Showing 6001 words to 9000 words out of 60716 words
Chapter 3 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt
cake a bani"Ta faɗa tana tuna irin daɗin da za ta ji idan ta damƙi kuɗin.
"Ai kuwa yau ina ɗakin nan daga na siyo waina zan dawo in yi zaman jiranki" Ya faɗa yana fita domin zuwa siyan waina ransa kuwa fari ƙal.
"Yawwa gwara ka zauna ka jira ni" Ta faɗa tana linke ledar vivan ta buɗe akwatin ta ɗakko ledar sarƙar ta saka a ɗan tofinta ta yafa mayafi ta ɗauki ledar vivan aka sako takalmi ɗan madina aka fito ana wata tafiya irin ta masu jiran zuwan kuɗi.
"A dawo lafiya" Aliya da Maimuna da suke tsakar gidan suka haɗa baki wajen faɗa.
"Allah sa, kuma kar wanda ya sake ya kai mini dambu ɗaki dan idan na gani ma zuciyata tashi za ta yi wanda kuka kai na safe ma suna nan ajiye yadda aka kai mini ni yau wankin ciki zan yi" Ta faɗa ba tare da ta jira amsar sh ba ta saka kai ta fice.
Tun da ta fito bakinta yake a washe tafiya kaɗan ta saka hannu ta taɓo ledar sarƙar cikin aljihun nata, sai ka ce wanda ledar za ta ɓace.
"Bari na fara zuwa gidan Dillaliya dan kar in tafi in siyar a kasuwa ta ga ban biyo ta hannunta ba ta samu alkairi" Ta faɗa lokacin da ta karya kwanar gidan Dillaliyar.
"Allah dai ya sa tana nan ita ɗin uwar ƴan yawo" ,Ta faɗa idanunta kafe a ƙofar gidan dan tana zaton ko ƙofar a rufe.
Cikin sa a kuwa a buɗe tana zuwa ta tura ƙofar ta shiga da sallama, amsa mata ta yi.
"Lale marhabin da iya Ansai" Cewar Dillaliya da take sanye da doguwar atamfa an cokara ɗaurin ɗankwali.
"Yawwa ana gida kenan"
"Wallahi kuwa ban kai ga fita ba, amma ina shiri dan yanzu zan fita karɓar basussuka"
"To madallah"
"Daga toi ko daga matoya?" Cewar Dillaliya tana dariya.
"Uhmm daga gida nake kuma tafe nake da abin arziƙi na ce bari na biyo ta hannunki kin san ƴan magana sun ce dillalin jariri shi ya san kuɗin wada"
"Wannan haka yake, amma kuma sai na ganki hannu na dukan cinya Iya"
"Eh kin san ba kowace ganima ake gani ba a hannu ba, wannan a aljihu na taho da ita ledar da za a saka kuɗin ce ma na rage buri na ɗakko viva, dan ba dan na kai zuciya nesa ba buhu zan ɗakko"
"Ikon Allah na zaune ya faɗi, yanzu iya sai ka ce wacce ta riƙo damid(Diamond) ko lu,u-lu,u ko kuwa babban zinare" Dillaliya ta faɗa tana kama haɓa cike da mamaki a zuciyarta kuma tana fatan wata banza ce ta faɗi ita ma ta kwashi rabonta dan ta san dai dole ta wanki gara dan tsohuwar ba lissafin kuɗaɗe masu yawa za ta sani ba, dan a nata tunanin Iyar ko tsuntuwa ta yi.
"Kina kan hanya Dillaliya ai babu maraba to idan ma akwai to sai dai abin da na ruƙo ya doke waɗanda kika lissafa a kuɗi"
"Na shiga aljanna na maƙale ni Dillaliya, bani in sha Iya Ansai saboda na gaji da gafara sa ban ga ƙaho ba" Dillaliya ta faɗa cike da ƙosawa dan a son kuɗi irin nata har ta fara tunanin idan har sarƙar gwal ce ta zo da ita to babu makawa ta dannawa Iyar filo har sai ta daina numfashi, idan ya so idan dare ya tsala ta fitar da gawar ta jefar dan ba za ta bari a yi babu ita ba dan sai ta ci karenta babu babbaka.
Murmushi Iyar ta shiga yi irin na ni kaɗai na san abin da na riƙo.
"Iya sai ja mini rai kike"
"Bari dai na fiddo ba dan kin nuna kin matsu bama kuma ni ma ina son a je a yi mini hanyar masu siya kema ki samu rabonki da sai kin bani goron albishir"
"Kar ki damu daga baya ma zan biya bashin goron albishir ɗin" Ta faɗa cike da jin haushin tsohuwar. Hannu iya ta saka a aljihun ɗan tofin nata bayan ta wangale zanin jikin nata, ledar ta fito da ita tana ƙoƙarin sincewa Dillaliya ta karɓe ledar hannunta har karkarwa yake tana sincewa.
"Taɓ akwai gwarama kenan tsuntsu daga sama gashashshe ina zaune har gida rabo na minallahi, dole ma ki garzaya barzahu a yanzu ba sai anjima da dan na ji sarƙar da nauyinta Allah kaɗai ya san gram in da za ta yi i aka auna" Dillaliya ta faɗa a zuciyarta lokacin da ta kai ledar ƙarshe. Tana buɗewa suka yi ido huɗu da sarƙar murjani irin mai rafka-rafkan nan mai kama da ta yarbawa, sakin ledar Dillaliya ta yi cike da takaici Iya ta bi ledar da kallo rai a ɓace ganin Dillaliya ta jefar mata da kayan kuɗin da take saka ran karɓarsa ba kaɗan ba.
"Haba Dillaliya wannan irin jefarwa ai sai ki rage musu farashi haba ke da zan ga kina murna kina tsalle kina sanya mini albarka na kawo miki kayan arziƙi har gida"Takaici ya hana Dillaliya magana sai da ta haɗiya wani malolon baƙinciki sannn ta buɗe baki ta ce
"Ina kayan kuɗin? Wannan ne abin arziƙin ko dai na tsiya ni amma tsinta kika yi a bola ko?"
"A kakar bola na tsinta bana son iya shege Dillaliya ni za ki wa tonon silili, da cin fuska, ki kalli sarƙar miliyoyi ki ce a bola na tsinta to wannan tun ta aurena ce "
"Ai ni ba zan biye miki ba sai dai in ce ki kwashe tarkacenki ki fice mini a gida dan duk wanda na kai wa ya siya sarkar nan cewa zai yi bani da hankali dan wannan ko ƴan gwangwan da baban bola ba za su siya ba, su ne dai masu siyan tarkace, saboda son banza har da wani ɗakko ledar viva za ki sanya kuɗi to ai ko naira biyar babu mai siya"
"Ke kuwa Dillaliya Allah wadaran naka a lalace in ji jakin gida da ya ga jakin daji, ke ma ta su Umarun za ki mini da suka ce sai dai a kai wa baban bola, dan wulaƙanci sarƙar tawa ta mutan da wacce na daɗe ina tanadi" Haushi ya sanya Dillaliya tashi tsaye tana nuna wa Iya hanyar waje.
"Ko baki faɗa ba tafiya zan yi kuma wallahi kin yi wa arziƙi dundu, aikin banza jiran jirgi a tashar mota" Iya ta faɗa tana tashi daga zaunen da take ta saka ledar sarƙarta a ajjihunta ta fito daga gidan tana sababi.
"Wai ko dai akwai ƙamshin gaskiya lamarin nan, ya za a yi a ce bakin su ya zo ɗaya da su Umaru? Wani ɓangare na zuciyar Iya ta jefa mata tambayar.
"Babu wani nan kawai tsabar baƙinciki ne da hana ruwa gudu" Wani ɓangaren na yaudararriyar zuciyarta ya bata amsa.
Hankali kwance ta kama hanyar kasuwa tana addu'ar Allah sa ta samu masu siya da daraja. Tun da ta shiga kasuwar take yawo abinka da kasuwar ƙauye duk sai Iya take ganin kuɗin da take hari za a bata gaba ɗaya zai iya saye kayan kasuwar gaba ɗaya.
"Malam nawa-nawa" Cewar wata budurwa da ta ɗaga abin hannu na tsakiya mai ƙanana.
Hankalin Iya gaba ɗaya kan su ya koma ganin mutumin sana,arsa siyar da kayan tsakiya na wuya da kunne da na hannu duk ya rarrataye wasu kuma suna zube a kan tabarmar gabansa.
"Naira hamsin -hamsin" Ya faɗa yana kallon yarinyar Iya kuwa gabanta ne ya shiga faɗuwa ya saki baki tana kallonsu.
"Yo ke ai taki ta mutane da ce kuma mai manya -manya" Wani ɓangare na zuciyarta ya bata amsa, wata ajiyar zuciya ta sauke dan har ta ji hankalinta ya ɗan kwanta.
"Uku ɗari idan ka siyar"
"kawo" Ya faɗa ko musu babu.
"Yanzu abin hannun ne guda uku ɗari, saboda ma rashin darajar su ko musu bai yi ba?" Iya ta faɗa a zuciyarta tana ɗaga ƙafafunta da suka yi sanyi ƙalau ta nufi wajen mai kayan.
Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay
TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃
Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada.
Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi.
Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa.
Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰
Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari.
Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851
[12/23, 15:51] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1
ƳAN ADAIDAITA SAHU
(Masu keken napep)
NA
MAMAN AFRAH
GARAƁASA💃GARAƁASA💃💃💃
Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.
ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳
kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu.
a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳
Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA.
09013181851
Page3️⃣
Sai da ta tsaya ya sallami yarinyar sannan ta matsa kusa da shi kamar za ta masa raɗa.
"Ala gafarta malam ina son magana da kai"
"Sarƙar za a baki ko abin hannu"
"Abin da na zo maka ya fi gaban wannan" Ta faɗa tana waiwaya wa hagu da dama kamar wata munafuka, ganin kowa yana sabgar gabansa sai ta ji hankalinta ya kwanta.
"Kamar yaya?"
"Babu komai sai alkairi dan haka ka kwantar da hankalinka ni ba da sharri na zo ba, taimakon juna za mu yi, wato ina ɗauke da kayan kuɗi ne a jikin nan nawa, to shi ne nake so mu yi sirri tsakanina da kai Allah ya zame mana shaida" Ta faɗa har lokacin tana masa maganar kamar raɗa amma kuma ana iya jin duk abin da take cewa, daga gefe guda wasu samari ne guda uku a zaune a wani benci ɗaya daga cikinsu yana zuƙar sigari kana ganinsu ka ga ƴan jagaliya, dan duk kamar ma sun shayu idanunsu jawur. Duk abin da Iya take yi suna kallonta a fakaice kuma suna jin abin da take faɗawa nutumin sai dai babu wanda zai ce ma suna sauraron su, domin dama duk wanda ya iya allonsa sai ya wanke.
"Wane irin abu ne na dukiya a jikin ki amma ni ban ga alama ba" Ya faɗa yana wani washe baki har da saka harshe ya lashi leɓɓansa saboda ya ji maganar kuɗi shi kuma dama mayen kuɗi ne duk da ya san ƙuda wajen kwaɗayi akan mutu, amma dai yanayin yadda Iya take magana ya fahimci gaskiya ce babu sirkin ƙarya dan haka sai ya ji ya amince da ita.
"Ba zan iya ambata maka ba saboda cikin kasuwa bashi da sirri, wuri ne na jama'a kuma wuri ne na ka zo na zo, sai dai ina maka albishir da cewa idan har ka nuna mini inda aka siyar da kayan nan to na tabbatar za ka samu abin da za ka gina kan ka da shi, dan ba lallai ma ka ƙara kasa sana'ar tsakiya ba, saboda ni kaina ina tunanin za a siyi hajar da mafi darajar kuɗin da ba lallai su lissafu ba"
Mutumin mai kimanin shekara sittin ya zaro idanu dan gaba ɗaya mamakin Iya ya kashe shi hakan ya sanya ko dogon tunani bai bari ya wahalar da kansa ba take yanke ya amince.
Gaba Iya ta shiga ya take mata baya ko takan kayan sana'arsa bai bi ba dan yana ganin banza ta faɗi. Da yake daga inda ya kasa kayan nasa akwai wajen da wata ƙofa take fita sai kawai suka bi ƙofar da ta fito da su daga kasuwar sauri Iya take yana binta iska sai kaɗa babbar rigarsa take wacce ya saka babu ko ƴar ciki.
"Mu tsaya mana a nan"
"A'a baka ganin daga ni har kai girma ya fara mana sallama kar a je wani ya warce kafin mu nemi ɗauki ya gudu gwara dai hanyar lafiya a bita da shekara" Sai da suka zo ƙofar wani gida suka tsaya Iya tana son fito da sarƙar tana tsoro saboda idanun jama'a duk da babu wanda ya kawo su a ka amma ita ganin ta riƙo kayan kuɗi sai take jin bata yarda da wajen ba.
"Malam mu shiga daga zauren gidan nan in nuna maka mu yi komai cikin sirri in ya so idan ka gani ka faɗi wajen da za mu je a siyar sai mu je ka san shi kuɗi da kuma kayan kuɗi suna son sirri, ba a son fitar da tsiraicin su saboda duniya yanzu ba gaskiya...
"Wannan haka yake ai kawai mu shiga muka baro cikin kasuwa ma har shiga zaure ya mana wahala" Ya faɗa yana bin bayanta dan shi saboda son kuɗi da kuma ganin banza ta faɗi sai kawai bai kawo cewa ko za ta cutar da shi ba. Sai da suka shiga zauren gidan Iya ta ɗan hango cikin gidan sai ta ji shiru kamar ma babu kowa dan haka sai ta ɗan tura ƙofar, hakan sai ya saka mutumin wani tsoro ya rufe shi dan sai ya fara tunanin ko aljana ce a take gumi ya wanke masa fuska jikinsa ya shiga karkarwa.
"Haba bawan Allah wallahi da mutum kake tare ba aljana bace" Cewar Iya dan yanayinsa ya nuna mata hakan.
"Kalli ka ga ƙafafuna babu kofato farce ne" Ta faɗa tana ɗaga zaninta yatsun ƙafar suka bayyana sannan ne ya ji hankalinsa ya ɗan kwanta. Baki ya washe cikin ƙarfin hali ya ce.
"Wallahi har na ruɗe"
"A haba wallahi mutum nake da a ce aljana ce ai da ba sai na nemi ka biyo ni ba da kaina zan kawo ka ta saman iska" Kai kawai ya gyaɗa mata kamar wani ƙadangare.
"A shegen son kuɗin nan nawa ai in kukar bulukiya ce ma za ta iya tafiya dani, ni wallahi bansan ma ya aka yi ban yi tunanin ko aljana bace sai yanzu"
Ya faɗa a zuciyarsa idanunsa kafe a kan Iya yana son ya ga ta fito da kayan kuɗin nan da take ta famar ambata. Tana ta ƙoƙarin fito da ledar shi kuma ya shiga waiwayen cikin gidan daga inda yake tana son ya tabbatar cewa babu mai ganinsu dan ya ga alama gidan kamar babu kowa a ciki.
"Idan na dannawa ƙofar nan sakata na maƙure tsohuwar nan sai na ƙwace koma mene ne na gudu da shi dan da arziƙi a garin wasu gwara a garinku" Ya faɗa a zuciyarsa yana fakon Iya da take ƙara zurmuƙa hannu cikin ɗan tofin nata ya ma kasa gane mai ya sa take ta nuƙu-nuƙu ga shi a gefe ɗaya gabansa yana dukan uku-uku dan kar ya je garin ƙwacewar ta rafka ihu asirinsa ya tono a je a masa duka a kasuwar nan, dan ya lura daga ganin matar za ta yi wuyar sha'ani dan ba lallai abin da ta ruƙo ɗin ya karɓu ta daɗin rai ba mai raba ta da abin sai ya yi da gaske. Basu gama tantancewa ba sai gani suka yi an banko ƙofar gidan da ƙarfi, samarin nan ƴan jagaliya guda uku ne wanda suke zaune kusa da mai siyar da tsakiyar nan ashe duk abin da su Iyar suka tattauna a kan kunnuwansu, sannan dama suna biye da su dan ganin yadda za ta kaya sai kuma aka yi sa'a su Iyar suka shiga zauren gidan samarin. Suna shigowa ɗaya ya danƙarawa ƙofar sakata idanun nan nasu jaawur, Iya da ta haɗe rai cikin hanzari ta mayar da ledar sarƙarta aljihu ta shiga aika musu harara.
"Yawwa gwara da kika mayar aljihu kar a rabamu da dukiyar mu, dan ni yanzu har na sakata a cikin tsarin rayuwata duk dama waɗannan ƴan shaye-shaye sai mu doddoke su ba wani ƙarfi za su yi tun...
Maganar zucin da mutumin yake ta tsaya ne ganin su duka ukun sun ɗaga riga sun fito da wuƙaƙe soke a jikin wandunan su, sun fito da su daga gidan wuƙar, idanu su Iya suka shiga zarewa musamman Iya da ta ji ta tsure lokaci guda hankalinta ya tashi dan take yanke zuciyarta ta faɗa mata ƴan fashi ne su, dan ta gan su lokacin da take faɗawa mutumin