Showing 339001 words to 342000 words out of 375662 words
Chapter 114 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx
Muhammad saboda
baki yan uwansa in sun zo. Na amince da
abinda tace, sai ta hada da kayan
kwalliyar da kayan lefen da aka kawo daga
gidan su Muhammad da kuma kayana da
na hada na gida wadanda zan tafi da su ta
bawa su Salima Hassan ya kai su suka kai
min gidan Muhammad.
Ni dai tunda muka yi maganar kaya da
Mommy ban kuma bin ta kan su ba, sai
dai duk wanda yazo yayi min godiya sai
inyi masa murmushi kawai. Da dare
Muhammad ya dawo kamar yadda yace
zai dawo. Ina tare da Daddy ya kira ni
yace yazo yana waje a mota. Na dan j
faduwar gaba amma na danne na saka
hijab dina na fita. A motar na tarar da shi
a zaune a seat din driver sai na zagaya na
zauna a gefen sa, na gaishe shi yayi shiru
bai amsa ba sai na dago kai muka hada
ido na sake mayar da kaina kasa, ya kira
sunana "Safiyya" na dago kai da sauri dan
ba zan iya tuna ranar da ya kira sunana
haka ba. Sai ya juyo ya kama hannayena duk biyun ya rike "look at me" na sake
dago kai muna kallon juna "me yake
damun ki?" Na dan kirkiri murmushi "ni
kuma? Nothing fa. Kawai abubuwa ne dai
suka dan yi min yawa" ya girgiza kai "ban
yarda ba. Ba zaki fada min ba?" Na sake
mayar da ido na kasa ina jin kamar zanyi
kuka.
"Ba kya son rabuwa da Daddy? Shine
damuwar ki" nayi saurin gyada masa kai
tunda hakan yana cikin damuwata. Yayi
ajiyar zuciya "ba zaki rabu da Daddy ba
kinji? Insha Allah kullum zamu ke zuwa
muna gaishe shi. Nayi miki wannan
alkawarin. Ki saki ranki ki daina damuwa
kinji?" Na sake gyada masa kai sai yace
'to kiyi min hira. I really miss the sound of
your voice " na danyi murmushi nace "to
me zance? Dazu ma ba muni magana
ba" yace "nayi magana dai. Ni kadai nayi
magana ta dazun ma. Kuma na san gobe
ba lallai in samu ganin ki ba. Ko inzo in kai
ku gurin gyaran gashin?" Na girgiza kai
"muna da yawa ai, ba zaka ji dadin shiga
cikin mu ba. Hassan sai ya kaimu ko mu
dauki driver" ya dan yi murmushi "ko dai
kina kishin kar a gane miki miji?" Na
harare shi tare da kwace hannuna in
kishin nake yi ma ai babu laifi
Miji na mai kyau ne kuma ina son sa" yaji
dadi sosai sai ya saka dan yatsa ya dago
haba ta yana kallon cikin ido na for some
seconds sannan yace "kina da kyau sosai
Piya. Ina son ki sosai",. Na danyi murmushi
sai yace "I am glad ba za'a yi taron da
maza ba, yadda kike ta kara kyau din nan
bana so maza su ganki ballantana ace
kinyi kyalliya" na dan yi dariya "ohh and
you are calling me sarkin kishi ko?" Ya
daga kafada "I wasn't complaining ai. Ina
son kishin ki sosai. Yana kara kin
confirming kina so na" nace "to yanzu su
friends din naka babu abinda zaka shirya
musu kenan?" Yace
"kamar kin san da zu
muka gama rigima. Sunce wai ban
gayyace su daurin aure na ba ballantana
in shirya musu reception and I told them
ni ma ba'a gayyaceni daurin auren na wa
ba. Haka suka zauna suka tsuye ni wai
nayi musu karya nace kin mutu" na bude
ido "what! Yaushe kace musu na mutu?"
Yayi dariya "lokacin wancan daurin auren
ne suka dame ni da tambayar ya akayi ba
ke zan aura ba, and su ba su san irin
heartbreak din da nake going through ba
a lokacin, Ni kuma nace musu kin mutu"
dariya nayi sosai sai ya tsaya yana kallona
kawai yana murmushi. Sai kuma naga yayi
sauri ya dauko wata leda a baya ya miko min "Har na kusa mantawa, I bought you
chocolate slurry, irin wadda kike so" na
dan bude ido kadan sannan na bude ledar
na dauko dan karamin cup din ina kallon
sa sannan na kalli Muhammad "a hana ni
sha fa, kai fa kace min in ban daina sha ba
zan zama katuwa" ya dan daga kafada
"yau dai kadai. Daga yau ba zaki kara sha
ba" na bude cup din na dauko dan
karamin spoon din da yake makale a jikin
cup din na diba na saka a bakina ina jin
dadin narkakkiyar chocolate din da aka
chakuda da madara kuma ba'a saka sugar
ba, na kwantar da kaina a jikin motar tare
da lumshe ido na memories din rayuwata
da Muhammad yana dawomin kaina. Na
bude ido naga idon sa yana kaina, na sake
diba da spoon din na kuma sha sai yace
"babu tavi ko?" Ban ce komai ba na dibo a
spoon din na mika zuwa bakinsa. Mai
makon ya sha sai ya kama hannu na ya
dawo da shi baya ya mayar da spoon din
cikin cup din sannan ya saka dogon dan
yatsa na a cikin chocolate din ya
dangwalo sannan ya kai bakin sa, na
lumshe ido ina jin wani irin feeling na
yadda yake yi wa finger din nawa a cikin
bakinsa, nayi kokarin karbe wa amma yaki
saki, sai ya sake mayar da shi ya kuma
dangwalo wa ya sake mayarwa bakin sa,
"hmmm" yace "chocolate din nan akwai dadi fa" ya sake kokarin mayar da yatsan
nawa cikin cup din for the third time sai na
janye cup din, "zaka shanye min ai'" na
fada trying to make him stop, yace "rowa
ko? To shikenan, ki rike taki chocolate din
in rike tawa" ya fada tare da mayar da
hannuna zuwa bakinsa. Sai da yabi
fingers din daya bayan daya kamar wanda
ya samu sweet din gaske, sannan ya juya
hannuna ya manna min kiss a tsakiyar
tafin hannun. Nayi saurin janye hannuna
tare da boye shi a bayana trying to hide
yadda yake saka ni nake ji. Ya sake cewa
"rowa ko?" Na mika masa cup din gaba
daya,
"gashi na bar maka" yace "taki ce
wannan ai, ki bani nawa kawai" na girgiza
kai sai yace "okay to bana son wannan
din, ki sha kayar ki kawaj" na dauki spoon
din na cigaba da sha da sauri da sauri, ina
son in rage wa zuciya ta bugawar da take
yi. Sai da nayi nisa da sha sannan ya
karbe cup din daga hannu na da hannun
sa daya, daya hannun kuma ya kamo
fuska ta ya juyo dani gare shi and
unexpectedly ya hade bakin mu guri daya.
Sanda ya sake ni babu sauran taste din
chocolate a bakina, ya shanye tas, abinda
ya rage min a bakin kawai taste din sa ne,
wanda nake jin sa kamar ba'a iyakacin
bakina kadai ya tsaya ba, kamar dukkan
jijiyoyin jikina ya zagaya. Na bude idanuwa na da suka yi min nauyi na ssuke su a
kansa, har lokacin fuskarsa tana kusa da
tawa, idanun sa a cikin nawa, murmushi
mai fadi akan fuskar ta sa yace "nima na
sha tawa" sannan ya daga min gira yace
"and mine is sweeter" na tura baki tare da
saka hannu ina goge lips dina nace "kai
kazami ne Allah kuwa" ya danyi dariya
"kar ki damu, da sannu zan jaki zuwa
class dina, watakila ma ki fini kwarewa"
na murguda baki ina magana kasa kasa
sannan na
bude kofar motar na fita nace masa "kayi
wa kanka, na fasa yin hirar da kaj" na rufe
kofar sai kuma na sake budewa na dauki
cup din chocolate dina nace
"kuma ba
zan bar maka chocolate dina ba" yayi
murmushi "na sha tawa ai" har zan rufe
kofar sai yace "hey Piya" na tsaya sai
yace "I love you" na danyi murmushi ina
jin har na huce nace "I love you too Baby".
Na rufe masa kofar amma sai ya cigaba
da zama a motar har na shiga cikin gida
sannan ya tafi,
Na danyi kokarin calming kaina down a
compound amma shima da mutane dan
haka na wuce cikin gida, ina shiga sai nayi
sauri na wuce kitchen na wanke fuskata gabaki daya dan duk dankon chocolate
take yi, sai kuma na zauna a kitchen din
na cigaba da shan chocolate dina ina ta
zabga murmushi ni kadai.
Washegari da sassafe muka tashi muka
shirya zamu tafi gurin gyaran gashi, na
shiga yiwa Mommy sallama na tarar har
lokacin rabon kaya take tayi, har zan fita
sai ta kira ni "Safiyya, ni kuwa yaron nan
bai yi miki maganar yadda yake ciki akan
Safina ba?" Na danyi shiru ina kallon ta,
trying so hard kar in nuna bacin rai na, sai
kuma kawai na girgiza mata kai nace "a'a.
Bai ce min komai ba" sai nayi sauri na fita
daga dakin kar ta sake yi min wata
maganar. Ni bana son jin duk wani abu
daya shafi Safina da Muhammad, bai taba
yi min maganar ta ba nima kuma ban taba
tambayar sa ba. Duk wani hukunci da ya
yanke ko zai yanke a kanta abinda ya
shafe su ne bana son shiga ciki kuma
bana son a shigar da ni.
Muka je tare da Salima aka yi mana
gyaran gashi, sannan aka yi min pedicure
da manicure, aka kuma yi min teeth
whitening sannan saloon din suka yi min
massage for free a matsayin wedding gift din su. Daga nan muka dawo gida muka
tarar mai kunshi har tazo, nan da nan na
zauna aka fara rangada min jan lalle,
bayan an gama akayi baki shima amma
kadan as adon jan, sai ya fito yayi kyau
sosai, har yamma bamu gama ba. Tun da
rana kawayena na kano suka karaso, naji
dadin zuwan su sosai dan akwai da yawa
daga cikin su da mukayi shekaru rabon da
muyi magana sai da bikin nan ya tashi na
neme su kuma sai gasu sun zo. Ko dan
nima na san I was quite popular a
makaranta kuma da yawa kawayena suna
sona.
Lokacin yan gidan mu suna ta shirye-
shiryen zuwa gidan su Muhammad wunin
da aka gayyace su, sai a lokacin na lura
ashe tare da garar da akayi min zasu tafi
su kai musu, ni kuma ana gama min na
shiga wanka nayi da special man wankan
da mai gyaran jiki na ta bani, ina fitowa ta
zo ta kuma turarani da turaren ta mai
kamshi da kama dukkan sassan jiki, cikin
sauri na saka rigar da na tanada for
today's occasion sannan nay sallar
magrib din da ake yi a lokacin sannan
muka zauna zaman kwalliya,
Sanda aka gama kwalliyar ni kaina zaman
kallon kaina nayi a gaban madubi, lallai da
gaske Muhammad yake da yace yana murna babu maza a bikin, dan ni kaina sai
nayi kishin nunawa mazan da ba nawa ba
wannan kwalliyar da kyan da nayi. Sai
kuma naji ina son ya gani shi, ba wai a
hoto ba, dan haka na dauki waya na kira
shi "hey baby" duk yammatan gurin suka
juyo suna kallona, nay musu fari da ido
bayan naji ya amsa "kana ina?" Yace "ina
gidan ki. Kin san ni yau nake tarewa. I am
here busy arranging ny things" nace
"zaka iya zuwa nan yanzu?" Ya danyi
shiru "is everything okay?" Nace "komai
lafiya. Nayi kwalliya ne nayi kyau, and I
want you to see me" ya danyi murmushi
mai sauti. "I won't miss this for a thing.
Zan ajiye komai in taho. Sai in kaiki gurin
taron. Ki ce suyi gaba zamu taho tare"
nace "okay, sai kazo" na katse kiran ina
kallon kawayena da suke bina da kallo,
Nan da nan suka kama surutu "ba tun yau
ba na fada, mijin Fiyya zai sha iyayi"
"wannan soyayyar in da ace kina da
kishiya ai sai ta hadiyi zuciya ta mutu" "ni
kam zan so inje gidan ki watarana in ga
yadda za'a ci wannan soyayya " "in dai
mijin bai yi a hankali ba Safiyya will have
him licking at her fingers" na sake juya
idona nace "na nawa kuma? An wuce
wanna gurin ai". Haka suna ji suna gani suka shiga motoci
suka tafi nace ba zan tafi da su ba, Salima
ma data makale sai ta bini wai ai ba'a
barin amarya ita kadai haka na kora ta
nace in dai bata tafi tare da su ba sai dai
ta tafi ita kadai dan ba zata shiga motar
mijina ba. Sauran mutanen gidan ma babu
wanda bai yaba da kyan da nayi ba dan a
lokacin suke dawowa daga event din
gidan su Muhammad hannunsu cike da
abin arziki. Suka yi ta daukan hotuna da ni
har sai da Muhammad yace yazo sannan
twins suka raka ni na fita wajensa.
Bridal gown na saka fara sal, silky material
a ciki mai karamin hannu sai kuma aka
dora lacy material a sama shi kuma da
dogon hannu, aka kuma yi dogon trail
yana jan kasa sosai a baya na. A dai dai
waist din rigar kuma anyi ago da flowers
different colors an zagaye ni da su, sai
kuma gashi na da aka gyara aka zubo min
da shi ta side din kunnen hagu na sannan
ya sauka har kafadar hagun ya kuma
nannade a bayana, Anyi wa gashin ado da
pins masu different colors kamar na
flowers din jikin rigata. Sannan aka lullube
gashin nawa da farin lacy veil, Takalmi da
jakar hannu na duk sunyi matching da flowers din jikin rigata. Ya fito daga motar
yana kallona baki a sake. Daga kallon
kawai a san kwalliya ta biya kudin
sabulu.
[07/01, 10:48 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Safiyya❤️🩹
Episode Sixty Six : Avenged
Not completely edited 😁 I am tired as always.
Tun daga fitar Aunty Hajjo sai na koma
nayi shiru, tun kawayena suna tsokana ta
har suka ga ina neman saka musu kuka
sai suka rabu dani suka cigaba da
hirarrakin su da shewa, suna ta labarin
gida na da yadda komai na gidan yayi
kyau ya kuma da ce da inda aka ajiye shi.
A lokacin naji Farida tana tambayar "ku
wai da gaske wadancan sababbin
motocin da muka gani da bow a jiki gifts
ne aka kawo mata?" Salima tace "eh fa.
Kanin baban sane ya kawo musu ita da
angon as wedding gift" Hasina tace
"gaskiya mutanen nan suna da Naira, Kin
san kuwa tsadar motar nan? Guda biyu
just like that wai wedding gift?" Salima ta
dan tabe baki tace "in dai kudi ne gidan
su suka zo" sai muka hada ido na girgiza
mata kaina, dan ni idan akwai abinda bana
so shine bragging da arziki, in ka sani kawai
ka sani in kuma ba ka sani ba bana
bukatar ka sani sai dai in ta kama dole.
Suna nan dai har suka yi sallar isha' i,
kawayena da suka zo min from outside of
Abuja duk gidan mu zasu koma su sake
kwana sannan washegari su koma gidajen
su. Around 8:30 sai ga kiran Muhammad,
ban dauka ba sai na mika wa Salima, a
zuciya ta ina tuna cewa tun safe rabon da
inji muryar sa, da ta dauka sai naga tana
murmushi tana kallona sannan tace "ba
ita ba ce ba. Salima ce. Kunya take ji wai
ba zata dauki wayar ba" sai kuma tayi
dariya, sannan tace "okay, gamu nan
zuwa" ta miko min tana murmushi "yace
suna first floor, mu sauka mu same su".
Muka tashi gabaki daya, suka sake gyara
min laffaya ta suka rufe min koina har kafa
ta, sannan suka kara min turare suka
kama hannu na muka sauka zuwa falon da
yake a hawa na biyu. Ni dai jana kawai
suke har suka kaini kan kujera suka ajiye
ni. Sai da na zauna sannan na fahimci a
kusa da mutum aka zaunar da ni. Sai
kuma naji muryar Ya Amen yana amsa
gaisuwar da kawayena suke yi musu, tare
da muryar wasu mazan amma kamar basu
da yawa ba zasu fi su uku ko hudu ba.
Daga nan kuma aka gabatar da addu'a
aka shafa sannan Farida kawata tun
primary school sarkin surutu ta fara zuba,
har da yin speech akan wai sun bawa
Muhammad amana ta, sai tazo ta kama
hannuna ta dora akan nasa tana lissafa
masa irin kyawawan halaye na, ta kara da
cewa "amma fa sai kayi hakuri, akwai iyayi
da taurin kai" ina jin Muhammad yana
dariya. Sai kuma Usman abokin sa shima
ya gode wa kawayena for hidimar da suka
sha a lokacin bikin, ya kuma koda abokin
na su da lissafa irin kyawawan halayen sa
shima, sannan ya tabbatar wa da
kawayena cewa abokin su zai rike amanar
da suka bashi.
Daga nan kuma sai aka fara cinikin
fuskata, kawayena suka dan ware gefe
daya suka yi meeting sannan suka yanki
kudi mai tsoka suka fada, abokan ango
suka fara jayayya, sun jima suna to and
fro sannan suka daidaita akan price din da
kawayen suka ki sauka daga kansa, daga
nan abokai suka ce a bayar da account
details din da za'a basu kudin, suka fadi
account aka tura musu, sai da kudin ya
shiga sannan naji kawayena sun hau
shewa da hun murna, kudin da aka basu
har yafi wanda suka tambaya da farko.
Daga nan Salima tazo zata bude fuska ta
ango ya hana, kiri kiri yace babu wanda
zai ga fuska ta a cikin abokansa a ranar, ai
kuwa nan rigima ta kaure tsakanin sa da
su, suka yi masa gorin dama babu abinda
ya shirya musu a bikin nasa, kuma fuskar
amaryar ma yanzu ya hana su gani. Anan
na jawo shi na rada masa cewa ya gaya
musu ina gayyatar su cin taliyar amarya
nan da kwana uku, amma da Muhammad
ya tashi fada sai yace next week.
Haka dai aka gama komai cikin raha da
walwala sannan suka tashi suka yi min
sallama suka tafi, duk wadda ta leka
fuskata sai inji kamar in rike ta in hana ta
tafiya amma ina ji ina gani suka tafi