Showing 327001 words to 330000 words out of 375662 words
Chapter 110 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx
agogo, nayi sauri na bude ido.
"shikenan zaka saka gobe in tashi da
kumburarrun idanu. Go and sleep Mr
Man" yace "duk wanda yace miki me yasa
baki yi bacci da daddare ba ki ce masa
nine na hana ki yin baccin, in kika ce haka
zasu kawo ki da wuri" nayi murmushi
kawai "good night" yace "sai dai good
morning kuma yanzu ai. But just one more
thing please, Tambaya ce da n'" nace "Allah yasa na sani" yace "Akwai abinda ya damyi confusion dina, lissafina bai tafi dai dai ba gaskiya, dazu ma muna
maganar da Mama sai naga kamar ta
share maganar bata son y" na danyi shiru
ina jin sa ina tunanin wanne lissafi ne, sai
yace "date din da kika gaya min uncle
Ahmad ya kawo sakon takardar nan. Har
zuwa yanzu a lissafina ba'a yi wata biyu
ba ma ballantana uku. I thought sai kinyi
wata uku tukunna or somewhere close to
that. I know you and Daddy all have the
Islamic knowledge concerning that so
dole akwai explanation" yayi shiru nima
nayi, na gane abinda yake nufi na kuma yi
realizing yadda yake avoiding mentioning
sunan Mukhtar.
Jin nayi shiru sai ya sake cewa "kin gane
abinda nake nufi? I just want to know
why" direct na bashi amsa "saboda banyi
masa idda ba. Babu iddar sa a kaina" ya
danyi shiru kamar bai ji me nace ba amma
na san yaji, sanda yayi magana naji relief
mai yawa a tare da muryar sa "and hakan
yana nufin me kenan?" Nace "ni ma ban
sani ba. Sai dai a tambayo" yace "wa za'a
tambaya? Bayan gaki nan ina tambayar ki
Kawai ki fada min abinda hakan yake nufi
n ban sani ba" nace "to ni ma ban sani ba, Good night" yace "zaki fada ne, Zaki yi min dogon bayani ne in details…..." Na katse shi "good night" sai na katse kiran na ajiye wayar ina murmushi duk kuwa da
cewa kaina yayi min nauyi sosai saboda
baccin da yake cikin sa.
Sai bayan da nayi sallar asuba sannan
nayi bacci mai nauyi, ban tashi ba sai
around 12 shima kuma dan ina son inje
inga Daddy ne tunda jiya ma ban samu
ganin shi da daddare ba. Da sauri nayi
wanka na shirya cikin doguwar rigar
atampa na fito as usual banyi kwalliya ba,
ina fitowa Esther ta shiga ta fara hidimar
gyaran dakin dama jiya duk na hargitsa
closet din.
Dakin Daddy na wuce direct, na tarar da
shi tare da uncle Ahmad suna magana,
ina shiga suka juyo suna kallona suna
murmushi "amarya" uncle Ahmad ya fada,
nayi kamar zan koma da baya dan kunya,
sai Daddy ya miko min hannunsa "come
here" na karasa na saka hannuna cikin
nashi sannan na zauna a kusa dashi tare
da gaishe shi, ya amsa na gaishe da uncle
Ahmad shima ya amsa tare da cewa "ya
shirye shire?" Sai nayi kamar banji ba sai
yace "umman ku zata shigo in anjima ai,
Salima zata zo itama kuyi magana. Duk
abinda kuke bukata sai kuyi magana kinji? Ko ba zaki fada min ba ki fada wa Salima
sal ta gaya min" a gyada kai idona a
kasa, Daddy ya dan matsa hannuna a
cikin nasa na dago ido na kalle shi sai
yace "kin shiga gurin Sa'adatu?" Na
girgiza kai "yanxu na tashi, na fara zuwa
wajen ka ne amma yanzu zanje wajenta"
ya gyada kai "alright ki shiga. And be nice
to her" nace "to" har zan tashi kuma sai
na sake cewa "Daddy kunyi magana da
Hajiya? Ta sani?" Yace "eh, I told her tun
kafin a daura. And I will call her yanzu in
gaya mata an daura din, jiya na manta ne"
uncle Ahmad yace "kar ka dora wa kanka
laifi yaya, ai ba kai ya kamata ka gaya
mata ba, Sa'adatu ce zata gaya mata" ni
dai sai ya zame hannu na na tashi, ina jin
Daddy kamar kar ya saki hannun nawa,
sai naji zuciya ta wani iri, he is already
missing me.
Har na kai bakin kofa kuma sai uncle
Ahmad ya sake kira na, na juyo sai ya
nuna min gurin zama dan haka na dawo
na zauna sai yace "na manta ba muyi
maganar ba. Akwai kayanki na gidan
Mukhtar, naje na gansu an hada komai a
waje daya, na saka yau za'a kwaso su a
kawo su nan gidan, ban sani ba ko akwai
abinda zaki yi amfani da shi a ciki.
Kayan sakawar ki da kika bari a can ma na
saka Salima ta hado miki su, tare da lefen
ki ashe duk baki yi amfani da komai ba, in
anjima in zasu zo zasu taho miki da su",
Na danyi ajiyar zuciya sai kjma naga
kamar ni duke jira suji abinda zance,
Daddy zainiya fadar abinda za'a yi ko ya
gaya min abinda zanyi amma Daddy baya
min haka, baya taba yanke min hukunci
sai dai ya tambaye ni abinda nake tunani
in na fadi abinda ya san ba dai dai bane
ba sai ya gyara min zuwa abinda yake dai
dai ta hanyar bani shawara.
"Ni sam ban saka lissafi da su ba. Banyi
tunanin komai a kansu ba. Abubuwa da
yawa ba'a taba using ba except for kujeru
da aka dan zauna akai. I don't know ko
za'a ajiye wa Salima tunda babu abinda
zasuyi har Allah ya kaimu bikinta. In ma
kuma bata son colours din ko design din
za'a iya siyarwa a siya mata wasu"
Uncle Ahmad ya fara girgiza kai, "kayan
masu tsada ne sosai, abubuwa da yawa
ba sai an sake siya miki ba. Kayan suna da
yawa sosai" ya yi ta fada irin ka rasa abin
cewa din nan. Ni kaina na san kayan masu
tsada ne dan sanda Mommy tayi order din
su sai da na jinjina kudin amma tace su
suka fi dacewa da ni. But there is trauma attached to them and I cannot use them.
Kuma wanna kyautar ina ganin zata kara
bonding zumuncin da ya fara samun
baraka tsakanin mu. Daddy yana
murmushi yace "kai da ba kai aka bawa
ba ina ruwanka? Kanwarta ta bawa ai" jin
hakan sai nasan yayi accepting decision
din nawa, na sake mikewa sai uncle
Ahmad ya sake cewa "at least ki karbi
kayan lefen to. Ni na siya dama ai ba shi
ya siya ba, sai ki kara akan dinkunan da
zaki yi na zuwa can gidan" na gyada kaina
nace "zan karba, Thank you Uncle" na
fada dan bana son inyi jayayya da shi kar
ya dauka wani abun ne daban.
Dakin Mommy na wuce duk kuwa da
yadda Esther take bina da cup din coffee
a hannun ta, bata falon ta, babu kowa a
falon dan haka na wuce bedroom din ta
ina fatan kar mu hadu da Safina a can.
Nayi knocking na tura kofa tare da
sallama ina jin yadda gaba na yaje
faduwa, ina cherishing relationship dina
da Mommy sosai ina kuma kokarin
avoiding abinda zai lalata shi. Tana
kwance akan gadon ta amma idonta biyu,
ta dan juyo ta kalle ni sannan ta mayar da
kanta ta kwantar, na zagaya ta side din da
fuskarta take na zauna akan carpet nace
"good morning mommy" ta bini da kallo
tare da dan motsa bakinta kadan ba tare
da naji abinda tace min ba, Banji dadin yanayin fuskar ta ba dan idanunta sun
nuna bayan kukan da tayi jiya bata yi
cikakken bacci ba. Na cigaba da zama a
gabanta amma bata ce min komai ba har
wajen mintuna goma, ina so muyi magana
dan haka nace "I am sorry Mommy" a
hankali tace "for what? What are you
sorry for?" Na danyi shiru ina tunani,
menene abinda nayi wa Mommy ne? Sai
kawai nace "I am sorry for whatever I did
that made you cry" ta dafa gadon ta mike
zaune tare da jingina bayan ta da
headboard. Tana kallona tace "tell me
something Safiyya. Tunda Allah ya hada ni
da ke akwai abinda na taba yi miki that
made you feel I am not your mother?" Na
danyi tunani kadan, I can mention a few
things but I didn't, sai na girgiza kaina
"babu" ta cigaba "but you still think I am
not good enough to be your mother ko?
Ke ma irin ta mahaifin ki ne ko? Kullum
kina tunanin zan cutar da ke ne ko? Kina
kallona a matsayin kishiyar uwa, bayan
kuma da ace Safiya tana da rai da ba zan
taba zuwa gidan nan ba" na girgiza kai
"ko tana da rai Mommy dole zaki zo ai.
Twins kuma fa?" Tayi shiru tana kallona
"you are always smart, with your words
with your actions and with your choices.
You have no idea how much hard it was to
raise you, especially with idanun babanki
da ko kallon banza aka yi miki sai ya chanja fuska, especially with idanun
mutane akai suga me zanyi, Wannan ba
yar ta bace ba wadancan ne yayanta.
Kuma bana taba yin dal dai. Adam will
criticize, Ahmad will criticize, Hajiya will
always have something to say. But I did
my best, Through it all I did my best. Idan
ku baku gani ba Allah ya gani ai. Ban taba
cutar da ke ba kuma ba zan fara daga yau
ba. Yes naso Mustapha ya aure ki amma
ban tura shi yaje ya ci zarafin ki ba. 12 1d AM
Tabbas ina son Safina amma ba zan goyi
bayan ta rabaki da saurayin ki ta aure shi
ba. Ni bana son yaron ma. Har yanzu ma
da kike matsayin matarsa still bana son
sa. Ban sani ba ko nan gaba zaiyi abinda
zai saka in so shi. Amma ina so daga ke
har Adam ku sani cewa it hurts so much
that you do not trust me after all these
years, that you treat me like an outsider
ba wai uwa ba da ya kamata ace ta fi
kowa kusanci da ku, ba zaku bude baku
ku gaya min magana kuyi min bayani ba."
Ta karasa hawaye yana bin fuskarta. Naji
zuciya ta ta kara karyewa, na tashi na
zauna a bakin gadon nace "kiyi hakuri
Mommy, dan Allah ki daina kuka. I am
sorry, I never meant to hurt you wallahi
ban so na saka ki kuka. Ke kadai ce
uwata, ke kadai na sani uwata kuma ke
zaki cigaba da zama uwata. Dan Allah ki
yale min" ta girgiza kanta "there is nothing to forgive ai. Kawai yana yin
tunanin ki akaina nake so ki gyara. In ma
da akwai na yafe miki. Allah ya ji kan
Safiya" nace "Amen. Nagode Mommy"
sai kuma na zagaye ta da hannayena na
rungume ta ina jin wani iri a raina. Nayi
missing our hugs and kisses. Nayi missing
yadda muke zama muyi hira muyi wasa da
dariya. Nayi missing dinta. Ta zagaye ni
da hannayenta ita ma sannan ta dan buga
bayana kadan sai kuma ta sake ni.
Na tashi na fita daga dakin ina jin nauyin
zuciyata ya dan ragu akan issue din. Ina
gama breakfast a kasa su Umma suna
zuwa tare da Salima da uban lodin
kayana, kayan sakawa ta da kuma
akwatinan lefe na da har yau Allah bai
bani ikon bude su na ga menene a ciki ba.
Aka shigar da su wani daki a ka ajiye su.
Sai a lokacin Mommy ta sauko still kana
ganin ta ka san tana cikin damuwa. Suka
gaisa sama sama da Umma, a raina ina ta
addu'ar kar Umma ta ce zata gaya mata
magana kuma sai naga bata yi din ba.
Daga nan Umma tace uncle Ahmad yace
suyi maganar shire shiryen tariya ta,
amma already Daddy yace baya son biki,
baya son duk wani abu da zai jawo
attention din mutane, nima dama banyi
lissatin yin biki ba, Ina dai tunanin shirya
walima for my friends da sukayi ta mitar na watsar da su tun lokacin wancan bikin,
Nan na gaya musu cewa ni walima kawai
dan shirya for my friends, Umma tace to
suna nasu Mutanen sai su zo walimar
kawai, a take Salima tace ba zai yiwu a
kawo mana tsofaffi cikin walimar mu ba,
suna ta musun su sai ga Aunty Hajjo nan
tazo itama. Na gaishe ta nan take ta shige
cikin maganar itama, ita ta goya wa
Salima baya. "A'a ba zaku shiga walimar
su ba. Kinga Salima, ku chanja wa event
din naku suna daga walima zuwa wani
sunan da zai nuna na yammata ne kawai,
in ba haka ba har da kakanni sai kun
ganj"
Ni dai ban ce musu komai ba. Mommy ma
few words kawai take dan sakawa dan
hankalin ta gabaki daya kamar baya gurin
kawai a zaune take. And I asked myself
again ina Safina take? Ko dai ta koma
gidan Muhammad ne?
Ban samu amsar ba sai da na tafi daki yin
sallar na hadu da Esther sai na tambaye ta
ko taga Safina a gidan? Sai tace "ya da
dare bayan kin taho daki Mustapha yazo
ya dauke ta. Na gyada kai, maybe gidan
Hajiya ta tafi ita ma, Ina yin sallar
maimakon in koma kasa sal na dauki waya
la na kira Muhammad muka sha hira, ya gaya min wai already har sunje da Abba kamfanin da zasu vi musu
Renovating gidan, har sun zabi plan, "kamfanin su Ya
Amen ne fa, they are into construction,
Dama su suka gina gidan tun farko, yanzu
ma kuma su zasu yi aiki a kansa" da ya
fara tsara min yadda suke so ayi wa gidan
sai da naji kana yana neman bugawa "ni
fa ba gane wa nake yi ba wallahi. Ka
barshi kawai in an gama naje sai in gani"
ya dan mararaice "inzo in dauke ki yanzu
muje in nuna miki?" na danyi dariya "me
zaka nuna min tunda ba'a fara komai ba?"
Ya danyi shiru "yeah, right. To wani abu
zan nuna miki daban. Wani abu ne da
nasan kina son gani" nace "dauki hoton
sa a waya ka turo min" yace "it is too big,
ba zai dauku a waya ba. Please inzo
muje?" Nace "ko kazo ma ba zan fito ba.
Wallahi gidan mu a cike yake da iyaye na.
Ba zan wuce su in tafi gurin a ba" yace
"ni fa mijin ki ne.
Maganar wa zaki ji? Tawa ko tasu?" Yadda
ya fadi maganar da authority ya sa na
mararaice "Please Baby, dan ni suka zo
gidan fa, Kuma kawai sai in bika mu fice
mu bar gidan?" Ina maganar Salima ta
bude kofa ta shigo tace min "Fiyya ki zo
ga Hajiya nan tazo" nayi mata alamar ina
zuwa sannan nace masa "kaji ko?" Ya
danyi shiru sannan yace "Hajiya
Maryama?" Nace "yes ita" yayi ajiyar zuciya "hey Piya! How are you coping? I
mean ya kuke ciki da Mommy and her
children?" Na sauke ajjiyar zuciya ina jin
dadin concern dinsa nace "yanzu dai
zanje gurin Hajiya. We will talk about it
later insha Allah" yace "okay. Just take
care of yourself kinji? Kar ki bar komai ya
bata min ranki. And ....... Zan shigo in an
jima da dare idan sun tafi. Kuma babu
zama a falo with the cctv thingy" nayi
dariya "okay. Bye Baby. Love you "
Da sauri na sauka kasa, ban san yadda
Hajiya zata dauki maganar ba kuma tana
daga cikin mutane masu muhimmanci a
rayuwa ta wadanda no matter the
situation ba zan so mu samu sabani ba.
Tana zaune a kan carpet ta mike kafarta,
na sauko reluctantly ina tunanin abinda
zata ce min sai cewa tayi "ina akwatin
kayan ki? Nace wa adamu fa ya gaya miki
ki hada kayan ki tare zamu tafi, wannan
karon ni zanyi gyaran amarya" Aunty Hajjo
tayi saurin cewa "a'a fa. Wannan aikin ai
na iyayen amarya ne ba kakanni ba. Ke dai
zaki iya kawo gudummawar abinda kika
tara" na dan saki raina kadan tare da
karaso wa nace "Adam, Hajiya, ba Adamu
ba" ta jeho min throw pillown da yake
kusa da ita "jaira, Adamu zan ce ba zance
Adam din ba" nace "already ai kin fada". Aka sake yin dariya,
Daga nan suka cigaba da lissafe lissaten
su yayin da ni kuma muka ware da Salima
muke namu. Decisions din mu na kayan
da zan saka ne a event guda daya da
nace zanyi sai kuma na kai amarya. Amma
kuma dai bamu sani ba ko gidan su
Muhammad zasu shirya wani abu. Karshe
dai muka ce zanyi dinkuna na fitar biki set
biyar in case, sai kuma sauran dinkunan
da zanyi. A take na dauko system dina
muka fara neman material, shiga can fita
can da kyar muka samu guda biyu da
suka yi mana, to matsalar kowanne sai an
nemi abun da za'a hada shi da shi. A
karshe dai kawai muka yanke shawarar
neman fashion designer da zata yi mana
komai. A karshe dai Salima kin bin Umma
tayi tace a waje na zata zauna "akwai
abubuwa da yawa da zamuyi kuma bamu
da lokaci" Umma tace "au har kun saka
ranar ne mu bamu sani ba?" Sai akayi
dariya kawal.
Da daddare Muhammad yazo kamar
yadda yace, na san da zuwan na sa dama
dan haka naje nayi wanka na shirya cikin
riga da skirt na atampa na gyara gashina
nayi daurin dankwali mai kyau. Dinkin ya
zsuna das a jikina, na shafa turaruka na
masu dadin kamshi, Salima tana ta
tsokana ta wai sai ta raka ni ta gaya masa ita ta shirya ni ko zai dan miko mata wani
abu. Ban samu lokacin yi masa girki ba
amma na saka Esther tayi masa kuma na
san zata fitar da ni kunya. Amma mutumin
nan yana zuwa sai yayi zaman sa a mota
sannan ya kira ni "ina waje a mota" nace
"waje kuma? Ka shigo mana ga ...." "Not a
chance. Ki same ni a mota" ya katse
kiran.
Na sauke wayar daga kunnena ina hararar
ta. "Kinji