Showing 45001 words to 48000 words out of 60716 words

Chapter 16 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt

27 Dec 2024

3523

hijaban nasu bata ma san ta yi wurgi da ledar ba dan da a ce bom ya tashi da su a banza gwara su je gida da mayafi iyayen in tsire su za su yi ma su tsire dan wannan rana ita ake kira da yauma tubulas sara'ir wato ranar tonon asiri da yake ba a unguwar ma suke ba gidan ƙawar su ne suka zo.


Haka suka
zo riii suna gudun amma kamar masu tsallan kwaɗo saboda ɗamammen siket da kowacce take sanye da su wanda aka zige zip ɗin su dakyar saboda yadda ya ɗame musu jiki ga wannan takalmi kamar masu gudu yara ƴan koyon gudun tantanta wanda basu ƙware da gudu a tafiyar ba wanda tafiyar bata gama nuna ba amma dan karambani suke yin gudu.






Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay


TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃






Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada.


Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi.


Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa.


Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰


Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari.
Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851
[12/23, 15:52] Mom mashkur & Afrah: ƳAN ADAIDAITA SAHU
(Masu keken nape)







NA






MAMAN AFRAH


Page1️⃣2️⃣




Abin da suka kasa lura da shi, shi dai mai bada rahoton tashin bom wato Jabiru, tun fa da ya bada labarin mai yake wakana bai matsa daga inda yake ba yana nan sunkuye inda yake yana kallon duk abubuwan da suke wakana dariyar da takw cin sa ta kasa barinsa sai danneta yake abin da yake saka shi dariya kuwa yadda jama'a suke masa kallon mahaukaci lokacin da yake nasa gudun amma yanzu da suka ji dalilin gudun nasa sai su nasu gudun ma ya fi nasa, lallai mutane basa son mutuwa ita kuwa mutuwa a kullum kusanto mutum take! Sai dai in lokaci bai yi ba shi ya sa wanda ya tafi bai yi bai yi sauri ba wanda bai tafi ba kuma bai yi jinkiri ba tana nan tafi saboda duk mai rai mamaci ne. Ɗaya daga cikin su ce ta yi ƙarofin halin cire takalmin ta rungume a ƙirjinta tamkar wani zai ƙwace mata shi, saboda ta san sai da ta yi adashe da kuɗaɗen samarin da take yaudara ta siya takalmin dan kawai ta kece raini a cikin ƙawaye saboda ta ga shi suke yayi, abin da yake ba Jabiru dariya yadda siket ɗin nasu ya sauka har ƙasa duk dan gayu haka aka buɗe shi daga ƙasa, wannan dalilin ya sanya idan suna gudun sai iska take ɗaga siket ɗin tamkar filfilwar wasan yara da suke yi da takarda da kara da tsinke wacce idan suna gudu iska take kaɗawa haka siket ɗin ƴan matan suke ɗagawa filfilfil.


"Na cikin gidaje ku fito dan tsira da rayukan ku an saka bom a unguwar nan ya kusa tashi ma, bom har uku ƴan bindiga suka saka" Ƴan matan nan suka ware murya suna faɗa dan su yi ceton sauran jama'a da suke cikin gida basu san abin da yake faruwa ba. Kafin kance kwabo sai ga mata suna tuttuɗowa daga cikin gidajen su tamkar tururuwa kowacce tana fitowa sai ta hangi ƴan matan nan sun miƙe layin suna zabgar gudu ga wasu maza can a gabansu wanda su ma gudun suke tamkar ana hankaɗa su wannan dalilin ne ya sanya daga sun fito sai su gane cewa inda mata da mazan ne suka yi shi ne wajen tsira shi ya sa kowacce ta fito sai ta ranƙaya habyar da ta ga sun yi. Wani mutumi da ya siyar da shanunsa guda biyu jiya ya zo gida da kuɗin yana cewa sai gobe zai kai banki dan haka sai ya ɗauki wata jaka ya saka kuɗaɗen a ciki yana tsaye a tsakar ɗaki matarsa tana kan gado tana zaune tana masa Allah da annabi a kan ya bata kuɗin cefane a cikin kuɗin yana ta masifa cewar ko naira biyar ba zai bayar ba ko dai ta siyi abincin ko kuma ta zauna da yunwa, dan shi babu mai saka shi ya taɓa kuɗinsa dan kuɗinsa na kayan lefen amaryarsa ne da zai aura, ya ajiye jakar a kan gado yana ta kalle kallen inda zai mata maɓoya a cikin ɗakin da yake jakar irin wacce ake goyawar nan ce mai kamar ta ƴan makaranta bai ankara ba sai ya ji ana faɗin an sanya bom a unguwa ya kusa tashi hakan ya sanya ya ruɗe wani tashin hankali ya ziyarce shi, matar ma hankalinta ne ya tashi dama bata da ɗa ko ɗaya tun da suka yi aure bata samu rabo ba wannan dalilin ne ma ya sanya yake mata wulaƙanci shi ne zai yi aure, tana shirin tashi tsaye domin guduwa ta tsira sai ji ta yi an kinkime ta an saɓa ta a baya, mamaki al'ajabi ne ya baibaye ta dan ta san dai mijinta ko karen hauka ne ya cije shi ba zai taimaka mata va sai dai ta yi ta kanta amma kuma ga shi har da ɗaukanta ya saɓa ta a baya hakan ya sanya ta fara godewa Allah a kan ko canji ne ya samu na lokaci guda yake son su tsira a tare don a nata zaton ta ɗauka guduwa zai yi ita ma ta yi ta kanta amma sai ta ji ya warce ta ya saɓa a baya ko nauyinta bai ji ba shi da ko a irin soyayyar nan ta ma'aurata bai taɓa ɗaukanta ba amma yau ga shi dalili mai sa a leƙa jikin sirika ya ɗaga ta cancaras ya goye a barsa. A ɓangaren miji kuwa bai san cewa matarsa ce ya goya ba da yake a kusa a ita ya ajiye jakar kuɗin a kan gado jin an ambaci tashin bom a lokaci ƙanƙani a ruɗe da kuɗinsa da kuma gudun kar ya mutu wani ya auri amaryar da ya ci burin aure wacce ya tafi ƙauyensu saboda ita ya siyar da kadararsa ta shanu dan su yi aure. Duk a tunaninsa jakar ce ya goya ba matarsa ba dan yadda matar ta maƙalƙale sai ya ɗaukan hannuwan jakar ne ya maƙala, ita kuma matar ganin ya goye ta sai tausayi irin na mata ya sanya wani son sa da ƙaunarsa ya ratsa ta ta miƙa hannu ta ɗaukar masa jakar ta a haka ya bazamo daga cikin gida niƙi-niƙe goye da matar da yake ma tana da jiki sosai hakan ya sanya yake gudun tinƙis-tinƙis ko takalmi babu ga shi daga shi sai singileti yana fitowa ya ga inda jama'a suke dirfafa sai gudu ake mata wasu ɗauke da yara sai kuka ɗiya suke ganin abin da basu taɓa gani ba shi ma a haka ya bi ayari tamkar ƴan gudun hijira sai tada ƙura ake a layin sai ka ce masu gudu a sahara.




Wani gida da yake kallon gidan da mijin nan ya fito goye da matarsa, ita kuma matar gidan tana wanke -wanke ta ji ana cewa bom zai tashi kowa ya yi ta kansa, tsabar rikicewa kwandon wanke-wanken ta ɗauka ta kifa a kanta a tunaninta hijabinta ne a haka ta taho tana gudu kai a kife da ƙaton kwandon zuba kwanukan wanke-wanke tana fitowa ta bi bayan mijin nan da yake goye da matarsa, ta cikin tular kwandon take kallon yadda yake zandama gudu ko ƙaƙƙautawa babu shi ne abin da yake bata darita duk kuwa da halin da ake ciki na tashin hankali. Dan kowa a unguwar ya san mijin matar bashi da mutuncin ba ya ganin kan uwar kowa da gashi amma dai ita kanta ta san wuya ce in ji tsula ta sanya shi goyon matarsa kallon su take tana gudu kwandon yana kangal-kangal amma da yake bata ma san abin da ta kifo a kan nata ba da sai ta yi wa kanta dariya.


Kowa ya bazamo har da masu himilin kayan wanki a ƙulle a zannuwa dan gudun kar su yi asarar kaya sai su kinkima su ɗora a kai suke zabga gudu, wata mata ta fito ɗauke da randar ƙasa wacce ake zuba ruwa yake sanyi ita kaɗai tana gudu tana faɗin


"Gwara na rasa komai a akan na rasa randar nan saboda sanyinta ƙafata ƙafar randata" Ta ficr fuuuu. Jabiru ya take wa wasu miji da mata makafi baya da suka fito daga wani gida kowa riƙe da sandarsa amma a hakan mijin yana dafe da kafaɗar matar a haka suka fito, Jabiru da shegantaka ganin suna sauri basa gudu duj da kaancewar su makafi amma bai tausaya musu ba ya buɗe baki ya ce




"Ya fara ƙara bom jama'a ya kusa tashi kowa ya ƙara ƙaimi wajen gudu kuna dai ganin an ce a film ɗin turawa wasu sai sun kusa tsira idan bom ya tashi sai ka ga ya tashi da su bayan taku kaɗan ne za su ƙara yi su tsira" Wannan jawabi nasa ya sanya makahon nan ɗauke hannunsa daga kafaɗar matarsa ya daina dogara sandar ita kanta sandar sai ya mata hawan doki yadda yara suke yi ya shiga zabgar gudu. Matar tasa ma gudun take tana kiran


"Malam kana ta ina?" Amma Malam ba ya ma jin ta dan ya daɗe da bada tazara a tsakaninsa da ita yana can gaba yana biye da wata mata mai siyar da taliya da manja ta gama tace taliyar kenan sanarwar ta sauka a kunnuwanta haka ta ɗoro robar taliyar haɗe da kaskon manjan tana zabgar gudu abinta. Jabiru shi ne a ƙarshe sai kwasar dariya yake yana ta mamakin gudun mutuwar da jama'a suke ya tabbatar da a ce za su san ƙarya yake sai sun sumar da shi in ma sanadin dukan da za su taru su masa basu kashe sa ba, bare kuma in suka san ta'asar da ya aikata wa Ƴan karota suka biyo su shi da kakarsa ya tabbatar sai sun kai shi hannun ƴan karotan sun damƙa shi i ma mai za a masa na hukunci a masa.




"Dan wulaƙanci Barira maimakon ta kinkimo tukunyar tuwon nan shi ne ta kamo hannun ƴaƴan suka gudu ita ce kaza uwar ƴaƴa, ta bar tukunyar a gida sai an je wurin yada zango yara suke kukan yunwa hallaw ga Badamasi uban nemo abinci sai in ƙara tafiya neman abin da za su ci bayan ana cikin halin tsoro ai kamata ya yi duk inda mutum zai je ya tafi da guzuri gudun ko ta kwana" Jabiru ya ji wata muryar mutum a bayansa yana gudu yana faɗa tamkar zai ari baki wai a kan matarsa Barira bata ɗakko tukunyar tuwo ba. Waiwaya wa ya yi ya ga mutumin wani ɗan lukuti ɗauke da wata tukunya lamba uku jikinta duk miyar kuka da ludan ɗaukan tuwon ma a cikin tukunyar da alama ɗumame ne a ciki tukunyar duk baƙin tukunya a jiki duk ya goga a jikin farin yadinsa amma bai damu ba shi kawai ta tuwon yake dan kar ya tafi nemo wani.


"Haka kawai a zamanin Tinubun nan yadda masara da hatsi suke tsada kai hatta maggin miya tsadar da ya yi bai taɓa yin irinsa ba amma dan rashin tausayi tana ganin ba ita ta nemo ba ta gudo ta bar ɗumamen a gida bom ya tashi a unguwar tukunyar ta yi ƙurmus a can inda muka je kuma a saka ni salati da salallami na nemo wani abin da yara zasu ci" Ya faɗa yana yi yana ɗan gudu.


"Hmmm! Kai ba tsuntsu mai wayo ba to ai tsuntsu mai wayon ma ta dabara ake kama shi, in dai tukunya ce da kan ka za ka jefar da ita yanzu nemowar da ka ƙi dai sai ka sake nemowa tun da kai Allah ya ɗorawa nemowar ba matarka ba da ta kwashi ƴaƴan ma ai ta yi ƙoƙari dan wauta irin taka da kuma ƙiwiya sai a bar ɗan mutun a ɗakko tukunyar tuwo?" Jabiru ya faɗa a ransa yana ɗan rage gudun da yake sai da mutumin nan ya wuce shi ya bashi ƴar tazara ya wangame baki ya ce


"Jama'a a ƙara wuta dai a ƙara mai wajen gudu ga wani ƙara can daga nesa hayaƙi yana tasowa da alama ɗaya daga cikin bom ɗin ya tashi" Kowa da yake ta kansa yake babu wanda ya samu damar waiwayowa bare ya ga da gaske hayaƙin ne yake tashi ko kuma su lura cewar basu ji wani ƙaran tashin bom ba duk sai suka danganta hakan da rashin nutsuwar da suke ciki. Mutumin nan mijin Barira wanda yake ɗauke da tukunyar tuwon ɗumame jin gudu sosai yana neman gagararsa sai ya yi wurgi da tukunyar tuwon ya fara sheƙa gudun a ransa yana cewa.


"Haba sai yanzu na ji ina gudu sosai ashe dai tukunyar nan ce take hana ni rawar gaban hantsi" Jabiru kan dariya sai da ya kasa gudun ma ya dakata sai da dariyar ta tsagaita sannan ya daure ya ci gaba yana zuwa inda mutumin ya yi wurgi da tukunyar sai ya ga tukunyar da ban, murfin da ban ludan ma ya yi nasa wuri sai tuwon da yake ta masifa a kansa ashe ba wani tuwon kirki bane duka guda huɗu ne wato yankan ɗumamen huɗu wanda bai fi ma yaran su cinye lokaci guda basu ƙoshi ba tun da yankan ma ƙanana ne.






Sai da ya tabbatar jama'ar unguwar nan su yi nisa ya dawo wani shago da mai shi ya bazama ya bari a buɗe ya ɗauki cincin da lemo a frige mai sanyi ya ci ya yi hani'an ya kwashi wani cincin ɗin ya zuba a aljihu da lemo roba ɗaya ya ce


"Oh ni ko ina Iya Ansai ta buya ita kuma na san dai yanzu yadda kawo ya bazama babu wani mai bada labari idan an tambaya wato idan ƴan karota sun zo sun ce basu ga wasu masu napep sun shigo unguwar ba, kin ga babu mai cewa ya ga wani saurayi ko wata tsohuwa ta zo da alamar rashin gaskiya a tare da ita ko ma ƴa unguwar su ce basu yarda da su ba bare har a shiga bincin a unguwar a gano inda muka ɓoye adaidaitar mu yanzu dai cincin da lemo ba sata na yi ba wale-wale aka yi fa su ba adana ba" Ya faɗa a ransa yana kallon shagon tare da fashewa da dariya a fili ya ce


"Kaico ni Jabiru jikan Iya Ansai yanzu da gari banza na zo na ce ko alewar naira biyar a bani a shagon nan sadaka sai an kai rana za a bani in ma ba a mini korar kare ba, amma sai ga shi an bar shagon a buɗe na shiga ciki ina wadaƙa har da shan lemo da cincin kai Allah dai ya biya" Ya faɗa yana fitowa daga shagon ya samu wani kango ya buya cike da tsoron abin da ya faru jiya a kango da su da mutanen ɓoye amma haka ya daure ya zauna a ciki sai da magriba ya fito domin zuwa ya samu kakarsa su san na yi.


"Amma kuwa wannan an yi ɗan iskan saurayi to mene ne rubarsa da ya yi hakan? A she dai ƙarya yake babu wani bom haka kawai ya bazama mutane da yara kowa yake gudun famfalaƙi, hatta jama'an tsaro da aka sanar da su suka kasa zuwa unguwar kowa yana tsoron ya zo abu ya ritsa da shi" Cewar wasu samari da suke tsaye a layin da Jabiru ya baza su ya zo wucewa yaji ana ta batun abin da ya faru.


"Wannan an yi ja'irin yaro haka kawai ya tafa ha kulan jama'a ina barci na ji matata tana tashina a kiɗime cikin gagan barcin nan na suri sandata muka fito ko gama warewa ban yi ba, kai da abu ya yi abu sai gani na hau saman sandar tamkar wani ƙaramin yaro wato ina dokin kara irin na yara da sandar bara ta" Cewar makahon nan da suke magana da wani mutum.


"Yo Malam Abashe ba har gwara kai ba ni fa nan na saɓi matata a bayan nan nawa wallahi duk tunanina jakar kuɗina ce ta goya wai ashe ita ce kuma sabo da rashin tausayi da imani irin nata sai ta yi lifet a bayana nake zabga gudu da su tumemiyar mace a bayana ga tana ɗauke da jaka duk ni kaɗai, wallahi bayan nan nawa kamar na ɗauki buhun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login