Showing 291001 words to 294000 words out of 375662 words

Chapter 98 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx

10 Oct 2025

7954

a hankali, jin

karatun ta ne ya saka ya karasa shigowa

tunda ya tabbatar a suturce take sai ya

zauna acan gefe yana kallon ta. Bata dago kai ba duk kuwa da zuciyar ta tana son gain sa musamman tunda an gaya mata bashi da lafiya. Haka suke yi

yanzu, tunda aka sallamo shi daga asibiti

take yin fushi da shi akan laifin dukan

matarsa da yayi, amma kuma zuciyarta

tana matukar tausaya masa halin kuncin

da tasa zuciyar take ciki kuma tana neman hanya mai kyaun da zata bi ta saka dan lelen nata a farin ciki in dai hanyar ba haramun bace ba kuma ba zata cutar da shi in the future ba. Sai dai ta cigaba da

tsare gida ne dan jikinsa ya gaya masa ya

san cewa abinda yayi ba dai dai bane ba

kuma ya bata musu rai sosai saboda ya

kiyayi gaba. Plan dinta shine sai yayi

laushi sosai ya bada hakuri sannan ta

saka shi a gaba yaje ya bawa Safina

hakuri a gabanta sai kuma ta hada su su

koma gida tunda alhamdulillah jikin su duk

su biyun yayi sauki sai abinda ba'a rasa

ba. In yaso ita sai da daukarwa safinan

yan aiki tunda Mommyn ta tayi fushi ta

kwashe nata. Kuma ita ta fahimci

Mommyn sosai, dan idan ita ce in her

shoes aka yi wa Mufida abinda akayi wa

Safina ta tabbatar sai tayi abinda yafi

wanda Mommyn tayi. Sai dai kuma ba ta

jin zata kasance in her shoes din, dan

halin Safiya da na Mufida ba daya ba ne

ba. Sannan yanayin auren Mufida da na

Safina ba iri daya bane ba. Amma kuma yau duk plans din na ta sun ruguje…..... She is no longer sure about

what to do, Not after what Safina told her

da yamman nan and also what Hajjo told her

"Mama" Muhammad ya kira sunan ta a

hankali bayan ta kai karshen surar da take

karantawa. Ta dago kai ta kalle shi,

gabanta ya fadi tayi sauri ta dauke kanta

ta kalli gefe, kuka yayi, maybe tun dazu

ne yayi ba yanzu ba but yau yayi kuka, Ba

zata iya tuna ranar da taga dan nata yana

kuka ba tun bayan girmansa. Wannan

kam shine limit dinta, Already kullum

zuciyar ta a karye take in ta ganshi cikin

dakuwa ballantana kuma ace wai yana

kuka? Muhammad Gidado? She can walk

to the end of the earth to prevent that.

She can walk to the end of the earth to

put a smile on his face.

"Mama" ya sake kiran sunan ta. "Mama

dan Allah ki daina fushi da ni. Kiyi hakuri.

In dai akan Safiyya ne na riga na gaya wa

Abba cewa na hakura da ita. Tunda ba

kwa so shikenan. I will accept duk abinda

kuke so. Ni dai dan Allah ku daina wannan

fushin" ta dawo da dubanta gare shi, ta

sauke idonta akan abin karin ruwan da

yake makale a hannun sa, yayi kokarin

boye hannun, ta dauke kanta tace a

hankali "kayi sallah?" Yace "eh nay)" yana

mamakin yadda har yau bata daina yi

masa irin wannan tambayar ba. Tace "kaje

kaci abinci. Me zaka ci? Akwai tuwo kana

so" ya dan bata rai, shi yadda yake jin

makogwaronsa a rue baya jin ruwa ma zai wuce ta cikin sa ballantana tuwo, Ya girgiza kansa "na koshi" ta dauke idonta daga kansa sannan tace "ta shi ka je" ya mike ya fita yana hada hanya, amma a

ransa yasan maganar bata kare anan ba.

Ta bi bayansa da kallo har ya fita sannan

ta sauke ajiyar zuciya. Kowa da irin

kaddarar sa. This is not what they had

planned for him, aure suka so suyi masa

na gata, a lissafin su auren da wuri zai

saka shi ya kara zama responsible mutum

kuma ya kara masa himma gurin kafa

roots din sa ya yi nasa family din and live

happily ever after. Amma plans din su

gabakidaya ya rushe sanda suka fahimci

yarinyar da suka jima da sanin yana

matukar so ta yaudare shi. A lokacin ne

suka yanke shawarar samun wata su aura

masa dan gyara barakar da suke ganin

Safiyya tayi wa rayuwar sa, not knowing

jefa su sukayi a cikin ramin da har yanzu

ya kasa fito da kan shi. Amma yanzu ta

dauri aniyar ganin ta saka igiya ta jawo

kayanta da kanta, ko da kuwa duniya zata

vi mata tofin ana tsine akan hakan.

Sai da ta gama duk abinda zata yi sannan

ta saka kayan baccin ta ta dora dogon

hijab akai ta tafi kitchen, da kanta ta hada

masa abinci marar nauyin da take ganin

zai ya ci, noodles irin dahuwar da yake

so, sannan ta hada masa hot chocolate yana tiriri. A’isha da ta tayata yanka vegetables din tana murmushi tace “Gaskiya zance da yaya karami (haidar) shima yayi rashin lafiya dan ake hada mashi wannan delicious din” murmushi kawai mama tayi bata ce komai ba sai kuma tace mata ta dauka ta kai mata kofar dakin Muhammad din. Ita kuma ta bita a baya.

Sai da A’isha ta ajiye ta juya sannan Mama tayi knocking kofar, shiru ba’a yi magana ba, ta sake knocking shima shiru sai ta tura kofar ta shiga da sallama da tunanin ko yana toilet ne amma sai ta ganshi a zaune akan study table din sa da laptop a bude a gabansa. Hankalin sa gabaki daya yana kan screen din laptop din. Kasacewar ya juya mata baya ne ya saka itama ta tayashi kallon abinda yake kalla.

Safiyya ce akan screen din, kamar video ne yayi mata tana zaune akan swing shi kuma yana tsaye a gefen ta yana dan tura ta da hannun sa kadan. Daga dukkan alama hira yake yi mata mai dadi dan sai murmushi take yi Amma Mama bata jin abinda yake cewa daga inda take tsaye. Yayi zooming fuskarta a lokacin da ta dan kwantar da kanta jikin igiyar swing din tare da lumshe idonta alamar hiran yana mata dadi. Sai a lokacin Mama ta kara tabbatar kyawun halittar Safiyya

[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: Safiyya ce akan screen din, kamar video

ne yayi mata tana zaune a kan swing shi

kuma yana tsaye a gefenta yana dan tura

ta da hannun sa kadan kadan. Daga

dukkan alama hira yake yi mata mai dadi

dan sai murmushi take yi amma Mama

bata jin abinda yake cewa daga inda take

tsaye. Yayi zooming fuskar ta a lokacin da

ta dan kwantar da kanta a jikin igiyar

swing din tare da lumshe idonta alamar

lilon yana yi mata dadì. Sai a lokacin

Mama ta kara tabbatar da kawun halittar

Safiyya. Kyakkyawa ce ajin farko and she

has a unique kind of eyes masu melting

zuciyar duk wanda ya hada ido da ita, and

her smile is contagious, da wahala tayi

murmushi wanda yake tare da ita bai taya

ta yi ba. Ya jima a haka yana kallon

fuskarta Mama da take bayansa tana taya

shi. Sai dai a cikin videon without warning sai

Gidado ya tura swing din da karfi, ta dan

yi karamar kara tare da bude ido cikin

toro, ta kuma kankame igiyar a lokacin

da lilon yayi sama da ita. Daga inda Mama take tana iya jiyo dariyar Gidado daga cikin laptop din, dariyar da ta jima bata ji yayi irin ta ba.

Ta danyi gyaran murya, yayi sauri ya kife

fuskar laptop din amma kuma bai juyo ba

dan ya tabbatar ta gani. Sai data kira

sunansa "Gidado" ya juyo da kujerar da

yake kai amma bai daga ido ya kalle ta ba.

Tace "kazo ka dauki abinci gashi nan a

bakin kofa" ya taso ba tare da yace komai

ba ya zo ya dauka ya koma kan kujerar ya

zauna yana kallon abincin tare da jin

soyayya mahaifiyarsa tana karuwa a

ransa, "ka tabbatar ka cinye kuma ka sha

maganin ka. Zan dawo in gani" yace "to"

da murmushi a fuskarsa, yana mamaki

kuma yana son yadda Mama take bashi

umarni tare da treating dinsa kamar dan

primary.

Har ta juya sai kuma ta tsaya ta yi masa

tambayar da dazu ta manta bata yi wa

Hajjo ba "how did Safiyya's mother die?"

Tambayar ta zo masa a bazata. Ya daga

kai yana kallon ta amma kuma bai ga

alamar wasa a fuskar ta ba. Sai a amsa, a

ransa yana yiwa Safiyya godiya da ta gaya

masa komai "she drawn" ya fada, sai

kuma ya yi tunanin kara mata bayani

"Safiyya ce ta fada cikin water reservoir

when she was 2 years old, Her mother jumped in to save her. Ta fito da ita, ita kuma ta mutu a ciki",. Ta cigaba da kallon sa kamar ba ta fahimci abinda yace ba, amma ya fahimci maganar ta taba zuciyar

ta sosai. Ta juya masa baya da sauri,

maybe trying to hide her tears, sai kuma

ta ce "goodnight" sannan ta fita.

Part din mai gidan ta ta wuce direct, ta

bude kofa ta shiga ta tarar da shi yana aiki

akan computer, ya juyo yana kallon ta sai

kuma yayi murmushi tare da daga hannun

sa yace "na daina, na daina" ya san ta

saka dokar cewa dare lokacin iyali ne da

hutawa da kuma ibada, duk wani abu da

za'a yi na neman duniya to ayi shi da rana.

Amma sau da yawa ba bin dokar tata yake

yi ba sai dai in ta kama shi ya bada hakuri.

Bata kula shi ba dan abinda yake ranta ya

fi wannan, sai ta wuce kan lounging chair

din da take dakin ta zauna, yayi wheeling

study chair din tasa zuwa gabanta ya

tsaya yana kallon ta. Da karyayyiyar

murya tace "dazu naji kace Gidado bashi

da lafiya, me yake damun sa?" Abba ya

dan yi mata murmushi "he will be okay

kamar yadda na gaya miki, Rigima ce da

taurin kai da ya dorawa kansa kwanan

nan" ta gyada kai tana kara fuskantar inda

maganar ta saka gaba "akan Safiyya ne

ko?" Abba yace "yes. Kamar sun samu matsala ne I think. He told me wai sun rabu tunda bama so. Ita ma kuma wai babanta baya so. Amma na san fada

kawai yake yi ba wai rabuwar suka yi ba"

ta danyi murmushi, ita taga abinda ta gani

yanzu a dakin sa.

Ya danyi gyaran murya sannan with

serious voice yace "kince zamu yi

magana akan Muhammad. Wacce

magana ce?" Ta danyi ajjiyar zuciya tare

da cewa "kai ma ka fadi haka ai. You first"

ya sauke ajiyar zuciya sannan yace

"yaron nan ba zai hakura da yarinyar can

Safiyya ba. I think we need to look into

other options than rabasu da karfi. A

shawarce zan saka a yi min bincike akan

yarinyar, sannan zan je inga mahaifinta inji

shi menene take dinsa on all this tunda

Gidado yace min shima ya hana yarinyar

haduwa da shi. Ma'ana yasan abinda ake

ciki kenan. Amma sai mun fara bincike

akan yarinyar dan a lot of things don't add

up about her",

Mama ta dan girgiza kanta a hankali tace

'"ba ka bukatar yin bincike, I have got all

the informations we need about yarinyar"

yayi shiru yana kallon ta da mamaki "how?

When?" Ya tambaya dan ya san bata boye

masa komai. Tace "dazu nayi magana da

Safina, akan zancen komawarta gidan mijinta tunda jikin su duk yayi sauki. She told me wadansu maganganu da suka razana ni sosai" ta fada da karyayyiyar zuciya, ya bata rai, baya son bacin ran

matar ta sa ko kadan, yace "wadanne maganganu kenan?" Ta girgiza kai "maganganun basu da muhimmanci. Surikar muce still.

But she is not the right choiceor Gidado."

Ta danyi shiru kamar yadda shima yayi

yana kokarin fahimtar ta, sai kuma ta

cigaba "sanda Hajjo tazo garin nan tazo yi

mana murnar bikin su Muhammad ta ga

pictures she told me ta san Safina, she

told me they are family friends, and dazu

maganar da Safina ta gaya min akan

Safiyya ta daga min hankali har na fara

mummunan tunani akan Gidado so l

called Hajjo and asked her a favor, nace

dan Allah ta gaya min duk abinda ta sani a

kan Safiyya step sister din Safina. Farko

kamar ba zata fada min ba, sai da ta

fahimci hankali na a tashe yake kuma na

gaya mata abinda yake tsakanin Gidado

da Safiyya da kuma abinda Safina tace

min akan safiyyan wanda har ya tayar min

da hankali nake neman gaskiyar lamari,

Sai ta saka nayi mata alkawarin ba zan

gaya wa kowa a duniya ba, har kai, sai da

nayi mata wannan alkawarin sannan ta gaya min komai".

Ga mamakin sa sai yaga hawaye yana bin

fuskarta, ta saka hannu ta share sannan

tace masa "na riga nayi mata alkawari, bana son in karya alkawarin da nayi mata. Amma abinda zan gaya maka shine yarinyar nan Safiyya ta sha wahalar da

ban taba gani ko jin labarin wadda ta sha

irin ta ba. Ta fuskanci kaddara mai zafi. Kaddara kuma irin wadda zata iya fadawa a kan kowacce ya mace" ta danyi shiru still idonta yana kasa sannan ta sake cewa

"ni mace ce, kuma ni uwa ce, watakila ku maza ba lallai ku fahimta ba amma ni na fahimta. Tunda har Allah ya sarke zaren kaddarar Gidado da na Safiyya har yanzu ta zamanto ita ce farin cikin sa, ni na amine kaje ka nema masa auren Safiyya ko dan mu samu ladan yarinyar nan sannan kuma mu samar da farin ciki ga dan mu".

Ya dan girgiza kai cikin mamakin maganar

ta yace "amma ba kya ganin this will be

too much for him? I mean mata biyu at his

young age? Kuma mata biyun ma

makusantan juna? Zai fuskanci crises

sosai a gidan sa" ta danyi murmushi

"wannan kuma zabin sane, zama da su

gabakidaya ko aka sin hakan zabin sa ne, mu namu shine mu sauke nauvin sa da Allah ya dora mana sannan muyi musu addu'a baki daya".

Tana gama fadar haka ta mike ta cire hijab

din jikinta ta rataye tare da hawa kan gado

ta fara gabatar da addu'ar kwanciya

bacci. Ya bita da kallo abubuwa da yawa

suna yawo a cikin ransa. Duk da cewa

shima tun dazu zuciyar sa ta fara karkata

zuwa da wannan barin amma bai dauka

tata zata chanja akala a lokaci daya ba.

Me Safina tace mata? Me kawarta Hajjo

tace mata? Baya son ya matsa mata har

ta gaya masa tunda tace alkawari tayi

cewa ba zata fada wa kowa ba har shi. Shi

kuma zai so matarsa ta kasance mai cika

alkawari.

Sai dai in dai har zai aikata abinda ta

ambata na aurawa Muhammad Safiyya, to

dole ne sai ya san abinda taki gaya masa

din, ko da kuwa ba'a wajenta ba ne ba.

Da maganar ya kwana da ita kuma ya

tashi, Da ita yaje office da ita kuma ya

tashi, Wannan ya sa daga office din bai

tafi gida ba sai ya gayawa driver dinsa ya

kai shi gidan Alhaji Adam Muhammad, Ya

san address din gidan ne sanda yana

bincike game da Safina lokacin auren

Muhammad. Mai gadi ya bude musu cikin sauri saboda gain kamalar sa, sai kuma ya tsaya yana kallon sa bayan ya fito fuskar sa tana nuna alamar ya gane shi,

ko kuma ace ya gane waye shi.

Ya kara gaishe shi cikin girmamawa sai ya

gaya masa cewa gurin mai gidan yazo.

Take ya ga fuskar sa ta dan saura cikin

yanayin jimami sannan yace "baya jin dadi

kam. Bashi da lafiya. Yau kuma kamar jikin

ya matsanta masa dan tun safe babu

wanda aka bari ya shiga gurinsa. Amma

bara in fada a cikin gidan na san zasu san

abinda za'a y" ya fada yana dosar

Hussein da ya fito daga cikin gida da key

din mota a hannun sa daga alama fita zai

yi, suka dan yi magana da Hussain sai

kuma Hussain din ya kalli Abba sannan ya

koma cikin gida da sauri.

Sai Abba yaji babu dadi a ransa, tunda

bashi da lafiya bai kamata ya zo ya dame

shi ba, Wannan ya sa ya sake kiran mai

gadin ya gaya masa "zan koma kawai.

Allah ya bashi lafiya, Zan dawo gobe ko jibi insha Allah" mai gadin ya gyada kai cikin fahimta sannan

cikin girmama wa yace "zan gaya masa

insha Allah, da zarar na samu ganin sa zan gaya masa" driver din Abba ya bude masa kofa ya shiga sannan suka fita daga gidan a nutse kamar yadda suka shigo.

Hussain ya shiga cikin parlour da sauri,

Mommy tana zaune tana waya da sister

dinta da take aure a Kaduna "wallahi har

yanzu bai ce min komai ba Sakina. Na

rasa yadda zanyi. I tried all I can possibly

do amma babu wata amsa. Yau ma

gabakidaya ya kara rikicewa, ya ki ganin

kowa ya hana kowa ganinsa sai Dr

Ma'aruf. Shima kuma duba lafiyar sa kadai

yayi amma bai ce masa komai ba".

Tana cikin maganar Hussain ya shigo, ta

lura magana yake son yayi mata sai tayi

masa alama da hannu cewa ya fadi abinda

yake son fada, yace "baban yaya

Muhammad ne yazo, yana waje wai yana

son ganin Daddy" cikin sauri tace "Sakina

zan kira ki later" ta katse kiran tana kara

kallon Hussain da shima yake tsaye yana

jiran abinda zata ce "baban Muhammad

kace? Wanne Muhammad din?" Ya dan

bata rai "Muhammad din Safina mana,

Shine yazo gashi can a waje yace yana

son ganin Daddy, gashi kuma kinga

Daddy tun safe yace kar wanda ya shiga

gurinsa shine nazo inji me za'a gaya

masa?" Ta mike da sauri kamar zata fita waie sai kuma ta dawo da baya "je ka sake duba Daddyn naku ka ga ko ya bude kofar" ya fita amma bata iya hakura ba sai

ta bi bayansa tana jin dadi a ranta, at last iyayen Muhammad sun yunkuro da niyyar yin maganar da zata gyara auren


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login