nesa har ta zo gifta adaidaitan bai ɗauke idanunsa ba ƙurrr yake kallonta ko ƙiftawa ba ya yi, ita kuwa tana ankare da shi amma sai ta yi kamar ma ba a yi ruwansa a wajen ba.


"Malam tafiya za ka yi ne?" Ta masa tambayar a yangance tana farfara idanu Jabiru da shegen son mata ya ga matar birni a take ya fara kaɗa kai kamar ƙadangare dan da ta yi magana sai ya ji tamkar an watsa masa ruwa mai ƙanƙara, domin abu ne ya haɗe masa goma da ashirin ga daɗin sautin ta ga kuma abinka da ba a saban ba yau sun samu fasinja.


"Ko ba tafiya za ka yi bane?" Ta jefa masa tambayar lokacin da ta ɗan dawo da baya har tana ɗan wani karkata kai gefe. Wannan karon har wata in ina ya ji ta same shi.


"Eh, eh, eh tafiya zan yi"


"Ohk " Ta ce tana ƙoƙarin shiga bayan, Jabiru kan kallonta sai da ƙeyarsa ta amsa saboda ƙoƙarin waiwaye ba komai yake birge shi ba sai yadda bakinta ya sha jambaki da lips stick sai sheƙi yake. Tana shiga babu wani dogon tunanin tambayarta inda zai kai ta sai kawai ya saka mukulli ta tashi adaidaitar ga shi babu wata nutsuwa a tare da shi duk ya susuce dan shi a take sai ya ji ya kamu da son budurwar i dai yadda ya ga yanayinta ya san ko a ƙafa aka ɗaura mata shi sai ta kunce ta jefar.


Riiii ya warce adaidaitar ya yi wata uwar kwanar da ta sanya Iya da take bacci ƙafarta ɗaya a waje ɗaya a ciki jin za ta wuntsulo cikin bacci ta ji hakan sai ta ɗauka ma ko faɗa ne ya tashi tsakanin fulani da hausawa a ƙauyen su wani ya hankaɗa ta dan ita a cikin bacci take kuma ta ma manta cewar a Kano suke, yanzu ba a ƙauye ba bare har ta tuno zaune take a cikin adaidaita sahu. Jabiru da yake ta Allah, Allah ya nuna ƙwarewarsa wajen tuƙi kar budurwar ta ce ta fasa hawa ta sauka ga shi yana jin shauƙin ganinta duk ƙamshin turarenta ya buɗaɗe napep ɗin, kwata-kwata ya ma manta da wata Iya tana bacci bare har ya tashe ta ta gyara zamanta duk kuwa da tana sakin munshari, ita kuma budurwar ko da ta shiga tana ɗan danna waya bata ma lura da Iya ba bare har ta yi la'akari da munsharinta, Iya da buɗe idanunta kanta ya sauka a saman napep ɗin kawai sai ta gane bacci take dan ta tuna a inda take, da sauri ta maido ƙafarta tana rafka salati ta rirriƙe napep ɗin da hannu biyu.


"Lahaula wala ƙuwwata illah billah, Jaburu amma yau na ƙara tabbatar da cewa albasa bata yi halin ruwa ba, idan ubanka Umaru ne ya mini wannan ƙanƙanci dama ai na san a rina an saci zanen mahaukaciya, wato kai ga mai arincaɓa ko abin nema ya samu, ni Ansai gamu ga Allah ɓarawo a hannun mata" Cewar Iya da ta takarkare tana faɗa cike da faɗa ganin kamar tana magana da bango.


"Wai dan matar ubanka wacce bai aura ba Jaburu ba magana nake maka ba, ji yadda ka sha wata uwar kwana sai ka ce za ka karya kan arincaɓar? Kana ganin ƙafata a waje amma ko ka ce in tashi in mayar da ƙafar ciki son ka guntule mini ƙafa in dawo yawo da sanda to ahir ɗinka wallahi ko so kake ka kashe ni ka ci gadon arincaɓar da kuɗinta ma bamu biya ba kai da ba wani ƙwa... Bata ƙarasa ba Jabiru da sai yanzu ma ya lura da masifar da take faman masa ya ji tana neman masa ɓaran-ɓaramar cewar bai ƙware a tuƙin ba ta sanya ƴar fasinjar da suka samu su rasa kuma shi ba rasa ta ɗin ne damuwarsa ba shi bai gaji da ganinta ba. Signa yake mata a kan ta yi shiru kar ta jiƙa musu aiki, ita kuma budurwar tun da ta lura da Iya sai ta ji duk ta cika mata kunne da ɓaɓatu, ta mudubi Jabiru ya lura da yatsina fuskar da budurwar take tana yi wa Iya kallon tara saura kwata Iya kuwa da bata san wainar da ake toyawa ba tana birinkaɗuwarta sai ta ce


"Uban kuturu ma ya yi kaɗan bare na makaho ɗan banza, ni za ka watsawa ƙasa a ido har ka isa ina magana kake nuna in yi shiru wato ga Ansan mahaukata ni da bakina a dake ni a hana ni kuka... Kansa ya mayar gefe yake mata nuni da baya. Wata harara ta aika masa tare da juyawa ta kalli bayan dan tunaninta cewa yake ta koma baya ta zauna.


Wani irin washe baki ta yi tamkar ba ita take ta faman faɗa ba yanzu ta ce


"Ayyo Jaburu ai sai ka ce Iya muna da baƙuwa, yo ni ai na ɗakko shashancinka ne jiran jirgi a tashar mota ka ja arincaɓar baka tashe ni bawan Allah ashe dai fasinja muka samu a'ah wallahi sago abin sai sambarka" Ta faɗa tana gyara zama bakin nan ya ƙi rufuwa saboda murna. Jabiru ma daddagewa ya yi ya washe haƙoransa da basa samun wanki ya ci gaba da tuƙi ba tare fa ya tambayi budurwar inda za a kai ta ba ita ma kuma bata ce ga inda za a kai ta ba.


"Ɗiyata ina wuni, ya gida?" Iya ta faɗa dan ji take tamkar an saka ta a a janna dan daɗi sosai take jin farin cikin samun fasinjan da suka yi, dan har ta fara ganin sun kusa haɗa kuɗin bashin da suka ciyo tun da Allah ya tarfawa garin su nono sun fara samun fasinja.


"Lafiya" Kawai ta ce ta mayar da kanta tana cigaba da danna waya.


"Jaburu ina za ka kai ta ne, na ga ta kama bakinta ta ƙame ƙam kamar mai ciwon haƙori bata maka kwatancen. Shi Jabiru sai yanzu ma ya tuna bai faɗa mata take kwatanta inda za a kaita ba sam ya manta duk ta dagula masa lissafi da za ta zauna wuni guda yake kallonta yana ganin bakin nan nata mai jambaki da yake ƙyalli da ba zai gaji ba sai ya biya ta kuɗin kallonta ma da zai ke yi.






"Tirƙashi! Wato fasinja ne ma zai ke kwatanta inda za a ke kai shi" Budurwar ta faɗa a zuciyarta cike da mamaki ita dama dan ba takamaimana wurin zuwa gare ta ba shi ya sa ma bata ce ga unguwar da zai kaita ba nufinta idan yana tafiya in ta ga inda ya mata sai ta sauka saboda akwai abin da ta fito yi.


"Ina, ina za a kai ki?" Ya faɗa yana in ina da inda-inda Cike da mamaki Iya take kallon Jabiru dan sai yanzu ta lura da rashin nutsuwarsa sai dai diriricewarsa ta wuce a ce saboda samun fasinja ne.


"Jaburu yaushe ka fara in ina ban sani ba?"


"Lah ba in'ina bace Iya" Ya faɗa yana yin murmushin yaƙe.


"Kake tafiya kawai duk inda na ga ya mini to zan ce ka tsaya na sauka" Ta faɗa da shaƙeƙƙiyar muryarta da take gwalli. Wani daɗi ne ya lulluɓe Jabiru jin furucinta dan dama shi bai gaji da ganinta ba dan sai satar kallonta yake ta mudubi. Iya kuwa mamaki ne ya cika ta jin wai a yi ta tafiya da ita sai inda ya mata za ta sauka.


"Taɓɗi! Wannan ina ma tun safe muka haɗu da ke yo ai da mun gama cinikin yau a kan ki" Iya ta faɗa a zuciyarta tana ganin sun kasa sun siyar tana ta faɗin sai kuɗin da suka yanka mata za ta bayar tun da bata san ma ina za ta je ba bare har a yi cinikin da alama kulin sun mata yawa.


"Bari zan siya kati a can" Ta faɗa cike da yanga. Wani uban birki Jabiru ya ja maimakon su je saitin wurin siyar da kati sai dai tun kan a ƙarasa ya tsaya haka ta fita tana taɓe baki da yatsina fuska hannun nan a lanƙwashe.


"Jaburu yau mun yi babban kamu sai inda mai ya ƙare shiga motar mahaukaci, tun da dai ita kanta bata san ina za ta je ba"


"Wallahi Iya ni son ta ma nake dama ta aure ni"


"Amma dai Jaburu baka da hankali, ka duba zuƙeƙiyar mace ya wannan irin su ne matan da ake cewa wanke hannu ka taɓa, kuma wannan ko da kuɗinka sai da rabonka kana ganin tana mana kallon ƙasƙanci kamar ta ga kashi, kai da baka ajiye ba baka ba wani ajiya ba da a ce kana da kuɗi to ko kuturu ne kai ba za ka rasa matar da za ta so ka ba amma ka ga yadda baka da ƙwandalar nan baka da naira biyar to aradu kai da shanddar kashi ɗaya kuke a wajen mata"


"Iya to ba sai mu je gida ba tun da dai...


"Jaburu rufani ka saya ni ba da ni ba wannan ɗanyen aiki ai shi ya sa na ce dama da sarƙar nan tawa ta siyu da har kuɗin aurenka a ciki za a ɗauka saboda jaraba irin taka yaro bai tafasa ba zai ƙone haka kawai in yarda ka haikewa yarinyar mutane son ka sa a kore mu daga garin nan" Hawaye ne suka fara sintiri a kumatunsa ya kumburo baki.


"Rufa mini asiri Jaburu kar ka watsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login