Showing 3001 words to 6000 words out of 375662 words

Chapter 2 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx

10 Oct 2025

7906

sannan na dira goshina akan gwuiwowina. Abinda kawai nake bukata kenan tun dazu, seclusion din da zan saki kuka na son raina ba tare da wani yayi min magana ba.

A lokacin waya ta tayi kara, da kida na musamman da na saka wa Gidado, kidan da yakan saka zuciyata cikin nishadi a duk lokacin da na jishi saboda dokin jin muryarsa. Na dauko wayar na tsaya ina kallon sunan sa da yake blinking akan screen din "Pyar❤️"

Naji wani sabon kukan yazo min "Allah sarki Muhammad" na fada a fili. "Allah ka dubi bawan ka ka bashi sassauci" na tuna da irin bakaken maganganun da ya gaggaya min daxu a office dinsa, amma mintina kadan har hana kira na. It won't be easy for him. It won't be easy for me.

Kiran yana katsewa na lalubo block button na danna wa number din sa. Abinda ban taba tunanin zan iya yi ba a rayuwa ta. Amma nasan halinsa a kaina, he won't stop calling hakan kuma yana nufin I might answer, in na amsa kuma komai ya rushe kenan.

Sai dai ina dauke hannuna kiran sa yana sake shigowa through my other line. Shima jiran sa nayi ya katse sannan nayi blocking dinsa ta chan din ma.

Abinda kawai nake hangowa a idona shine fuskar Gidado a yadda na baro shi a office dinsa da zu. I have never in my life seen someone as broken as he looked. And why won't he? Na yaudare shi iyakacin yaudara, na cutar da shi iyakacin cuta, na kuma tabbatar ba zai taba yafe min ba.

Amma a ganina hakan shine dai dai, hakan shine zai fi masa alkhairi, he will heal with time dan ban taba jin wanda yaki warkewa daga heartbreak ba, he will find someone and marry and have children kamar yadda yake da buri, and life will go on while I face my demons alone.

Na shafa cikina wanda shine silar komai, a raina ina jin ina ma dai zan iya gayawa Gidado gaskiya, ina ma dai zai iya sanin gaskiyar cikin. Maybe it will reduce his suffering na dan lokaci kadan, but it will torment him for the rest of his life. Ni kuma simplest way out nake nema masa.

Karar knocking naji a kofa, banyi magana ba dan nasan muryar ba zata fito ba, aka sake wani tare da magana a lokaci daya, muryar Safina "Fiyya na san kina ciki fa, Daddy ne yake neman ki tun dazu" na girgiza kaina, a raina nace "Daddy, Daddy na" sai kuma na mike da sauri na bude lock ɗin kofar, saurin da na tashi da shi da kuma yanayin da nake ciki ya saka jiri ya debe ni, Safina da take tsaye a bakin kofa tayi ssurin rike ni. "Fiyya? Lafiya kike kuwa? What happened again?"

Ban ce komai ba na ture hannunta daga jiki na na kama tafiya da sauri zuwa part ɗin Daddy. Safina ta biyo ni a baya tana cigaba da magana. "Magana fa nake miki Safiyya, at least ki tsaya mana kiji abinda nake ce miki. Ne yake damun ki ne? Nasan kina cikin wani hali and I sympathize with you but that doesn't gives you the right to be rude to us. Dazu naji Yaya Mustapha ma yana gaya wa Mommy cewa yayi miki magana kin share shi. Ko ba komai ai ......"

Tana ta maganganun ta ni kuma ina kallon jerin hotunan da akayi wa stairs ɗin Daddy ado da su, hotunan segments na kamfanonin sa, kamfanoni na.

A lokacin muka kawo bakin kofar part ɗin Daddy, na juyo da sauri ina kallon ta nace "what exactly do you want Safina?" Ta tsaya tana kallon na cikin mamaki, sannan kuma sai tace "I tried to help you, we, your family, are always trying to help you because we love you. At least a thank you would be....."

"Thank you" na ce mata sannan na bude kofar na shiga na mayar na rufe.

Ina shiga parlon idona ya shiga cikin nasa, Allah kaɗai yasan irin dadewar da yayi a zaune yana kallon kofa yana jiran shigowa ta. A fuskarsa naga alamun damuwa sosai, ya kalle ni ya kalli cikin jikina. Yanayin fuskarsa kadai ya isa ya saka mai karyayyiyar zuciya fashewa da kuka.

Mommy tana zaune a kusa dashi itama tata fuskar cike da damuwa.

"Am sorry Daddy" na fada tare da sunkuyar da kaina kasa ina kallon yan yatsun kafata.

"You are sorry?" Ya maimaita cikin muryar da take kara nuna halin rashin lafiyar sa.

Jirin da bai gama sakina ba ne ya sake ɗibana, na ga ya yunkura da sauri zuwa gurina sai Mommy tayi sauri ta rike shi ta zaunar da shi sannan ita ta taho gurina. Ta rike ni a jikin ta tare da fara faɗa. "Kin gani ai, zaki jawo wa kanki matsala ki jawo wa mahaifinki shima matsala, Safina me kike so ki zama ne ni Sa'adatu?"

Sai kuma ta tsaya tana karewa fuska ta kallo. "Me ya faru da ke Safina? Kukan menene kike yi haka ?"

Daddy na ga ya sake kokarin mikewa. Nayi sauri na saki Mommy na karasa inda yake na durkusa a gaban sa. Ya koma ya zauna yana kallon fuskata wadda duk da ban kalli mirror ba na san ta kumbura saboda nauyin da naji ta yi min.

Ya sauke ajjiyar zuciya. "What am I going to do with you Safiyya?" na sunkuyar da kaina kasa. "Me zan yi miki ne wai?" Ya sake tambayar no one in particular.

Ban amsa ba dan bani ya tambaya ba. Ko ni ya tambaya din ma bani da amsar da zan bashi. Mommy ta dawo ta zauna a kusa da shi. Sai naga ya juya yana kallon side ɗin sa, ni ma na juya na taya shi ganin abinda yake kallo

Hoton ta ne, tayi kyau sosai tana murmushi kamar za'a ce Safiyya ta amsa. Sai naji ina jin haushinta dan ita ce silar komai. Daddy might not know it yet but ni na sani in my bones and soul cewa ita ce silar komai. Sai dai bani da wani evidence da zan nuna masa. Bani da yadda zanyi in kare kaina.

****.    ****.    ****.    ****.     ****.     ****

Please vote, comment and share as widely as possible.

Ina yan kasuwar mu wadanda suke son samun more visibility for their kasuwanci? ina masu neman followers a social media pages din su? To ga dama ta samu. Ku sani cewa mai talla shi ke da riba. Come and advertise with me and I assure you that you will get value for your money. No matter how big your business is, dole kina bukatar advertisement dan samun cigaba a kasuwancin ki. Kar ki manta, hatta manyan companies irin su CocaCola, Apple, Dangote etc kullum suna cikin tallan hajar su so why not you….

Duk wanda yayi sponsoring episode zan yi masa tallan business dinsa in the episode which will be posted on Whatsaap, Facebook, Intagram and Wattpad, zan kuma saka number dinsa da kuma link na social media account din business din sa, zanyi posting pictures and links din on my Whatsaap, Facebook and Intagram stories for 24h. Kar ku manta, the advert on the pages will last for as long as social media exist, that means forever.

Yes, we will give this a trial muga yadda zai kasance. After the 10 free pages, we will start posting as soon as we get at least 20 sponsors. Insha Allah this will be a win-win for all of us. And it will be a beginning of a beautiful journey. But if it didn’t work, though it will sadden me but Safiyya will become a “paid” novel.

I will announce kudinsa in hakan ta kasance.

So ku tayani addua cewa it will work. Lol. Cos I want all my fans to meet the amazing “Piya” and her soulmate, “Gidado” as they embark on their journey of a lifetime filled with so much love and obstacles set by their enemies, or should we call them their lovers?

Please share as widely as possible. 

For sponsorship, contact

0704 203 0419

on WhatsApp or send a dm to my Instagram page

https://www.instagram.com/maman.mamas.words?igsh=MW5yaXFqOHhubnIwaQ==

Save my business number

0704 203 0419

and say hi on WhatsApp dan inyi saving naku.

Please, dan Allah, abeg, ban da kira.

Sai na jiku, sai kun jini.

One Love

[07/01, 10:41 pm] +234 906 816 1960: ❤‍🩹*Safiyya*❤‍🩹

*By*

*Maman Maama*

Daga marubuciyar:

Maimoon

A'isha Humaira

Diyam

Tagwaye

Jidda

And now..... Safiyya

*Episode Two: The Young Passengers*

Na sauke idona daga kallon hoton zuwa kasa, ita ta jawo min duk abinda yake faruwa da rayuwata na sani, amma kuma na san cewa dan Adam baya taba wuce kaddarar sa, rayuwar da tayi ita ce tata kaddarar, nima kuma halin da nake ciki shine tawa kaddarar, kuma na sani cewa addu'a tana chanja kaddara dan haka har yanzu ban gaji ba kuma ba zan taba gajiya ba wajan gyara rayuwata.

She was my role model, she has always been. Courage da determination dinta su suke hana ni giving up a lokuta da dama. Yadda ta chanja rayuwar ta from worst to best haka nima nake fatan chanjawa. Giving up has never been in her dictionary and it is not in mine. Kamar yadda Daddy yake yawan yin comment a lokuta da dama, lokutan da muke good time da shi, cewa her fire is burning in me, cewa I have her zeal, strength, bravery and stubbornness, wannan shi nake so in yi proving right.

Maganar Daddy ce ta dawo dani daga tunani na. "Safiyya, daga ina kike? gurin sa kika je ko?" Na dago kai na kalle shi, sai na yi sauri na sake sunkuyar da kaina dan ba zan iya cigaba da hada ido da shi ba.

Mommy tace "baban Mustapha, kasan dai ɓata lokacin ka da ranka zaka yi a gurin tambayar Safiyya a game da maganar nan, ba zata yi magana ba, wata nawa ana fama? Wacce irin tambaya ce bamu yi mata ba?" Yayi ajjiyar zuciya cike da damuwa yace "na sani Sa'adatu, na kasa hakura ne, gani nake kamar watarana zata tausaya min a matsayi na na mahaifin ta"

Naji hawaye na yana sauka akan hannayena da suke kan cinyata.

"Am sorry Daddy " na fada a hankali

"Sorry she said" ya maimaita. "Abinda ta iya fada kenan in anyi mata magana tace sorry" ya fada cikin kokarin daga murya, sai kuma yayi shiru yana mai da numfashi.

Mommy tace "abinda yasa kika dage da nacin sai mun biyo ta Abuja kenan ko? Kika yaudare mu mukayi tunanin you are after your father's health ashe ke kina da plan din ki da kika shirya ko Fiyya?" Na girgiza kai da sauri amma kuma part of me knows gaskiya take faɗa, except maganar daddy's health, tabbas dan in ganshi na nace sai mun tashi ta Abuja.

"Ba kuma zaki fadi ko waye shi ba ko?" Ta sake tambaya with hopelessness in her voice. Daddy yace "ba zata fada ba kin sani. Wallahi da na san zaki iya risking mutuncin ki da na family dinki ki fita ki tafi gurin sa da na ɗana miki tarko, da na saka an biki a baya an gano min ko waye shi, kuma wallahi da nayi masa abinda har ya mutu ba zai manta ba kamar yadda yayi min abinda har in mutu ba zan manta ba, da na rusa rayuwar sa kamar yadda ya rusa taki, da na....." Sai yayi shiru yana jan numfashi a kokarin daidaita numfashin sa da ya fara fita sama sama.

Na fara tracing tun sanda na fita har zuwa sanda na dawo a raina, ina so inga ko na haɗu da wani da ya san ni ko kuma na bar wani hint da zai taimaka wa Daddy yayi tracing Gidado, har sai da na tabbatar babu sannan naji hankali na ya fara kwanciya. Ba damuwa ta abinda Daddy zai wa Gidado in ya kama shi ba, cos I doubt idan zai iya yi masa komai, damuwa ta shine in akayi tracing Gidado to zai san komai, zai san gaskiyar komai and his parents will be involved too, our school management will also be involved, wannan duk yana nufin bacin sunan Gidado, sannan yana nufin goga masa baƙin fenti na har adaba. Wannan kuma shine abinda nake gudu, shine abinda zuciya ta ba zata iya dauka ba.

Ina cikin tunani na naji Daddy yana waya, "Mustapha kazo sama yanzu ina neman ka". Sai hankali na ya dawo jikina, wancan tashin hankalin ya marsa ya bawa wani sabon tashin hankalin gurin zama a cikin zuciya ta. "God, not him please" na fada a hankali ina mummurza yan yatsun hannuna cikin tsananin damuwa.

Tabbas ni nace da Daddy na amince da duk wani hukunci da zai yanke a kaina duk a kokari na ganin na rage masa radadin abinda yake tunanin nayi masa, amma kuma zuciya ta tana kakkaryewa a duk lokacin da ta hasaso hukuncin nasa, na san aure zai yi min, kuma na amince da auren amma kuma damuwa ta shine wa za'a aura min? Wanene Daddy zai zaba min a matsayin abokin rayuwata ta har abada. Shin zai zama blessing to me or a curse?

A raina nasan few choices ɗin da Daddy zai iya yi. A kokarin sa na kare mutuncina dana family din mu dole na san auren gida zai yi min. Wannan yayi limiting choices dinsa zuwa mutum uku kacal, mutum ukun da dukkan su babu wanda ba zai iya lasar tafin kafata ba in dai za'a aura masa ni, mutum ukun da duk kan su babu mai sona, mutum ukun da duk kan su babu wanda nake so. Mutum ukun da daya daga cikin su yake da hannu wajan bata tsakanina da Daddy, daya kuma yake da hannu dumu-dumu a cikin halin da nake ciki a yanzu.

Sai dai bani da tabbas ɗin who is who. Ba kuma ni da shaidar nuna wa Daddy.

But the fork is my only way out.....

If only I can find the fork.....

If only I can find it's marks....

Muryar yaya Mustapha ta katse min tunani na. Na dago kai muka hada ido sai nayi sauri na mayar da kaina kasa ina jin bugun zuciya ta yana ƙaruwa. Ya zauna a kasa nesa da ni kaɗan. "Daddy gani" Daddy yace "kaje motar Safiyya, check the dashboard camera, find out ina taje dazu, if possible, find out da wa ta hadu".

Ban daga kai na kalle su ba har ya fita, sai dai yawun baki na gabaki daya ya dauke, numfashi na ya tokare a kirjina. "Why didn't I think of the damn camera?" Na rafa lissafin way out a raina. Tabbas camera ba zata nuna Gidado ba, amma zata nuna makarantar mu da kuma dai dai inda nayi packing wato kofar building din da yake dauke da offices na some staff. And weekend ne. Few staff ne suka shiga a ranar. If police got involved zasu iya gano wadanda suka shiga a ranar and it will take Daddy closer to Muhammad.

Mara ta naji ta rike da wani mugun fitsarin tsoro. Hawayen ido na ya kafe. Na zauna zaman jira ina jina kamar akuyar da aka kai mayanka take jiran turn ɗin ta.

Bai jima sosai ba ya dawo ya sake zama a inda ya tashi. "Daddy ta kashe camera din kafin ta fita" ya fada yana kallon Daddy. Na dago kai da sauri na kalle shi. Muka haɗa ido sai ya kuma dauke kai fuskarsa expressionless ya cigaba da kallon Daddy.

Daddy yayi ajjiyar zuciya "I should have known. She is always too smart for her age, tun tana yarinya she has always been two steps ahead of mates din ta. But still ban dauka zata yi tunanin wannan angle din ba".

Mommy tace "ban taba dauka kawaye zasu yiwa mutum rana ba sai akan case ɗin Safiyya. Da ace tana da kawaye na tabbatar zamu samu wani information ko yaya ne daga gare su. Safina kuma tayi iyakacin nata kokarin"

Na tuna da kokarin da Mommy take nufin Safina tayi. A raina nace "munafuka ba" tunanin abinda tayi ɗin ya kara min zafi a zuciya ta.

But yaya Mustapha, me yake up to da zai yi wa Daddy karya? Akwai wani abun da yake bukata tabbas.

"Tashi ki tafi" Daddy yace

Na mike still idona a kasa, har na fara tafiya naji Mommy tace "ko parlor ban yarda ki sake fitowa ba sai in zamu bar gidan nan. Kuma wallahi kika fita sai ranki yayi mugun baci". Na ɗan dakata sannan na juyo ina kallon ta nace "to Mommy" a raina nace na riga na gama abinda ya kawo ni abuja ai, na gama da Nigeria ma gabaki dayan ta, bana fatan wani abu ya sake dawo dani kasar nan.

Na kai bakin kofa naji Daddy yace "kai Mustapha ka zauna, akwai maganar da zamuyi" na sake dakatawa tare da rintse ido na, sannan ba tare da na juyo ba, na yunkura na bude kofar na fita.

Kafin in shiga dakina na haɗu da Esther duk a tsorace. Ta biyo bayana "Madam am sorry, ban san an shiga dakin ki ba. Sai dana ce mata kar ta shiga. Na dakata da tafiyar ina kallon ta ina mamakin yadda ta daga hankalin ta akan karamin abu nace "it is okay Esther, relax, she is my elder sister ni kaina ba zan iya hanata yin abinda take so ba".

Na dauka Esther tana yi min maganar knocking da Safina tayi dazu a dakina ne, sai da na bude kofar dakin na shiga sannan na fahimci ba wannan bane ba.

Duk an zazzage contents ɗin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login