Showing 258001 words to 261000 words out of 375662 words
Chapter 87 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx
get
you back to the hospital, and I need to
get back home" ya tayar da motar tare da
cewa "it is a long way ai. You can tell me
in the way",
Muka juya mota muka koma daya hannun
muka dauki hanyar komawa cikin gari,
amu jima muna tafiya ba yayi packing a
gaban wani masallaci ya shiga yayi sallah
nima nayi alwala na dauko sallaya a cikin motarsa nayi sallah, na lura da motar guards dina a dan nesa da mu kadan. Ina idarwa ya dawo ya sake tayar da motar
muka cigaba da tafiya, muna fara tafiyar
ya kalle ni yace "uhun. Ina jin ki. Start
talking" na danyi shiru ina kallon sa,
thinking of where to start from.
Na san yana bukatar ya fahimci komai, tun
daga dalilin da yasa na kasa kai shi gidan
mu a wancan lokacin zuwa uzurin Daddy
na hana yi min samari wanda shine dalilin
da yasa ban kai shi gurin sa din ba, amma
ba zai fahimci duk wannan ba sai ya san
labarin Ammie. Dan haka daga labarin
Ammie ya kamata in fara yi masa, ko
kuma ma ince daga labarin Baba Hadiza.
Na dauki waya ta na bude pictures nayi
scrolling zuwa hoton su Ammie da na
dauka ranar nan a waya ta, na nuna masa
tare da nuna Ammie nace "wannan ita ce
mahaifiyata" ya kalle ta sannan ya kalle ni,
"kuma kama sosa'" nayi murmushi
"Nagode" yace "Allah ya yi mata rahama"
nace "Amen" sai kuma na nuna Baba
Hadiza nace "wannan mahaifiyar ta ce,
sunan ta Baba Hadiza, wadannan kuma
yan'uwan ta ne, uwa daya uba daya" ya
gyada kai cikin fahimta tate da mayar da
hankalinsa kan driving din da yake sai nace "duk sun mutu gabakidaya" yayl sauri ya kalle ni da mamaki "what? Ga baki dayan sup" Na gyada kai "yes,
Ammie ce kadal ta girma a cikin su, ita ce
ta karshen mutuwa" yace "how? Accident
ko menene?" Nace "no they died in
different kind of tragedies" na danyi
murmushi nace "| used to say that
tragedy is another name for my family.
Yanzu kuma zan fahimtar da kai dalili",
Daga nan sal na bashi labari, labarin Baba
Hadiza da iyayenta da yan'uwan ta da
yanayin rayuwar su, sai kuma na bashi
labarin auren ta da Alhaji Haladu da
yanayin zamanta da abokan zamanta har
zuwa mutuwar Alhaji Haladu da kuma
yadda rayuwa da kasance musu bayan
nan. Sannan one by one na bashi labarin
yadda suka mutu, tun daga kan Khadijah
har zuwa kan Sauda, da kuma yadda
Ammie ta gudu dan kar ayi mata irin auren
Baba Hadiza, dan kar ta haife ni in rayu
cikin wahala kamar yadda su suka yi, na
bashi labarin shigowar ta Abuja da
zamanta a gidan Hajiya.
Duk a cikin labarin nawa in dai aka zo kan
abinda bai fahimta ba zai tambaye ni in
sake fahimtar da shi, amma sai na ga
labarin Hajiya ya dauki hankalin sa sosai.
"you mean Hajiya Maryama? Yayar Mommy?" Na gyada kai "eh ita. I guess you already know her" yace "naje gidan ta ones, she said ta san grandma dina, and ranar nan ita ma grandma take ce min ta
san ta and she said she knows her
daughter mai suna Safiya, wai kuma ta
auri wani mai suna Adam. I told her bata
da yaya amma she insisted tana da ya mai
suna Safiya" nayi murmushi ina jin dadi,
nace "haka take cewa, cewa take yi yarta
ce, amma in reality yar aikin ta ce. And
she was so kind to her in ways that I
cannot describe" muka sake yin shiru a
lokacin da muke shigowa unguwar mu. Ya
je yayi packing a kofar gidan mu yana
kallona yace "yanzu cewa zaki yi zaki
shiga gida ki bar ni ko?" Nace "ko zaka zo
mu shiga tare?" Ya kama handle din kofa
"finally za*a kai ni wajen Daddy" nayi
dariya "rufa min asiri. Wasa nake maka fa"
ya langwabe kai "still da'" nace "ka dan
kara min lokaci kadan. I need to prepare
him. I need to find words da zanyi using
to convince him" ya kalli gate din mu yace
"you need the words now" na juya nima
na kalla and I saw Malam Ya'u a tsaye
yana kallon mu sai kuma ya juya ya koma
cikin gidan. Nayi ajjiyar zuciya nace "l
really don't know me zan ce masa, amma
kaima kana bukatar words din da zaka
fada a gida" yayi ajjiyar zuciya "I think we
should just tell them the truth, sai muga abinda zasu yi akai. Kamar yadda kika ce, they love us and will make the right decision for us". Na dauki wayata na rike ina juijuya ta ina kallon sa, feeling reluctant, kamar kar in
fita daga motar, kamar kar in rabu da shi,
but kamar yadda nace, we must face our
reality. Sai kuma nace "good night Malam
Muhammadu" na bude kofa na fita da
sauri sai ya kira sunana "Piya" na juyo ina
kallon sa sai yace "don't get married
again" nayi murmushi "I will, I will get
married. And you will be the groom" sal
kuma naji kunyar kalion da yayi min na yi
cikin gida da sauri. Amma sai na tsava a
jikin gate, ban matsa ba sai da naji alamar
ya tafi sannan na yi hanyar cikin gida ina
harhada kalamai a raina.
A hanya muka hadu da Baba Ya'u yana
fitowa daga bangaren Daddy, nace
"sannu Baba Ya'u" ya bini da kallo yace
"sannu ranki ya dade. An dawo lafiya?"
Nace "lafiya lau" sai ya koma gurin zaman
sa ni kuma na shiga cikin gidan.
Na san dai Mommy tana asibiti wajen
Safina, though ban sani ba ko ta dawo
gida bayan na fita, Mustapha kuma da
twins tunda ban gansu a waje ba kuma
basa falo na san maybe sunyi bacci, amma Daddy na san idonsa biyu tunda yanzu naga Baba Ya'u ya fito daga gurin sa. Ma san kuma ya kamata inje in gan shi
ya ganni, amma kuma ban san me zan ce
masa ba. Kitchen a fara shiga ina neman abinda
zanci dan yunwa nake ji, gwara ko fadan
za'a yi min ayi min da abinci a ciki na kar a
gama yi min fadan kuma in kasa cin
abinci. Na samu abinci na zuba, na hada
smoothie na na sha sannan na tafi part din Daddy.
Yana zaune ya saka tv a gaba amma daga
gani kasan ba ita yake kallo ba. Na shiga
da sallama "Daddy ba ka kwanta ba?" Ya
daga kai ya kalli agogo sannan na juyo
yana kallo na fuskarsa cike da damuwa.
Na karasa gabansa "barka da dare
Daddy" yace "kin dawo? Ya jikin Safinan?"
Na sunkuyar da kaina ban ce komai ba ina
jiran inji ta inda fadan zai fara sauka kaina,
ko kuma at least ya tambaye ni ina naje
amma sai naji yayi shiru bai ce komai ba,
sai dai fuskar sa a cike take fal da
damuwa, Haka na gaji da zama sai nace "Daddy a
kashe maka tvn ka je ka kwanta? It is
getting very late" yace "ki barshi, Ki je ki kwanta" sat nail ban Il dadi ba, bana son
jayi fushi da ni, so hake yayi min tada ya
aye min abinda nayi ba dal dal bane ba
in yaso ni kuma sat inyi masa bayant
Amma kuma ko bayanin ne ina bukatar
hada kalmomin da zanyi bayanin da su.
Dan haka wannan fushin da yayi duk da
dal banji dadin sa ba amma ya bani
chance din shirya case dina, Amma eluk
da haka sal nace "Daddy kayl hakur'" bal
amsa min ba daga farko sal daga baya
yace "akwal abinda kike so kl gaya min
ne? Akwai laifi da kike so kiyi confessing?* Na bude baki sal na mayar na rufe ban ce komal ba, sal yace "tashi kI je ki kwanta" har na tashi zan Ata /lkl a
sanyaye sai ya kira sunana, na juyo sal
yace "abinda ya faru a da ba zai maimaita
kansa ba. Do you understand me?" Na
gyada kai da sauri *yes, Daddy" na fita da sauri,
Daki na na wuce da sauri ina /in babu dad
a raina, Na san dal Baba Ya'u abinda zal
ce masa shine mjin Safina yazo ya dauke
ni a mota, Sannan kuma yanzu zai ce
masa mijin Safina ne ya dawo da ni a
mota, And I thought he will confront me
about menene alaka ta da mijin Safina da
har zai bar asibiti ya taho wajena? Kuma
ina muka je, But he didn't. And only God
knows why.
Ina shiga daki na zauna a favorite spot
dina, kan gado na ina facing my mother's
picture. A raina ina ta saka da warwara ina
so in samo hanyar da zanbi wajen
warware wanna lamarin ba tare da ran
iyayen mu ya baci ba. Kamar yadda
Muhammad ya fada, we will have to make
them understand, Yes, da mun gudu din
da gaske they may understand but in a
hard way, ni kuma so nake mu samu
mafita ba tare da ran su ya baci ba.
Ban samu kwanciya ba sai after two na
dare, and still without a concrete solution.
Sai dai ina kwanciya waya ta tayi kara na
duba naga number din Muhammad, nayi
murmushi, duk damuwa ta tana gushe
wa, na dauka nace "hey Baby" yace "hey,
bulala nawa aka yi miki?" Nace "ko daya.
Kai fa?" Yace "they are giving me a silent
treatment. Ko fadan ma ba'a yi min ba.
Mama da Abba sun gane gurin ki na taho,
but the rest are thinking cewa ba'a cikin
hayyacina na fita ba. Maybe su maman sun reserving fadan ne for later, " nace "to ko dai meeting
suka yi tare da Daddy sanda bama nan?
Shima kamar reserving yake yi for later". but the rest are thinking cewa ba'a cikin hayyacina na fita ba,
Maybe su maman sun reserving fadan
ne for later. " nace "to ko dai meeting
suka yi tare da Daddy sanda bama nan?
Shima kamar reserving yake yi for later".
Yayi dariya, na fahimci he is feeling much
better than sanda ya bar asibitin and naji
dadin hakan sosai. Yace "I guess we will
find out soon enough, Ni dai na san cewa
wannan battle din bamu fara shi dan mu
daina ba. Yanzu problems a side, yaushe
zaki cigaba da bani labarin? I need to
know all the details kafin in ja damarar
yakin" nace "as soon as any discharging
din ka from the hospital. For you to fully
understand the next part of the story, ina
bukatar in nuna maka wani abu" yace
"Okay. Tomorrow zasu sallame ni insha
Allah. Highest next tomorrow" nace
"Okay, baka da lafiya, bara in barka ka
samu bacci sosai, good night" yace
"good night, and don't forget to dream about me".
And I did dreamt of him, Muna ta hira
muna dariya, And it was the best dream
da na vi a cikin shekaru.
Him👳🏻♀️
Sai da ya tabbatar ta shiga gida sannan
ya tayar da motar yana murmushi, ya tuno
kalaman ta na karshe sai ya girgiza kansa
cikin jin dadi, sai kuma yayi sauri ya dafe
kan "ouch!" Ya fada vana jin zafin ciwon
da yake kan nasa, shi da har ya manta da
shi, lokacin da suke tare kamar ciwon ya
warke, kamar ma bai ji ciwon ba, yanzu
kuwa sai yaji ciwon ya dawo. Maybe dama
ita ce maganin,
Ya fara tunanin abinda yake gabansa,
yadda zai fuskaci iyayensa dan ya
tabbatar zuwa yanzu sun san me yayi,
gashi ya kashe wayarsa dan haka sun yi ta
neman sa a waya ma basu same shi ba.
Ya yarda Safiyya ta fi shi gaskiya, their
parents do not deserve this. But he just love her a lot.
Yayi tunanin zuwa gida saboda ya san by
now sun bar asibitin sun koma gida amma
kuma cion da kansa yake yi masa ya
saka ya chanja shawara ya juya zuwa
hanyar asibiti, ga shoulder dinsa ma sai
yanzu ya tuna da ciwo a wajen, and
maybe driving din da yayi ne ya saka take
masa zugin azabar zafi. Kafin ya karasa
asibitin ya hada gumi, yana zuwa yayi packing sannan ya shiga reception, yana shiga Wata nurse ta ganshi ta ce "ga patient din da ake nema ya dawo". Ya
karasa kan kanta yace da attending nurse
*just give me something for the pain* sal
wani doctor yazo ya kama shi yace "let
me take you to your room, and then we
will see what we will do about the pain",
Aka mayar da shi dakin da va gudu daga
ciki aka kwantar da shi a kan dawo
sannan aka mayar masa da drip din da ya
cire, ya kwanta ya rufe idonsa yana jin
likitocin suna ta zirga zirga a kan sa, a
hakan ya fahimci cewa su Mama sunyi ta
neman sa anan asibitin sai suka yi waya
gida aka ce musu yaje can shine suka tafi
neman sa can din, maybe har gidajen
yan'uwa an zagaya neman sa.
Ai kam sanda suka zo kungiya guda suka
Zo, with all his uncles and aunties, yana jin
mamie tana maganar zata nemi asibitin
suyi referring dinsa zuwa asibitin ta, she
is a neurosurgeon kuma wai suna tunanin
buguwar da yay aka ce ta saka shi ya fita
ba tare da ya san ya fita din ba.
Kowa sai lallaba shi yake yi, tun daga kan
ma'aikatan asibitin har zuwa kan family
dinsa, a cikin yan duba shin yaji har da
muryar Mommyn Safina, amma sai ya cigaba de pretending kamar bace/ yake yI har sai da ta fita, amma daya bude Ido ya kalli Mama sa yasan cewa ta san yana sane ya fita, kuma tasan inda yaje. And
she looks very disappointed in him, Sal
dai bata ce masa komai ba. Ranar Abba
ne da kansa yace zai kwana a gurinsa a
asibiti instead of Haidar da yake kwana
da, Sai bayan da kowa ya tafi Abba kuma
yayi alwala ya tayar da sallah sannan
Muhammad ya mike ya dauki wayarsa ya
cire drip din hannunsa ya shiga toilet
kamar zai kama ruwa and he called her.
She answered immediately with "hey Baby".
And ranar yayi baccin da ya jima bai yi
mai dadi irin sa ba. Ba wai problem din ne
babu ba, but with her by his side, yasan
they can overcome any obstacle together,
Maman Maama✍🏻[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Satiyya❤️🩹
Episode Fifty Three: A Forever Thing 2
Washegari da safe ma yayl bacel sosal
bayan ya koma ya kwanta after subh,
Maganganun Mamie da Mama ne suka
tashe shi, "Wannan yaron fa babu abinda
yake damunsa ina gaya miki Moon, ki rabu
da shi kawal, tsabar rashin Jin magana ne
a cikin kansa ba elwo ba" Mamie tace
"amma ya kamata muy) confirming first
kafin muce babu komal, Ni sam bana jin
dadin ganin sa a haka wallahi, KI bari in
tafi da shi can asibitin koma menene sal
mu tabbatar a can" Mama tace "kashi ina
baki kina kin karba, Yana sane ta yake
komal in gaya miki. Wal yaron nan jlya fa
shirin guduwa yayl, har da zuwa gida ya
hada kaya akwati guda, har da daukan
takardun makaranta ya zuba a mota ya
tafi, Kamar irin yammatan nan na da da
suke guduwa daga gida su shige duniya
idan za'a yi musu auren dole", Mamie ta
yara dariya "kal Zainab, gidadon ne zal
gudu daga gida, Salihin yaro irin wannan.
A cikin yaran mu fa Allah Gidado yana
daga cikin nutsatstsun cikin su. To saboda me zai gudu? Mama tayi kwafa yanzu kike cewa nutsatstse, yaron nan fa duk inda kike tunani ya wuce nan. Wai
dan nayi masa fada ne fa shine ya je ya
hada kaya zai gudu, ko gidan war wa zai
je?" Mamie tace "amma akan menene
kika yi masa fadan? Let's start from there,
nina san ruwa baya tsami banza babana
ba mutumin banza bane ba" Mama tace
"ai dama bayan sa zaki bi. An kusa a fara
lissafa shi a cikin mutanen banzan ai in
dai bai chanja halin sa ba. Duk wanda zai
bijirewa maganar iyayensa menene shi?"
Mamie tace "ni dai ki gaya min Please,
akan menene?" Mama tace "to wadannan
yaran suna da wani problem ne da ya
wuce guda daya?akan wata yarinya ce.
Akan wata tsi....." Sai kuma tayi shiru sannan tace "bana son in tsine mata kar ta dawo ta karasa tarwatsa rayuwar yaron nan" sannan sai ta bawa Mamie labarin abunda ta sani game da Safiyya.
Duk, maganar da suke yi Muhammad yana
jin su, amma sai ya cigaba da pretending
kamar bacci yake yi, a ransa yana lissafin
cewa wannan ranar is going to be a long
day, dan haka bai shirya fara ta yanzu ba.
Yana nan kwance har suka gama
maganganun su, Mamie ta fahimci point
of view din Mama, kuma ta fahimci
damuwarta a matsayin ta na uwa, Amma
kuma sai ta bata shawara. "Sai mun bi abin a hankali, tunda har yaron nan duk soyayyar da yake yi muku da mu bakidaya ya iya hada kaya zai bar gida to gaskiya
sai mun hada da dabara. He loves her
deeply. Kuma love either make a person
or breaks him. Ya kamata mu bashi
listening ear, muji mu kuna saka ido sai
mu bashi shawara. Amma kar muyi
kokarin forcing din sa in ba haka ba zamu
tura shi bango, a karshe kuma zamu iya rasa shi".
Mama tace "to wanne irin tura wa zuwa
bango ne ya wuce hada kayansa da yayi
zai shiga duniya?" Mamie ta sake yin
dariya sannan tace "to ba gashi nan ya
dawo ba? Yadda ya tafi da kafafuwansa
haka ya dawo da kafafuwan sa. So let's
start from there. Mu fara tambayar sa
dalilin tafiyarsa da kuma dalilin dawowar sa sai muji"
Sun jima suna