Showing 3001 words to 6000 words out of 60716 words

Chapter 2 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt

27 Dec 2024

3521

lokacin da ya zauna.


"Babu wanda ya ganni"


"Yawwa ko da na ji, ai na san ku kaɗai ne ƴaƴana kuma ku kaɗai ya kamata mu rufe mu binne kowanne sirri" Ta faɗa tana tsare su da idanu.


"Haka ne Iya" Suka haɗa baki waje faɗa dan sun ƙosa su ji abin da ya sa ta tara su wanda take ta nannago bayan ta ambaci dukiya, bayan kuma a iya sanin su ko kuɗin siyan ƙosai sai sun bata amma kuma yau ɗaya tana maganar dukiya sai dai suna ta maganar ko dai shiriftun tsufa ta fara duk d sun san ragas take sai dai in yau shiriftun ya same ta.


"Ko dai mafarki ta yi ta tsinci kuɗi a leda" Baba Mamman ya faɗa a ransa dan ya rasa mazaunin da zai ajiye maganar tata.


"Iya dai ko cewa za ta yi bara za ta fara tun da mun kasa cikawa Jabiru alaƙawari, take maganar dukiya bayan tana ta neman kuɗin da za ta siyawa Jabiru adaidaita kuma yau tana maganar dukiya" Baba Umaru ma yake maganar a zuciyarsa.




"Bismillahir rahmanir rahim" Bismillar da Iya ta yi ta katsewa kowa zancen zucin da yake. Da kallo suka bita ganin ta tashi tsaye ta basu baya ta ɗaga zani tana ta lalumen siket ɗin ɗan tofinta. Kowa ya zubawa sarautar Allah ido. Sai da ta gama ta dawo ta zauna tana jan hailala da salatin annabi S.A.W. Da kallo suka bi ledar hannunta.


"Iya ba dai tsuntuwar kuɗi kika yi ba, kuma irin wannan ai da tun da zamu masallaci kika bayar aka kai cigiya" Baba Mamman ya faɗa yana bin ledar da kallo.


"Wallahi kuwa dan ma kar a zo a fara yekuwa ana cewa za a gewaya laya" Baba Umaru ma ya faɗa yana kafe ta da idanu.


Baki sake galala take kallon su kafin ra yi ƙarfin halin cewa


"Oh Allah na tuba ni Ansai an zo zamanin da yara suke yi wa iyaye hawan ƙawara, yanzu bakwa bari in mutu ku binne ni ba, ina abu kuna tarar numfashina, to masu gewaya layar sun daɗe basu gewaya ba"


"A'ah Iya ba a yi haka ba, mu ai ba ma so mu rasa ki ba" Baba Umaru ya sake faɗa.


"Mtsss aikin banza shafa lalle a ɗuwawu" Ta faɗa tana fara since ledar. Babu wanda ya ƙara magana illa iyaka sun zubawa sarautar Allah ido, ɗakin ya yi tsit baka jin komai sai ƙaran ledar da Iyar take sincewa.


"Haba Umaru hasken fitilar taka fa yana barin saitin ledar lai da za kake haska saitin inda nake buɗewa" Ta faɗa tana ɗago kai ta aika masa wata harara da ta sa ya gyara riƙon fitilar.


"Kai ma Mamman baka saita sosai ba, yo ni ina dalili ina ɗan mafari kowa hankalinsa yana wani wuri, wato kowanne yana tunanin ƙeƙasassiyar matarsa matan fa ba haihuwa suke ba duk da kun tara mana taron yuyuyu, sai cika mana masai suke da kashi sun kasa haihuwa sai shegen cin abincin tsiya kamar gara" Ta faɗa tana aikawa kowanne su harara. Basu tanka ba dan idan da sabo sun saba da halin mahaifiyar tasu.


Baki a sake suke bin abin da ta fito da shi daga ledar ganin sarƙar tsirkiya irin ta ƴan da, wato irin manyan tsakiyar nan da ake yin sarƙa da su murjani.


"Iya mene ne wannan?" Suka haɗa baki wajen tambaya da mamaki fal a maganar su.


"Ƙundun ubanku ne, na ce ƙundun ubanku ne, in banda yaran zamani har kun sa na yi suɓutar baki ina zagin marigayin ubanku, in fito da kayan kuɗi tsababa amma kuna mini tambayar rainin wayo da rainin hankali"


"Kayan kuɗi?" Suka ƙara haɗa baki a karo na biyu.


"Aikin ɓur in ji tusa, ai ni a nawa ganin duk mai zuwa sama ya taka leda haƙiƙa ya ci ƙarfin tafiya, to abin da ya gagare ku ne ni na taƙarƙare zan yi, dan ku gane irin so fa ƙaunar da nake yi wa Jaburu(Jabiru) Tun da kun kasa siya masa arincaɓa (Adaidata sahu) Shi ni na ce bari na ceto zuciyar maraya daga damuwa ko na samu rabauta ranar ƙiyama, wannan kayan sarƙoƙin a yanzu na san ya ƙara daraja fiye da tunanin duk wani mai tunani yanzu na san ya fi zinari(Gold) Daraja girman nan nasa na san ba ƙaramin kuɗi zai yi ba. Dan haka na ɗakko a siyar a kawo kuɗin a siya masa arincaɓa, a siya masa fege(Fili) A siyi kayan gini da kuɗin masu gini a gina masa gida ka ga ko aure za a masa an huta, sauran kuɗin in je makka da madina ɗakin manzo ku ma kwa sami kasonku na ladan ganin ido ku ja jari"


Tun da ta fara magana bakin su yake buɗe wanwar kowa sakin baki ya yi kamar layar mai tafiya yake bin Iya da kallo na tsagwaron mamaki ganin tsakininta da Allah take magana.




Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay


TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃






Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada.


Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi.


Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa.


Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰


Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari.
Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851
[12/23, 15:51] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1




*ƳAN ADAIDATA SAHU*
(Masu keken napep)






NA






MAMAN AFRAH




*ASSALAMU ALAIKUM*


Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.


ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳


kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu.


a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳


Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA.


09013181851


Page2️⃣


"Iya Yanzu da kuɗin murjanin ne za a siya masa adaidatan, har da fili a yi gini sannan ki je makkah duk a ciki?" Baba Mamman ya yi ƙarfin halin jefa mata tambayar.


"Au Allah, ni abin da na kasa ganewa ma shi ne tambaya kake yi ko neman sani? Magana aka baka ita a buɗe amma kana mini wata magana mai kama da rainin wayo" Ta faɗa tana aika masa harara.


"Ba haka bane Iya abin ne dole a sanya ayar tambaya yanzu waye zai siya wannan murjanin?" Baba Umaru ya faɗa cike da tsoron maganar da za ta faɗa.


"Yo ni da zan nemo masu siya ma ina zan tara ku ai da sai dai ku ga arincaɓar a ƙofar gida, amma ni wannan duk ba damuwata bane, idan kuna ganin a garin nan masu siya da daraja zasu yi wuya sai a ranci kuɗin mota a je birni a siyar idan an kawo kuɗin sai a biya wanda aka ranci kuɗin motar ba shikenan ba dai tun da yake kuɗin motar kuke yi wa ido" Ta faɗa tana karkata kai gefe.


"Iya ba maganar babu masu siya da daraja bane...


"Yawwa ko da na ji" Ta katsewa Baba Mamman hanzari.


"Iya wallahi fa babu wanda zai siya wannan tsakiyar, ban sani ba ko wajen ƴan gwangwan wato baban bola, irin wannan masu yawo da baro suna siyan tsoffin kaya da ƙarafe, idan ya siya da daraja wallahi bai fi ya baki ɗari biyu ba ita ma sai an kai ruwa rana tun... Baba Umaru da ya taƙarƙare yana rattabo bayani ganin Iya ta tsaya tana kallonsa sai ya yi tunanin fahimta take ashe haushi ne ya turnuƙe ta, ya fara ƙoƙarin ƙara ƙaimi wajen mata bayani bai ankara ba ya ji ta wanke fuskarsa da mari.




"Bolo, na ce bolo, dan gwafar ubanka saɓo kake so ka yi? Murjanin nawa ne tun na aurena da ubanka za a bawa baban bola ya siya? Abin da nake saka ran samun miliyoyi a jikinsa,dan na san iwar haka darajarsa ta fi ta zinare (Gold) Amma dan baƙin ciki ka ce wai jaka ɗaya(200) Za a bani sai ka ce wata wacce uwata ta ce in je na gani, sarkar da ko masu ajiye kaya a gidan tarihi suka samu siya za su yi, a ajiye ta a gidan tarihi' Ta faɗa tana rushewa da wani marayan kukan takaici dan gani take Umaru ya gama rainata har zai ce ta kai sarƙar da ta kwashe shekara da shekaru tana ajiya amma a ce wai baban bola za a kai wa ya siya.


"Allah huci zuciyarki Iya" Baba Umaru ya faɗa yana dafe da kunci.


"Iya ki yi haƙuri amma gaskiya ya faɗa miki, dan ko baban bolan ko masu kayan gwangwan ɗin da ya ambata to wallahi ba lallai su siya bama ko da naira ashirin ne, ni ina ganin ki ajiye kike saka kayanki, dan ko ta kwanan baya da aka tsiro yayinta za ki ga ana yin su masu ƙananan tsakiya ne, kuma basu fi ɗari biyar ake siyar da setin su ba yanzu ba a yayinsu sosai bare kuma wannan murjanin da yanzu sai kaɗan daga cikin yarbawa ne suke sakawa yarbawan ma maza s... Tun kan Baba Mamman ya kai aya shi ma ya samu nasa kason marin Iya sai muzurai take cike da ɓacin rai ta buɗe baki cikin muryar kuka ta ce


"Amma ƙur'anin Allah kun gama cin tuwo a kaina,dan cin fuska murjanin ne yarbawa suke sakawa yarbawan ma maza" Ta faɗa tana ɗaga sharɓeɓiyar sarƙar da idan ta saka sai ta zo har kan cikinta saboda tsawo kallon sarƙa da tuna irin burikan da ta daɗe tana ci a kanta ya sanyata fashewa da kuka tamkar a gidan mutuwar da ba a ɗauke gawa ba


Baba Umaru ne ya buɗe baki zai yi magana amma ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu.


"Ya isa! Ku tashi ku fice mini daga ɗaki bana cikin masu wauta kamar ku banzaye masu tunanin banza da baku da aiki sai bin ɗakin matayenku, ku tashi ku ɓace mini a gani tun kan ran kowa ya ɓaci dan idan aka jima kuna cigaba da aibata murjanin nan ina iya ɗaga muku nono d... Tun kan ta kai aya suka tashi sumi-sumi ɗaya yana bin bayan ɗaya Baba Umaru da fitilarsa ko kashewa bai yi ba suka buɗe ƙofar suka fice.


"Mutanen banza kowa da kai tun na haihuwa, ana harkar arziƙi suna yin batun tsiya, to wallahi a bakin ku, da kuɗin murjanin nan zan cika gaba ɗaya burikan da na lissafa muku, mu zuba mu gani, murjanin nan tun yana sabo na daina sakawa, bai fi a ƙirga ba sakawar da na masa n ajiye saboda na san idan da rai akwai ranar da zai yi dajara ake nemansa ido rufe" Ta faɗa tana ɗaga sarƙar ta mayar da su cikin ledojin ta ƙulle ranta duk a matuƙar ɓace dan babu abin da ya ɓata mata rai ya kuma dagula mata lissafi sama da yadda suka ce wai baban bola ne ko ƴan gwangwan za su siya, kuma abin haushin ma wai a bata ɗari biyu.


"Na yi alƙawarin babu wanda zan ƙara kirawo wa a cikin ku a kan batun siyar da sarƙar nan, da kaina zan tafi na siyar a yau ba sai gobe ba, a ɗuro mini kuɗin a ledar viva dan na san sun yi kaɗan a ƙaramar baƙar leda, kai sai na siyo buhhunan barkono guda takwas ma dan daga na dawo idan suka ga ana shigo da buhhunan barkono su san kasuwa ta yi kyau dan sai sun ƙaryata kansu da kansu na cewa sai baban bola ne zai siya, dan yau har kasuwa sai na je dan sai tayin da ya mini dan ba zan siyar da araha ba in zo daga baya in ji wani zai siya da gwaɓi in ke cizon yatsa" Ta faɗa a zuciyarta tana zuwa ta buɗe akwarin ƙarfen nata ta saka ledar a ƙasan kayanta.






Tana shirin rufe akwatin sai gani ta yi an bankaɗo labule baki ɗauke da sallama Aliya matar Baba Umaru ta shigo ɗauke da samirar turon Iya da baban kofi mai koko a ciki. Da hanzari Iya ta rufe akwatin ta yi saurin matsawa daga wajen tana haɗe rai ta ce.


"Na ga ikon Allah faɗa da mai gari ranar salla, ke dai Aliya mai hali ba ya fasa hakinsa wallahi yanzu a ce ba za ki yi sallama ba ki fara nemen izini sannan ki shigo ij an baki dama in ba a baki ba ki koma, amma sai dai ki bankaɗo labule gidif ki shigo sai kin zo tsakiyar ɗaki ki yi sallama" Ta faɗa tana aika wa Aliya harara. Aliya kuwa turus ta yi jin maganar Iya dama ta saba da ɗora hau a gado irin na Iya shi ya sa ma ko damuwa basa yi dan abu kaɗan sai ta ringa sababi.


"A yi haƙuri Iya sallamar nan dai sai da na yi uku ƙwarara a waje na ji shiru ba a amsa ba, to sai na yi tunanin ko kina bayi shi ya sa ma na shigo" Ta faɗa tana durƙusawa za ta ajiye kwanon tuwon da jug ɗin koko.


"Ke dakata! Kar ki ajiye mini tuwon nan naku ci kat ka mutu, abu ɗanye lagaf baya wani dahuwa ku a duniyar nan a ce baku iya tuwo ba ya nuna, ake ci ana santi a ji turo ya tuƙu ya dahu dumurmur da shi kullum abu lagafgaf kamar ɗanmalele" Ta faɗa a fili tana yatsina fuska, a zuciyarta kuma ta ce


"Taɓɗi! Allah tsari gatari da saran shuka, ni Ansai Allah raba ni da aikin da na sani haka kawai ni da zan damƙi sulalla yau, zan zauna cin tuwo da koko haka kawai su ruɗe mini ciki in kafa yin kashi ina sawu bayi, ai ni yau sai dai in ci tsire da balangu da lemon kwalba in siyo kayana idan zan dawo, mu yi burunshi (Brush) Ni da Jaburu"Ta faɗa a zuciyarta tana kallon kwanon tana yatsina fuska kamar ta ga kashi.


"A yi haƙuri Iya za mu gyara"


"Ko ku gyara ko ku cigaba da yin ɗanyen naku ya rage" Ita dai Aliya bata ce komai ta tashi ta fita daga ɗaki


"Idan ma kasuwa ta yi yadda nake so, kayan abincina zan siya in ke girkina in huta da wannan ci kar ka mutun" Ta faɗa tana taɓe baki.
Bayan ta watsa ruwa ta ɗauki galleliyar atamfarta ta saka, tana cikin naɗa gwaggwaron su na tsofaffi Jabiru ya shigo yana tafiya yana kumbura baki lo sallama babu ya shigo ya zauna.


"Jaburu shalelen Iya ɗan gaban goshina waye ya taɓa mini kai"


"Yo ba yunwa nake ji ba ina can masallaci da na yi sallah na kwanta nake bacci sai yanzu na falka cikina sai ƙugi yake yana ƙwallawa ciroma kira"


"Kai amma ban ji daɗin maganar nan ba, amma ungo jaka guda (200) Ita kaɗai ta rage mini amma da yake yau akwai bushasha na san za mu riƙi miliyoyinta, ka je ka siya waina yau babu kai ba cin tuwo" Ta faɗa tana miƙa masa kuɗin bakinsa da nata washe kamar gonar auduga.


"Allah tsunduma ki aljanna Iya, ga shi kin ce yau za a cika mini burina"


" Amin ɗan nan da yardar Allah kuwa yanzu zan tafi na ci kasuwar sarƙar murjanina, kuɗin ma a ledar viva zan sako shi na siyo mana tsire da balangu da lemon kwalba sai mun ci mun ture yau, dag ana dawo za a siyo maka arincaɓa kai har gida zan sa a siya maka a maka aure ni kuma in je makka in siyo maka kayayyaki" Ta faɗa tana dafa kafaɗarsa. Wani tsalle ya doka yana ta murna.


"Amma gwara mu je in raka ki"


"Babu in da za ka je ni kaɗai mintina kaɗan zan dawo iyayenka na ce su je su siyar suka watsa mini ƙasa mai tsakuwa a ido, yanzu da kaina zan je in siyar yanzu kuma zan dawo ka san masu kai kayan irin su barkono da kalwa su ne suke jimawa a kasuwa suna talla da neman mai siya ni kuwa da zan kai kayan maƙudan kuɗi ina zuwa za a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login