Showing 375001 words to 375662 words out of 375662 words

Chapter 126 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx

10 Oct 2025

7899

wanda na gani

a Kura faranta min rai, Yayun Baba Hadiza

guda biyu Jabiru da Audu suna garin a

lokacin, Shi Jabiru shekaru ne suka yi

masa yawa and he chose to spend the

last of his days a inda iyayensa suka rasu.

Shi kuma Audu wanda shine Baba Hadiza

take bi ashe tun zagayowar sa garin ta

farko wadda yayi musamman dan kanwar

ta sa sai kuma yazo ya tarar da munanan

labarai a jere, babu Hadiza kanwarsa

babu yayanta. An dai ce babbar

haukacewa tayi ta bi duniya saboda

tashin hankalin abinda ya faru. Wannan

shine last labarin Ammie da yaji. Ya kuma

yi kuka tare da takaici mai yawa akan

hakan dan yana son kanwarsa Hadiza

sosai kasancewar ita kadai ce yar war sa

mace, Daga nan bai kara barin gari ba,

Dagaci ya bashi guri a bayan gari ya kafa

ruga suka zauna shi da iyalinsa yana fatan

watarana Safiya zata dawo kuma zata z0

ta neme su. Lokaci zuwa lokaci ya kan je

Kura ko zal samu labari, amma babu

labar in komai kuma shi bal ma san gurin

wanda zai nemi labarin ba. Bai san kowa

ba sai Alhaji Haladu sai kuma wani kanin

sa. Shima kuma kanin ba'a jima ba ya

rasu.

Daga baya ma sai ya tarar babu gidan

Alhaji Haladu an rushe anyi masallaci. Ya

kan shiga masallacin duk sa da yaje yayi

sallah ya fito amma bai san komai gane da

masallacin ba. Shima ya manyanta, amma

da kwarinsa kuma da yake jikin fulani ne

babu kiba sai ya kasance girman bai kama

shi sosai ba.

Nayi kukan ganin su, kamar yadda suka yi

nawa. Jabiru har sai da na tausaya masa

na koma ni nake bashi hakuri, duk ya

dauki laifin abinda ya samu Baba Hadiza

ya dora akan sa, gani yake laifin sa ne

tunda yazo gari lokacin mutuwar Alhaji

Haladu. Amma ya tafi ya barta da kananan

yara bayan ya san bata da mataimaki sai

Allah,

Sai da aka gana koke koke kuma aka fara

murna. Fulatanci suke yi suma sai hausa

jefi jefi, a lokacin na fahimci fulatanci

dialect daban daban ne dan nasu ya

banbanta sosai da na Muhammad. Suna

gane juna amma ba sosai ba, Sai an dan

hada da hausa wani lokacin kuma sai an

kara bayani, shi kuma sai yayi min bayanin

abinda ban fahimta ba. A haka akayi

communication din. Sai inno matar Audu

ta saka ni a gaba da tsokana wai

maimakon ni zan ke fassarawa mijina

tunda gidan mu aka zo amma shi yake

fassara min. Sai kuma ta tafi wani abu da

ya saka shi murmushi tare da yi min

gwalo. Na harare shi sannan na tambaye

shi abinda tace sai yace cewa tayi ya fi ni

kyau. Ai kuwa na dage nace kishi take yi

tunda ni jika ce a wajen ta tana son ta

kwace min miji.

Sai a fahimci Muhammad yafi sakewa da

su akan a Kura. Nan da nan aka yanka kaji

aka soya mana su aka dama mana kunun

nono, kunun yayi min dadi sosai har sai da

na tambayi Khadija autar Baba Audu ta

koya min yadda ake yi. Muka ci sosai

muka koshi. Muhammad da kansa ya ce

wa dan rakiyar mu ya koma anan zamu

kwana, naji dadin hakan sosai, suma

kuma mun raba dare da su muna hira. Sai

naji nafi sakin jiki da su, na basu labaran

duk abinda ya faru da kuma rasuwar

Ammie na tare da matsayina a yanzu.

Sunyi mamaki sosai sun kuma yi jimami

tare da godiya ga Allah. Sai na basu

labarin Daddy na da halin da yake ciki na

rashin lafiya. Baba Audu yayi shiru sannan

ya tambaye ni abinda yake damunsa, na yi

masa bayanin cutar duk da bansan sunan

ta da hausa ba ballantana da fulatanci. Sai

yace "dan zaku tafi zan bi ku in ganshi.

Zamu warkar da shi da ayar Allah tare da

sauyoyin mu na daji"

Maman Maama✍🏻


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login