Showing 9001 words to 12000 words out of 60716 words
Chapter 4 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt
zancen sai dai bata taɓa zaton sun ji mai take cewa ba, ashe dai shuka ta yi a idon makwarwa.
"Na shiga uku ni Ansai fashi da rana tsaka ni ina zan sa kaina idan suka ƙwace sarƙar nan bayan burikan da muka ci a kanta ni da Jaburu" Ta faɗa a zuciyarta jikinta yana karkarwa ganin babban cikinsu wani ƙato da shi ya ɗaga kakkaifar wuƙar ya kai saitin wuyanta yana mata wani muzurai da idanunsa jajaye.
"Ku wuce mu shiga ciki" Suka faɗa cikin tsawa daga Iya har mutumin nan basu da tsumi basu da dabara haka suka shige cikin gidan kowa an saka masa wuƙa a wuya.
"Lahaula wala ƙuwwata illa billahi aliyal azim,tabarakal lazi bi yadihil mulku wa huwa ala kulli shai'in ƙadir" Shi ne abin da Iya ta tsira da shi wajen ambata a zuciyarta ƙirjinta sai dakan lugude yake, tana jin wani taahin hankali marar misali dan tana ganin idan suka rabata da sarƙar nan tata wacce ta kwashe sama da shekaru tana ɓoyonta a ƙasan akwatin ƙarfe saboda irin wannan rana, to tana jin mutuwa ce kaɗai ba za ta yi ba dan baƙinciki.
"Allah ka cece ni in koma wurin sana'ar tsakiyata, kar mahaukatan ƴan shaye-shayen nan su burma mini wuƙa in shiga uku, a shegen son banza na na baro kayan da suke mallakina na zo wurin da za a jinyata ni ko akasheni ma gaba ɗaya" Cewar mutumin nan a zuciyarsa yana wani zare ido kamar wanda ya yi wa sarki ƙarya.
"Kai gaba ɗaya ku zubewa mutane a nan kuma ku fito da kayan kuɗin nan" Babban cikin nasu ya faɗa bayan sun shigar da su cikin ɗaki da yake ciki da falo ne sai suka ajiye su a falon.
"Ni dama ban santa ba kuma ban ga kayan kuɗin ba suna jikinta" Mutumin ya faɗa cikin karkarwar murya dan wannan karon wuƙar har taɓa wuyansa aka yi da ita.
"Innama amruhu iza arada shai'an an yaƙula lahu kun fa yakun" Iya ta faɗa a zuciyarta lokacin har hawaye sun yi wa fuskarta sallama, saboda irin yadda ta ji a zuciyarta da a ka ce ta fito da kayan kuɗi.
"Ba, ba, babu wani kayan kuɗi a jikina dama murtala biyu (40) Zan bashi ya siyowa yara goruba zan kai musu tsaraba" Iya ta faɗa bakinta yana karkarwa tana addu'a a ranta Allah sa su yarda da batun ta.
"Ah kin manta bishiyar ɗorawa za a siyowa yaran ba goruba ba" Ɗaya ya faɗa yana aika mata harara.
"Gaskiya nake faɗa muku babu...
"Idan ba za ta bayar ba ku farka cikinta sai ku ɗakko mana kayan kuɗi...
Tun kan ya ƙarasa aka ɗaga rigar Iya, Iya tan zare idanu jin an ce a farke mata ciki kuma ta ga babu alamun imani a tare da su.
"Ku yi wa iyayenku kar a farka ni kamar wata ledar tsakar ɗaki, dan Allah ku mini rai zan fito da kayan kuɗin, dama sarƙa ce da ɗankunne da abin hannu... Tun kan ta ƙarasa maganar suka fara yi wa junansu murmushi irin na mun yi babban kamun nan, babban nasu har wani gya kai ya yi, dan sun san ba zai wuce a ce sarƙar gwal bace tun da an ce kayan kuɗi kuma an ce sarƙar da ɗan kunne.
"Kai amma matar nan kin gama da ni ƙur'anin Allah kuwa ashe sarƙar gwal ce a jikin ki kika yi jinkirin faɗa ga shi wasu a banza a wofi za su je su mori kuɗin ni da kika sakawa a rai ina kallo" Mutumin nan ya faɗa a zuciyarsa har da hawayen takaici suna sarto masa.
"Fito da ita"
"To bawan Allah amma dan Allah ka cire mini wuƙar nan daga wuyana, haba mu ba ragunan layya ba amma an ɗora mana wuƙaƙe a wuya" Cewar Iya tana saka hannu a aljihun take ƙoƙarin fito da ledar sarƙar, tana fito da ita ta kasa miƙa masa dan ji take har ranta za a raba ta da abin da ta fi so, hannu ya kai ya warce a lokaci guda yana sakin wuƙar hannun nasa dan yana ganin kakar su ta yanke saƙa sun samu abin da za su daɗe suna mora, dan dama ƙwace da yankan aljihu ne ya kai su kasuwar shi ne sana'ar su.
Kurrrr kowa idanunsa kafe a kan ledar da yake kuncewa banda Iya da ta sunkuyar da kai ƙasa hawaye na kwaranya baƙinciki ya cika mata zuciya.
"Allah kar ka kamani da ƙin cikawa Jaburu alƙawari, wayyo ni zan saka marayan Allah ya shiga damuwa" Iya ta faɗa a ranta tana jin ɓacin rai.
"Ni da na ce a yau za a siyo masa arincaɓa(Adaidaita sahu) Amma ga shi zan koma babu kuɗi...
Babu wanda ya lura da Iya kowa idanunsa suna kan ledar musamman da suka ga an saka mata uban ledoji wata cikin wata mutumin nan ji yake da a ce yana da yadda zai yi da gaba ɗaya zai musu rubdugu ya bubbuge su har Iyar ya gudu da sarƙar amma babu hali. Sai da ya fitar da ledojin saura ɗaya wacce a ciki ne sarƙar take, hannunsa har karkarwa yake wajen fito da sarƙar yana zarowa mai za su gani, sai ga sarƙar murjani danƙwala-danƙwala, kowa sakin baki ya yi ganin abin da suka ɓata lokaci a kansa, guda ɗaya daga cikinsu ya fashe da dariya dan wallahi abin ya bashi dariya sosai ma yadda suka raja'a amma a ce a kan wani abin banza da wofi ne. Hatta mutumin nan sai da dariya ta so ƙwace masa amma sai ya damƙe bakinsa yake yin dariyar a zuciyarsa dan ba ƙaramin dariya abin ya bashi ba, a gefe ɗaya kuma ya yi farinciki da ba sarƙar gwal ɗin bace saboda yadda bai mora va su ma kar su mora.
"Buhun ubancan kayya! Ke tsohuwa mu za ki rainawa hankali ki yi wasa da tunaninmu a kan wannn abin?" Ya jefawa Iya tambayar yana jefa mata harara da jajayen ƙwala-ƙwalan idanunsa, sannan ya dakatar da ɗayan nan da yake dariyar dan shi mai maganar shi ne ogansu, a take kuwa ya haɗeye dariyar a inda mutumin wannan ma ya sake danne tashi dariyar saboda ya ga an tauna tsakuwa dan aya ta ji tsoro.
"Wallahi ba haka bane, dan Allah ku mini rai kayan maraya ne za a siya idan an siyar da sarƙar dan haka dan Allah na yarda kuma za ku samu kaso mai tsoka dan Allah kar ku raba ni da ita"
"Kai karɓi ƙazamin abin nan je ka saka shi a shadda (Toilet) Ka zuba ruwa ya wuce" Ogan ya faɗa yana cillawa ɗaya daga cikinsu, wani kukan kura Iya ta yi za ta ƙwato amma ya ɗaga mata wuƙa a take ta koma ta zauna tana sakin kuka mai cin rai.
"Ni da na hana nake cewa an raina mini hankali a baiwa ƴan gwangwan sai ga shi za a saka a masai (Toilet) " Ta faɗa a zuciyarta tana sakin kukan takaici. Suna nan ya dawo ya ce ya jefa har ya zuba ruwa sarƙar ta tafi.
"Gaskiya matar nan kin ci dubu sai ceto a kan wannan abin da yanzu babu mai siya ko da kobo ne kika rabo ni da wajen kayan sana'ata da nake yi cikin rufin asiri kika kawo ni cikin wannan masifa da ban san mai za a mini ba...
"Ku tattale mutumin nan ku masa shayi da sabuwar addar nan" Maganar babban cikin nasu ta katsewa mutumin nan zancen zucin da yake.
"Shayi fa ka ce ɗannan wallahi ɗan wanzan ya mini shayi tun ina ƙarami" Ya faɗa hankali tashe jin za a masa aika -aika.
"Kai ba shayi za a masa ba ku getse masa mafitsarar tun daga farkonta a cire ta duka ku saka mini a leda zan b karena"
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un ka yi mini rai dan Allah kar ku yi kisan kai" Ya faɗa yana rushewa da kuka, Iya duk da tana cikin alhinin jefar da sarƙarta amma kuma sai da murmushi ya suɓuce mata ganin yadda mutumin ya saka hannu biyu ya danne gaban wandonsa yana ciccira idanu.
"Zan dawo kan ki, ki daina gaigaye dan za ki ci tumo, mu duka nan sai mun yi watanda da tsufanki dan bana ce ƴanmatancinki ba dan yanzu kin tsufa" Idanu Iya ta zaro jin ɗanyen aikin da ya ce za su mata.
"Na shiga uku da tsufana za a mini fyaɗe yaran ƙanana dan jaraba Allah ka cece ni kar su keta mini haddi" Iya ta faɗa a ranta tana karanto lahaula.
Idanu ta runtse ganin an banƙare ƙafafun mutumin nan za a cire masa wando.
"Allah ka fishshe ni aikin da na sani, kar ka sa idanuna su yi mugun gani" Ta faɗa a ranta, mutumin kuwa ganin sun zamo masa wando ya shiga ƙoƙarin ƙwatar kansa, ɗayan ya mayar da hankalinsa wajen Iya biyun sun maida hankali wajen cire masa wandon ya dage ƙarfinsa ya datsa musu haƙora kowa a hannu suka sake shi suna sakin ihun azaba kafin su tantance ya zuba a guje ko da suka biyo bayansa har ya buɗe sakatar ya gudu haka suka dawo jijjiga hannu saboda azaba.
"Ku dai an yi sakarkaru wallahi ko biyu shi kaɗai kuna sabon jini shi kuwa da ya sha miya amma ya gudu"
"Taɓ dan ba kai ya datsawa haƙoran bane wallahi yadda ka san kacar keke haka muka ji zafin cizon" Suka faɗa suna kallonsa wani dogon tsaki ya ja.
"Wayyo ni Ansai yanzu sai ni kaɗai babu mai ceto na Allah ka kawo mini ɗauki" Ta faɗa a ranta.
"Ku kinkime ta ku kai mana ita cikin ƙuryar ɗaki (Bed room) Yau sai ta faɗawa aya zaƙinta sai mun mata fata-fata za ta san mu ta rainawa hankali" Iya tana ji tana gani mutum biyun suka mata cali-cali kamar wata igiya, aka shige da ita ɗakin da babu komai sai kayan wankin su, ban da wari babu abin da kayan suke, a haka suka ɗora ta a kan tulin kayan wankin. Suna ajiye ta suka fito falon, hannu Iya ta saka a lajihun ɗan tofinta ta ɗakko abu ta damƙe a hannunta.
"Ni zan fara shiga idan na fito ku ma sai ɗaya ya shiga ya fito ya ba ɗayan" Yana faɗa ya shige ba tare da ya jira cewar su ba ya shige
"Haba ɗan nan ka ji tsoron Allah mana kai kuwa tsohuwar Allah ta'ala amma ku haike mini da tsufana da komai" Iya ta faɗa cikin karkarta kai ko Allah zai sa su ƙyaleta.
"Ke tsohuwa ruwan kashe gobara ba sai mai kyau ba" Ya faɗa yana zare wando, fakar idanunsa Iya ta yi ta ɗago allurar da take jikin sirinji.
"Allah sarki Jaburu wawtarka ta mini rana yau, kai da na aika ka siyo mini allura wacce ake sakawa a zarw ka siyo mini allura da sirinji na saka a ɗan tofina yau ga shi za ta mini amfani ta mini rana" Ta faɗa a ranta tana ɗagowa ta shammace sa ta riƙe ƙasan sirinjin ta daɓa masa a cinya,a take ya zaro idanu cikin azabar da ya kasa yin ihu zubewa ya yi a wajen a ƙasa yana faman zare idanu. Hannu Iya ta saka ta zare sirinjin da yake haɗe da aluurar dan har allurar ta nitse a jikin cinyar ta bar shi yana murƙususun azaba, a hankali ta lallaɓo ta leƙo falon hango su ta fi suna cire nasu wandunan sun bata baya sai dai kowanne yana gefe guda. Da sanɗa ta fito ta ɗaga sirinjin nan mai allura ta daɓawa ɗayan a gefen mazaunai guda ɗaya ta zare ta ƙara sukuna masa da ƙarfi a ɗaya ɓarin mazaunan a take ya dare ido sai ga shi ya zube a ƙasa hannu biyu dafe da mazaunan. Ɗaya ya yi nisa wajen gyara belt ɗin wandon nasa da yake wandon ya zo masa cinya sai dai bai gama cirewa ba sai belt ɗin ta sarƙafe, shi ma bai ankara ba ya ji cakuwar wani abu mai kama da mashi, yana shirin yin ihu ya ƙara jin a soka masa a ɗaya ɓarin.
"Ihu an kawo mana farmaki maƙiya sun kawo hari a yi hanzarin yin shirin yaƙi sun fara sakin mashi ko ta ina duk sun soke mini mazaunai" Ya faɗa da ƙarfi yana sakin ihu ya zube a ƙasa Iya kuwa ko zare masa bata yi ba ta fice da gudu takalmin ma ƙafa ɗaya ta ɗauka. Ficewa ta yi a gigice da yake ƙofar gidan an ɗan yi wurin alamar shigowa da machine ba tare da ta lura ba ta taka aikuwa suuuu ta tafi ta je a zaune da haka ta rarrrafa ta bar ƙofar gidan amma dan ƙarfin hali har lokacin ledar vivar tana hannunta. Gaba ɗaya ƙugunta ya bugu ƙafafunta kamar ba a jikinta ba suke dan ba ƙaramar faɗuwa ta yi ba dan haka sai ta zauna a wajen wata bishiya tana jiran ƙugun nata ya lafa ta tafi. Wani mutumi ya zo wucewa da rogo dafaffe a leda fara da ya ganta zaune da leda a hannu sai ya ɗauka almajira ce dan haka ya karɓi ledar ya saka mata rogon a matsayin sadaka Iya bata iya ce masa komai ba. Tana nan zaune da yake la'asar lis lokacin dan haka hango wani mai baro yana cewa.
"Dako, ina wanda za a masa dakon kaya muna ɗaukan kaya zuwa tashar mota ko zuwa gida"
"Kai bawan Allah zo ga dako" Da sauri ya nufo ta yana zuwa ya saki baki ganin bai fa ko da ƙullin kaya bane a wajen nata.
"Tsohuwa ya ban ga kayan dakon ba"
"Ɗan nan ni za ka ɗauka a baron taka, ni za ka yi dakon"
"Haba Baba ɗan musulmi da rangwame aka san shi yo ina zan yi dakon ki to ma wa zai saka ki a baron kin zauna daɓas a waje guda.
"Ka saka ni a baron zan biya har kuɗin ɗaukan nawa wallahi hantsilowa na yi to kwankwason nawa ne kamar ba a jikina ba" Jin haka sai ya kinkimi Iya ya saka a baro tana ta ƙorafin ya saka ta da ƙarfi kamar ya jefa buhun goruba, shi dai bai amsa mata ba ya tambaye ta inda zai kai ta ta faɗa ya tura baron suka fara tafiya, ita ba a kwance ba ita ba a kishingiɗe ba ƙafagun nan nata sun yi sama su kake hangowa.
.
Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay
TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃
Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada.
Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi.
Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa.
Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰
Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari.
Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851
[12/23, 15:51] Mom mashkur & Afrah: https://www.youtube.com/@MAMANAFRAHNOVEL
ƳAN ADAIDAITA SAHU
(Masu keke napep)
NA
MAMAN AFRAH
GARAƁASA💃💃💃💃💃
Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.
ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳
kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu.
a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳
Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA.
09013181851
Ga link nan na chanel ɗin duk wanda ya yi SUBSCRIBE ɗin ya tura mn screen shrt PC.
Page 4️⃣
Jabiru haka ya wuni babu abin da ya ci yana jiran dawowar Iya ta kawo tsire da balangu da lemon kwalba su yi wankin ciki, ga shi ya kasa zaune ya kasa tsaye tun da ta ce a yau za a siya masa Adaidaita sahu. Bayan kaf ƙauyen nasu ma babu adaidaita sahun amma saboda ɗora rai da kuma sangarcin da Iya ta masa shi ne za a siya masa, tun yana saka ran dawowarta har ya fara fusata ga shi kuma yunwa tana ƙwaƙularsa amma ya ƙi cin komai. Waje ya fito yana kallon hanya, daga can gefe