Showing 30001 words to 33000 words out of 60716 words

Chapter 11 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt

27 Dec 2024

3529

ƙoƙarin fita daga napep ɗin da Jabiru ya ƙara sakar masa wuta sai kangal-kangaltu suke saboda ba wai ya ƙware bane sai napep ɗin ya yi can sai ya yi nan dan tuni an wuce kwanar da tsohon ya ce a nan layin gidansa yake.


"Gaba dai gaba dai Jaburu mai tuƙin ƙwararru, kai ko wanda suka ƙera arincaɓar ma baya suke take maka kai ne ɗaya tamkar da miliyab a kaf masu tuƙa arincaɓar Kano, tuƙinka azimun ne dan mutum ko da kuɗinsa sai da rabonsa, Jaburu masallacin kura mai yawan ƙasusuwa yautai mugun tsuntsu masha miyarka sai ya yi dare" Iya ta taƙarƙare sai zabgo masa kirari take tamkar ta ari baki, shi kuwa Jabiru ai tuni ma Iya ta ɗora shi a keken ɓera dan ji ya yi kansa ya masa wani gingiringim musamman da ta ce shi ne shugaban ƴan adaidaitan Kano baki ɗaya. A take ya manna wuta yana wani daddagewa tamkar dai da ƙarfinsa ne yake tuƙin, tsohon nan kuwa sai ya fara zabgo salati ganin an wuce inda za a kai shi a take zuciyarsa ta raya masa cewar ƴan yankan kai ne ko dai suna da haɗin baki da ƴan yankan kan shi ya sa aka turo su, da yake shi ne mai tsautsayin sai aka rufta da shi.


"Hadiri malafar duniya, baƙin hadari fito ta gabas kowa ka kashe kare ka ka kashe in ni ka kashe mutun ka kashe" Iya ta sake zuga Jabiru wanda hakan yake ƙara ruɗa tsohon nan yana ji dama bai hau adaidaitar tasu ba tun da yana ganin ga shi ya yi gudun gara ya tarar da zago.


" Ban da lalacewa a kashe mutum a ce kare aka kashe jama'ar annabj, na ga annabi in na yi hali na gari wato kowa ya kashe kare ya kashe in ke ya kashe mutum ya kashe ko? To wallahi in ya kashe ki ma alade ya kashe" Cewar dattijon a zuciyarsa a fili kuma sai ya ce


"Dan Allah ku taimaka mini kar ku kai ni a yanke mini kai, wallahi kan nan nawa tsufa ya sa ya yi lagafgaf har loɓawa yake ko an yanke babu kuɗin da zai yi" Ya faɗa yana kuka shaɓe-shaɓe.




"Jaburu ka ji mutuminka ya ɗauka kansa za a yanke mu bai san kuɗin hannunsa kawai muke buƙata ba ko yankan kai muke ai sai dai mu nemi samari ɗanyu sharaf masu rusheshen kai yadda za mu zama muloniya" Iya ta faɗa cikib raɗa. Kai kawai Jabiru ya gyaɗa mata.


"Jama'a taimako, za a tafi da Malam Tukur a gille masa kai" Malam da yake ɗaga hannu hagu da dama yana neman ɗauki ya faɗa duk da babu mutane sai jefi -jefi kuma babu wanda ya hango shi bare ya san abin da yake cewa sai dai suna mamakin gudun adaidaitar ne kawai. Shi kuma Dattijon nan su Iya ne suke kiɗan su suke rawar su tun da basu san cewar inda ya fito asibiti bane bare su san mai ya fito da shi, su dai sun ɗauka gudun famfalaƙin dukiyarsa yake, basu san cewa mai jinya bane ya gudu daga asibitin ba.


"Ni Tukur na ga ta kaina, wannan mutane ba za su sauke ni ba, dan na ga babu niyya ango ya kwana da wando, tabbas na yi gudun gara na tarae da zago da a tunanina wanda za shi sama idan ya taka leda ya ci ƙarfin tafiya amma dai yau na tabbatar ba haka bane" Ya faɗa a ransa yana ta share hawaye. Jabiru sai da suka shige can ciki ƙarshe-ƙarshe inda ake sabbin gine-gine ba a gama ba.


"Jaburu ga kango can, ka ga nan babu kowa mu je can mu ci karenmu ba babbaka, tun da mu da haka muka fara kuturu ya ga mai ƙyasbi" Inna ta faɗa a fili tana murmushin jin daɗi ganin za su samu maƙudan kuɗi a ɓagas su mayar da gurbin kuɗin gonar da sukabayar jingina. Jikin dattijon ne ya jau ƙyarma dan zuwa yanzu ya saddaƙar da cewa kwanansa ya ƙare.


"Tabbas ba a gujewa mutuwa duk inda mutum yake ajalinsa yana biye da shi sai dai in lokacinsa ne bai yi ba" Ya faɗa a ransa yana jin dana sanin baro asibitin da ya mutu a can ɗin mutuwa cikin salama ba irin wannan mutuwar ba da za a raba shi da kansa ɗungurugum yana ji yana kallo.


Jabiru ne ya fara fitowa ya tsaya a ƙofar da baya inda dattijon yake, Iya kuma ya fito tana hangar ko ina sai da suka tabbatar babu kowa.


"Jaburu mu kai shi cikin kangon kar mu warci abin nan a nan ya je ya mana ihu mu gudu a bi mu a far mana, amma a cikin nan sai mu yi maganinsa babu wanda ya gani" Ta raɗawa Jabiru a kunne kai ya gyaɗa mata.


Artabu aka fara da dattijo ya kafe a kan cewa ba zai sakko ba ya ƙanƙame rigar filonsa da net ɗin sa yana zubar hawaye.


"Wato taurin kai da tirkiya za ka nuna mana, to ai idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi" Cewar Iya tana damƙe baki. Haka suka masa cali-cali da yake dama ɗan falaulayi da shi babu ƙiba ga uwa uba jinya sai ya zamana bashi da nauyi cidak suka ɗago shi, Iya ta riƙe ƙafafu Jabiru ya riƙe uban jikin ga an cusa masa gefen net ɗin nasa a baki dan kar ya yi ihu ga kuma har lokacin rigar filon a ƙanƙame a ƙirjinsa ya danne da hannuwansa, rigar filon da su Iya suke son kai wa wawaso. Ɗakunan ma wani cikin wani haka yanayin kangon yake ga tsawo gare shi gidan amma haka suka shige can ciki suka kai shi ɗakin ƙarshe baka ganin komai sai ruwan hawaye sharaf-sharaf kamar an kunna lalataccen famfo. Jaɓar aka ajiye Malam Tukur tamkar ana jefar fa kayan wanki.


"Ku mini rai kar a yanke mini kaina" Ya faɗa duk da akwai net a bakin amma kana iya jiyo diri maganar. Babu wanda ya kula shi suka saka net ɗin suka ƙulle masa ƙafafu.


"Kuɗi ko rai" Iya ta faɗa tana kallonsa.


"Gwara ma ka bayar salin alin dan idan na kira oganmu da bindigu za su taho kuma suna zuwa babu sauƙi ciwon arne za su ɗakko maka kai... Tun kan Jabiru ya kai ƙarshen maganar Malam Tukur ya saki wani marayan kuka marar sauti, domin ya san ƴan magana sun ce gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah, yana jin abarin yadda ake cewa ƴan kidinafin suna ɗauke kan mutane da bindiga yau kuma abin ya zo kansa.


"Kar ku mini ta ƴan kidimashin(Kidnaping) Kar ku mini ta ƴan boko haram ku mini ta ƴan mahammadiyya wato haƙuri halin annabawa, wallahi ni ko sisi bani da" Ya faɗa dan lokacin an cire masa net ɗin daga bakin.










Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay


TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃






Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada.


Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi.


Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa.


Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰


Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari.
Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851
[12/15, 16:07] Mom mashkur & Afrah: ƳAN ADAIDAITA SAHU
(Masu keken napep)




NA




MAMAN AFRAH



😂😂😂😂😂




Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.


ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳


kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu.


a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳


Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA.


09013181851




Page 8️⃣


"Jaburu zazzage mini rigar filon nan nashi mu kwashe rabonmu tun da ya ƙi ya bayar sai a ƙwaƙwata ta ƙarfi mu arce mu bar shi a nan" Cewar Iya tana aikawa Malam Tukur wata uwar harara.


Da sauri Jabiru ya ɗauke rigar filon hannunsa har rawa yake wajen zazzagewa, amma me wani dogon wandon shadda ne da ya gaji da koɗewa, sai wani katalallan silifas wanda saboda sakawa tsakiyar har ta cinye, sai lemon fata guda uku biyu ɗayan ma a yanke yake. Baki sake Iya da Jabiru suka bi shi da kallon jin haushin saka ran samum maƙudan kuɗin da suka yi a jikinsa.


"Dama na faɗa muku ni bani da ko ƙwandala, dama ko kuɗin adaidaitar da kuka ɗakko ni sai naje zan ranta in baku, saboda nan inda kuka ga na fito asibitin Malam Aminu ne, hawan jini nake bansan lkcn da aka kwashe ni muraran rai a hannun Allah aka kaini asibitin ba, bayan an san bana ƙaunar zuwa asibiti, to shi ne na farfaɗo na faɗawa ɗana mu bar asibitin nan saboda na fi son na ganni a gida amma suka ƙi, ni kuma ganin Malam Audi na kusa da ni ya margaya(Ya mutu) Rai ya yi halinsa shi ya sa na yi wa kaina ƙiyamul laili na haɗo kayana na yayumo gidan saurona (Net) Da yake duk ƴan zaman jinyar suna waje na lallaɓa na bi ta ɗayar ƙofar zan gudu shi ne fa wasu ma'aikatan jiya suka ganni suke kirana da yake su ne masu kula da mu kuma sun san ba a sallame ni ba. Suka biyo ni shi ne na gudo dan kar su mayar da ni dan ni ban shirya mutuwa ba duk da sai kwana sun ƙare" Ya kai ƙarshen maganar yana saka bayan hannunsa ya share hawayen da suke zuba shaɓe-shaɓe.


"Kuturun kare amma kai wannan da ɗanyan aiki a gabanka jajawur ma kuwa, yanzu dama ka san babu kuɗi a cikin ƙunshin rigar filon nan sai tarkacen banza da wofi amma ka sanya muka ba kanmu wahala? Ai kuwa sai mun jibgeka ladan wahala da ka bamu" Cewar Iya tana dunƙule hannu.


"Wallahi Iya ga man da muka ƙona ina fa ya yi mu yi sati guda cur muna amfani da shi" Jabiru ya faɗa cike da ɓacin rai.


"Yo ba dole dama a ƙona mai ba baka ji ya ce unguwa uku ba, to unguwar tasu ce aka haɗa uku a wuri ɗaya nisan unguwa guda uku a guda ɗaya ga wannan dogon zangon da muka ɗakko zuwa wurin nan ka ga in aka haɗa unguwa huɗu kenan"


"Yo ai dole ma mu jibge shi ta bakin naki" Ya faɗa yana dunƙule nasa hannun. Iya da take saitin jikin katangar ne bata lura da wani miciji da ya sako kansa ba, babu wanda ya lura Malam Tukur yana ta bada haƙurin kar su duke shi saboda bashi da cikakkiyar lafiya amma babu wanda ya saurare shi, Iya ta daddage ƙarfinta ta sakarwa Malam Tukur ƙulli ta ɗago dan sai da ta sunkuya ta kai masa ƙullin, ɗagowar da ta yi ya yi daidai da sakowar micijin wuyanta ya laulaye mata wuya, Iya jin motsin abu ya kanannale mata wuya ta kai idanunta wajen aikuwa ta yi mugun gani idanu ta zaro tana rarraba idanun cike da fargaba ta sauke idanun nata a kan Jabiru da ya sauke wa Malam Tukur ƙulli har biyu.


"Allah ka yafe mini zan yi hakan ne ba dan in cutar da maraya ba sai dan in ceci kaina, domin na san matsawar Jaburu ya ga micijin nan to ko ni ce ubansa da ya diro da shi duniya ba zai tamaka mini ba saboda tsoron da yake da shi kamar farar kura guduwa zai yi ya bar ni micijin ya kashe ni in zama mushe" Ta faɗa a zuciyarta tana nufar hannun Jabiru ta riƙo tare da riƙo kafaɗarsa ta kai wuyanta kusa da na shi wuyan kamar micijin ya gane mai take nufi ai kuwa ya haɗo da wuyan Jabiru ya kanannaɗe su a tare.




"Iya ya haka kika maƙalƙale ni? Ya na ji kin maƙala mini abu a wuya ko tsumma ne"


"Duba da kyau Jaburu abin ya fi ƙarfin tsumma abinda yake wuyanka ya fi ƙarfin mai rai" Ta faɗa cikin tsoro idanun nata har sun cika da hawaye, na tausayin kanta da kuma tausayin maraya da ta masa haka. Bai wani kawo komai ba ya miƙa hannu gefen wuyan nasa bai yi wa hannnun masauki a ko ina ba sai a wajen jelar micijin ya damƙo dan ya ga mene ne yana damƙa ya ji wani santsi bai kawo komai ba ya kalli hannun nasa ai kuwa ya yi arangama da jelar miciji damƙe a hannunsa, da sauri ya maida kallonsa kan Iya ya ga kan micijin a nata wuyan ya nannaɗe. Idanu ya shiga zarewa tamkar za su faɗo dan shi hatta ƙadangare tsoro yake bare kuma mai gayya mai aiki miciji, micijin ma a naɗe a wuyansa ai kuwa babu lafiya a take ya ji fitsari ya cika masa mara. Salatin da ya ji Iya ta yi ƙarfin halin karantowa shi ya kama ya cafe yana fatan Allah sa su ƙwaci kansu kar abu ya gagare su.




"Haba Jaburu kaima ai sai ka nemi naka salatin ko wata addu'a ka kama amma ma kama abu ɗaya gwara dai kowa ya kama nasa ko Allah ya sa a dace" Ta faɗa lokacin ruwan hawaye sun yi wa fuskarta sallama fuskar da ta jiƙe da gumi sharƙaf sai ta haɗu da ruwan hawaye.


"Alhadisil auwal,hadisi na ɗaya...


'Haba kai kuwa Jaburu ai sai ka samo na hamsin ko ɗari ka karanto ka san an ce in mutum zai roƙa to ya roka da babban masaki, amma ka fara daga na ɗaya fisabilillahi Allah na tuba ka mini aikin gafara" Cewar Iya dan ita ta ɗauka idan ya karanto hadisi na hamsin ɗin sai sun fi saurin samun mafita. Jabiru bai ma san abin da Iya take faɗa ba dan tun da ta zo duniya shi bai taɓa cin karo da tashin hankali mai lasisi kamar na yau ba, dan haka ma da Iya bata ba kanta wahala ba wajen masa bayani dan da ta yi haƙuri daga wurin alhadisil auwal ɗin a nan ya tsaya babu inda zai iya ɗarawa dan ƙasurgumin jahili ne.


"Murtala a haɗa da murtala, murtala biyu kenan (Ashirin a haɗa da ashirin arba'in kenan), Zobiya a haɗa da zobiya, zobiya biyu kenan (Hamsin a haɗa da hamsin ɗari kenan)" Haka Iya ta shiga karantowa tana maimaitawa dan har a'uziyya take yi idan za ta faɗa saboda tsurewa da ta yi da gigicewa duk ta dibirbirce. Malam Tukur yana nan zaune a gefe kamar yajin ƙosai yana ganin abin al'ajabi da mamaki. Suna cikin wannan fargabar ne kawai sai suka ga micijin ya rabe a biyu ɓangare ɗaya inda da kan a wuyan Iya ɗaya ɓangaren inda da jela a wuyan Jabiru. Sai tashin hankalin ya fi na farko. Iya kuwa ganin abin ba na ƙare bane kuma gudun kar ta je ta rasa ranta da rana tsaka a hayar ADAIDAITA SAHU sai ta fara lallaɓawa ta tsugunna dan ta ji an ce idan miciji yana wuri ko ƙwaƙƙwaran motsi ba a yi bare kuma ita da yake kanannaɗe a wuyanta.




A gaban Malam Tukur ta yi masauki dan tana ganin yanzu basu da wata mafita da ta wuce shi, tsugunnawarta ke d wuya Jabiru ma ya ɗaga nasa sanyayyun ƙafafun.




Sai da ta je ta miƙa hannu biyu ta damƙo ƙafar Malam ta dama, Jabiru ya tsugunna kenan sai jelar micijin ta dawo gaban fuskarsa ta shafa wajen saitin idanunsa hakan ne ya sanya gabansa ya cigaba da bugawa gifgifgifgif dan tunaninsa ko makanta ce za ta same shi, shi ya sa jelar ta taɓa idanunsa tsabar tsoro bai san lokacin da ƙarshen wata waƙa da suke yinta suna yara ya kufce masa ya fito ba Iya sai ji ta yi ya ce


"Malamai ku ji tsoron Allah za a kai akuya makaranta" Ya faɗa cikin ficewar hayyaci.


" Ai ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login