Showing 93001 words to 96000 words out of 375662 words
Chapter 32 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx
mutu, Alhaji Haladu ma ya
mutu, Menene kike so zaki yi yanzu?" Tayi
shiru tana tunani sannan tace "ni ban sani
ba, Ni ban taba yanke wa kaina hukunci ba.
Yanzu tunda kazo kai zaka gaya min abinda
zanyj" ya kalli su Safiya da suke gefe suna
wasa yace "ki hado kayan ki ki taho mu tafi,
kina da sauran yarintar ki wata kila Allah zai
baki wani mijin sai ki sake yin auren ki" ta
danyi tunani sai ta gyada kai da sauri
"shikenan yaya, dama nima ba jin dadin
zaman gidan nan nake yi ba, zamu hada
kayan mu sai mu biku kawai" ya girgiza kai. kayan mu sai mu biku kawai" ya girgiza kai
yana kallon ta yace "ki hada kayan ki nace
ba ku hada kayan ku ba. Wadannan yara ba
da su kika zo gidan nan ba, ki bar su a inda
kika same su nan ne gidan uban su. Ke kadai
ce nauyi na, da ke kadai zan tafi, su nauyin
dangin ubansu ne, su zasu kula da su".
Ta bude ido tana kallon sa sannan ta kalli
yaran nata da suke ta wasan doki a tsakar
daki, Safiya tana yiwa Khadijah doki Sauda
kuma tana binsu a baya. Jabiru ya mike yace
"zan kara kwana biyu a garin nan saboda ki
samu ki shirya a nutse, jibi zan shigo in
dauke ki mu tafi". Ya dauki sandarsa ya juya
ya fita.
Ta zauna ta dafe zuciyar ta tana kallon
yaranta. Kamar yadda ta fada, bata taba
yanke wa kanta hukunci ba a rayuwarta, sai
dai duk hukuncin da aka yanke mata ta bi
shi, yanzu kuma gashi an yanke mata
hukuncin rabuwa da yayanta, yaran da basu
da kowa kaf duniya sai ita. Ya zata vi ta tafi
ta barsu? A gurin wa zata tafi ta barsu? Me
zai faru da su in ta tafi ta barsu? Ita bata da
ilimi, bata san abubuwa da yawa na rayuwa
ba amma ta san cewa duk duniya babu
abinda take so sama da wadannan yaran
guda uku,
15
A
4
P
8:16 PM
Kwana biyun nan haka tayi su cikin rashin jin
da din zuciya, har sai da matar Jabiru da
take tare da ita har lokacin tayi ta tambayar. take tare da ita har lokacin tayi ta tambayar
ta abinda yake damunta amma sai ta dauka
kewar mijinta ne, a rana ta biyun Jabiru ya
dawo daukan su, ya fita da kayan iyalinsa da
suka zo dasu ya dawo yace da Hadiza ina
nata kayan? Ta girgiza kanta tana goge
hawaye daga idonta tace "bazan iya rabuwa
da su ba. Ba zan iya tafiya in bar su ba. In
har na rabu da su to a cikin makara nake
za'a kai ni kabari na, ko kuma sune a cikin
makara za'a kai su nasu kabarin" ya kalle ta,
ya kalli yaran da suke zagaye da ita suna
rike da zanin ta amma duk da haka bai ji
cewa ya kamata ya tafi dasu gabaki daya ba
shi a iya fahimtar sa ta rayuwa gani yake yi
yara, musamman yara mata dole ne su
zauna a gidan uban su, a ganinsa haka shine
dai dai.
Yace "shikenan. Ki zauna tare da su din,
amma ki sani in kina zaune a gidan nan tare
da yaran nan babu namijin da zai aure kj" shi
babbar damuwarsa akanta ita ce kar ta rasa
mijin aure, Har zai tafi kuma sai ya dauko
kudi daga aljihunsa a kulle a leda ya mika
mata sannan ya juya ya tafi. Ta bishi da kallo
tana tunanin ko zasu sake haduwa ko kuma
shikenan?
A ranar yadda Hadiza taga rana haka taga
dare da yayan ta a gabanta tana lissafin
yadda zata fara wannan rayuwar amma ta
kasa yanke shawara. In ta kalli yarn ta tuna
cewa yanzu dukkan nauyin su yana wuyanta
sai taji toro ya kamata. In sun tashi da safe
ma yanzu ita zasu ce ta basu abincin. ma yanzu ita zasu ce ta basu abincin
karyawa, da rana ma haka, suturar
sakawarsu makarantar su, magani in basu
da lafiya, ga kuma overall tarbiyyar su. Ta
kirga kudin da Jabiru ya bata "dubu goma"
su kadai ne abinda ta mallaka a yanzu. Ta
ina zata fara?
Hayaniya ce ta tashe ta da safe da yake sai
da assuba ta samu bacci, a cikin hayaniyar
ta taji ana ambaton sunanta, ta mike da
sauri taga yayanta su ma duk sun tashi suna
kallon ta fuskokin su cike da toro. Ta kuma
fahimci hayaniyar a kofar dakin ta ne, Ta
tashi ta bude kofa tare da tura yayan ta baya
tana kare su da jikinta yadda ko ma menene
ita zai sama ba su ba. Matan gidan ne da
yayan gidan mata wadanda basu koma
gidajensu ba suke ta masifa. Kusan duk a
lokaci daya suke maganganu amma ta tsinci
was daga cikin maganganun nasu
'"wallahi ba zamu yarda ba, abinda akayiwa
baban mu ba za'a cigaba da yi mana shi ba"
"tunda yan'uwan ta suka fara zuwa, Allah
kadai ya san me suke kawo mata"
"wanda yazo jiya ina kallo ya mika mata wani
abu a leda, jikina kuma ya bani asiri aka
kawo mata zata binne mana a gida mu ma ta
mallake mu"
Hadiza ta fara kokarin kare kanta "wallahi
babu abinda suka kawo min, kudi ne kika ga
ya bani", ya bani"
Amma babu wanda ya saurare ta, aka jawo
ta ita da su Safiya aka fito da su waje
sannan aka fara watso musu kayan su
wajen, tana kuka tana rokon mutanen nan
amma basu barta ba, sai da makota da
sauran yan unguwa suka shiga cikin
maganar amma aka kasa sasanta su, su
haushin duk abinda Alhaji Haladu yayi musu
ne suke kokarin hucewa akan Hadiza da
yayanta suna gain cewa sune sanadi,
bayan su kuma a nasu bangaren basu da
laifin komai musamman ma yaran.
Daga karshe dai aka tafi gurin dagaci aka
sanar da shi, ya aika aka kira su har yara
mazan dan a sasanta su amma abu yaki
yiyuwa sunce su ba zasu zauna da ita a
gidan ba, a karshe dagacin yace to ai itama
Hadiza ita da yayan ta suna da gadon Alhaji
Haladu, dan haka ya umarci limamin
unguwar su da yaje ya raba gadon Alhaji
Haladu a bawa Hadiza nata ita da yayan ta
dan su samu gurin zama da kuma abinda
zasu rike kansu.
Amma sai dai da aka zo rabon gadon sai
babban dan gidan yaya Malam yace ai Alhaji
Haladu duk ya siyar da kadarorinsa kafin
rasuwar sa yay wa Hadiza da yaran ta
hidima, yanzu abinda ya rage kawai shine
gidan da suke ciki, Wannan ya sa gidan
kawai aka raba a matsayin gado, shima
kuma gidan su ka nemi cewa a fitar wa da
Hadiza bangaren ta daga gefe dan basa son. Hadiza bangaren ta daga gefe dan basa son
zama da ita. Shima kuma limamin sai yayi
hakan dan in ba'a raba su din ba ba za'a
samu kwanciyar hankali ba.
6
3
8:16 PM
Hadiza da yayanta sun samu dakin soro,
inda nan ne da dakin Alhaji Haladu, tare
kuma da rabin soron dan su samu hanyar
shiga dakin nasu. Dakin ciki da falo ne da
bandaki a ciki, sai dai kuma matsalar shine
dakin nasa yafi ko ina tsufa a gidan, ginin
yafi na ko'"ina lalacewa. Amma duk da haka
Hadiza taji dadin samun seclusion daga
jama'ar gidan. Ta gyara dakin ta jera
furnitures dinta da kayan sakawarsu da
sauran tarkacen ta. Suna cikin gyaran kayan
nasu ne suka ga anzo da kwano irin wanda
ake rufi da shi an raba soron biyu dai dai
yadda liman ya raba musu, wato hanyar ma
ba zasu hada da su ba. Bata gama mamakin
hakan ba sai ji tayi ana buga musu wani
kwanon a windows din su wadanda suke
tsakar gidan. Wannan ya sa dakunan nasu
suka yi tsananin zafi tunda babu taga ko
daya kuma kofar ma gashi an saka musu
kwano an rufe inda iska zata shigar musu,
Kuma tunda basu da kitchen zai ya zamana
a kofar dakin su suke hada wuta suyi girki.
Wannan shima ya taimaka gurin kara zatin
dakunan.
Farko sauran kudin hannunta suka fara
cinyewa, daga nan ta koma daukan kayan
dakin ta daya bayan daya tana kaiwa gurin
dillaliya tana siyarwa a wulakance tana siya. dillaliya tana siyarwa a wulakance tana siya
musu abinci. A haka har suka cinye duk
samiru da kwallayen ta na aure, a lokacin ne
kuma ta fita daga takaba. A lokacin da take
lissafin inda zata samu wasu kudin ne Safiya
ta kawo mata shawara "Baba Hadiza ki ringa
dafa min wake da shinkafa ina yi miki talla,
sai muke samun kudi muna ajiyewa" Sauda
tace "nima zan ringa yin tallan, nima zan
¡ya" Khadijah tace "Baba Hadiza nima zan
yi".
Hadiza ta tsaya tana kallon su sai ta girgiza
kai, "ba zan dora muku talla ba, in kun tafi
talla ta yaya zan kula da ku? In wani abun ya
same ku a can kuma fa? In kuna zuwa talla
kuma a wanne lokacin ne zaku je
makaranta?" Safiya tace "in mun dawo daga
makarantar zamu ke zuwa tallan ai" Baba
Hadiza ta sake cewa "ba za kuyi talla ba" sai
kuma ta kara da cewa "ni zanyi. Zamu ringa
yin abincin siyarwa ku ku tafi Makaranta ni
kuma in tafi talla, a haka zaku yi karatu har
ku girma kuje babbar makaranta ku samu
babban aiki ku gina babban gida sai ku zo
ku dauke ni ku kula da ni, yanzu amma ni ce
zan kula da ku".
Washegari ta kira dillaliya har daki ta sayi
gadajen ta gida biyu tun na aure, ta sauke
musu katifun kasa tace sun she su kwana,
Kudin kuma da su tayi jari. Daga nan sana'ar
wake da shinkafa ta fara, kullum zata shirya
Safiya da Sauda su tafi makaranta ita kuma
ta dafa wake da shinkafa ta goya Khadijah ta
dauki abincin aka ta tafi bakin kasuwa da. dauki abincin aka ta tafi bakin kasuwa da
tasha talla, su kuma in sun taso zasu zo suci
abincin da ta ajiye musu sannan su yi wanke
wanke su gyara musu dakin su sai su tafi
makarantar islamiyya, kafin su dawo ita
kuma ta dawo sai tayi musu wanki ta
shanya akan langa langan kofar dakin su
dan ko shanya ba'a yarda ta shiga cikin
gidan tayi ba. Sannan tayo cefanen abinda
zasu dafa gobe. In dare yayi kuma anan
soron su suke shimfida tabarma su zauna
suyi ta hira tana basu labarai, wani lokacin
na babansu wani lokacin na nata yan uwan,
wani lokacin kuma lissafin abinda take so su
zama nan gaba.
Farko ba sa samun wata riba, except that
suna samu su ci abinci kuma jarin su bai
karye ba, daga baya kuma sai Allah ya buda
musu sana'a ta kankama sosai har jarin ya
ishe su suka fara yin awara da daddare a
kofar gidan. Tun a ranar da suka fara dora
kaskon awara Dauda yazo wucewa ya gani
yace "ba zaku mayar mana da kofar gida
dandali ba, ko ku sauke kaskon nan ko kuma
duk ranar da na kuma ganin sa in barar da
shi". Safiya ta tashi zata yi masa rashin
kunya Baba Hadiza ta hana ta, sai suka
janye suka koma kofar gidan makota suke yi
a can,
Shekarun su biyu a cikin wannan yanayin, a
cikin wadannan shekarun sun kuma
shakuwa da junan su sosai, Basu da wani
tension zasu ci su koshi sue makaranta
kuma suyi wasa da junan su. Basu da kudi. kuma suyi wasa da junan su. Basu da kudi
amma suna da junan su kuma suna gain su
kadai sun isi kansu.
12
8
2
8:16 PM
A lokacin ne wata rana suna tafiya a kasuwa
zasu yi cefanen abincin siyarwar su sai
Safiya ta ga gidan hoto "Baba Hadiza dan
Allah mu shiga muyi hoto muma" Baba
Hadiza tace "wanne irin hoto kuma dan bata
lokaci? Muyi sauri mu tafi gida kar lokacin
dora awara yayi azo nema bamu fara ba"
Safiya ta kara rike hannun ta "dan Allah
Baba Hadiza mu dauka, kinga yanzu Baba
ko hoton sa bamu da shi". Wannan ya karyar
da zuciyar Baba Hadiza, tabbas ko hoton
Alhaji Haladu basu da shi. Sai ta amince
suka shiga suka dauki hoton. Not knowing
wannan hoton shine zai zama memory din
su.
The first tragedy struck shekaru biyu da yan
watanni da rasuwar Alhaji Haladu, ranar
Khadijah ta tashi da mugun zazzabi lokacin
tana da shekaru shida a duniya, Baba
Hadiza ta bata magani ta kwantar da ita a
daki amma har su Safiya suka dawo daga
makaranta zazzabin bai sauka ba sai ma zafi
da jikin ya kara yi, aka sake bata wani
maganin har zuwa washegari amma zazzabi
bai sauka ba, a lokacin ne kuma suka lura
cewa wuyanta ya sankare bata iya juyashi
gefe, sannan kuma bata iya hadiyar abinci.
Sai kuka take yi "Baba Hadiza wuyana ciwo
yake yi, ki kaini asibiti" ta fada da kyar. yake yi, ki kaini asibiti" ta fada da kyar.
Babu shiri Hadiza ta kaita chemist aka duba
ta aka ce sai asibiti, suka je asibiti a take aka
kwantar da su aka ce sankarau ce ta kamata
saboda rashin wadatacciyar iska a dakin da
suke kwana. Aka rubuta musu ma gunguna
da allurai ga kuma kudin gado, babu shiri
hadiza ta fasa bankin da take fara ribar
sana'ar ta ta biya duk kudaden da ake
nema. Kwanan su biyu a asibitin jikin ya sake
ta'azzara aka tura su asibitin Gusau, a
lokacin Khadijah ko magana bata iya yi. A
can sai da duk abinda Baba Hadiza ta tara
suka kare wajen magani, dama ba wani abun
kirki ta tara din ba. Da kudin hannun ta suka
kare ta shigo mota ta dawo Kura ta ringa bin
gidajen yan uwa da yayan Alhaji Haladu
akan su taimakawa yar uwarsu Khadijah su
cece rayuwar ta amma babu wanda ya
taimaka mata, haka ta ranci kudin mota a
makota ta koma Gusau, kwanan ta biyu da
komawa Allah yayi wa Khadijah rasuwa.
Mutuwar Khadijah ta taba Baba Hadiza fiye
da sauran mace macen da akayi mata,
yayanta sune treasure din ta, zata iya bada
ranta a saboda su amma ita mutuwa bata
tambayar zabi wanda lokacin sa yayi shi
take dauka. Su Safiya sunyi kuka kamar
idanun su zasu fado kasa dan suna matukar
kaunar kanwar ta su amma Allah ya fi su
santa. Sai dai ta tafi ta bar wani rami a
zukatansu wanda babu wani wanda zai iva
cike shi. zukatansu wanda babu wani wanda zai iya
cike shi.
Daga nan kuma sai rayuwa ta komawa su
Safiya baya, babu jari babu riba babu abinda
za"a siyar a samu jarin sai tarin basussuka
da suke kansu, ga kuma kewar Khadijah. A
neme nemen jarin da Baba Hadiza take yi ne
taje gidan Hajiya Kyauta.
Hajiya Kyauta macece yar kasuwa, tana
dillancin manyan kaya kuma tana kasuwanci
zuwa garuruwa da yawa a Nigeria wani
lokacin ma har kasashen waje take zuwa.
Baba Hadiza ta nemi ta bata aron kudi ta
sake tayar da jarin wake da shinkafar ta
amma ita kuma sai ta nemi ta bata jinginar
wani abu kafin ta bata jarin. Baba Hadiza ta
gaya mata bata da komai sai tsofaffin
katifun da suke kwana akai sai kuma kayan
sakawar su. A lokacin ne Hajiya Kyauta ta
bata shawara "kina da yammatan yara
kamar wadannan, ki bani ko da babbar ne in
tafi da ita wani garin in kaita aikatau, duk
wata za'a ke aiko miki da kudin da zai isa ki
kula da kanki ki kuma kula da karamar, ita
kuma kin ga an dauke miki nauyin kula da
ita" Baba Hadiza ta juya tana kallon Safiya
da duk ta fita daga hayyacin ta saboda
wahala, tace "aikatau kuma Hajiya, Satiya ba
zata iya aikatau ba" Hajiya Kyauta tace "to ai
koya zata yi. Na kai yara da yawa kuma
sunyi arziki iyayen su ma haka. Baki san a
inda arzikin ta yake ba" Baba Hadiza ya
girgiza kanta "ba zan iya yi mata haka ba. Ba
zan dora mata nauyin kula da ni da yar uwar. zan dora mata nauyin kula da ni da yar uwar
ta ba. Ni ce mahaifiyar ta. Ni zan kula da ita.
In aikin ne ma ni ki nema min in ringa yi ina
samun kudi ina kulawa da su".
14
5
8:16 PM
Hajiya Kyauta tace "to ai in dai zan dauke ki
in tafi da ke sai dai ki barsu anan ke nan.
Kina da wanda zaki barwa su?" Hadiza tace
"bani da kowa sai Allah. In kina da hanya
dan Allah ki samar min aikatau din anan
garin yadda ba zan rabu da su ba. Sai in
ringa yin aikin ina tara kudi har in samu jarin
da zan dawo da kasuwanci na".
Haka ce ta kasance, aka samo wa Baba
Hadiza aikatau take yi a gidan wasu masu
hannu da shuni, kullum da safe su Safiya
zasu fita makaranta ita kuma zata tafi gurin
aikin ta bayan ta dafa musu abinci ta ajiye
musu, in sun dawo zasu ci abinci suyi
ayyukan su a gida sannan su taflislamiyya,
da daddare zata dawo ta taho musu da
abinci daga can. Albashin ta dashi suke
samu suke cin abinci da kudin sabulun
wanka da wanki da littattafan makaranta,
dan duk talaucin su Baba Hadiza ba ta yarda
sun daina karatu ba, Suttura kuma mostly
kwance ake basu a gidan aikin ta da kuma
makotan su, A haka suka sake yin wasu
shekaru biyun, Baba Hadiza ta dan tara jari
kadan sai ta dawo da yin awarar dare tunda
da rana tana gidan aiki babu damar tallan
wake da shinkafa.
A lokacin ne kuma second traaedv va faru. wake da shinkafa.
A lokacin ne kuma second tragedy ya faru.
Lokacin Safiya ta yi jarabawar kammala
primary school, Sauda kuma