Showing 12001 words to 15000 words out of 60716 words

Chapter 5 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt

27 Dec 2024

3526

su Baba ne zaune a tabarma dan su da suka ga Iyar ma bata nan duk tunaninsu gidan ƙawarta Jummai ta tafi. Jabiru kamar daga sama ya hango wata kamar Iya a cikin baro ƙafafun nan suna reto ɗaya da takalmi ɗaya babu bai gama dawowa daga mamaki ba sai da suka kusa ƙarasowa ya ji muryarta tana faɗin


"Can ne gidan ga jikana Jaburu can a tsaye" Tana faɗa tana nunawa da hannu. Da sauri Jabiru ya matso kusan baron yana rarraba idanu ta inda zai ga ledar kuɗin dan shi ba ma ta halin da Iyar take ciki yake yi ba, ba ya ma tunanin ya aka yi aka kawo ta a baro, ledar ya warta daga hannunta ya ɗaga ya zazzage a ƙasa kullin rogon nan ne ya faɗo ashe har da ƙarago a ciki wurgar da ledar ya yi yana cewa


"Iya ina maƙudan kuɗin kar dai ɓarayi ne suka tare ki" Ya faɗa daidai ƙarasowar Baba Mamman da Baba Umaru da wani maƙocinsu da suke zaune tare, salati suke suna bin Iya da kallo.


"Kai lafiya mene ne hakan, mai ya same ta?"


"Haba Baba kwa tambayi agwagwa hanyar rafi ai kawai ku tambayi kaza ku sha labari, ni aikin kuɗi nake dako na ɗakko" Ya faɗa yana wani ɗaga kai sama irin na marar kunya.


" Haba ɗan nan yanzu ni ce ma kazar a gaban ƴaƴana kake ce mini kaza kuma kake cewa dakona ka ɗakko sai kace wata buhun barkono" Cewar Iya tana sakin kukan takaici amma ba takaicin maganarsa take yi ba takaicin sarƙarta take yi.Jin ta kasa tashi sai ta koma ta kwanta tana cewa


"Umaru ku ɗago ni ku shiga da ni cikin gida tun kafin jama'a su fara taruwa ana cewa an ɗakko uwarku a baro, baku ji haƙarƙarin nan nawa ba yaron nan mai baro ina ga jefa ni cikin baron ya yi" Ta faɗa har lokacin tana kukan. Jabiru kuwa so yake ya ji batun kuɗin sarƙar amma yana tsoron iyayen nasa su ce bai damu da halin da Iyar take ciki va.


"Ko ma dai a yaya na saka ki ai na taimake ki kuma ni a kan sana'ata nake kuma aikin kuɗi nake"


"Kai nawa ne kuɗin naka"Cewar maƙocin su Baba ganin da Baba Mamman da Baba Umaru sun fito da Iya daga baron za su shiga da ita gidan.


"Dubu ɗaya ne, ɗari biyar kuɗin ɗaukanta na saka ta a baro ɗari biyar na tuƙo ta da na yi"


"Wallahi ƙarya yake duka daga ɗaukan nawa har turani a baron jaka ɗaya(200) Za a bashi ni da ba nauyi gare ni ba" Iya ta faɗa tana daga hannun su Baba ana daidai shiga zauren gidan da ita, babu wanda ya bi ta kanta aka bashi dubu ɗayarsa ya tafi yana wani fito.




Ɗaki aka shiga da Iya tana ta raki tana faɗin


"Waɗannan yara ƴaƴan Allah bani, wanda suka kwashe kayansu daga gaban ma'aiki, yadda kuka saka mini tsabar dukiya a masai Allah ya bi mini haƙƙina" Ta faɗa tana rushewa da wani marayan kuka. Su Baba da suka buɗe baki za su yi magana ma dakatar da su ta yi ta ce


"Ku fice mini daga ɗaki mutanen banza da kun je kun siyar mini mai zai fitar da ni" Sumsum suka fice babu wanda ya tanka dan su basu ma fahimci mai take magana a kai ba.


"Wai Iya Ansai ina dukiyar ne kin ce leda za ki ciko da kuɗaɗe amma na ga ledar sai rogo da ƙuli kamar wasu mayunwata"


"Kai Jaburu wa ma yake ta kuɗi ina rogon da ƙulin ɗakko mini in ci cikin nan nawa tun safe babu abin da ya shiga cikinsa, ina can ina gallafiri cikina kamar an yi sata rogon ma sadaka aka bani...


"Haba Iya ya za ki ce wa yake ta kuɗi bayan kin saka mini a rai kuma ai ni ma tun wainar da na ci da safe ban ci komai ba ina jiran ki kawo nama da lemo"


"Wai kai ka san rijiya da bayan da na tsallake kuwa? To aradu ƙattai uku majiya ƙarfi suka so haike mini Allah ya sa akwai alurar nan na ƙwaci kaina da ita ai ni na san halin da na shiga yau"


"Iya ina kuɗin da za a siya mini ni fa na gaji da gafara sa ban ga ƙaho ba, ga shi har an doshi magariba babu adaidatan"


"Wai kai baka da tausayi ne duk bayanin da nake maka baka ji ba, tun safe ban ci ba ban sha ba, ba sallah ba salati, ga rijiya da bayan da na tsallake na ce ka bani rogon nan na afa a bakin salati na je na yi sallah wa yake zancen kuɗi bayan ba a siyar da kayan kuɗin ba to ɓarayi ne ƴan fasa ƙwabri masu hana ruwa gudu suka ƙwace sarƙar suka saka a masai (Toilet) Ta faɗa tana muskutawa daga inda aka zaunar da ita ta ɗan rarrafa inda kwanon tuwo da kokon da aka kawo mata na safe ta ce


"Ina kwanon abincin rana?" Cikin kuka Jabiru ya fara magana.


"Ba ke kika ce kar wanda ya kawo dambu ba ai ko rabawa basu yi da mu ba,wayyo Allah maraici Allah jiƙanki Babata na yi maraici" Ya faɗa yana ƙara fashewa da kuka. Iya bata masa magana ba sai da ta buɗe kwanon tuwon nan ta ci sosai sannan ta ɗaga kokon ta kafa kai bata ajiye ba sai da ta sha fiye da rabi. Ajiyewa ta yi tare da sakin wata gyatsa, sai sannan hankalinta ta ji ya ɗan dawo jikinta ta gyara zama ta yi tagumi da hannun hagun ɗinta ta fashe da kukan ita ma gaba ɗaya ɗakin ya ruɗe da kukan su ita da Jabiru.




"Kai duniya Allah jiƙan tsohuwarka Jaburu Allah sa kwanciya ta zame mata hutu, wallahi ba da son raina haka ta faru ba ka san abin da baka san shi ba wuyar sha'ani gare shi ashe dai wannan abu babu wanda zai siya ni nake rashin hankalina"Ta faɗa cikin kuka tana zayyane masa abin da ya faru. Nan ta shiga lallashin sa tana cewa.


"Ka yi haƙuri Jaburu gobe an ce masu rabon dabobi za su dawo garin nan, to an yi sanarwa cewa wannan karon da dabobin za su zo ba irin wancan zuwan ba da suka zo su bayar da takarda sai daga baya su dawo su kawo dabobi, duk da an ce zafin nema ba ya kawo samu amma na san wanda ya riga wani kwana dole ya riga shi da tashi gobe asubanci zan yi in tafi yadda zan samo sa da saniya ka san matar bukari wancan zuwan shanu takwas ta samu wasu akuyoyi biyar wasu ma rago ne, to kowa dai rabonsa yake samu ni in sha Allahu shanu zan samu narka-narka wanda za su ishe mu buƙatun mu in an siyar" Ta faɗa tana kallon fuskar Jabiru da ta washe kamar gonar auduga dan shi ma ya ji labari a gari cewa gobe zaa yi wa mata rabon dabbobi wanda wani hamshaƙin mai kuɗi yake rabawa talakawa sai dai a takarda ake rubuta sunayen dabobin da yawan dabbar da za a baya mutum sai a watsa kowa ya ɗauki ɗaya idan aka duba sai a ba mutum dabbar da ya zaɓo sunnanta a takarda. Da wannan Iya ta shawo kan Jabiru ya kwantar da hankalinsa har ta je ta yi alwala ta yi sallolinta tana ja wa ɓarayin nan tsinuwa da Allah ya isa.




Da daddare ta kira su Baba ta sanar da su cewa kada wanda ya bar matarsa ta je wajen rabon dabobi saboda ita za ta je dan haka bata so ake nun ta ana cewa ita da sirikanta sun je tare, wai sai dai su bari idan an ƙara dawowa sa je. Haka suka yi ta nuna mata cewa ta yi haƙuri amma ta kafe sai haƙuri suka ba matan nasu dan a zauna lafiya amma ba dan ran su ya so ba su ma matan sun yi biyayya ne kawai ba dan komai ba domin kowa ya ci burin zuwa wajen ko dan mutum ya samu abin kiwo wancan karon wanda suka samu sun samu alkairi sosai.


*DA ASUBA*


Tun kan a kira assalatu Iya ta tashi daga bacci, dan ma kar ta je baccin gajiyar jiya ya sanya ta makara fita da wuri wajen rabon dabobi dan ta ci alwashin a can za ta yi sallar asuba dan ta hau layi ta samu manyan shanu, bata san cewa ko layi ake hawa kowa rabonsa yake samu. Ana kiran assalatu ta yi alwala ta ɗauki sallayarta sai da ta ji fitar su Baba masallaci sannan ta tashi Jabiru ta sanar da shi idan ya tashi da sassafe ya share jigon da za a ɗaure shanayen kuma ya samu murɗiga-murɗigan ita ce ya musu jigo yadda ana kawo su ɗaure su za a yi. Amsa mata ya yi yana murna dan yau ko nauyin bacci bai yi ba da yake zancen abin duniya ne.


Lokacin da ta fito titin shiru babu mutane dan lokacin duk an shiga masallacin asuba sai mutane da take hanga tsilli-tsilli wanda suka makara suna kan hanyar masallacin.


"Kai yau akwai shagali idan na samu shanaye taɓ lallai za a ga ɗaga kai ni ko raini bana so Allah sa ma in samo shanaye biyar wayyo daɗi garke guda zan yi na shanaye" Take faɗa a zuciyarta tana tafiya duk daɗi ya cika ta gani take ta samu shanaye ta gama.


"Kai ranar nan da ana bani labari na sha dariya wai wata ce ta samu kaza da zakara yo ita kuwa garin yaya" Iya ta faɗa a fili tana tuntsurewa da dariyar mugunta a haka ta ƙarasa wajen da yake filin makaranta ne kuma asabar ce ranar sai ya zamana babu makaranta. Ko tsoro bata yi wajen duhu dilim ta shimfiɗa sallaya ta ajiye fitilar ta ta kabbara sallah ta idar.Tun tana sa ran zuwan mutane wajen har dai ta fara jera hammar yunwa amma bata damu ba burinta kawai ta samu rabonta.


Sai ƙarfe takwas manyan motoci suka fara zuwa, motar shanaye, raguna, akuyoyi, da wacce take cike da akurkin kaji irin abin nan da masu tallar kaji suke zuba kaji, sai kuma wanda suke ɗauke da ƴaƴan kaji wato ƴan tsaki, jaririn kaji. Tun da motocin nan suka tsaya idanun Iya a kan motar shanaye tana ƙiyasta wanda za ta samu dan sai ta hangi ƙoshashshe a zuciyarta ta ce


"Wannan ma yana cikin nawa" Mata sun cika wurin fal dan haka masu rabon suka tsara yadda suka hau layi aka watsa takardu sai kowacce ɗaya bayan ɗaya ta je ta zaɓi takarda ɗaya. Sai da adadin da suke so su ɗauka suka gama ɗauka sannan suka dakatar dan dama takardun da aka watsa ɗin sun ƙare.


"A taho ɗaya bayan ɗaya ana kawo takarda" Haka aka sanar da su, kowacce tana kai wa ana karanta abin da ta zaɓo ana bata, wasu saniya wata akuya wata ɗan akuya kowa dai da abin da yake samu. Wata mata da aka haɗa ta da samarin da ,a su kai mata shanu biyu ƙosassh gida sai faman godiya take har da hawayen farinciki. Wata kuma da wata mtsatstsiyar akuya ƙarama, tun da ta kama igiyar ta fara tafiya Iya take mata dariyar ƙeta a zuciyarta har da ce mata "A gaida gida"


Ana zuwa kan Iya wato layinta ya zo har wani rausaya-rausaya take, ta je tahj miƙa takardar.


"Ƴan tsaki guda uku (Wato ƴaƴan kaji jarirai guda uku su ne Iya ta canko. Wani irin amsa kuwwa maganar ta yi wa Iya a kunne a take annurin fuskarta ya ɗauke.
mm
"Ƴan tsaki uku Malam sai mka ce wata mayya, ko dai shanaye uku kake nufi?"


"Ya shanayen nan? Ƴan ztsaki dai, ba ga shi a rubuce ba"


"Babu wani ko dai baka iya karatun bokon bane, kai na kusa da shi karɓi ka karanta dan Allah kar ya mini maguɗi" Ta faɗa lokacin har idanunta sun fara cikowa da ƙwalla.


"Baiwar Allah ƴan tsaki kika canko guda uku dan haka su me rabonki" Ɗayan ya faɗa yana kallon Iya da har ta fara share hawaye tare da fyace majina.


"Kai jama'a wannan abun naku dai ya zama zaɓe wato sai wanda kuka zaɓa kuka dama kuke ba wa abin arziƙi yanzu saboda Allah ina abin kirki a ƴan tsaki Mai mutum zai ce ya samu kawai dai harkar ƙasar nan ce ta mulkin Tilibu(Tinubu) Amma in ba haka ba ai ba a kyauta mini hatta ku ma'aikatan na riga ku zuwa wajen nan, tun da assalatu na fito, ko sallar asuba a nn na sallata amma sai ga shi wanda suka zo daga bisani sun fini samun abin kirki, har ina yi wa wata dariyar ƙetar samun motsotsuwar akuya ashe dai ni ko kaza ba zan samu ba sai ƴan tsaki...


"Haba Baba wa kika gani ya yu musu a wurin nan kowa fa aka bashi albarka yake sawa ya tafi" Ɗaya daga cikinsu ya faɗa.


"Yo ya na yi ai faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar da shi, gado dai ba na uwata ba aka bani ƙyallan zani ai na samu" Ta faɗa tana matsawa kusa da mai bada ƴan tsakin ya ɗakko wani ƙaramin kwali ya saka mata ƴan tsaki guda uku ya miƙa mata ta karɓa tare da juyawa cikin ɗacin rai ta bar wajen tana tunanin yadda za su ƙarƙe da Jabiru.






A hanya tana ta ganin wanda suka samo shanaye da raguna suna tafiya samarin da suka riƙo musu abin da suka samo suna biye da su, duk wanda Iya ta yi wa kallo ɗaya ba ta maimaitawa saboda takaicin ganin ita tana riƙe da kwali da sallayarta sai fitila.

Jabiru da yake tsaye wajen jigon da ya yi wa shanayen da Iya za ta samo ya kasa zaune ya kasa tsaye jiran zuwanta kawai yake, jikinta sanyi ƙalaw ta shigo gidan bakinta ɗauke da sallama. Wani uban tsalle Jabiru ya doka ya taho wajenta har yana neman faɗuwa.


"Ga Iya, ga Iya" Ya faɗa cike da murna.


"Iya na gama jigon su waye suka taho miki fa shanayen namu bari in taro su" Ya faɗa yana ƙoƙarin yin hanyar wajen ba tare da ya lura da yanayinta ba. Hannu ta kai ta riƙo rigar Jabiru idanunta yana cikowa da ƙwallah ta ce


"Jaburu ban samu shanaye ba"


"A'uzubillahi haba Iya mai za mu yi da raguna ai buƙatunmu sun wuce raguna"


"Kayya! Jaburu abin ya wuce raguna sai dai mu ce lahaula wala ƙuwwata" Tun kafin ta gama faɗa masa sauran ƴan tsaki ta samu kukan ƴan tsaki ya karaɗe masa kunnuwa.


"Ciyat-ciyat" Suke ta kuka. Ƙaran da ya ji ne ya sanya ya warci kwalin hannun Iya ya ajiye a ƙasa cikin sanyin jiki ya buɗe.


"Ciyat-ciyat" Ya yi idanu huɗu da kajin suna ambaton ciyat sai wata ƴar leda wacce aka ƙulla dusar da za a basu.


"Ƴan tsaki fa kika samo Iya" Ya faɗa yana fashewa da kukan takaici, Aliya da Maimuna da suke ɗaki suna jin komai suka tuntsure da dariya dan suna ganin hakan ma alhakinsu ne da ta hana a bar su su je wajen rabon.


"Wallahi Jaburu ka dai gan su suna ciyat-ciyat dan baƙinciki tun da duku-duku nake wajen rabon sallar asuba ma a can na yi wai amma dan wulaƙanci in rasa abin da zan canko sai ƴan tsaki" Ta faɗa tana tsallake kwalin ƴan tsakin ta tafi ɓagarenta cike da takaici, su Baba dama basa nan sai matan nasu da suke mata dariya a ɓoye daga cikin ɗaki.


Jabiru a gaban kwalin nan ya zauna yana ta risgar kukan takaici su kuwa ƴan tsakin suna ta yawon a wurin suna cin abinci a ƙasa, Iya ma a ɗaki ta zauna tana mammatsewa hawayen, tana nan zaune a bakin gado Jabiru ya shigo d hawaye shaɓe-shaɓe ya yi zaman dishan yana kuka wiwi


"Haba Jaburu ka yi haƙuri mana bana son zubar hawayen maraya kar ka saka a rubuta mini alhaki a kan na yi sanadin zubar da hawayenka, Allah ya sani ya kuma gani na yi iya bakin ƙoƙarina amma ban samu damar faranta maka ba" Iya ta faɗa tana rushewa da wani marayan kukan.


"Haka ne Iya Ansai amma ki bar ni in yi kukan maraici na san da mahaifiyata tana raye da yanzu ta yi duk yadda za ta yi ta siya mini adaidaita sahun amma ga shi...


"Haba Jaburu kar ka zama ɗan adama mai manta alheri mana, kar kuma ka zama ciki mai manta kyautar jiya, kana gani dai yadda na sha fama amma hakan bai samu ba ya kake so in yi ko sata zan yi" Ta katse masa maganar ita ma tana kukan shaɓe -shaɓe da hawaye.


"Iya kina da abin da za ki siyar fa ki siya mini"


"Yanzu Jaburu in ba ƴan atamfofin da nake sakawa ba zan siyar in yi yawa tsirara ba, mai nake da shi dama sarƙar nan ce kuma ga shi yadda hali ya kasance"


Yo Iya bakya faɗawa su Baba su baki kashin gonarki ki siyar ki siya mini indai da gaske kina son hana hawayen maraya malala... Kukan Iya da take yi ne ya tsaya cak dan lokaci guda ta haɗiye sai ga ta ta tashi daga zaune ta tsaya a kan ƙafafunta baki a buɗe


"Anya Jaburu kana cikin hayyacinka kuwa gonar da ake nomawa muke ci a cikinta za ka ce in ce a bani rabona?"


"Shikenan Iya babu damuwa a cigaba da noma gonar"


Komawa ta yi ta zauna daɓas tana share hawaye a take wani gumi yana keto mata ba dan son Jabiru da ya mata katutu ba da babu yadda za a yi ta yi ko da maganar nan ne, tana sane da cewa ko sati ba a yi ba Alhaji Audu mai kuɗin garin nasu ya zo yana son ya sayi gonar ta masa tatas ita da su Baba Mamman a kan cewa ba za su taɓa siyar da gonar gadon da mijinta kuma baban su Baba Umarun ya mutu ya bari a matsayin gado. Amma dai ynzu haka za ta daure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login