Showing 36001 words to 39000 words out of 60716 words
Chapter 13 - YAN ADAIDAITA SAHU Book Complete by Mamn Afrah.txt
shi salin alin an maido da shi aikin mutanen ɓoye ai sai su. Dama an ce in za ka gina ramin mugunta ka gina shi gajere da a ce ya tsaya ya taimaka mata sun gudu tare wataƙila su tsira tare amma yanzu ga shi babu wani ɓata lokaci sun zama ɗaya. Cikin taɓaɓɓan baki Jabiru ya kalli Iya tamkar ya saki ihu dan takaici ganin an maido da shi wannan kango da ya yi wa laƙabi da baƙin kango.
"Da abu ya haɗo ka da mutanen ɓoye sau ɗaya gwara ya haɗo ka da bil adama sau dubu saboda shi bil adama in dambatuwa ma za ku sai ku dambatu ku kwashi ƴan kallo in bai fi ba ƙarfinka amma mutanen ɓoye sha'aninsu wuya ne da shi, yanzu ga shi dai tattabarar tana cikin kangon amma ni da na fita an maido da ni a saman iska a saman iskar ma da baya da baya ba tare da ina ganin gabana ba ya Allah ka fishshe mu aikin da na sani" Jabiru ya faɗa a ransa. A hankali tattabarar ta shiga juyowa sai dai me tana gama juyowa mai makon su ga tattabarar sai suka ga ta zama agwawa. A 360 Jabiru ya tashi zaune daga reran ɗin da yake dan dama tun da aka jefo shi bayansa ya bugu da wurin ko motsawa ya gagara yi amma yanzu ganin abin ba na ƙare bane ya miƙe babu shiri, suka liƙe a waje ɗaya tamkar kantuzar da aka cura ta haɗe.
"Za ku shiga cikin rigar filon nan kafin ƙiftawa da bismillah matsawar ɗaya daga cikin ku ya bari ɗaya ya riga shi shigewa cikin rigar filon nan to fa zai samu an mayar masa da ƙafafunsa sun dawo wajen kansa ƙansa kuma ya koma ƙasa a haka zai cigaba da rayuwa har ranar barinsa duniya!" Suka tsinkayi muryar Malam Tukur ta cika cikin kangon har tana yin amsa kuwwa. Iya sau biyu tana yunƙurin tashi tana komawa daɓas saboda tsabagen fargaba da tsurewa ta san dai idan ba aljannun bane za su mayar da su kiyashi tayaya da girmansu goɗai-goɗai a ce su shige cikin rigar filon zanin gado, ai ta san dai ko kura ta rame ta fi ƙarfin a yagalgala namanta. Har rige-rige ake wajen ɗaukan rigar filon amma cikin rashin sa'a Jabiru ya riga yi Iya ɗaukan rigar ita ma cikin azama ta miƙa hannu ta karɓo suka riƙe su biyu kowa yana ja yana son ya riƙe gefen da zai bi ta wurin da zai shiga cikin rigar filon.
Iya kallon rigar filon ta yi tana jin kamar ta saki kuka amma babu hali.
"Minti ɗaya aka baku ... Tun kan a ƙarasa maganar kowanne ya miƙa kansa kawunansu suka gwaru da juna amma basu damu da raɗaɗin da ya ziyarce su na gwaren da suka yi ba dan kowanne au burinsa kawai ya shige cikin rigar filon.
"Iya ki yi wa Allah da mazonsa ki bar ni in shige ni ne fa Jabirunki marayan Allah" Jabiru ya faɗa cikin raɗa-raɗa dan ya san matsawar su biyu za suke miƙa kansu cikin rigar filon to tabbas za a yi biyu babu domin kuwa babu kan wanda zai shiga bare a yi zancen shigewar mutum ciki har ƙafafunsa. Wata uwar harara Iy ta gallawa Jabiru jin furucinsa.
"Baka da hankali Jaburu wato ga Iya kuka mai daɗin hawa, ni in haƙura wato kai ka shige a mayar mini da ƙafafuna saman kaina, kaina kuma a ƙasa wanda hakan zai sa kowa ma ya guje nu in ma ba a samu masu kai ni bakin ruwa sun ce ƴar ruwa ce ni ba, in ce nan nake roƙon ka ɗazu har ƙafarka na riƙe dan ka tallafa mini mini mu gudu tare mu tsira tare amma ka yi kunnenki uwar shegu ka tsere ka barni wai kai gaja sabon jini ko? Da yake Allah almusawwiru ne ba ya bacci gyangyaɗi ba ya kama shi sai ga shi cikin ruwan sanyi ƙarara an dawo da kai gani ga ka tif da taya to dan haka a nan ka ajiye maganar jika da kaka kowa ya yi ta kansa wato nafsi-nafsi" Ita ma ta faɗa cikin raɗar tana masa hararar ƙasan ido. Wani takaici ne ya turnuƙe Jabiru dan shi a nashi tunanin tun da shi yanzu yake cikin ganiyar shekarunsa ai sai ta tausaya masa ita kuma ta ci nata zamanin dan haka yana ganin ko cikinta aka ce za a mayar mata bayanta a maido ata da bayanta cikinta ba za ta damu ba dan yanzu ai a nashi ganin mutuwa ce kawai ta rage mata. Leɓansa ya danne da haƙori yana raya cewar sai ya shige ya barta in ya so idan ta ga ya shige ta haƙura dan ba zai bari su yi mutuwar kasko ba ko kuma a yi ba wan ba ƙanin karatun ɗan koli. A kusan tare suka ƙara kai kawunansu cikin rigar filon tsabar yadda kaka da jika suka kai kansu cikin rigar filon kuma rigar filon ta musu kaɗan sai kawai rigar filon ta fara yagewa daga kan.
Ɗinke amma cikin su babu wanda ya saurara kowa ƙoƙarinsa ya ture kan ɗan uwansa ya samu nasa kan ya shige dan gudun kar hukuncin ya hau kansa.
"Minti ɗaya aka baku amma kun gagara shigewa, duka jikinku har ƙafafunku za ku shige ni kuma zan rufe rigar filon sai in tafi daku bangon duniy... Tun kafin ya kai ƙarshen maganarsa daga Iya har Jabiru suka shiga rige-rigen fito daga kan nasu daga ciki dan jin maganar da ta girmi tunaninsu dan da a nasu tunanin kan nasu kawai za su saka a ciki amma yanzu sun ji wani sabon salo kiran sallah da usur, wato har ƙafafun su kuma bayan har ƙafafun ma ashe bangon duniya za a tafi da su a cikin rigar filo.
"Turƙashi! Ana dara ga dare ya yi yanzu kenan burinmu na tuƙa arincaɓa a Kano ba zai cika ba haka za mu tafi bangon duniya ƙasar aljannu mu bar su Mamman da bashin jinginar gonar da muka karɓa basu ji ba basu gani ba, mun ga ta kanmu wai an rufe kwarto a cikin ɗakin mai gida" Cewar Iya a zuciyarta.
"Wayyo Allahn mu shikenan mu kuma tamu ta ƙare, wato dai bngon duniya za a tafi da mu dan na san ko a garin gaɓa-gaɓa wannan runɗuma-runɗuman kan namu mai kama da bishiyar giginya ba zai shige ciki ba bare kuma har ƙafafunmu kamar wasu jarirai" Jabiru ya faɗa a zuciyarsa idanunsu suna cika da ƙwalla.
"Bari ku ga aiki da cikawa" Agwawar nan ta faɗa tana nufo su, da sauri suka mayar da kan nasu garin cusa kai sai rigar filon ta rabe biyu saboda dama ta tsufa ga shi kuma an bata ƙarfi. Ganin ta zo gabansu ga shi sun yaga rigar filon ma babu inda za su shiga.
"Allah na gode maka" Iya ta faɗa da ta ga rigar filon ta yage sai dai tumo da cewar idan mutum bai shiga rigar dilon ba hukunci da za a masa mai zafi ne sai gabanta ya shiga dakan lugude.
A take wata iska ta taso ta ɗaga su Iya sama amma ba sosai ba sun dai bar ƙasa amma saman da aka yi da su ko tsawon mutum ba zai yi ba aka fara jujjuya su Iya bata yi ƙasa a gwiwa ba ta datsi tsakiyar suratul fatiha take karantawa da ƙarfi har sai da ta kai ƙarshen surar ta sake sakowa daga farkon sura tana faɗa Jabiru yana maimaitawa sun karanta fatihar kusan sau goma sannan ne fa didimm aka sake su daga saman suka faɗo ƙasa. Babu zato ba tsammani suka nemi agwagwa suka rasa , shirin guduwa suka fara yi sai dai sai da suka ɗauki hanya sai kawai suka ga agwagwar ta ƙara fitowa. Jabiru ko tsayawa bai yi ba ya falfala da mugun gudu Iya ta take masa baya a haka aka fara wasan tseran daga cikin kangon kafin ka ce kwabo Iya ta sha gaban Jabiru ta wuce shi dan ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba ya tsere ya barta ta shiga uku ga zaninta sai cincewa yake tana ɗaurawa daga cikin kangon zuwa wajen ta sake ɗaurin zane ya fi a ƙirga goshin nan nata kuwa duk ta gware a banza saboda gudun ceton rai.
Tsabar ruɗewa da suka zo gaban napep ɗin a tare maimakon Iya ta shiga bayan napep ɗin ko kuma ta zauna a aljihun sai kawai ta kama napep ɗin tana ta ƙoƙarin hawa saman sa ƙafafunta suna zamewa sbodnsantsi ganin babu haza ta saka ta zauna a mazaunin direba kiɗime, shi ma Jabiru da yake a ruɗen yake ai kawai ya shiga baya ya zauna ƙwam yana hangen ƙofar kangon dan gudun kar ta kwana domin yana tsoron abin da ya faru da shi ɗazu ya faru da shi yanzu na mayar da shi cikin kangon da aka yi a saman iska.
Iya duk zaman da ta yi da yake a ruɗe take jira take ta ji Jabiru ya ja napep ɗin sun tafi amma kuma sai ta ji ɗiff.
"Jaburu ka ja mu san na yi mana kar a samu mashkila" Sai lokacin ma Jabirun ya lura da ashe a baya yake a zaune, a hanzarce ya taso daga bayan sai da ta ga ya zo zai shiga sannan ta gane katoɓarar da ta yi na zama a mazaunin direba ko uffan bata ce ba ta tashi ta koma bayan har tana tuntuɓe. Girrrrr Iya ta fara jin wani irin ƙara da napep ɗin yake da aka fara tafiya tamkar zai girgiɗe mata mazaunai sai da ta duba ta gane ashe ta cikin wasu tsakuwoyi da wani gini ya zube aka barbaza a wajen ya bi da napep ɗin kuma daɗin daɗawar ma ba ta hanyar da suka biyo suka bi ba kawai ya hausa wata hanyar ne. da yake ƙarshen unguwa ne wajen ma kamar jeji haka yake.
"Jaburu, kai Jaburu" Jabiru ya tsinkayi muryar Iya tana rangaɗa masa kira, gabansa ne ya faɗi tashin hankalin da yake ciki ya linku dan duk tunaninsa cewa za ta yi ga aljanin nan ya fito a cikin napep ɗin da haka sai ya sha jinin jikinsa tare da jan wani uban birki dan ya gwammace ya fita daga napep ɗin ya gudu a ƙafa dan ba ya jin zai samu wani sauran ƙarfi da nutsuwar da har zai iya tuƙa napep. Iya kuma ganin ya ja birki wanda sanadin hakan ta yi gaba da ƙarfi dan kaɗan ya rage ta hantsila waje, sai da ta yi jarumtar damƙe ƙarfen napep ɗin wanda bakinta ya kusa arba da buguwa a jikin ƙarfen, dan da a ce bakinta ya yi masauki a jikin ƙarfen ba lallai a samu ragowar haƙora a ciki ba.
So yake ya fita a guje sai dai yana tunanin mai zai je ya zo, kar ya tafi da gudu ya ƙarar da ƙarfinsa a gudun sai ya yi nisa ya tsinci aljanin a gabansa an yi ba a yi ba kenan wai rufin ƙofa da ɓarawo.
"Jaburu yawwa dama rai ɗore na gani(Majamfari, wani ganye ne da ake tafasawa mai zazzaɓi ya turara jikinsa da shi) Ka ciro mini in mun je gida kar zazzaɓi ya rufe ni ake A'i ina Indo, ka san an ce riga kafi ya fi magani d... Tun kan ya gama jin abin da xa ta ce wani haushi ya turnuƙe shi a take ya game babu wani aljani da ya shigo napep ɗin dan haka ya warci napep ɗin da mugun gudun da ita ma Iyar ta yi zaton ko aljanin ya hango ya taho jin irin fisgar da ya yi wa napep ɗin. Dan haka bata yi wata-wata ba ta yi dibara ta ɗare can bayan napep ɗin(Boot) Ta shige ji kake jijif ƙaran faɗawarta, ƙafafunta ta ƙudundu ne ta totsu tare da kifa kanta ita a dole ta ɓuyowa aljani.
Allah da ya taimake shi yana bin wata siririyar hanya sai ya ga sun dawo hanyar da suka bi wajen da Malam Tukur ya ce kwanar gidansa, ko kallo kwanar Jabiru bai yi ba gudun ma kar ya kalla ya yi arba da rundunar aljannu dan haka sai ya bi inda suka biyo. Iya da take baya jin napep ɗin ya tsaya cak an daina tafiya sai cikinta ya bada ƙukuluuuu domin bata san mai zai wakana ba, tana can ƙarshen bayan da ta shige ta cusa kanta.
"Iya Ansai sai ki fito ki buɗe mana gidan" Ta ji muryar Jabiru. Shiru ta yi tana kissima abubuwa da yawa dan kar ra je ta fito ta ga cewar wata arangamar suka sake yi, dan yanzu Jabiru ya sar mata tun da har ya iya gudu ya bar ta a cikin kango yanzu sai take ji a ranta sai tana kaffa-kaffa da shi dan gudun ɓacin rana.
"Ni miƙo mini mukullin in sha'awar zama adaidaitar kike" Kanta ta ɗago a hankali tana yin dogon wuya tamkar wata munafuka dan tabbatar da gaskiyar abin da yake faɗa, hango get ɗin gidan nasu da suka mallaka a jiya sai ta ji wani sanyi ya baibaye mata zuciya, haka ta fito tana cewa
"Kai jama'a shiga matsatsi ina ya ga daɗi, Allah ka raba mu da matsin kabari" Ta faɗa lokacin da fito tana kallon Jabiru da ya yi wujiga -wujiga duk ya haɗa gumi sharkaf, wata dariya ce ta so kufce mata amma sai ta maje ta ce
"Yanzu Jaburu sai ka dawo da mu gida, ko cinikin naira biyar bamu yi ba, haka kawai mun ƙone mai a banza da wofi ai da ka bari mun samu fasinja ko jaka biyu mun yi(400) Ma rage asara" Ta faɗa tana saka hannu a ɗan tofinta ta fito da mukullin gidan. Wani kallon kin samu matsala ya jefa mata, dan yana ganin ko ƙoƙarinsa bata gani ba da ya iya dawo da su gida bai yi ɓatan kai ba, sannan da irin jarumtar da ya yi wajen iya tuƙa napep ɗin duk da halin da yake ciki na tsoro da fargaba.
" Allah ka bamu ikon haɗa kuɗin da muka bada jinginar gonar nan, Allah ka kawo mana kasuwa mai albarka albarkacin ma'aiki S.A.W kar damuna ta zagayo Alhaji Audu ya hana gonar nan" Iya da ta ji Jabiru ya ƙyaleta ta jero addu'ar tana mai ɗaga tafukan hannayenta sama.
Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay
TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃
Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada.
Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi.
Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa.
Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰
Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari.
Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851
[12/23, 15:52] Mom mashkur & Afrah: https://youtu.be/qEcb6XGVcBg?si=_yNQhtP6MlL7zcUy
ƳAN ADAIDATA SAHU
(Masu keken napep)
NA
MAMAN AFRA
*Shin kin tura naki screen short ɗin ki na SUBSCRIBE? Free pages yana dab da karewa idan kuma 5OO za ki bada akwai acc no a jiki*
Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp.
ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳
kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu.
a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳
Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA.
09013181851
Page1️⃣0️⃣
Bai ce mata uffan ba har zuwa lokacin, gidan ta buɗe musu ya shigar da napep ɗin ciki ya mayar da get ɗin ya rufe.
"Ah ni Ansai kai ma wannan arincaɓa (Adaidaita sahu) Ka ga ta kanka yau ba dan kai ba da mun faɗawa ƴan garinmu, ko dai mu faɗawa aya zaƙinta" Cewar Iya tana shashshfa jikin adaidaitar.
"Iya na ga