Showing 99001 words to 102000 words out of 375662 words
Chapter 34 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx
/>
Baba Hadiza da irin burukan ta akan su,
hirar Khadijah da surutun ta, da kuma hirar
rayuwar su a yanzu. "ni dai Safiya bana so
mu rabu, ko kin girma kin yi aure ma sai na
biki gidan ki, duk inda zaki je sai na biki"
Safiya ta ce mata "babu inda zanje ai na
gaya miki. Kuma ni ba zan yi aure ba. Zan
zauna da ke har sai kin gama karatun ki, kin
samu aiki kin gina babban gida sai ki zo ki
dauke ni muje mu zauna tare" Sauda tayi
dariya "ina kewar Baba Hadiza. Ina so inje
gurin ta" suka yi shiru sai kuma tace "ni
kuma so nake in kin kara girma kin yi aure
kin haihu, ina so yar da zaki haifa ta zama
duk abinda Baba Hadiza take so mu zama.
Ta zama yar gayu mai tuka motoci masu
kyau, ta zama mai ilimi da turanci kamar
baturiyar ingila, sannan ta zama kyakkyawa
kamar Baba Hadiza" Safiya ta jawo ta ta
kwantar da ita tace "duk ke zaki zama haka,
Zan cigaba da yin wankau da suyar awara
har sai kin zama haka" Sauda ta rungume ta
tare da cusa fuskarta a wuyan ta tace "bacci
zanyi yanzu, na daina jin toro yanzu. Kiyi
mana addu'a. Sai da safe" safiya tace "to. mana addu'a. Sai da safe" safiya tace
"to
shikenan. Kiyi baccin ki. Sai da safe" sannan
ta karanta adduoin kwanciya bacci ta shafa
musu.
Da assubar fari Safiya ta farka. Amma ba wai
kiran sallar asuban ne ya tashe ta ba. Ji tavi
kamar ana kiran sunan ta cikin baccin ta, ta
zare hannun Sauda daga jikinta ta mike
zaune, sannan kuma ta tashi tsaye ba tare
da ta san me take yi ba. Ita ba ido biyu ba ita
ba a farke ba. Kamar mai sleepwalking. Ta
bude kofar dakin ta fita sannan ta cigaba da
tafiya ba tare da tasan inda take saka
kafarta ba. Sai da ta kai tsakiyar tsakar
gidan su sannan taji wata kara daga bayanta
"yif!" Karar da ta farkar da ita daga baccin
da take yi, sannan kuma lokaci daya tun
kafin ta juya bayan nata jikin ta ya bata
abinda ya far sannan kuma zuciyar ta ta
tabbatar mata da cewa Sauda ma ta tafi ta
barta.
Ta juya da sauri ta kalli dakin da ta fito daga
ciki just few seconds ago, tun daga cikin
dakin har falon har toilet din har soron
gabaki daya katangunsu sun afka ciki, sun
fada akan Sauda,
Tayi wata irin kara wadda gabaki daya
unguwar babu wanda bai ji ta ba, sannan ta
fita a guje ta hau kan tarin kasar ta fara
kokarin daga kanukan rufin da suka rufe
kasar, Kusoshi biyu ta taka a lokaci daya
amma babu wadda taji zafin shigar ta cikin
kafarta, Kuka take yi da iyakacin karfin ta. kafarta. Kuka take yi da iyakacin karfin ta
tana kiran sunan yar uwar ta "Sauda, kar ki
tafi ki barni", Makota ne suka fara shigowa,
wadansu dama already sun tashi da niyyar
zuwa masallaci, daga baya jama'ar gidan
suma suna fito, da kyar aka samu wani
makocin su ya rike Safiya, hannayensa biyu
ya saka ya rike ta gam a jikinsa yana tofa
mata adduoi sannan aka samu ta nutsu ta
tsaya a guri daya yayin da matasa suka hau
aikin hakar kasar. Gini ne irin na da katangar
mai kauri ce sosai gashi ta sha ruwa dan
haka suma mazan da kyar suke dauke ta.
Ba'a samu tono Sauda ba har sai da gari ya
waye rana ta fito sosai. Tun kafin a dauko ta
dama duk wanda yake gurin ya fitar da ran
samun ta da rai. Sanda aka fito da gawar ta
shi kansa wanda yake rike da Safiya gagara
sa tayi. Tayi kan Sauda tana wani irin kuka
mai ratsa zuciyarsa da ruhin duk wanda
yake sauraronta. Ta rungume ta kamar zata
tsaga kirjinta ta saka ta a ciki. "kar ki tafi ki
barni, dan Allah kar ki barni ni kadai"
A ranar hatta yan'uwan Safiya da basa ga
maciji da ita sai da suka zubar mata da
hawaye, Da kyar aka banbare gawar Sauda
daga jikin Safiya aka yi mata suttura aka yi
mata sallah aka dauke ta a makara zuwa
gidan ta na gaskiya, A lokacin da ake fita da
gawar kowa a gidan kuka yake yi, ba kuma
wai kukan mutuwar Sauda ake yi ba ko kuma
kukan sabo da ita ba, kukan tausayin Safiya
ake yi, da yawa mutane sun dauka ba zata yi
rai ba, sun dauka bin yaruwar tata zata yi. ake yi, da yawa mutane sun dauka ba zata yi
rai ba, sun dauka bin yaruwar tata zata yi.
A lokacin mutane da yawa sun fadi
albarkacin bakin su akan dalilin faduwar
dakin da kuma mutuwar Sauda
6
8:47 PM
'"wannan sabon ginin da akayi shi ya kashe
dakunan"
"to da ya akayi ma aka barsu suke kwana a
wannan gurin su kadai?"
"Ai ruwan cikin gidan gabaki daya cikin
katangun dakunan yake shiga"
Amma kuma babu wanda ya daga maganar
ballantana har a dauki matakin shari'a akai.
Daga nan Safiya ta sake bude wani yet
another page na rayuwa.
She became totally depressed, ta daina cita
daina sha ta daina wanka ta daina magana
da kowa, babu abinda ta so a lokacin kamar
mutuwa, da ana siyan mutuwa da tabbas
zata nemi kudi ta siya wa kanta, Ta koma
dakin Inna Gaje da kwana, tunda bata da
wani gurin zuwan idan ba can din ba, ita ma
kuma Inna Gajen ta dan sassauta mata
yanzu dan bata saka ta aikin komai kuma ko
ta saka tan ma babu tabbas din cewa zata
yi.
Wata daya bayan nan tana kwance a inda. Wata daya bayan nan tana kwance a inda
take kwanciya kamar kullum taji shigowar
yaya Malam, yazo ya shige ta ya shiga gurin
mahaifiyar ta sa a gaishe ta sai safiya taji
Inna Gaje tace "dama jira nake kazo, gwara
ka san yadda zaka yi da yarinyar can kar ta
mace min a daki azo a barni da salati" yace
"me ya same ta?" Tace "bata ci bata sha,
yadda ka ganta din nan a kwance haka take
wuni take kuma kwana. Ni fa ba zanyi jinyar
ta ba. Ku da take yaruwarku ubanku ya bar
muku wahala sai ku san yadda zakuyi da ita,
ni nayi na Allah kuma na gaji haka". Yaya
Malam yace "to Inna ni ai bani kadai ne
yayan ta ba, dan ina babba shikenan komai
sai ace ni? Ba ga su Namadi nan ba su da
suke birni ai sun fi ni arziki" Inna Gaje tace
"to ai ba zasu yi ba, in ta mutu kuma ba za'a
zage su ba kai da aka sani kai za'a zaga.
Dole ka san yadda zaka yi da ita"
Yayi shiru sannan yace "na san me zanyi a
kanta. Ni ba zan kaita gida na ba wallahi in yi
ta rigima da iyali a kanta. Aure zanyi mata.
kwai tsohon hedimastern mu da yayi retire
kwanan baya, dama ya taba yi min maganar
ta yace ko zan bashi ita sai na mayar da
maganar wasa, gwara inyi mata auren kawai
in taje gidan mijin zata warke a can. Gobe in
na hadu dashi zanyi masa magana in har
yanzu yana son ta yazo kawai ay"
Inna Gaje tace "hakan ma yayi, Kace masa
sadaki kawai zai kawo ba sai yayi hidimar
komai ba in yaso sai yayi mata kayan daki,
dan babu abinda zamu siya mata" yace "sai. dan babu abinda zamu siya mata" yace "sai
ta je itama tayi irin zaman da uwar ta tayj"
Baba Gaje tace "to Allah ya sa dai kar a
maimaita, kar taje ta kwantsama yaya shima
ya mutu ta debo yayan ta sake dawo mana
nan".
Safiya ta bude idonta, sannan ta tashi zaune
tana kare wa dakin kallo sai kuma ta mike
tana jin kamar kafafuwan ta ba zasu dauke
ta ba. Waje ta fita, taje ta hau kan tudun
kasar da yake nan ne dakin su a da, inda tayi
rayuwa da iyayen ta da yan'uwan ta. Ta
kwanta ta sake rufe idonta tana jin iskar
damuna tana kada ta, tana shakar kamshin
kasar da take kwance akai. Anan ta yanke
hukunci. Anan ta bude sabon babi a rayuwar
ta.
Ta mike kafarta ko takalmi babu tana tafiya
iska tana yawo da ita, tiryan tiryan ta taka
har gidan da tayi niyyar zuwa, gidan Hajiya
Kyauta. Hajiya Kyauta tana zaune a tsakar
gidan ta sai gain yarinya tayi kamar aljana
ta shigo mata, kafarta da ciwon kusar da ta
taka garin tono gawar yaruwarta, Hajiya
kyauta ta mike a tsorace, sai kuma ta tsaya
tana kallon yarinyar ta a tunanin a inda ta
san fuskarta,
Safiya tace "sunana Safiya, Dan girman
Allah ina so ki taimaka min" sai a lokacin
Hajiya Kyauta ta gane ta, ta koma ta zauna
tare da cewa "ke ce yarinyar nan Safiya yar
gidan marigayiya Hadiza, bana gari ta rasu,
sai da na dawo sannan aka bani labarin. da na dawo sannan aka bani labarin
abinda ya faru da ita. Ina yaruwar ta ki?"
Safiya tace "ta mutu, duk gabaki dayan su
sun mutu. Ni kadai na rage. Ni kadai suka
bari", Hajiya Kyauta taji wani iri a zuciyar ta,
yanayin yarinyar kadai ya isa ya bawa
mutum tausayi ballantana abinda ta fada,
tace "Allah sarki. Allah mai iko. Yanzu to ni
me kike so in taimaka miki da shi? Abinci
kike so ko kudi?"
fan 11
2
1
8:47 PM
Safiya ta girgiza kanta "so nake ki dauke ni
daga garin nan. Bani da sauran abinda zanyi
a garin nan. Bani da iyaye bani da yan uwa
bani da kakanni, ban san dangin uwata ba
dangin ubana kuma basa so na, aure suke
so suyi min, so suke yi in maimaita rayuwar
wahala irin wadda Baba Hadiza tayi, so suke
yayan da zan haifa su maimaita rayuwar
wahala irin wadda ni da yanuwana muka yi.
Ba zan yarda hakan ta kasance da ni ba. Ba
zan bari hakan ta kasance da ni ba. So nake
ki kaini garin da zanje in nemi kudi, kudi
nake so inyi irin wanda yayan da zan haifa
ba zasu taba fuskantar rayuwa irin wadda na
fuskanta ba, kudi nake so in yi yadda ni ce
zan zamanto mutum ta karshe a zuri'a ta da
zai san dacin talauci",
Hajiya Kyauta tayi shiru tana kallon yar
yarinyar da take gabanta tana kuma jin
yadda take zarar magana kamar wadda kae
yiwa wahayi. Tace "ke yarinya ce Safiya. Shi
arziki da talauci ai duk na Allah ne shine
kuma yake rabawa ga wanda yaso" Safiya. kuma yake rabawa ga wanda yaso" Safiya
tace "Allah kuma shine ace mu roke shi zai
amsa mana, zan roke shi ya bani, na kuma
tabbatar zai bani din".
Kyauta tace "to ke yanzu kima da jari ne? Da
me zaki nemi kudin?" Safiya tace "bani da
jari, amma ina da rai na ina kuma da lafiya
ta, da su zan nemi jarj".
Hajiya Kyauta ta sake yin tunani tace "kina
da rai da lafiya amma baki da karfi. Da ke
namiji ce sai in kai ki Kano can ne cibiyar
kasuwanci, sai in kai ki kiyi dako da
laburanci ki samu jari" ta juyo tana kallon
Safiya tace "amma ke macece, yarinyar
mace. Aikatau zan kai ki gidan masu kudi,
Abuja zan kai ki a can masu kudin suke.
Suna bada albashi kuma mai kyau in dai
zakiyi musu aiki mai kyau. Tunda baki da
nauyin kowa kinga zaki tara kudin ki ne
kawai. Daga nan zaki samu jarin da kike
nema" tayi shiru tana cigaba da kallon
Safiya, sai ta sake cewa "gidan Hajiya
Maryam zan kai ki. Yar kasuwa ce sosai
kuma bata da matsala, Zata baki ci da sha
da sutura da magani kuma zata baki albashi,
Sannan zaki koyi dabarun kasuwanci idan
kina zaune da ita, Sai dai akwai yarjejeniya
da zamuyi ni da ke" Safiya ta gyara zama
tace "kome kike so in dai ina da damar yi
miki zanyi mikj" Hajiya Kyauta tace "bana
bukatar ko kwandalar ki, zan taimaka miki ne
saboda girman Allan da kika hada ni da shi.
Amma idan yan uwanki suka kama ki kina
kokarin gudu, ko kuma bayan kinje can suka. ko kuma bayan kinje can suka
gano inda kike, babu sunana a cikin
maganar, bana son shiga cikin rigima".
Safiya tayi murmushin takaici tace "ba zasu
neme ni ba ko sunga bana nan. In sun gano
inda nake ma kuma ba zan dawo ba. In na
bar garin nan na bashi kenan har abada".[07/01, 10:42 pm] +234 906 816 1960: . EPISODE TWENTY TWO
owner
12:54 AM
Safiyya
Episode Twenty Two: A Green Snake
Bara mu bar Safiya ta huta haka nan......
Let's go back to Fiyya
Naga kunyi missing Malam Muhammadu da
"'Yaya, Yaya, Yaya!"
Naji ana fada ana kuma jijjiga ni. Duk da ban
gane muryar me magana ba amma na san
mutun biyu ne duk duniya suke ce min yaya,
either Hassan ne ko Hussain. Nayi kokarin
bude ido a amma sunyi min nauyi da yawa,
naji ina jin haushin ko ma wanene yake
kokarin tashina, I wanted to go differ into
tunanin Ammi na da yanuwanta, maybe
watakila in nazo gurin da take tafiya ta barni
zata tafi dani wannan karon,
Naji an sake taba ni, wannan karon kuma
muryar macece, muryar Mommy "Safiyya?
Bude idonki ki kalle ni, talk to me" na bude
ido na kamar yadda tace amma dishi dishi
nake ganin ta, na bude baki zanyi mata. nake ganin ta, na bude baki zanyi mata
magana kamar yadda tace amma sai bakin
ya furta "Baba Hadiza" ta kalli wanda yake
kusa da ita? Zaka iya daukan ta, go and look
for someone ko Mustapha" "Mustapha yana
gurin Daddy" ya amsa mata "Daddy " na
maimaita sunan.
Naji an dauke ni, naji kuma an saka ni a
mota, daga nan sai maganganun mutane
mostly muryar Mommy ce tana fada duk da
ban san me take cewa ba.
Sanda na dawo hayyaci na a asibiti na samu
kaina, a kwance akan dago da ruwa a jiki na.
Na kare wa dakin kallo sai naga Daddy a
gefe a zaune akan electric wheelchair dinsa
da dan karamin Alqur'ani a hannunsa. Na
jima ina kallon sa kafin ya fahimci na farko
sai ya rufe qur'anin ya karaso kusa da ni.
"hey there" na kirkiri murmushi "hey"
"ya jikin? Akwai inda yake miki ciwo ne?"
Kusan komai na jikina ciwo yake yi min
amma sai na girgiza kaina nace "babu
komai, Babu abinda yake damuna" yayi
ajiyar zuciya yana kallo na, and once more
na saka gain disappointment a fuskar sa,
Na sunkuyar da ido na kasa, "Doctor ya baki
bedrest amma baki huta din ba ko? You
were supposed to be resting 24/7 amma
shine kika fita" na da go ido na kalle shi sai
na sake mayar wa kasa, ya cigaba "yes,
twins sun gaya min kin fita, kika yaudare su
cewa gurin dinner zaki je, and you ran away. cewa gurin dinner zaki je, and you ran away
daga gurin dinner din suka neme ki suka
rasa. The poor kids have been looking all
over for you. Ina kika je?" Na cigaba da shiru
na "gurin sa kika je ko?" Still shiru.
Ya ja kujerar sa baya "ya Rabb. What should
I do. What should I do ya Rabbi. Safiyya aure
ne akan ki fa yanzu"
Mommy ta bude kofa ta shigo, Esther a
bayan ta da baskets na abinci. Ta kalle shi ta
kalle ni sannan tace "wannan ba lokacin
fada bane ba. Wannan yarinyar da kyar aka
dawo da ita duniyar mu, she called me Baba
Hadiza. Sai kace ta san Baba Hadizan" ya
juyo yana kallo na "Baba Hadiza huh? In ita
take kiran ki tell her ban gama da ke ba. She
took all her kids with her nima ina so ta bar
min tawa" ya karasa yana murmushi.
Mommy ta fara kokarin hada min abinci shi
kuma ya cigaba da magana "Safiya loved
them with everything in her. A lokuta da
dama har kishi nake yi cewa ni bata damu
da ni ba ni da nake da rai kamar yadda ta
damu da su su da basu da rai, And I was
angry at her when she chose death over life,
I thought ta zabi zama da su akan mu ni da
ke. I thought she chose to left us because
she did not love us enough, Sai da na huce
sannan na fahimci gaskiya, she lost
everything sanda ta rasa su, she couldn't
save either of them, and then she got you
and you were her everything, she could save
you so she did. I am sure she didn't even. you so she did. I am sure she didn't even
had a second thought before she jumped
into that water to save you because without
you her life would have been meaningless.
All their lives would have been meaningless.
You are their legacy. You are their dreams"
Na rufe idona ina hango fuskokin su a cikin
hoton da shine kadai abinda na mallaka na
su. Duk da talaucin su but they looked so
contented and happy a cikin hoton.
Mommy ta ajiye farfesun naman da ta zuba
a bowl a gaba na ta fara kokarin tashi na
zaune, na tashi ina rike cikina kamar mai
kokarin hana dinki na budewa. Ta bini da
kallo sannan tayi tsaki "ba kya jin maganar
Fiyya. Ji yadda kika koma dan Allah.
Skeleton ma ya fiki kyan gani. Ba zan kai ki
gidan miji a haka ba wallahi.
16
15
12:56 AM
Sai kin dawo hayyacin ki. Kuma ba zaki dawo
hayyacin naki ba sai kina cin abinci".
Mustapha ya bude kofa ya shigo tare da
sallama, Mommy ta juya kansa "daga ina
kake? Ka barni ina ta