Showing 54001 words to 57000 words out of 60716 words

Chapter 19 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt

27 Dec 2024

3518

ya shiga ɗakin ba sai dai in lokacin da na shiga ni da wannan yarinya yana ɗakin ya yi likimo kai ina jin ma shi ya farwa yarinyar ba Jaburu ba dan yadda Jaburu yake babu wata alama ta aikata sunna a tare da shi, tabbas da sauran rina a kaba ashe dai ni wani na yi wa tanadi har cikin gida har ɗaki ba Jaburu ba kuma dan rashin ta ido bayan ya kalailaye ƴar mutane babu sadaki shi ne ya nakaɗawa jikan nawa duka ni ma yanzu yake son a jaɓi banza sai ka ce ya samu bayi, ni ina nan zaune ina wa Jaburu gadin ƙofa ashe dai bonono na yi rufin ƙofa da ɓarawo haba shi ya sa nake jin ihun Jaburu ya yi yawa duk tunanina sunnar da yake aikatawa yake yi wa ihun ashe dai ashe dai" Ta faɗa a zuciyarta.


"Wato ke tsohuwar banza shi ne kika mini shigo -shigo ba zurfi kika kai wa jikan ki ni har ɗaki duk a tunaninki mace ce to ba mace bace ni ne nan kika kai masa ɗakin kin ga sakamakon da ya karɓa a hannuna" Ya faɗa rai a ɓace yana aika mata harara. Wani irin dimmm di dimmm gaban Iya ya bayar jin wai ashe ba mace bace ta kai wa Jabiru ashe ƙato ne ta saka ya shiga ya garƙame ƙofa ashe rabon ya ci na jaki ne. Idanunta ta ɗaga wanda suka kaɗa suka yi jawur saboda tsoro ta sauke a kan cibiri-cibirin gashin kansa tana mamakin ina kitson da taga ya zubo a kafaɗarsa tana al'ajabin ya aka yi aka haihu a ragaya ta ji ya ɗora da faɗin


"Ni maraya ne dan haka ma a shagon wasu abokaina nake kwana, na zaɓi hanyar wannan ta yaudarar maza a matsayin mace ne dan in ke samun kuɗi ina kashe uzurin gabana, ina saka wa a mini kwalliyar nan na yi mama(Breast) Da famfas na bazama yawo dan bani da takamaiman wajen zuwa ina yawo a ƙafa wata ran na shiga napep idan na ga wani mai abin hannun sai na sauka na san yadda zan ribace shi ya ce yana sona idan ya tashi kaini gida sai na faɗi unguwar ƙarya na nuna wani gida ya sauke ni a ƙofar ya sallame ni da kuɗi ya tafi in zamu yi waya na yi muryar mace, in zai zo na je wajen gidan da na ce gidanmu ne to a haka nake samun abin da nake so dan na san ina garsamemen namiji babu mai ɗaukan kuɗi ya bani shi yasa na zaɓi hakan, shi ya sa ma da jikan ki ya ce ina zai kai ni na ce idan na samu wurin sauka zan sauka saboda bani da takamaiman wajen zuwa, dan haka sai kin karɓi sakamako kamar yadda ya karɓa, amma ke ba dukan ki zan yi ba kin san hadisi ya ce kama tidinu tidaan (Duk abin da ka yi sai ana maka) To ke ma yanzu zan haike miki kamar yadda kika so ɗanki ya haike mini kika goyi bayansa, kuma ɗauke nake da cutar ƙamjamau kin ga za ki samu guzurin zuwa kabari" Ya faɗa yana fisgar hannunta tana turjewa ya shige ɗakin ya banko ya saka mukulli Jabiru sai idanu ya runtse hawaye masu zafi suna kwaranyowa saboda ko yatsansa ba zai iya ɗagawa ba dan ba ƙaramar kila ya sha ba tabbas ya ji maza.


"Lahaula wala ƙuwwata illah billah Jaburu kana ganin abin da nake gani kuwa ni Ansai da tsufana mai ƙanjamau zai haike mini, wayyo Allah duk abin da ya samu shamuwa dama watan bakwai ne ya yawo mata" Ta faɗa a zuciyarta lokacin da ta ga ya rufe ƙofar ruf sai lokacin ta ji tashin hankalinta ya ninku.


"Yau ya zan yi ina mafita ya zan yi in tsira, na jawa kaina ni dai zuwa birni bai mini rana ba amma tabbas duk abin da ya samu rago inuwa ce ta jawo masa" Ta faɗa a zuciyarta hawaye suna kawaranya tana kallon yadda aka yi wurgi da ita a kan gado a gidan da babu kowa sai kowar wake wato Jabiru da babu abin da zai iya tsinanawa ga gida a garƙame ɗaki ma a garƙame da mukulli.










akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.


ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳


kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu.


a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳


Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA.


09013181851
[12/23, 15:52] Mom mashkur & Afrah: ƳAN ADAIDAITA SAHU
(Masu keken napep)



NA






MAMAN AFRAH





Page1️⃣5️⃣



Babu abin da bakin Iya yake ambato sai magiya a kan ya haƙura ya ƙyale ta amma ya yi kunnen uwar shegu da magiyar da take masa, saboda shi ma bata ji tausayinsa ba take gadin a masa fyaɗe a matsayinsa na mace bata san cewa shi namiji bane.


"Haba amaryata ke da za mu angwance mene ne na damuwa ke da kika yi gam da katar na samun yaro ɗanye sharaf, ai kin dace da tsuntsu daga sama gasasshe" Ya faɗa cike da sheƙiyanci yana saka hannu ya warto leɓen zaninta, da sauri ta saki rigarta da ta riƙe ta mayar zuwa ƙugunta waɗan nan ƙafafu kuwa ta haɗe su waje ɗaya ta matse ita ala dole mai ƙarfi.


"Haba ɗan nan mai za ka yi da tsohuwa mai shekaru aru-aru wacce ta ga jiya ta ga yau, duk na yamalmale na yi yaba babu mamora a jikina...


"Kar ki ce haka baby ai ruwan kashe gobara ba sai mai kyau ba...


Fashewa Iya ta yi da kuka jin ya kira ta da suna baby kuma ma wai ita ce ruwan kashe gobara yau, ruwan kashe gobarar ma a wajen ɗan da ta yi jika da shi.


"Haba baby duk kukan ɓaci ne wannan ɗin?" Ya tambaya yana ƙara jan leɓan zanin Iya wanda ta daddage iya ƙarfinta tamkar a filin yaƙi ta danne.


"Ka yi wa darajar iyayenka ka ƙyale ni ɗan nan, wallahi na faɗa maka babu wani wurin moro ka je ka samu ƴan mata masu jini a jika" Ta faɗa cikin muryar kuka hawayen nan shaɓe-shaɓe, jin bai tanka mata ba sai ta ɗaga ido ta kalle shi ganin ya tamke fuska tamkar magribar ɗinya sai ta sha jinin jikinta, jikinta ya shiga karkarwa dan yanayin da ta ga fuskrsa a ciki yanzu ya mata kama da rashin sassauci kuma komai zai iya faruwa. Rigar ya farɗa ita ma ta ɗago hannunta ɗaya daga ƙanƙame zaninta da ta yi ta kai jikin rigar saitin ƙirjinta ta danne ɗaya hannun kuma yana riƙe da zaninta. Rigar ya ƙara fisga tamkar zai yaga.


"Haba kai kuwa mai za ka ɗauka a nan wurin da kake faman ja?"


"Abin da ake ɗauka mana" Ya faɗa yana ƙara tamke fuska.


"Wallahi billahillazi huwar rahmanu na faɗa maka babu wata mamora, shi kansa maman(Breast) Ya gama ganin wahalhalun duniya, ya yamutse ya jeme tare da yagalgalewa, babu abin da ya fi dacewa da a kira sunansa ma sai jelani" Ta faɗa lokacin da ta sauke idanunta a ƙirjinta ta ga ko alamarsa babu .


Ganin ya ja rigar da ƙarfi kuma da yake rigar atamfar dama ta gama cin duniyarta duk ta tsofe jin an nuna mata ƙarfi sai keeet ta yage daga gaba tun daga ƙasa har sama hannuwanta ne da suke cikin rigar kaɗai ya hana rigar fita sai rigar ta zaman kamar falmaran, a firgice Iya ta wuntsila gefe guda a kan gadon sai ta yi wata uwar shala sai gata a tsakiyar gadon ta tashi tsaye cankarkar tana muzurai da haki, ganin ya ƙara tahowa sai ta tsugunna ta saka kanta a kan gadon ta yi wata adungure sau biyu sai ga ta a bakin gadon ta zara ƙafa ta dira idanu ta sauke a kan ganan rigarta da yake a buɗe wayam sai kuwa ta yi ido huɗu da mamanta da suke reto, ganin ya taho wajenta sai ta shiga ɗan gudu a cikin ɗakin da take ɗakin yana da yalwa sai kuwa su ma maman nata suka fara ɓalai-ɓalai suna gwaruwa da juna. Dariya ce ta so suɓucewa matashin ganin abin da take yi ita ala dole ƙwatar kanta za ta yi bayan da ya ga dama a cikin minti ɗaya zai gama da ita.




Tana ta faman riƙe gaban riga har ta manta ta saki zanin nata kuma zanin bai ɗauru sosai ba saboda jansa da marashin ya yi ta yi ita ma tana ja, dan haka zanin ya warware daga tsantsa bata sani ba har leɓen ɗaya ya fara jan ƙasa, matashin da yake bin ta suna zagaye ɗakin sai ya saka ƙafa ya take leɓen zanin nata sai kuwa ga zanin a ƙasa ta bar shi bata lura ba ya sunkuya ya ɗauka ya rataya zanin nata a kafaɗarsa.


"Na gode Allah da kika cire zanin da kan ki kin hutar da ni" Ya faɗa yana kallon Iya da take riƙe da gaban rigarta da hannu biyu ta yi wajen madubi. Da sauri ta waiwaya ta kalle shi ai kuwa ta yi mugun gani domin kuwa zaninta ta gani a wuyansa a rataye da sauri ta sauke idanunta ta ganta daga ita sai ɗan tofi(Siket ɗin da tsofaffi suke sakawa a ciki wanda ake ɗinka musu mai aljihu) A take ta shiga rafka salati da ƙarfi tamkar za ta ari baki.


"Na shiga uku ni Ansai wannan yaro an yi ja'irin yaro, yau na gayyato taƙadiri har cikin gidana wai ni ɗin nan tsofai-tsofai da ni bai lura da tsufana ba zai haike mini dan jaraba irin ta yaran zamani, yo ni ba gwara ba ya lakaɗa mini dukan irin yadda ya yi wa Jaburu a kan wannan baƙi kuma ɗanyen aiki da sheɗan yake kwaɗaita masa, na shiga tara ba ma uku ba yanzu yadda ya ɓarka mini riga kuma ya yi nasarar cire zani ai sai abin da Allah ya yi ɓarawo a hannun mata" Ta faɗa a zuciyarta tana jin ina ma ta samu ta kuɓuta da idan ta zangaya da mugun gudu Allah kaɗai ya san a inda za ta tsaya.


"Yo Ansai ko buɗe miki ƙofa aka yi ina za ki je a haka, ke dai wanda babu kaya a jikinsa ai baku da banbanci" Cewar wani ɓangare na zuciyarta.


Idanunta ta sauke a kan ɗan tofin nata sai ta ga gaba laya a tsangale da yake ba wani tsawo ne da shi ba.


"Kin yi kyau baby kamar turawan nan masu saka tsangalelan siket d...


Salati Iya ta kwasa jin yana haɗa ta da matan turawa wanda aka ce shigar su tamkar tsirara take, kuma ko ranar nan ta ga wata baturiya a garin Kano duk cinyoyi a waje har take cewa Jabiru wannan ai daman ma sangalarta ta fito(Tsirara ba kaya) Ya ce mata ai baturiya ce su ba ruwansu amma shi ne dan wulaƙanci zai haɗa ta da arna. Da ta ga yana kallonta ma daga inda yake sai ta saɓa da gudu ta yi wajen drower tana gudun ne sai ga kuɗinta sun faɗo daga aljihun ɗan tofin nata. Taku ɗaya biyu saurayin ya yi sai ga shi ya isa wajen kuɗin ya sunkuya ya ɗauka Iya da ta je take neman maɓoya ko da kuwa saman drower ɗin ne ta haye dan ta tsira da tsufanta da mutuncinta kamar an ce ta juyo sai kuwa idanunta suka yi arangama da mummunan gani, domin kuwa hango gaba ɗaya tattalin arziƙin su a hannun saurayin sai da hankalinta ya tashi domin kuwa sai da ta kai hannu ta lalumo ɗan tofin ta ji wayam ta tabbatar da cewa kuɗinta ne. Ita kanta bata san ya aka yi ba kawai sai ganinta ta yi a sukwane ta ƙarasa gabansa. Idanunta ƙurrr a kan hannunsa da yake ɗauke da kuɗin.


"Yawwa baby kin taho... Tun bai kai ƙarshen maganar ba Iya ta gane katoɓarar da ta yi, da sauri ta juya a sukwane ta koma inda ta fito wato wajen drower. Dariya sosai matashin yake dannewa yadda har idanunsa suka kawo ƙwalla saboda yadda dariyar ta ci ƙarfinsa amma yake dannewa, shi dariyar da take bashi wai ita ala dole tana gudunsa shi kuwa in ba bakin uwa ne ya kama shi ba mai zai sa shi tarawa da matar da ba halaliyarsa ba kuma tsohuwa. Nufar wurin da ta je ta rakuɓe a jikin drower ta ƙanƙame jikinta, yana zuwa ya saka hannu ya ja ƙafarta wani uban ihu ta saki tana faɗin "Wayyo Allah na wayyo Jaburu wayyo matantakata(HQ) Wayyo mashayar yara(Breast)" Ta faɗa lokacin da ta daddage ƙarfinta tana faɗa. Ƙafar ya sakar mata tare da juyawa yana dariya marar sauti ya koma ya fara tattara kayansa da ya cire ya fara mayarwa jikinsa lokacin Iya ta ɗago tana kallonsa ya mayar da komai sai ga shi tamkar mace, mamaki ya cika Iya ta ce a zuciyarta.


"Da na san daga waje mace kake, daga ciki kuma namiji da babu wani abu da zai sa in yarda da ƙudurin Jaburu bare har ta kaimu ga wannan mummunam halin" Babu inda ya fi bata mamaki irin lokacin da ya saka bra ya ɗauki famfas ya sassaka ya ɗora riga tsaf ya fito babu mai cewa ba mace ba ce, ga hular gashin da ya saka ya ɗaura ɗankwali. Mukulli ya sa ya buɗe ƙofar ya juyo cikin muryarsa ta mata da yake canjawa ya ce


"Bye-bye baby nah sai na sake dawowa" Ya faɗa yana juyawa zai fice.


"Na gode ɗan nan da ka barni da mutuncina Allah maka albarka ya baka sana'ar yi ka daina shigar mata dan wallahi babu kyau"


"Amin, amma fa ku daina gode mini ba za ki gane komai ba sai na fita na arce da adaidaita sahun ƙofar gida...Bai gama faɗa ba ya juya ya fice daga ɗakin, a tamanin da tara Iya ta taso ta ma manta da yanayin da take ciki dan ba komai ya ɗaga mata hankali ba illa jin wai zai arce da adaidaita sahun da suka ci bashi suka siya, ta tabbatar idan har ya ɗauke adaidaitar to tabbas ya tabbata gonar da suka bayar da jingina ta zama mallakin Alhaji Audu.




A sukwane ta fito daga ɗakin har tana ƙume goshi a jikin ƙofar ɗakin amma ba shi bane damuwarta burinta kawai ya rufa musu asiri kar ya ɗauke adaidaitar. Matashin kuwa yana zuwa falo ya ga Jabiru a yadda ya bar shi ko juyi ba ya yi.


*JABIRU*


Tun da ya ji an shige da Iya ɗakin an kulle yake ta faman yin kukan zuci domin bashi da yadda zai yi, ko ƙarfin kwabo babu a jikinsa ga fuskarsa da bakinsa sai raɗaɗi suke masa musamman bakinsa ji yake tamkar an saka gishiri a ciwo saboda tsabar raɗaɗin da yake ji ga jikinsa sai ciwo yake masa ko motsawa ya kasa ji yake tamkar wanda cutar shanyewar duka jiki ta same shi, ba ma cutar ɓarin jiki ba. Salati da Iya take yi da magiya kuwa ji yake tamkar ya zama tsuntsu ya je ya ƙwace ta baƙinciki da takaicin ya kasa ko da motsawa ne sai ya zamana kawai hawaye ne suke ƴar tsere a dandamalin fuskarsa. Lokacin da ya ji Iya ta ce Wayyo Allah! Wayyo Jabiru sai ya runtse idanunsa saboda ya ji tana ambaton wayyo matantakarta da mashayar yara hakan ya tabbatar masa da cewa tuni aikin gama ya daɗe da gamawa. Yana cikin wannan halin ne ya ji an buɗe ƙofar amma ya kasa ko da ɗago kai ne ya ga wanda ya fito sai idanu yake rarrabawa tamkar kwarton da aka kama a ɗakin sabuwar amarya. Matashin nan yana zuwa ya saka ƙafa ya buga ƙafar Jabiru da ƙarfi.


"Kar ka ƙarasa ni dan Allah" Cewar Jabiru a ransa dan ya tabbatar idan ya ƙara nakaɗa masa wani dukan sai dai a ɗauki gawarsa dan ba zai amfanu ba. Sai da ya ƙara buga masa ƙafa a kwankwanso.


"Ash..." Ya faɗa a zuciyarsa yana jin har gwara ranar da suka yi gamo da aljanin nan a kan wannan baƙar rana. Hangar mukullin get ɗin ya hanga a inda Iya ta tashi sai ya ƙarasa ya ɗauka, ɗaukansa ke da wuya sai ga Iya ta fito a hautsine dan gaba ɗaya ta sha'afa da shigar da take jikinta burinta kawai ta dakatar da matashin daga ƙudurinsa na ɗaukan napep ko Allah zai sa ya amince ya tausaya musu. Jabiru da yake kwance a reran sai ganin ƙafafun Iya ya yi watsal ta tsallake saman kansa, har tana bige masa haɓarsa, ganinta da ɗan tofi gaban rigar a yage ya rabe a biyu sai ɓalai-ɓalai rigar take iska tana ɗaga ta sai ya ji wani tausayinta ya kama shi yana ganin sanadinsa kuma a son zuciya irin nashi ga shi da tsufanta an mata fyaɗe, dan shi duk a tunaninsa matashin ya haikewa Iyar.


"Dan Allah, dan darajar ma'aikin Allah S.A.W ka yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login