Showing 33001 words to 36000 words out of 60716 words

Chapter 12 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt

27 Dec 2024

3530

akuya ba za a kai makaranta in saniya za a saka a cikin aji (Class) Sai ka yi da gaske yau za ka kuɓuta" Iya ta faɗa a zuciyarta tana da na sanin ɗakko tsohon nan da suka yi ga shi silar haka sun haɗu da jafa'in da basu san ranar fita daga ciki ba. Jabiru bai ankara ba sai jin jelar ta yi ta sauka a kan laɓɓan bakinsa lamarin da ya ƙara dagula masa lissafi. Cikin lallaɓawa ya samu shi ma ya zauna daga saitin gefen kakar tasa ya riƙo ɗaya ƙafar tsohon ta hagu da hannu biyu kamar yadda ya ga Iyar ta yi.


"Dama ƴan magana sun ce duk wanda ya samu rana sai ya yi shanya, wato shi ma wannan tsohon mai mazaunai kamar na tsatstsewala dan ya ga muna neman taimakonsa amma ya yi biris tare da yin kunnen uwar shegu" Iya ta faɗa a zuciyarta.


"Iya tun da ke kin kwana biyu ana murmurawa a duniyar ki saka hannu ki ɗaukewa marayan Allah miciji daga wuyansa, kin ga ni ɗan yaro ne"


"Au Allah, to ba murmurawa ba ko gurgurawa aka yi ba zan kashe kaina a kan ka ba da kake maganar yaro ai ko mahaifa ƙarewa" Ta faɗa cikin muryar kuka.


"Malam Tukur ka yi wa iyayenka ka cecemu daga wannan halin" Duka haɗa baki wajen faɗa. Kafin su rufe bakin su sai suka nemi micijin sama da ƙasa suka rasa kallon kallo aka shiga tsakanin jika da kakarsa. Amma kuma mai a take muryar da ta ziyar ce su damuwa ɗimuwa da tashin hankali ya maye gurbinta domin kuwa Malam Tukur ne ya koma tattabara, daga Iya har Jabiru sai ga su riƙe da ƙafar tattabara a maimakon ƙafar Malam Tukur da suka riƙe da hannu.




"Mun shiga uku ni Ansai kenan dama ba da bil adama ba muke tare ba, lallai yau mun ɗakko ruwan dafa kanmu" Cewar Iya a zuciyarta tana son ta yi ƙarfin ɗauke hannuwanra dafa riƙon ƙafar tattabarar amma ta kasa samun ƙardun gwiwar hakan daga ilahirin jikinta domin kuwa jikinta karkarwa yake kamar mazari.


"Wal fauru da gaggautawa fararun farilla ne, fasalun fiɗ ɗaharati fasali a kan tsarki" Iya ta faɗa a zuciyarta wajen ƙoƙarin ganin ta samu kamo addu'a domin tsira daga sharrin jinni tun da dai ga shi sun gani gamo suka yi.


"Innalillahi mun yi angamo ni Jabiru ashe aljani ne" Ya faɗa a zuciyarsa lokaci guda gumi yana baibaye shi saboda yanzu wani sabon tashin hankali ya tsinci kansa wanda ya fi na lokacin da ya ga miciji a wuyansa saboda miciji har gwara shi idan ya sare ka to wani lokacin in aka maka magani kana samun salama amma su mutanen ɓoye su suke ganinmu ba mu muke ganinsu ba, idan ka shiga gonarsu sai su yi ta bibiya tare da addabar rayuwarka.


Kuka gaba ɗayansu suke yi daga Iyar har Jabirun babu mai lallashin wani dan sai yanzu ne ma da suka yi ƙoƙarin janye hannayensu sai suka ji hannayen tamkar an haɗa sufagilu an damƙare ko alamar fita baya yi tamkar tif da taya. Kuka suke da magiya da neman ɗauki dan ita tattabarar ko motsi bata yi ba illa idanu da take ƙiftawa tana ɗan waige-waige da kanta.


"Wayyo ni Ansai wallahi na yi da na sanin zuwa binni ba dan kuɗin Alhaji Audi da na ciyo bashin jinginar gona ba da a yau ba sai gobe ba za mu koma ƙauyenmu tun da abin ya fara da angamo da aljannu" Cewar Iya a zuciyarta tana yi wa tattabarar ƙuri da ido dan idan har ba gizo idanunta suke mata ba sai ta ga ma tattabarar kamar murmushi take yi tana haɗawa da harara har da fari da idanu.


"Iya kuka fa tattabarar nan take kalli yadda hawaye suke zuba a idanunta kuma wallahi ni har ƙaran sheshshekar kukan nake ji" Jabiru ya faɗa cike da tashin hankali.


"Kai Jabiru ittaƙillaha ka ji tsoron Allah, ina ganin abin da idona tana murmushi da harara har sa fari da ido amma ka ce kuka take"


"Wallahi Iya kenan abin da kike gani da ban wanda nake gani da ban mun shiga uku mu kam" Iya dai bata ƙara samun bakin magana ba illa iyaka ta cigaba da rattabo duk addu'ar da ta zo bakinta.


"What is your name" Suka tsinkayi magana daga bakin tattabarar" Iya ce ta juya ta kalli Jabiru, shi ma Jabiru juyawar ya yi ya kalleta, a take fitsarin da ya cika marar Jabiru tun lokacin da maciji yake wuyansa ya samu nasarar zubowa tsuuuu, Iya kuma tun lokacin da Malam Tukur ya rikiɗa ya zama tattabara wata iska ta taru ta cika mata ciki sai dai tana dannewa ne dan bata son ta saki tusar ya zamana ta yi laifi sai dai maganar da tattabarar ta yi ya sanya ta saki iskar tusar kaɗan ba da yawa ba ƙwiiiii tusar ta bada ƴar ƙara kaɗan tamkar an hura matse ƙaramar balo an sace ta kaɗan.


"I say what is your name?" Tattabarar ta maimaita bakinta yana buɗewa alamar maganar kamar mutum.


"Wallahi tallahi, billahil lazi huwar rahmanu babu abin da na sani a yaren nasara, ko bihim ban sani ba, kuma shi ma Jaburu bigibagiro ne babu abin da ya sani duk girman kan nan nashi da kike gani kan kwakwa ne babu karatu ko na allo bare na firimari(Primary) A mahammadiyar babu abin da ya sani a bokoko a wutar ma kan fanko ne haka nan yake sinkin fakitin" Iya ta faɗa hawaye yana ta zuba dan ta san tabbas rashin iya amsar da ake musu magana zai iya zama wata gagarumar matsala.


"Maa is'muki? (Ya sunanki) Ta faɗa da larabci ba tare da ta fassara ba"


"Iyi? Na'am, wallahi babu almuski a wajena kin ga ko madarar turare ƴar ɗure ban shafa ba da yake ma tafiyar babu shiri muka taho jiya" Iya da take ganin ta bada amsa ta faɗa tana haɗiyar yawu dakyar.


"Min aina anta?( Daga ina kake? )" Ta faɗa lokacin da ta juya kai saitin Jabiru da ya fara ciccira idanu dan gaba ɗaya ma ya tsure bai san ya aka yi ita Iyar ta bada amsa ba ga shi babu damar ya ce ta fassara masa bai san cewa ita ma dukan iska bace cafar amsar ta yi ba wai ta amsa daidai bane.


"Ka bada amsa dan ubanka kana ji ana tambayarka an maka shayi(Kaciya)" Iya da bata san ya aka yi maganar ta fito daga bakinta ba sai dai ta san cewar tsabar son Jabiru ne ya sanya ta faɗin hakan dan bata so a cutar da shi kuma dai ta san bai san amsar ba.


"An mini shayi wallahi Mammadu wanzam ne ma ya mini da askarsa mai kaifi" Ya faɗa yana zare idanu da sauke wata ajiyar zuciya irin na sha dakyar ɗin nan.






Kamar almara ko kuma a mafarki haka Iya da Jabiru suka ji hannayensu sun ɓanɓaru daga jikin tattabara. Iya Ansai ajiyar zuciya ta sauke mai lasisi dan ta ɗauka amsar da suka bayar ce ta cecesu hakan ya sanya ta ji kanta ya yi ɗingirigim.


"Kai jama'a na ga annabi in na yi hali na gari, ashe dai ina jin yare da yawa ba tare da na sani ba, wallahi duk a tunanina ban da Hausa ta malam bahaushe kan nawa ba ya ja a kan komai ashe dai ni ma har ina jin da ban? Da farko na ɗauka bami nake amsawa ba sai da na amsawa Jaburu, ai yau Jaburu ya ƙara sanin amfanina tun da ga shi har wasu yaruka na yi wa mutanen ɓoye" Ta faɗa a ranta lokacin tana ƙiftawa Jabiru idanu alamar su ari na kare wato su gudu. Gira ya ɗaga mata alamar gamsuwa dan haka ganin tattabarar ta juya kai daga kallon su sai suka fara sanɗa domin ficewa daga kangon da suka kawo Malam Tukur su masa ƙwacen kuɗi sai kuma ga shi ido ya juye da mujiya. Jabiru ne ya fara tashi tsaye ita ma Iya ta lallaɓa ta miƙe za su gudu da yake Jabiru ne a hanyar da za ta fita da su to kuma shi ne a gaba. Sun juya kenan tattabarar ta juyo ganin abin da suke ta ɗaga ƙafa ɗaya ta sauke a bayan Iya, Iya da ke shirin aron na kare sai ta ji saukar wani abu a bayanta kamar ƙaya da wutsiyar ido ta kalla sai kuwa ta yi ara da tattabarar ta yi reran ta ɗaga ƙafa ɗaya daga hakan Iya ta fahimci ƙafar tattabarar ce a bayanta.


"Na shigesu ni Ansai Jaburu yau kam za ka ga duniya rawar ƴan mata na gaba ya koma baya, dan yanzu zan maido da kai baya ni in koma gaba sai a yi a zubda yaran gona gutsi-gutsi su yi kuka, dan na ga kai akwai ya babu ne kakar wajen uba kana namiji amma sai dai ni tsohuwa in taimaka maka" Cewar Iya a zuciyarta. Jabiru ma kamar an ce ya waiga ya ga abin da tattabara ta yi wa Iya dan haka a raya a ransa cewar ba ,a a yi biyu babu ba gwara shi ya gudu dan da muguwar rawa gwara ƙin takawa, dan ma kar a yi ba wan ba ƙanin karatun ɗan koli.


"Dama ni na san da wuya tsohon nan ya barmu mu tafi salin alin domin in maye ya manta uwar ɗa a zai yu ta manta ba.


"Jaburu yau dai mun yj bonono rufe ƙofa da ɓarawo" Iya ta raya a ranta tana jin tashin hankali su da ba kowa gare su ba a garin amma sun jawowa kan su jangwam.


"Tabbas akwai sauran rina a kaba, Iya sai haƙuri" Ya faɗa yana ɗaga ƙafa zai gudu dan ba zai tsaya shi ma a ɗora masa ƙafar ba. Iya ma nata ƙafafun ta ɗaga a nata tunanin su gudu tare amma ina tana motsawa tattabarar ta sauke ƙafar daga bayanta ta taɗe mata ƙafafu rigif Iya ta zube a ƙasa tamkar tsohon ginin da damuna ta tarar. Idanu ta zaro tana daga rufda cikin.


"Wallahi Jaburu sai dai mu yi mutuwar kasko dan ba zan bari ka gudu ka barni ba" Ta faɗa tana saka hannu ta taɗo ƙafar Jabiru jif kake ji shi ma ya zube da azama ta miƙa hannuwa ta damƙo ƙafarsa ta riƙe gagam.


"Wayyo Allah mu kuma da haka muka fara kuturu ya ga mai ƙyasbi" Jabiru ya faɗa a zuciyarsa da duk tunaninsa tattabarar ce ta yi nasarar kama shi bai san cewa Iya Ansai bace ta rafke shi.








Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay


LITATTAFAN MARUBUCIYAR TAKU


RAYUWAR MARYAMU
GIDAN MIJINA
ƳAN UBANCI
ƳAR KANWATA
SANADIN KISHIYA NE
ALAKAR YARINTA
BEELAL
YAR ZAMAN WANKA
MAI FARAR KAFA
KARA'IN INNA DELU
JALLI JOGA
UNGOZOMA
ƳAN ADAIDAITA SAHU


TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃






Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada.


Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi.


Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa.


Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰


Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari.
Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851
[12/16, 14:00] Mom mashkur & Afrah: ƳAN ADAIDAITA SAHU
(Masu keken napep)




NA








MAMAN AFRAH



*Shin kin tura naki screen short ɗin na SUBSCRIBE domin yin tafiyar da ke? Free pages yana dab da karewa idan kuma 5OO za ki bada acc no yana jiki* 🥰




Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.


ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳


kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu.


a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳


Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA.


09013181851




Page9️⃣




Kafin ƙiftawa da bismillah sai ga Jabiru da Iya wanda duka basu san ya aka yi ba sun dai gan su zaune dakaka a gaban tattabarar tana miƙo musu baki, sun kasa gane inda abin ya dosa dan gaba ɗaya sun sare. Taku ɗaya biyu tattabarar ta yi ta juya musu baya Jabiru da har yanzu bai cire ƙudurinsa na tafiya ba dan ya ci alwashin sai ya gudu in dai ya samu hali, dan ya ga babu alamar za a musu lamuni su bar wurin dan babu niyya ango ya kwana da wando. Ganin tattabarar ta basu baya ya fara jan mazaunai a wurin a hankali dan sai da ya ɗan faki idanun Iya da take ɗan mammatse hawaye dan lokacin da suka gan su zaune gaban tattabara da su ma kan su basu san yadda aka yi suka zo wurin a zaune ba dan su duka suna a rufda ciki ne, ya ga hannun Iya riƙe da ƙafarsa ɗaya hakan ne ya bashi tabbacin cewa da ya yi yinƙurin guduwa ba tattabara bace ta damƙo ƙafarsa ba kakarsa ce dan bata son ya tsere ya barta shi kuma yanzu ya ɗaura aniyar barin wurin ko ta halin ƙaƙa tun da yana ganin shi har yanzu yaro ne sabon jini yana da sauran shekaru a gaba idan Allah ya sa da kwanansa saɓanin Iya da ta sha duniyarta yana ganin ita ko yanzu ta koma ga Allah daidai ne.


Da sauri da sauri yake jan mazaunan duk ya kukkuje a ƙurunƙusan tsakuwar da take wajen zafi da raɗaɗi yana ziyartarsa amma babu halin tashi tsaye saboda tsaro kai har da tsoro ma. Har ya je ƙofar ɗakin da suke ciki sai lokacin ne Iya ta farga da abin da yake faruwa, wata shala ya yi ya kifa ya ƙara kifawa sai kuwa ƙafa mai na ci ban baki ba a haka ya arce sai waje duk da da sai da suka shige can ciki amma da yake hankalinsa a tashe yake ba ganin inda yake saka ƙafarsa yake ba haka ya bazamo ya fito da mugun gudu yana haki har ya fito daga gidan tare da jan iska a hancinsa da ƙarfi.


"Wash na shaƙi iskar ƴanci" Ya faɗa a ransa yana nufar adaidaita sahun nasa babu jira ya miƙa mazaunai zai zauna amma mai? A lokacin da Iya ta hango shi bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen sanar da tattabara dan bata ƙaunar Jabiru ya tafi ya barta dan haka ita ma sai ta ji tun da bai kalli tsufanta da ƙaunarta gare shi ba da ta siyar da ranta ta zauna to tabbas ita ma ba za ta ji nauyin faɗawa tattabarar ba.




"Jabiru zai gudu, Jabiru ya gudu" Ta faɗa cike da tsoro.


"Muna kallonsa kar ki ga na juya baya to ina da idanu a ƙeya" Tattabarar ta faɗa ko waiwayowa bata yiba.


A can ƙofa kuwa Jabiru da ya shiga adaidaita sai kawai ya ji tamkar an fisgo shi daga cikin kamar a saman iska haka ya ji ana ta janshi da baya da baya.




Iya tana zaune ta zubawa sarautar Allah, ido ta dai ga tattabarar bata fita ba, amma kuma ta kasa gane ya aka yi ta ce tana ganinsa ta bar shi ya tafi sai ta kasa natsuwa hankalinta a tashe dan tana ganin shikenan wataƙila a yi tsirenta. Tana zaman jiran tsammani a zuciyarta tana mamaki da al'ajabin halin da suka tsinci kansu.


Kamar daga sama Iya ta fara hango Jabiru da ake janyo shi da baya da baya tun kafin ya shigo wurin an buga shi a bango ya fi a ƙirga dan hatta bayansa sai da ya ji allon bayansa tamkar zai rabe biyu sai da aka kawo shi gaban Iya jaɓar aka warɓar da shi sai ga shi a reran yana mayar da numfashi, Iya kuwa dakyar ta yi nasarar danne dariyar da take cin ta saboda dai ta ga Jabirun ya gudu ya barta da tafiyarsa ta san wataƙila har ya shiga adaidaitan amma ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login