Showing 210001 words to 213000 words out of 375662 words
Chapter 71 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx
/>
min. She threatened me. Scissors fa ta dauko tace zata yi min illa, kuna jin ta fa a cikin maganganun. I told her what she want to hear dan kar ta illata ni. Amma
karya take yi min Abba. Ni ban san komai
akan abinda ya faru da ita ba. Dan Allah
Abba ka yarda da ni".
Na rufe ido na ina jin zuciya ta tana
tafasa, na bude na kalli Daddy naga yana
zaune ya dafe kansa sai maimaita salati
yake yi shi ya kasa ma magana. Na sake
kallon Mukhtar naga yadda ya dage yana
ta jera wa iyayensa karya da fatan lallai sai
sun yarda da shi. Sai naji Abba yace "biri dai kam yayi kama da mutum. Idan har abinda ya faru da ita
kenan da tuntuni me yasa ba ta fada ba
tun a lokacin sai yanzu tukunna? Me yasa
ba ta ce tana zargin sa ba sai ta amince ta
aure shi dan ta makala masa wannan
sharrin? Me yasa da farko da yace yana
son ta ta ki shi sai daga baya kuma da
kanta tace tana son auren sa, ya kamata
mu duba wannan maganar, Yaya ya
kamata muyi dogon bincike kafin mu
yanke hukunci",
Mommy tace "amma me yasa yayi karya?
In yana da gaskiya me yasa yace bai ma
san sanda ta bar gidan ba bayan gashi munji sai da suka yi maganganu kafin ta fita?"
Suka cigaba da maganganun su yayin da
ni kuma na kwantar da kaina kawai akan
kujera ina jin su, na fahimci iyayen
Mukhtar gabaki daya kokari suke yi sai
sun kare dan su sun ce sharri nayi masa,
ni kuma nawa ban ya kasa cewa ma
komai saboda rashin lafiya sai fuskar sa
da take nuna tsananin damuwa, sai
Mommy ce kawai bakin ta yaki yin shiru
sai kokarin mayar wa da su uncle Ahmad
maganganun su take yi. Na bude ido na
ina kallon su, a raina nace plan C it is.
Sai na jawo jakata ba tare da sun lura ba
na dauki scissor dina na boye a cikin hijab
dina na mike tsaye na fara magana. "okay
shikenan. Yanzu kunce sharri nayi masa.
Gashi kunji da bakinsa ya fada amma
Umma tace "me muka ji ya fada? Dauko
wayar ki sake kunnawa. Ni dai banji inda
ya amsa yayi wanna mummunan abun
ba" nace "ba zaku yarda ba dama. Ni na
san ba zaku yarda ba. Wai kuma a haka
Daddy yana da rai kenan. Idan babu shi
kuma fa? Me zai faru idan babu shi?"
Uncle Ahmad ya mike a zuciye "ke
Safiyya ki shiga hankalin ki, kar ki gaya
mana maganar banza. An gaya miki kudi
hauka ne da zaki saka mu a gaba kina daga mana murya da maganar banza alhalin mu iyayen kine?",
Na girgiza kaina ina jin hawaye yana bin
fuskata "maganar banza. Maganar banza
kake cewa uncle" na juya ina kallon
Mukhtar da dacin rai nace "you took
everything from me. Duk abinda na
mallaka, duk abinda nake takama da shi
sai da ka raba ni da shi, mutunci na a
matsayi na na ya mace, daraja ta a cikin
al'umma, soyayya da amincin iyayena, my
confidence, my good image, saurayina xa
nake so fiye da komai sai da ka raba ni da
shi saboda abinda kayi min, you almost
took my sanity dan sai da na kusa
zaucewa saboda bakin cikin abinda kavi
min and I promised you tun a lokacin
kuma yanzu ma a gaban iyayen mu ina
maimaita maka, i will take away
everything from you too ko da kuwa duk
abinda na mallaka zai kare akan hakan.
Bayan na gama nawa kuma I will make
sure you get the highest sentence da za'a
¡ya yiwa rapist a Nigeria".
Gaba daya duk sunyi shiru suna kallo na,
ni kaina ban san cewa da karfi nake
maganar ba sai da nayi shiru. Hawaye ne
kawai yake bin fuskata ina zagaye su, Sai
na saka hannu na share hawayen fuskata
a dai dai lokacin da na tsaya a saman kan
Mukhtar da yake zaune a kasa a gaban mu.
Ba tare da sun lura da abinda yake faruwa
ba kawai sai na durkusa na damki gashin
kan Mukhtar na yanka da almakashin
hannuna, making sure na dan yanke shi
kadan. Ya zabura saboda zafi ni kuma na
mike da gashin sa a hannuna. Na nuna
masa almakashin hannuna nace "I told
you zanyi amfani da shi dama. Ga abinda
zan yanka nan" na koma inda na ajiye
jakata na bude na dauko ledar da na ajiye
a ciki ta ziplock na saka gashin a ciki
sannan na ajiye ta a tsakanin uncle
Ahmad da Daddy nace "zan kawo muku
na yaron da na haifa. Run a DNA test ku
gani idan ba nashi bane ba. Idan kunyi
baku yarda ba ku sake asibiti ku sake yi
and I assure you ko sau dari zakuyi zaku
ga 100% compatibility. Dan sa ne".
Mukhtar ya mike yana kallona, daga
dukkan alama maganar da da nayi ta
mantar da shi zafin yankar sa da nayi,
yace cikin kidimewa "you told me he is
dead" na daga kafada "I lied" na koma na
zauna, Daddy yayi magana murya can
kasa "wanne irin dead kuma? Yaushe?
Jiya mana ganshi on a video call". Mukhtar ya zame saura kadan ya fadi sai ya zauna akan kujera tare da dafe kansa, cikin karyewar zuciya ya sake cewa "you
told me he is dead" na sake maimaita wa
nima "I lied", Daddy ya saka hannu ya
dauki gashin Mukhtar da na ajiye a gaban
su, sannan ya dago kai yana kallon
Mukhtar din fuskar sa cike da emotions
da ba zan iya kwatantawa ba yace "idan
har ta tabbata kaine Mukhtar. Idan har ta
tabbata kaine, wallahi, wallahi, sai na
tabbatar da cewa kayi nadamar zuwa duniya".
Ya zame daga kan kujerar da yake kai ya
sauko kasa, in ka ganshi zaka dauka
sanarwar cewa Umma ta mutu aka kawo
masa. Ya bude baki ya kai sau biyar amma
ya kasa furta komai. A karshe sai yace
"Daddy..... Abba ..... Dan Allah.…”
Na mike ina kallon sa nace "I will see you
in court" har zan fita kuma sai na juyo na
nuna uncle Ahmad nace "kai kuma ka
dawo min da kudin da ka sata nan da one
week ko kuma ka kawo min resignationletter din ka".
Na juya na fita, Yes, I know that last part
was petty and uncalled for but I didn't
care. I was beyond caring.
Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Safiyya❤️🩹
Episode Forty Four : Betrayed
Not edited….
Dakina na koma da sauri kamar wadda
ake hankada, ni raina a matukar bace. Yes
na san dama iyaye suna son yayansu and
it is only natural for iyaye to choose yayan
su over every one else, but that should be
on something not as serious as this.
Sanda abin ya faru da ni musamman
sanda maganar cikina ta bayyana every
hand was pointing toward me akan abinda
ni nasan bani da laifi akai amma babu
wanda ya yarda da ni, to me yasa yanzu
ba zasu juya hannun su nuna wanda yake
da laifin ba sai suke neman shield din da
zasu kare shi da shi? Me yasa ni lokaci
daya aka yarda nayi laifin amma shi ba
za'a yarda yayi ba?
But they are all in for a surprise.
Zasu sha mamaki na ba kadan ba.
Dan tabbas Mukhtar sai ya girbi abinda ya shuka sai dai in lahira zasu kai shi su boye shi. In can din ma suka kaishi walakiri yana can yana jiran shi, dan ban yafe masa ba kuma ba zan taba yafe masa ba.
Na shiga dakin na koma na zauna akan
kujerar da na tashi daga kanta ina mayar
da numfashi. Babu wanda zai fahimci
abinda nake ji a zuciya ta sai wanda ya
taba shiga cikin irin halin da nake ciki.
Babu kuwa wanda nake yiwa fatan ya
shiga irin halin da na shiga a rayuwata. Na
sha wahala. Na wahala ba kadan ba. The
pain and trauma of the rape was the
easiest part, sharrin shaye shaye da
Mustapha yayi min, kin yarda da ni da
Daddy yayi da kuma yadda maganar ta
fara kokarin juye wa zuwa kan
Muhammad duk ba sune worst abinda ya
fi bakanta min ba. My life got totally
destroyed lokacin da na fahimci ina da ciki.
. . . . .
11 months ago
Immediately after the night to
remember…..
Ba makaranta ba, a Abuja ma Daddy bai
barni ba ya dauke ni muka koma Kano tare, a lokacin babban tashin hankali na
shine Muhammad, na san yana can cikin
damuwa akan bacewar da nayi na barshi a
ranar da na saka masa rai na kuma yi
masa alkawarin zan kaishi wajen
mahaifina. I tried calling him amma sai na
kasa saboda babu abinda na wuni a ranar
ina yi sai kuka, muryata har dashewa tayi,
kuma yadda muke da fahimtar juna ni da
shi na tabbatar yana jin murya ta zai san
wani abu ya faru da ni, ni ma kuma na san
ina jin muryarsa zan sake wani kukan dan
it will remind me of all the love and the
promises da muka yi wa junan mu. Dan
haka sai na tura masa text, na gaya masa
cewa bayan ya fita aka kira ni cewa Daddy
sun zo amma jikin sa ya tashi, shi yasa na
tafi na barshi dan hankali na ya tashi. And
I forgot my phone in the car shi yasa ban
dauki kiran sa ba. Nace masa kuma da
muka kwana a asilitin jikin baiyi dadi ba
sai muka sake fita dashi da ga kasar, shi
yasa ba zai same ni a waya ba ko ya kira.
Daga nan na rufe dukkan sims dina yadda
ko ya kira ba zai samu ba. But I cried after
that, just the thought of him yana kara
sakani bakin ciki da bacin rai. Tun a
lokacin naji na fara tunanin rabuwa da shi.
A ganina bai yi deserving a used rug like
me ba, Tun kafin muje kano Mommy ta samu
labarin wai na zo gida a buge kuma
bincike ya nuna cewa saurayi ne yaje makarantar mu ya dauke ni ya fita da ni. Na kuma san wanda ya bata labarin....
Abinda ta fara saka ni a gaba da tambaya
muna zuwa gida shine waye saurayin
nawa?
"'Wanda kika ce zai zo gurin Daddyn ku
ne? Dama ba mutumin kirki ba ne ba
Safiyya? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
abinda kika zama kenan Safiyya?"
And then…..
"Na gaya maka dama baban Mustapha,
yarinyar nan aure za'a yi mata kaki yarda.
Tun da ta nuna auren ta ke so to ai auren
ya kamata ayi mata. Ga Mustapha nan
yace yana son ta amma daga kai har ita
kun nuna ba kwa son abin. Gashi nan ai ta
fara kula wadanda ba mutanen kirki ba.
Bayan ga wannan wanda kai kayi tarbiyyar
sa da kan ka". Naji kamar zuciyata zata kama da wuta,
Wata irin tsanar Mustapha tana kara shiga
ta. A zuciya ta ina kara tabbatar wa da kaina
cewa shi ya aikata min wannan aika aikan dan ya cimma burinsa, dama ya jima yana
nema ya ga tabbas ba zai sa mu ba, ya
shigo da maganar aure ba dam yana so
na da gaske ba sai dan kudin da yaji an
ambata a matsayin nawa, shima kuma ya
ga babu nasara ta wannan bangaren shi
yasa yayi min wannan abun, sannan kuma
ya kala min sharrin shaye shaye, dan a
matsamin dole in aure shi shikenan ya
samu riba biyu. Ni kuma tun a lokacin nayi
rantsuwa a raina cewa ko mazan duniya
zasu kare ba zan aure shi ba. Na kuma
rantsuwa cewa sai na tona mass asiri.
Amma kafin in tona masa asirin ai dole sai
na bayar da labarin abinda ya faru da ni
sannan in shigar da maganar wanda nake
zargi. Amma kuma maganar tayi min
nauyi da yawa a bakina, a zuciya ta. A
cikin first few weeks da faruwar abin na
gwada bude bakina in fada yafi sau a
kirga amma sai dai in mayar da bakin in
rufe ba tare da na fada din ba saboda
maganar taki fitowa, Magan6ce da bazan
iya yin ta da Daddy ba duk kuwa da
shakuwar da take tsakanin mu, ita kuma
Mommy da ya kamata inyi maganar da ita
dan ta nake zargi da aikata min wannan
abun dan haka ita ma sai ma kasa bude
bakina in gaya mata,
Sai dai kuma tun da abin ya faru sai na rasa lafiya. Farko tsananin
ciwon jikin da ma dangantashi da abinda
ya faru, sai kuma ciwon kan da nayi
tunanin tashin hankali ne da bakin ciki ya
saka min shi, daga nan bayan sati biyu sai
abin ya wuce ya zama zazzabi. Mommy ta
kaini asibiti suka yi min gwaje gwaje suka
bani magunguna har da su karin ruwa,
kwana na biyu aka sallame ni na dawo
gida na fara pretending kamar na warke
saboda yadda nake tsoron allura, amma
kuma sam ban warke ba din, tun ina boye
ciwon har na kasa na cigaba da bayyana
shi aka sake mayar da ni asibiti, suke
typhoid suce malaria haka dai muka yi ta
fama. Haka na cigaba da zama a gida ina jinya
ta ina kallon Safina tana zuwa makarantar
ta ni kuwa an rabo ni da tawa makarantar
kuma babu ma zancen komawa ta ko
kuma sake min wata. Daga cikin tashin
hankalin da nake ciki a lokacin shine
maganar Muhammad, ga mamaki na ya
yadda da karyar da nayi masa, da na
samu mukayi online call ma he sounded
so genuinely concerned about jikin Daddy
har yana tambayar in akwai abinda zai iya
yi to help. Sai kawai na saka masa kuka,
ina tausayin sa ina kuma tausayin kaina.
Ina kuma jin haushin kaina akan karyar da
nake ta shirga masa, amma abinda ya faru
da ni abu ne da budurwa ba zata iya bude baki ta gaya wa saurayin ta ba.
Through all these emotional rollercoaster
da nake ciki I missed my period ba tare da
na fahimta ba sai one week after lokacin
da ya kamata in ga period din, ranar da
nayi realizing na shiga toilet ne da niyyar
yin wanka na shire kayana kenan and I
noticed change a kirjina, farko ban yi wani
giving much thoughts to it ba sai daga
baya bayan na fito daga wanda ina shafa
mai sannan na sake fahimtar chanjin and
my first thought was abinda akayi min ne
ya saka naga wanna changing amma
ban kawo ciki ne ba, sai bayan nazo saka
kaya sannan na ga pad a cikin drawer and
it occured to me that ya kamata a ce nayi
period. Na dauko waya ta da sauri na duba app
din da make tracking period dina da shi
and it shows 8 days late. Sai da ma yanke
jiki na fadi. Allah ne kasai ya saka banji
ciwo ba amma na jima ban dawo cikin
hayyacina ba amma tashin hankalin da na
shiga ciki ba xai misaltu ba.
"Allah, Allah, Allah" kawai nake maimaita
wa, na ma rasa me zan roki Allahn, na
rasa me zan ce masa. Kukan ma a ranar
bai zo ba. Hijab dina kawai na saka na
dauki jaka ta tare da key din mota na fita
da sauri, Safina da take falo tana kallon series hankalin ta a kwance tayi ta min
magana amma ni ba ma jinta nake yi ba
na fice da sauri. Abinda nake lissafi kawai
shine inda zan je in tabbatar da zargin da
nake yi sannan kuma in ya tabbata in fitar
da shi. A lissafi na sati biyar kenan dan
haka bai kai matsayin da zai zama laifi in
na zubar da shi ba, sannan kuma na taba
jin waazin da aka ce idan rape case ne irin
nawa malamai sun yi saasauci akan
hukuncin zubar da shi. Sai dai o bayan da na fita daga gidan da mota ban san inda zan dosa ba. Ni dai na
san ba zanje gurin likitan gidan mu da
wannan zancen ba dan idan yaji to kamar
Daddy yaji ya gama ne, ni kuma zan iya
bayar da raina a lokacin dan kar Daddy
yaji wannan maganar.
Haka nayi ta yawo da mota a titinan garin
kano ban san inda zan je ba. Cikin ikon
Allah kawai sai naga signboard din wani
asibiti a bakin titi, I followed the directions
sai gani a kofar asibitin, dan karamin clinic
ne haka, Na shiga na je reception din su
na nemi gain likita suka ce sai na bude
file na bada kudi suka bude min na cike
info din da duka nema amma ko kadan
ban saka addres dina na gaskiya ko
number wayar wani a gidan mu ba.
Daga nan naje na hau layi, babu abinda
nake yi sai salati da istigfari a zuciyata ina
rokon Allah yasa kar zargi na ya tabbata, a
haka layi yazo kaina na shiga gurin likitan
direct na gaya masa pt nake so ayi min.
Ya tambaye ni symptoms dina na fada
masa sai ya rubuta min test din yace inje
lab suyi min, na je lab din suka dauki jini
na, for the first time in my life aka huda jiki
na ban ma san an huda ba dan zafin da
nake ji a raina ya ci uban zafin allurar.
Ina zaune dai har aka gama, zuwa lokacin
na tabbatar an fara nema na a gida dan
dai har lokacin layi na a kashe yake da an
fara kira na. Hankali na idan yayi dubu ya
tashi. A haka aka rubuta min result din
aka ce in mayar wa da Dr. Ban mayar din
ba na samu guri na zauna na bude
takardar da sauri ina bin rubutun da kallon