Showing 282001 words to 285000 words out of 375662 words

Chapter 95 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx

10 Oct 2025

7974

yi mata a gidan?" Mommy ta hau shi da fada "eh kai din nace kaje, ko ba zaka je ba? Ai ba aiki nace kayi mata ba, kawai kwana zaka taya ta zuwa gobe mu ganj" Hussain ya tura baki yana magana kasa kasa tace "wallahi idan ba ka mayar da bakin nan dai dai ba sai nazo na fasa shi. Marar kunya fitsararre", Ya mike ba tare da yayi wa

kowa sallama ba ya fita, sai Hassan ya tashi ya bishi, ta harari bayan Hassan din tace "na ga kashin awaki ma karewar hadin kai".

Shigowar Umma ce ta katse mata maganar ta, ta kara hade rai, Umma ta zauna suka gaisa sama sama ta tambayeta jikin Daddy sai ta tashi tace Salima ta zo su tafi, nima na tashi na raka su waje har zuwa bakin mota nayi musu godiyar zuwan da suka yi, uncle Ahmad yace min ya ga sakona kuma ya gode, zamu karasa maganar ta waya, na gyada kai kawai suka tafi ni kuma a koma cikin gida. Amma sai na koma part din daddy, na tarar shi kadai ne, yana duba wani abu a wayar sa amma yana gani na sai naga yayi sauri ya kife fuskar wayar a kasa sannan ya bata rai kamar babu abinda yake yi, nayi kamar ban gani ba nima sai na zauna a gabansa na tambaye shi saukin jikinsa ya amsa min da cewa yaji sauki sosai, muka danyi maganar feeding tube din da za'a saka masa da kuma

breathing machines din da za'a siyo. Sai kuma yace "Ahmad ya ce min kin mayar masa da aikin sa" na sunkuyar da kaina sannan na dago nace "I never

wanted to take it. Na fadi maganar ne cikin bacin rai sanda na fahimci yana kokarin goyon bayan Mukhtar.but aikin sa nasa ne except idan shine da

[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹Safiyya❤️‍🩹

Episode Fifty Seven; The Talk 2

Not completely edited, my tire is tired 😂

He sat like a stone as I told him all that has happened to me tun ranar birthday dinsa da muka je cin abinci restaurant, na bashi labarin gaskiyar abinda ya faru da ni a ranar da kuma duk abubuwan da suka biyo bayan hakan, nayi amfani da kalmomin da nasan zai fahimci abinda nake nufi ba tare kuma dana bayyana abubuwa masu nauyi ba. Sai da na dangane har ga labarin yadda naji maganar aurensa da Safina da kuma haihuwar Junior sannan da dawowata Nigeria.

Na bashi labarin zargin Mukhtar da na fara yi, aurena da shi da kuma tabbatar da zargin nawa da nayi bayan auren zuwa rabuwar mu da conditions din da na dora Mukhtar din a kai dan kare martaba ta da ta Junior.

Har na gama maganganun nawa bai ce komai ba. Ni ma kuma ban iya daga kai na kalle shi ba har sai da na kai aya dan bana jin zan iya hada ido da shi a yanzu, bana jin zan iya sake hada ido da shi ma

gabakidaya.

Jin ya cigaba da yin shiru tsahon lokaci bayan na gama magana sai na mika hannu a hankali na kama hannun sa da nake gani ta cikin hawaye na, na kuma yi

kokarin kiran sunan sa, "Muhammad.......?." Naji hannun sa yayi zafi kamar na wanda yake cikin zazzafan zazzabi, Sai ya zame hannun na sa daga

cikin nawa da sauri sannan kuma ya mike da sauri kamar wanda aka watsa wa wuta yayi hanyar fita daga falon. Na mike nima da saurin ina jin wani irin tashin hankali da fargaba suna mamaye zuciya ta. Na mike rigarsa tare da kiran sunansa cikin karyayyiyar zuciya "Muhammad……….." Ya kwace rigarsa da karfi sannan cikin wata irin muryar da ban san shi da ita ba ya fara magana "I will kill him.... I will kill him.….. I will kill him...." Na fahimci wa yake nufi da him din, hakan kuma ya kara tayar da hankali na, na sake shan gabansa da sauri ina kuka sosai a lokacin,"Muhammad dan Allah ka tsaya, Muhammad Gidado..." Na fada ina

kokarin ganin ya kalle ni amma sai ya ture ni gefe daya ya saka hannu zai bude kofar sai na zagaye shi da hannayena na dora kaina a bayansa na kama kuka mai ratsa zuciya,

Ya tsaya first, sai kuma ya dauke hannunsa daga jikin handle din kofar tare da kife kansa a jikin kofar, ina jin yadda dukkan jikin sa yake karkarwa da wata irin

zuciya da ban san yana da irin ta ba. Mun jima a haka sai kuma ya juyo da sauri ya zagaye ni da nasa hannayen tare da kife fuskarsa a saman kaina ya kama kuka. Nima nawa kukan na cigaba, ban san adadin lokacin da muka dauka a haka ba,amma mun ci kukan mu mun gode Allah. Sai kuma ya sake ni ya zare hannuna daga jikin sa ya koma cikin falon ya zauna tare da juya fuskar sa gefe. Na fahimci baya son inga kukan sa ne, wai shi namiji, ni kuwa babu abinda ya dame ni in kuka yazo min a tsakiyar titi ma zan iya zama inyi kuka na in gama in tashi in tafi, wanda ya gani matsalar sa ce ba tawa ba.

Na koma nima na zauna a gefensa, sai dai har lokacin yaki yarda mu hada ido nima kuma ban shirya yin hakan ba dan haka ban kalli fuskarsa ba nace "Please

Muhammad, promise me one thing, dan Allah kayi min alkawarin ba zaka ko kalli inda Mukhtar yake ba. Please, wannan ita kadai ce alfarmar da nake nema a wajenka" ya goge fuskarsa yana girgiza Kai, sannan yayi ajiyar zuciya yace *I can't. I can't make a promise that I cannot keep" na zamo daga kan kujerar na sauko kasa gabansa "you can. Dan Allah. I went through a lot to keep you clean and away from all these. Please don't go and get your hands dirty by touching him. Daukan doka a hannun mu ba zata jawo mana komai ba sai......" Ya katse ni cikin fada tare da sake mikewa tsaye "kina nufin shikenan? Yayi a banza kenan? Kin barshi saboda kina da sayin zuciya and family dinki sun goya miki baya just because dan uwa ne shikenan kuma magana ta kare? Shikenan babu abinda aka yi masa babu kuma abinda za'a yi masa?" Na mike nima "akwai abinda nayi masa Muhammad. Na kai shi kara grin alkalin alkalai na kuma tabbatar zai saka min. Ina zaune ne kawai ina jira. Sakayyar da Allah zai yi min ta fi hukuncin da kowanne irin alkali zai yanke a cikin alkalan duniyar nan. In ka taba shi yanzu hukunci zai dawo kanka ne kai kuma. Saboda baka da wani ground na shari'a da ya baka damar daukan hukunci akan abinda aka yi min. Please Muhammad, yadida na bar maganar nan ka barta kai ma. Idan da ace da akwai wata hanyar da zan bi mu wuce wannan level din ba tare da na gaya maka maganar nan ba Wlh ita zan bi. Idan da ace xan iya cire maka zafin da kake jl a zuciyar ka da na cire maka shi. You have no idea courage din da nayi amfani da shi wajen zama inyi maka wanna maganar"

Sai ya zauna a kasa a inda yake tare da dafe kansa da hannaye biyu a hankali ya ambaci "my God!" Nima sai na koma na zauna. Ya jima a haka yana rocking in one

place sannan ya dago kai yana kallona yace "you know what hurt me the most in all this? It is the fact that you went through all these ke kadai, without telling me Safiyya, You went through all that alone" ya karasa cikin karyayyiyar murya. Nayi shiru ina jin sabbin hawaye suna zubo min, ya cigaba "You should have

told me. You should have told me the moment it happened. You should have at least share all that burden with me but you chose to carry it alone. Saboda me? Saboda kina tunanin zan guje ki in naji

abinda ya faru ko kuma kina ganin ban kai matsayin da zaki gaya min bane ba?" Ya karasa tambayar cikin fada,

Na dago ina kallon sa, muka hada ido for the first time, idanunsa sunyi ja sun kumbura kamar zasu fado kasa, a hankali nace "i didn't tell you because I know exactly what you would do idan da kaji maganar" yace "and what is that?" Na lankwasa kai ina kallon sa hawaye yana bin fuskata nace "cewa zaka yi cikin ka ne. It would break you up to pieces but cewa zaka yi kai ne, cewa zaka yi naka ne Zaka yi hakan dan ka bani kariya kuma dan kayi forcing iyayen mu su bar mu tare".

Yace "then why didn't you let me do that? Yes, that's exactly what I would have done. Da kin barni nayi hakan da duk bamu zo wannan matsayin ba. Da magana ta wuce tuntuni" nace "da kuma iyayen ka har yanzu suna kallon ka da abin. Zasu yarda muyi auren but they will be very disappointed in you maybe har karshen rayuwar su akan abinda baka aikata ba. Yan'uwan ka, abokan ka, abokan aikin ka duk wanda ya sani ba zai kuma yi maka kallon mutumin kirki ba. Sunan ka zai baci akan abinda baka yi ba. And that's

something da ba zan taba yi maka ba a rayuwa"

Ya rufe idonsa tare da kwantar da kansa baya ya jingina shi a jikin kujerar da take bayan sa. Sannan a hankali yace "so you chose to lie to me. You chose to tell me that kina da aure. "I am married and I love my husband very much" ya karashe maganar cikin dacin rai, sai kuma ya juyo da kansa yana kallona yace "do you have any idea how much that hurt me?" Na girgiza kaina "it wasn't the best decision I know, But I wasn't thinking clearly. Tun daga samun cikin nan har zuwa haihuwar sa bana cikin hayyacina, Babu wani decision da nayi making a cikin lokacin da yake mai kyau ne except not telling you the truth, I mean, I tried to give up the innocent child for a close adoption a kasar da bama ta musulmai ba" na sunkuyar da kai na sannan na dago nace "I tried killing myself, twice" ya bude ido

sosai sannan ya gyara zaman sa yace "you told me kinyi kokarin cire cikin ko da a bakin ranki ne. Wannan ne second time din?" Na daga kafada nace "sanda kaje gidan mu ka gan ni tare da Mukhtar a mota, ya fita da motar, yana gudu a motar sosai and he said some bad words akan ka and I opened the door zan fita daga cikin motar".

Ya zaro ido sosai tare da rufe bakin sa da hannayensa, Fuskarsa cike da tashin hankali. Nace "na gaya maka wannan ne kawai dan ka fahimta kuma ka yafe min

maganganun da na gaya maka to break your heart dan ka rabu da ni" ya rike hannuna da sauri "ba maganar in yafe miki ake yi ba yanzu Safiyya. Promise me that you will never do something like that again" na gyada kai na "insha Allah", Sai kuma muka yi shiru for sometimes, kamar ya danyi calming down a little kuma ya dan fahimta duk da nasan sai yaje ya zauna ya tattauna da zuciyar sa sannan zai fahimta sosai ya kuma gane what he is getting himself into. Daga nan

kuma zai gane abinda ya kamata ya gaya wa iyayen sa, daga nan kuma zai san idan iyayen na sa zasu yarda da auren na mu or not, tunda shi ya sansu ya san abinda zasu dauka da wanda ba zasu dauka ba.

Mun jima a haka sannan ya ambaci sunana cikin sanyin murya "Safiyya" na dago kai na kalle shi sai na mayar da kaina kasa dan ba zan iya cigaba da kallon

jajayen idonsa ba. "I am sorry all this happened to you. Duk da har yanzu ban yarda cewa rashin gayamin was the best decision ba amma na fahimci girman soyayyar ki gare ni and na fahimci kin yi making that decision ne with my wellbeing in your mind, and I really appreciate that. And I will never take your love, understanding and care for granted. Kinji? Amma ina so kiyi min alkawari

saboda nan gaba, promise me you will never hide anything again from me. Through thick and thin, through joy and sorrow, for better or for worst, promise me we will always be together and look out for each other, Kiyi min wannan alkawarin kinji?"

Naji wata soyayyar sa tana karuwa a cikin zuciyata, shi a gurin sa wannan abin da na gaya masa bai ma kai abinda zai saka yayi considering rabuwa da ni ba. Shi kara jaddada min soyayyar sa yake yi a gare ni. Dama kuma na riga na san haka. But I want someone else to know. Dan haka na sake tambayar sa cikin karyayyiyar murya "Muhammad kamar kana manta wani abu. Ina da da. Dan da na haifa ba tare da aure ba. Wannan dan will always be attached to me and to yayan da zan iya haifa nan gaba. In kace zaka aure ni hakan yana

nufin abin zai shafe ka kai da yayan da zamu haifa nan gaba. Are you sure you want to........." Ya katse ni "I am more sure now than I have ever been. Babu abinda ya faru wanda yake laifin ki ko laifin shi yaron, kaddarar ku ce haka. Nima kuma soyayyar ki ita ce tawa kaddarar, kaddarar ki kuma ba ta rage ko kadan daga cikin tawa kaddarar ba sai ma karuwa da tayi. All I want to do now is to take care of you in tabbatar cewa ba ki sake zubar da hawaye ba sai na farin ciki" ,.

Na goge hawayen da suke bin fuskata, wadanda already na farin cikin ne ma. Ya sake matsowa kusa da ni. Yace "I want to marry you Safiyya. Will you marry me?" Na daga kai muka hada ido, murmushi yaso ya kubce min amma sai nayi sauri na rufe fuskata da hannuna na gyara mood dina sannan na bude fuskata a hankali nace "no".

Yayi shiru yana kallona fuskar sa cike da alamomin tambaya iri iri sai nace "I am sorry Muhammad. I am very sorry. This is the last part of maganar da zamu yi yau. And your answer is no. I love you so much, fiye da yadda kalmomin bakina zasu iya furtawa. Ba ni kuma da shakka akan son da kake yi min musamman yau

da ka sake tabbatar min. But I cannot marry you"

Ya koma da baya har sai da ya jingina da jikin kujera sannan ya zauna. Emotions dinsa mixed up. "Why?" Ya tambaya at last. Na fara kuka "saboda Daddy yace in

rabu da kai. Yace ba zai aura min kai ba. Ya kuma ce ko bayan ransa bai yarda in aure ka ba. Ba zan iya bujirewa maganar sa ba. He went through a lot a kaina, Ina so nima in faranta masa rai in yi masa

biyayya ko da kuwa hakan yana nufin zan rasa abu mafi soyuwa a gare ni. Dan Allah Muhammad kayi hakuri...…”.

Sai ya dafa kujera ya mike bai ce min komai ba, sai kuma jiri ya debe shi ya tafi zai fada kan kujura, na tafi gurinsa da sauri kamar zan rike shi sai ya daga mun hannu amma sai ya zauna akan kujerar, Na cigaba da kokarin yi masa magana Gidado, Iyayen mu sun fi koma muhimmanci a gare mu. Mama da Abba ba sa so. Daddy baya so. Both our families ba sa so. Soyayyar da muke yiwa junan mu is not enough especially in zata bata musu rai dan farin cilkin su yafi namu muhimmanci. Dan Allah ka fahimta." Ya dago kansa ya dafe da hannun sa yace "are you telling me inje in cigaba da zama da Safina kenan? Makaryaciya, mayaudariya munafuka? Ita kike so in zauna da ita ta haifa min yaya? And you? Who are you going to marry? Ko akwai wani ne dama da ban sani ba?

Na girgiza kaina tare da kneeling down a gabansa. “Babu kowa Muhammadu. Babu kowa a zuciya ta sai kai. Nima ban san wanda zan aura ba. Na yanke hukuncin zan bawa Daddy zabi ne kawai, duk wanda yaga ya dace sai ya aura min in dai hakan zai saka shi farin ciki. Dan Allah kai ma kayi haka. Ka bawa su Abba zabi”.

Ya mike tare da daukan key din sa sai na mike na kwace "dan Allah kar kayi fushi da ni Muhammad, It hurts me a lot to make this decision amma dole ne. Kai ne farin ciki na, amma farin cikin Daddy yafi nawa muhimmanci a gare ni. Dan Allah Muhammad kayi hakurj" ya miko min hannu, still expression dinsa unreadable '"bani key dina" na matsa baya ina girgiza

kai "ba zan barka kayi driving a wannan yanayin ba" cikin fada yace "you don't care. Don't pretend that you do" nace "but I do, more than you know" ya tako ya dawo gaba na ya tsaya yace "do you truly love me?" Na gyada kai na da sauri "fiye da yadda kake tunani" sai yace "then I will not give up. Ke kiyi abinda kike tunanin shine dai dai, nima zanyi abinda nake tunanin shine dai dai. Kamar yadda nace, soyayyar ki kaddara ta ce, then there is no turning back".

Ya juya ya sake yin hanyar fita nace "key din ka yana hannuna, I will not let you drive" yace "ki rike. Zan shiga ta haya".

Daga haka ya fita. Na koma na zauna akan kujera tare da dafe kaina ita share sauran hawayen fuska ta sai kuma na mike da sauri na bi bayansa, Sanda na hango shi har ya kusa kai wa bakin gate,. Tun daga tafiyar sa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login