Showing 1 words to 3000 words out of 60716 words

Chapter 1 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt

27 Dec 2024

3528

[12/23, 15:51] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/EuFGI1TIgdlAhVJXP2XqPJ




*ƳAN ADAIDATA SAHU*
(Masu keken napep)






NA






MAMAN AFRAH




*ASSALAMU ALAIKUM*




Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.


ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳


kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu.


a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳


Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA.


Ga no ta ku tura mn screen shrt domin samun shiga paid grp da zarar free pages sun kare


09013181851






Page 1️⃣➡️2️⃣








BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Kwance take a saman gadonta ta takarkare sai sakin munshari take hankali kwance, daga can gefe jikanta ne Jabiru ɗan kimanin shekara sha takwas yana kwance a tsakar ɗakin a kan katifarsa. Idanunsa biyu dama yana jiran Iya Ansai ta yi nisa a cikin baccinta dan ya fara mafarkin ƙarya babu ɓata lokaci ya buɗe baki ya ce.


"Ina za a kai ku ne Hajiya? Kuɗinki naira ɗari bakwai ne" Haka yake ta faman maimaitawa, tun Iya tana jin abin cikin bacci har dai ta tashi ta wartsake. Jin alamun tashinta sai Jabiru ya ƙara kaimi wajen faɗin abin da yake faɗa wannan karon har yana ƙarawa da faɗin.


"Ku hau zan ɗan sha mai a wancan gidan man sai mu tafi"


"Allahu akbar kabiran, ni dai Ansai ina neman kai kaina wuta wallahi, ina zan kai girman zunubin cin amanar yaro maraya, na kasa cika masa burinsa na siyan arincaɓa (Adaidata sahu). Ni yanzu bani da komai da zan siyar na siyawa yaron nan arincaɓa ga shi son abin yana shiga ransa har cikin baccinsa mafarkin abin nan yake" Ta faɗa a fili tana share hawaye. Duka abin da take Jabiru yana jin ta kuma yana ganinta ta hasken farin watan da ya shigo ɗakin. Fitila ta kunna ta sakko daga kan gadon har lokacin tana kuka tare da jan hanci, ta nufi wajen akwatin ƙarfenta ta buɗe ta zauna zaman dirshan a gaban akwatin ta shiga ɗaga atamfofinta da suke a linke, a can ƙasan ta ɗakko wata leda sai da ta dakata ta waiwaya alamar kar ko wani yana kallonta, ganin dai babu alamar mutum kuma Jabiru har lokacin yana ta maganganu shi a dole mai mafarki.


Ledar ta kunce sai ga wata ledar a ciki haka ta shiga kukkuncewa har dai ta kai ledar ƙarshe a ƙalla sai da ta since lodoji takwas sannan ta fito da abin. Irin danƙwala-danƙwalan sarƙar tsakiyar nan ce irin ta mutanen da, sarƙa da ɗankunne da kuma abin hannu masu duwatsu rafka-rafka. Ɗaɗɗagawa ta shiga yi a fili ta ce


"Ko a ina zan samu masu siyan waɗannan? Yanzu lalacewar zamani ta zo har an daina saka murjani, lokacin zamanin da, da a wancan lokacin ne na siyar da sarƙar nan ya isa in siyawa yaron nan arincaɓa in fita haƙƙin maraicinsa dan bana son abin da za a ce Jaburu (Jabiru) Ya yi maraicin uwa ni ce nan uwarsa ni ce ubansa, dan ubansa da shi da babu duk uwar ubansu ɗaya ba kula yake yi da shi ba ni kuwa sai Allah ya saka mini so da ƙaunarsa fiye da ƴaƴan nawa ma, amma dai kyakkyawan zato ina ga ma sarƙar nan tafi zinare daraja" Ta faɗa tana mayar da kayan. sarƙar tata ta mayar cikin ledojin nan haka ta saka su a leda cikin leda, ta rufe akwatin ƙarfen ta tashi ta koma ta zauna a bakin gadon hannunta riƙe da ledar da fitilar tocilan ɗin nata.


"Da safe sai Umaru ya nemo inda zai siyar da sarƙar nan, ya kawo kuɗin nan a siyawa yaron nan arincaɓa wallahi ba zan zauna in mutu Allah ya ƙona ni ba, ya kama ni da cin haƙƙin maraicin ɗan nan, ni kaina na san darajar sarƙar nan ta fi ta daham(Gold) Yo sarƙar da tun ta armena(Aure) Amma har yanzu gata nan kamar sabuwa dal, dan haka ina ga idan aka siyar har sai an samu sauran kuɗi wataƙila ma sauran kuɗin ya isa a siya masa fege(Fili) A masa gini a sama masa mata ya yi aure tun da shi ma na ga shegiyar jaraba ce da shi" Ta faɗa tana ɗaga filo ta saka ledar sannan ta sauka daga kan gadon ta je wajen katifar Jabiru ta shiga ɗan bubbuga shi a hankali. Miƙa ya yi tare da matso hawaye ya tashi zaune.


"Sannu ka ji Jaburu, wannan aboki naka da ya baka labarin arincaɓar nan da ake tuƙawa a binni ana samun kuɗi, sannan ya nuna maka hoton ta wallahi ya ɗau alhakin ka ya shiga haƙƙina, haka kawai ya hana mana zaman lafiya da yin bacci cikin kwanciyar hankali" Ta faɗa tana rushewa da kuka irin na tsoffi.


"Ki yi haƙuri Iya Ansai tun da na yi ido biyu da Adaidata sahun n...


"Jaburu ina faɗa maka wallahi ka guji yin saɓo, tun ba yau ba nake raba ka da kiwon kyallu amma kana cewa kyallu ta haihu, in banda kuna son kuke yin saɓo ina ka taɓa gani an ce "sahu" Idan ba sahun sallah ba haka kawai ka guji fushin Allah a kan ka tam ni dai babu ruwana bana ciki"


"Haba Iya Ansai wai sai yaushe za ki fahimta ne"


"Sai ranar da ubanka ya fahimta" Ta faɗa cike da faɗa. Kafin ta ɗora da maganar ya saki kuka irin na sangarta.


"Ash-sha ai ka ji irinta kai kuma baka san wasa ba haba Jaburu ya za a yi na ɓata maka rai dan Allah da manzonsa ka gafarce ni, kar ka saka wutar Allah ta ci ni a kan ɓatawa marayan Allah rai" Ta faɗa tana roƙonsa har da ajiye fitilar hannunta ta haɗe hannayenta kamar wanda aka ce ta masa wani gagarumin laifi.




"Zan yafe miki amma gaskiya ni sai kin san yadda za a yi a saya mini, kin ga ni ba sana'a nake ba, amma in kina ganin ba za a saya mini ba sai in haƙura dama ai in kana maraya sai dai ka ga masu uwa suna samun ab...


",Haba dan Allah Jaburu ai kai ba maraya bane uwa ce kawai ka rasa amma ni ai ni ce uwarka ni ce ubanka, kuma tun da har ka ce za ka yi sana'ar arincaɓan nan ai dama babu maraya sai rago, na maka alƙawarin a gobe ba sai jibi ba za a siyo maka shi sabo fifil a ledarsa dan na ɗakko kadarata wacce take ajiye shekara da shekaru wacce darajarta ta fi ta daham(Gold) Ita za a ɗaga a siyar a siya maka dan ni a kan son da nake maka hatta kaina zan iya yankewa in baka bare abin duniya ai na haƙura da murjanin nan nawa" Ta ta fsana dafa kansa, wani shu'umin murmushi ya saki a ransa yana jin daɗin tarkonsa ya kama tsuntsu dan dama ya san arina wai an saci zanin mahaukaciya, ya san dama dole duk runtsi sai Iya Ansai ta saka an siya masa Adaidata sahun.


"Allah ya saka ki a aljanna Iya Ansai ki sha jar miya da naman kaza"


"Amin, amin ɗan nan, ai addu'ar nan da kake minj kaɗai ma ta isheni tun da na kyauttawa maraya, ai mJaburu da ranka ya ɓaci gwara ko tafiya tsirara ne in yi dan cikar burinka" Ta faɗa tana ɗan darawa ta ɗauki fitilarta ta koma ta hau gadonta shi ma ya kwanta.


"Ai sai ka juya ka sha baccinka mu jira wayewar gari"


"Yanzu kuwa Iya Ansai tawa ta kaina gaki ga ni a aljanna"


"Kai amin Jaburu da na ji daɗi wallahi" Ta faɗa tana ɗan matse ƙwalla ta koma ta kwanta bacci ya yi awon gaba da su.


*DA ASUBA*

Da faɗuwar gaba Iya Ansai ta falka, saboda tinowa da ta yi ta fito da ajiyarta ta kadararta ta ajiye a ƙasan filo tsoronta ɗaya kar ko an shigo tana bacci an yi awon gaba da sarƙar, da yake lokacin da ta buɗe idanunta ta kai hannu ta kunna fitilarta sai ta ganta a can gefe ɗaya filon da ta saka sarƙar a ƙasansa ta ƙaƙume shi, shi ma yana can da ban. Hakan ya sanya ta yi tunanin ko ɓarawo ya shigo.


"La'ilaha ilallahu muhammadur rasulullahi S.A.W" Ta shiga rafka salati a zuciyarta gabanta yana tsanata faɗuwa tana ɗaga filon.


"Na shiga talatin da tara ni Ansai ɗiyar mai siyar da allo jikar mai siyar da tawada, idan aka ɗauke sarƙar nan ta murjani nan mai tsawon tarihi an taƙaita ni an sace dukiya mai ɗinbin yawa, ya zan yi da alƙawarin da na yi wa marayan nan jiya cikin sulusin dare?" Ta faɗa a ranta hawaye suna ambaliya ta wurgar da filon a can gefe tana lalumawa ashe zanin gadon ne ya rufe ledar shi ya sa bata ganta ba. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ƙwarara guda uku.


"Allah ya taimake ni, da ina zan kai nauyin alƙawarin da na yi wa marayan nan, ai da na ɗau alhakinsa, ai kuwa da wanda ya ɗau sarƙar nan sai na saka an gewaya laya dan ɗinbin dukiyar nan ba za ta tafi a banza ba" Ta faɗa tana sako ƙafafunta ƙasa ta sakko sai da ta waiwaya ta tabbatar babu kowa kuma Jabiru yana ta munshari sannan ta ɗaga zaninta ta saka a cikin aljihun ɗan tofinta(Siket na tsofaffi da suke sakawa a cikin zani).




"Ina yin sallah zan kirawo yaran nan mu zauna ai gwara ni in siyar da kadarata in siya masa ina raye ba zan bari ya yi maraici ba" Ta faɗa tana nannaga zip ɗin ɗan tofin sai da ta tabbatar ya zigu sannan ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita. Alwala ta ɗauro lokacin duk an shiga masallaci, da yake bayin nata a ɓangarenta yake dan haka babu ruwanta da zuwa can tsakar gidan bayan ta gama alwalar ta dawo ɗakin tana kiran sunan Jabiru.


"Kai Jaburu ni ina dalilin wannan bacci naka kai kullum baka zuwa sallar asubahi sai dai idan rana ta fito katakau ka zo kana sallah da ƙadangaru, yo sallah da ƙadangaru mana kana kai sujada ƙadangare ma yana gyaɗa kai ai shi ma lokacin ne yake sallah" Ta faɗa tana nufar shimfiɗar tasa ta shiga bubbuga shi amma ko gezau bai yi ba baki ta taɓe ta yi gaba


",Wallahi ba zan biye maka ba, haka kawai kai baka yi sallar ba ni ma in je ban yi ba lokaci ya ƙure a yi ba wan ba ƙanin wato babun baɗinuhu" Ta faɗa tana shimfiɗa sallayar ta kabbara sallar. Har ta idar da sallar amma Jabiru yana ta munshari. Bayan ta shafa addu'ar ta jiyo ƙaran ƙofar gida alamun dawowar ƴaƴan nata daga masallaci, tashi tsaye ta yi ta fito daga ɗakin nata ta taho tsakar gidan lokacin su duka kowa ya shige ɗakin matarsa.


"Mamman( Muhammad ne ake kiransa da Mamman) Umaru!" Ta shiga ƙwalla musu wani kira mai kamar babu lafiya. Shiru kake ji tsakar gidan babu kowa sai muryarta da take ta faman rafka musu kira. Baba Mamman ne ya fara fitowa daga ɗakin matarsa, sai Baba Umaru ma ya fito da sauri yana gyara zaman hularsa.


"Oh Allah na tuba waɗannan yara da jarabar son mata kuke wallahi, a ce ku bakwa rabuwa da ɗakin mata yo ina dalilin an kwana ana abu ɗaya da safe ma a ɗora sai ka ce jaraba, maimakon ku tafi turakar ku amma sai ku ƙare a bibiyar ɗakin mata dan jaraba kowanne ya kama mace ɗaya kamar rai kun kasa ƙara aure su ba haihuwa suke yi ba sai cikawa mutane masai da kashi(Toilet) Ai dama wajenku Jabiru ya yi gadon jarabar nan dole ma idan an siya masa arincaɓar nan sauran kuɗin a gina masa gida a masa aure kar ma a zo yake lalume ƴaƴan mutane a lungu ake A'i ina indo" Ta faɗa a ranta tana bin ƴaƴan nata da kallo da suka zo cike da girmamawa.


"Gamu Iya" Kowanne ya faɗa yana ɗan sunkuyar da kai saboda kunyar da ta lulluɓe su dan sun san halin Iya yanzu sai ta ce sun je sun maƙalewa matansu.


"Yo kwa zo ku tsaya mini getse-getse, kamar bishiyar dalbejiya, kuna sunkuyar da kai kamar mararsa gaskiya, ku wuce muje ɗakina maganar sirri nake so mu yi tun da yanzu gari ya fara haske kafin kowa ya fito tsakar gida, a mana laɓe a ji abin da za mu tattauna, yo kar a samu wani ya ji wannan babban batu a je a bini har gadon baccina a maƙure ni da filo saboda son dukiya" Ta faɗa bayan ta rage murya kamar mai raɗa sai wani dogon wuya take tana kallon ɗakunan matan ƴaƴan mata gudun kar wani yaji mai take cewa.




Duk da sun san halin mahaifiyar tasu amma sai da mamaki ya mamaye musu zuciya, sai dai babu wanda ya isa ya tambayi dalili, dan haka umarni kawai suka bi Baba Mamman ne ya fara yin gaba cikin ɗan sauri-sauri dan ya je ya tashi Jabiru ya yi sallah saboda basu da wani kataɓus Iya ta hana a tashe shi zuwa masallaci wai har yanzu yaro ne, kuma kar a shiga haƙƙin marayan Allah a tashe shi daga bacci a ɗauki alhakinsa har sun yi sun gaji sun ƙyale. Yana shiga ya ɗaɗa masa duka da sauri ya tashi yana muzurai da murza baya.


"Wuce ka je ka yi sallah sakaran banza da wofi kuma saura in ji ka ce wa Iya ni na tasheka" Ya faɗa yana aika masa wata uwar harara. Tashi ya yi yana gyaɗa kai kamar ƙadangare yana shirin fita daga ɗakin sai ga Iya ta kawo kai Baba Umaru yana biye da bayanta.


"To Jaburu har ka falka da sassafen nan garin ko gama wartsakewa bai yi ba?" Ta faɗa tana tsare shi da idanu.


"Eh ai dama tun fitarki na motsa" Ya faɗa yana ratsewa ya fice ita kuma ta taɓe baki ta shiga ɗakin.


"Kai Mamman kar dai a ce kai ka katsewa marayan nan baccinsa, wallahi Mamman ka kiyayi fushin ubangiji a kan ka idan kana shiga haƙƙin maraicin yaron nan"


"Haba Iya ni ma da na shigo zaune na same shi a kan katifarsa"


"Ayyo ko da na ji" Ta faɗa tana samun wuri ta zauna daga can gefe shi ma Baba Mamman ɗin dama a zaune yake.


"Umaru, Umaru, wai ina kake ne kai kamar ba ɗakin uwarka ba sai ka raɓe a jikin bango kamar wani ƙadangare" Ta faɗa cikin ɗaga murya ganin Baba Umaru bai shigo ɗakin ba. Baba Umaru kuwa ya tsaya ne a wajen yana yi wa Jabiru faɗan ƙin zuwa masallaci yana faɗa masa duk ranar da ya mutu Iya ba za ta je kabari ta cece shi a kan azabar da za a masa ta wasa da sallah ba. Yana cikin faɗan ya ji ta kira shi da sauri ya shiga bakinsa ɗauke da sallama ya samu wuri ya zauna.


"Uhm Bismillahi bari in tashi in saka mana labule rufin asirin ɗaki" Ta faɗa tana tashi tinƙis-tinƙis ta nufi ƙofar su dai da ido suka bi mahaifiyar ta su suna mamakin tarasun da ta yi da farar safiyar nan. Bayan ma ta saka labulen sai da ta garƙame ƙofar ta saka sakata, da kallo suka bi junansu kowanne yana raya cewa abin babba ne tun da har da su rufe ƙofa tamkar za a yi wani munfurci, bayan da safen nan babu kowa ma bare ta ce wani zai shigo.


"Ai shi batun dukiya abu ne na sirru(Sirri) Komai yana son a yi cikin hikima asiri a rufe" Ta faɗa lokacin da ta dawo ta zauna.




Babu wanda ya tanka illa iyaka kowanne mamaki ya kashe masa baki jin ta ambaci dukiya.


"Umaru maza fita ka ɗakko tocilan ɗin nan taka mai cin batira shida, na ga jiya ka mata sabon zubin sabbin batira"


"Iya mai kuma za a yi da fitila bayan gari ya waye tangararai?"


"Au Allah Umaru idanu ka fini da har kake cewa gari ya waye yo ai na san da garin ya waye amma na ce ka ɗakko ai tun da ka ji haka akwai magana kuma akwai amfanin da za a yi da ita a wannan zama namu, sannan idan ka ɗakko fitilar ka kalli gabas da kudu yamma da arewa ka tabbatar babu wani wanda ya ganka" Ta faɗa cikin halin ko in kula. Baba Umaru kallon Baba Mamman ya yi sai Baba Mamman ɗin ya gyaɗa mas kai alamar ya bi umarnint, tashi ya yi yana cewa


"To Iya"


"Au Allah, to wallahi Umaru ka fita idona in rufe, kana neman shigar mini hanci da ƙudundune yanzu har ni in yi magana saboda ka raina ni sai ka kalli Mamman ya gyaɗa maka kai, kamar ƙadangaruwa"


"Allah ya huci zuciyarki Iya ba haka bane" Ya faɗa yana tashi ya buɗe ƙofar ya fita jin kaɗan sai ga shi ya dawo riƙe da fitilar.


"Mayar da ƙofar nan ka rufe ruɓuk bana son tonom silili" Bai ce komai ba ya rufe ƙofar ya saka sakatar dan dai a zauna lafiya sai dai su duka suna mamakin abin da za a yi da fitila bayan gari ya waye kuma ma abin wai har da rufe ƙofa da saka sakata.


"Ka tabbatar babu wanda ya ganka ko Umaru?" Ta tambaye shi daidai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login