Showing 60001 words to 60716 words out of 60716 words
Chapter 21 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt
damar ta ƙwace saboda suna hannunta kuma ba za su ajiyu ba bare ta ajiye su, bakinta ta kai tana son ta ƙwace amma sai ta ga bakinta ba zai iya ba. A haka ta ɗago kanta ta sauke idanunta a kan Jabiru mai naƙuda.
"Iya ki kawo agaji dan Allah"
"Ka daure Jaburu ni ma ka ga waɗannan ba ajiyuwa za su yi ga shi sai fama nake da su a kan sai sun sha mini mama, ni wannan abu ban san wane irin abu bane kai da kake matsayin namiji amma ga cikin haihuwa a jikin ka tsoho kuma ga naƙuda ta tashi mun ga ta kanmu ni Ansai babban tashin hankalin ma ban san ta ina ɗan zai fito maka ba"
"Iya!!!"Ya faɗa da ƙarfi cikin zafin ciwo.
"Ka daure dai Jaburu haka naƙuda take wallahi lokacin da na haifi ubanka ma zafin ya fi wannan haka na sha gwagwarmaya ai haihuwa ba kanwar lasa ba ce, duk macen da ka ganta fa ɗanta ka kalle ta kawai s... Maganar ta maƙale ne jin an daɓa mata haƙori a maman ta, idanu ta zaro ta mayar da kallonta kan jariran ashe dai da hankalinta ya koma kan Jabiru mai naƙuda ashe sun samu nasarar kafa mata baki.
"Na shiga aljanna in na yi hali na gari ni Ansai haƙori kuma a bakin jarirai? Ban lura da haƙoran ba da suna kuka" Ta jefawa kanta tambayar a zuciyarta. Bata gama mamakin ba ta ji Jabiru ya saki ƙara tana maida idanunta kansa sai ta ga ya durƙushe a wajen ganin babu yadda za ta yi da jariran nn masu mamanta a bakinsu tsna jin suna datsa mata haƙora tamkar masu cizon ta da gayya, sai kawai ta yi dabara ta miƙe tsaye ga na bayanta ma basu bar kukan ba kuma suna jan rigarta duk sun cika gidan da kuka, dama jariri ɗaya ma in yana kuka cikawa mutane kunne yake bare jarirai biyar dan dai na hannun nata da suka saka maman a bakin su sai suka yi shiru a haka ta ƙarasa kusa Jabiru.
"Marata Iya bayana"
"Jaburu kamar fa haihuwar ta zo gadan-gadan, ni Ansai yau na ga abin da ya fi ƙarfina Allah ka kawo mana ɗauki a wannan gida da muka garƙame kan mu babu ma wanda ya san muna ciki bare a zo a taimake mu" Ta faɗa tana sakin wani marayan kuka.
"Wayyo ni ban taɓa jin ciwo haka ba, ina ga mutuwa zan yi"
"Bar ambaton mutuwa Jaburu ciwon naƙuda kawai ai haka mata suke fama, kama ƙafata ka riƙe amma kar kake nishi sai ka ji nishin ya zo da kansa" Ta faɗa a fili a zuciyarta kuma sai ta ce
"Yau na ga baƙar masifa da rana tsaka, to ni wannan yaro ta ina ɗan nan zai fito masa in dai ba ta wajen kashi ba ko kuma cikin nasa ya buɗe ɗan ya fito na san dai a halittar namiji babu mafitar ɗa kai wannan abu da wuyar sha'ani yake ni Ansai"
Ƙafarta Jabiru ya kama sai kuwa ta ji ya fara nishin fitowar ɗa, a gefe ɗaya kuma ga jariran bayanta sun ɗago rigarta kowa ya samu jikin fatar bayanta yana gwagwiya tamkar sun samu goruba, dan kowanne tana jin yadda tsinin haƙoransa suke cakar mata fata. Daurewa kawai take amma shi take tamkar ta yi ƙaramar hauka a take ta ji ta yi dana sanin zuwansu birnin ma gaba ɗaya.
*Last free pages domin shiga grp ki karanta har karshe ki tura 5OO ta acc faiza abubakar 9030283375 Opay ki tura shaidar biya ta 09013181851* .
. Kar ki bari mu yi tafiyar nan babu ke akwai cakwakiya a gaba ba zan ce komai ba🥰
KU MATSO DOMIN JIN DADDAƊAN LABARI
. ZAN CIKAWA KOWANE MUTUM ƊAYA DUBU GOMA 1OK
Shin kin taɓa jin labarin 52U? Yadda mutane suke register da cin moriyarsa, da dala 21 ake yi $21 kimanin 35k. Duk wacce za ta yi register a team ɗina zan cika mata dubu goma 1OK ta kawo 25k sannan duk wata zan ke bata 15k tsawon wata 3 idan acc ɗinta ya cika wata shida zai buɗe sai ta cigaba da kwashe kuɗaɗenta.
Mutum 2O nake nema kar ku bari damar nan ta wuce ku ki mini magana a PC 09013181851