Showing 81001 words to 84000 words out of 375662 words
Chapter 28 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx
yana so ya
dauke ni ni kuma ina iyakacin kokarin ganin
cewa bai dauke ni din ba, I needed to stay
awake and alert dan in samu damar planning
on my revenge on Gidado da Safina.
Ban samu bacci ba sai bayan da muka sauka
a lagos muka sake shiga wani jirgin zuwa. Ban samu bacci ba sai bayan da muka sauka
a lagos muka sake shiga wani jirgin zuwa
Abuja after waiting for 30minutes. Tun a
Lagos din naji Daddy yana ta waya da
Mustapha da kuma Mommy yana basu
labarin abinda ya faru, ya kuma gaya musu
gamu nan zuwa, sannan ya umarci
Mustapha yaje airport a Abuja ya dauke mu
sannan ya sanar da doctor din sa gamu nan
zuwa dan zai sake dubani in mun karaso. Na
fahimci su Mommy har lokacin a cikin
hidimar biki suke, a lokacin ne kuma na tuna
da cewa yau ne da daddare za'a yi dinner, a
yau din ne kuma za'a kai amarya, dan haka
na fara planning din yadda zan hargitsa
dinner din sannan in tabbatar da cewa first
night din su is the worst in history of
marriages.
Karfe biyu na rana da yan mintuna muka isa
Abuja, da kyar na iya mikewa daga kan
kujerar da nake kai saboda yadda gabaki
daya jikina yake min ciwo sannan gurin
aikina yana ta yi min zugi. Duk da ma na
kwantar da kujera ta ba wai a zaune nake
sosai ba. Ban iya tashi ba sai da wata
maaikaciyar jirgin tazo ta kama ni muka tafi
a hankali. Muna fita waje na hango Mommy
da Mustapha, Mommy ta taho da sauri inda
nake tana kare min kallo sannan ta juya
gurin Daddy shima ta bishi da kallo "me ya
same ku?" Ta tambayi no one in particular,
babu wanda ya amsa mata sai ta karbe ni
daga hannun air hostess din ta cigaba da
tafiya da ni zuwa motar da suka zo da ita.
Mustapha kuma ya cigaba da tura. Mustapha kuma ya cigaba da tura
wheelchair din Daddy. Muka karasa motar
ya taimaka masa ya zauna a gaba sannan ya
saka wheelchair din a boot din motar ya
shiga gaba mu kuma muka shiga baya ni da
Mommy. Na jingina kaina a kujerar motar ina
kallon titi da motoci da tituna da gidajen da
muke wucewa. A zuciyata nace Nigeria my
dear country, na dawo, let's see what you
have in store for me a wannan karon.
Na lura da ga Mommy har Mustapha
kwalliya ce a jikin su, kwalliyar bikin Safina.
Tun da muka shiga motar Mommy bakin ta
bai yi shiru ba tana ta fadan me yasa muka
taho a cikin halin rashin lafiya. Tace kuma
laifi na ne tunda a waya Daddy yace mata ni
ce na takura sai na dawo gida "kin san cewa
duk abinda kika fada kamar yankan wuka ne
a gurin sa, in baki damu da taki lafiyar ba ai
ya kamata ace kin damu da tasa". Ni dai ban
amsa mata ba, da ta cigaba ma sai na saka
hannayena biyu na toshe kunnuwana
sannan na rufe ido na. Can ness na jita tace
"shikenan ai" sai kuma tayi shiru.
Asibiti muka fara zuwa, muna zuwa suka
fara daukan vitals din mu a take suka sake
admitting Daddy. Ni kuma suka rubuta min
bedrest har sai sunce otherwise. A can
twins suka zo suka same mu. Suma daga
gani daga gurin bikin suke. Suka rungume ni
da murnar gani na. Ina jin Daddy yana musu
magana "careful, bata da lafiya" suka cika ni
suna kare kin kallo sannan Hassan yace
"you look terrible" nayi kokarin yi masa. "you look terrible" nayi kokarin yi masa
murmushi amma na kasa. Mommy suka fita
da Mustapha zata tura shi airport ya dauko
wasu kawayen ta da suka zo dinner din da
za'a vi yau. Suka barmu ni da Daddy da
twins.
Daddy yace musu su dauke ni su tafi da ni
gidan mu na nan garin "ba gidan bikin zaku
kai ta ba. Ba kuma gidan Ahmad ba. Ku kaita
gida ta huta, and stay with her" suka gyada
kai a tare. Har na mike zan tafi sai ya kira
sunana, "zo nan" daga yadda yayi maganar
nasan fada zaiyi min amma sai naji ban san
laifin da nayi ba kuma. Su Hassan suka fita
ni kuma na zauna a kujerar da take kusa da
gadon da yake ya sunkuyar da kaina kasa
sai ace "Safiyya. Baki gaishe da Sa'adatu
da Mustapha ba why?" Nayi shiru ina jujuya
hannuna yace "har yanzu fushi kike yi dan
sun taho sun bar mu?" Still ban ce komai ba.
21
11
1
7:46 PM
Ya sake kiran sunana "Safiyya" na amsa a
hankali, yace "Make peace with Sa'adatu
and her children. Kinji ni?" Na gyada kai na
kawai. Amsa ta bata gamsar da shi ba sai ya
sake cewa "kiyi min alkawarin ba zaki yi
rigima da su ba" na dago kaina ina kallon sa,
he looked so sick and tired, shine mutumin
da yafi sona fiye da kowa a duniya, shine
mutumin da nafi so fiye da kowa a duniya.
Nace "nayi alkawari Daddy. Ba zanyi rigima
da su ba" yace "good" na sake mikewa yace
"and one more thing" na sake dawowa na
zauna vace "wave Muhammad?" zauna yace "waye Muhammad?"
Nayi sauri na kalle shi da mamaki. Lokaci
daya mood dina ya chanza daga indifferent
zuwa tashin hankali. Yayi ajjiyar zuciya yace
"so, shine baban Adam kenan" na fara
girgiza kai na "Daddy.…... Muham.…waye
Muhammad?" Yace "oh ni kike tambaya
kenan. You call his name sau ba adadi sanda
baki da lafiya. And now you are telling me
baki san waye ba. Gashi kuma fuskar ki ta
nuna alamar rashin gaskiya karara. Na
fahimci shine baban wancan yaron. Na
fahimci kuma kina sonsa sosai shi yasa kike
cigaba da boye min shi dan kar inyi
punishing dinsa for what he did. Just tell me
who he is. I am not going to do anything to
him a yanzu. I just want to give him his son. I
just want that innocent baby to have a
father"
Na fara hawaye "Daddy ba nashi ba ne ba"
babu abinda yake tayar min da hankali a
duniya irin kin yarda da ni da Daddy yayi.
Yayi shiru bai sake cewa komai ba har
Mommy ta dawo. Na goge fuskata da sauri
amma sai da ta lura da hawayen tace "har
yanzu ana nan ana fama kenan" na kalli
Daddy sannan na gaishe ta. Ta amsa shortly.
Ina zama a mota na cigaba da kuka na.
Hussein yace "yaushe zaki daina kuka ne
wai yaya?" Ban amsa masa ba dan ni ma
ban sani ba. Na dauka xasu tambaye ni ina
baby amma sai naji duk basu tambaya ba,
and I felt bad for little Adam. No body. and I felt bad for little Adam. No body
wanted him. Not even his uncles.
Gab da magrib muka shiga gidan. Esther ta
tarye ni ta gaya min cewa dama Mommy
tace ta gyara min dakina. Na shiga dakin na
zauna twins suka shigo min da jakar kayana
da Aunty Hajjo ta hado min da ga can. A ciki
naga handbag dina, a cikin ta kuma naga
wayata da na yar a dakina a Berlin san da na
ga hoton Muhammad da Safina. Already
wayar har ta mutu charji ya kare.
Ina zaune Hassan ya dawo da tea a
hannunsa ya hado min, Hussein kuma yaxo
yace "yaya ko in hada miki smoothie irin
wanda kike sha kullum?" Na girgiza kaina
kawai ina jin babu dad yadda suke ta
kokarin kyautata min amma na kasa ko da yi
musu magana ne. Na bude jakar tawa na
dauko wani dan karamin hoto na rike a
hannuna ina kallon sa. Hoton mace da yayan
ta mata guda uku. Na shafa fuskar wacce
take mahaifiyata a cikin su ukun. She
suffered more than suffering din da nake
ciki, She lost more than abinda ni na rasa a
yanzu, She almost lost me too, but then she
gave her life for mine, Amma duk da yadda
rayuwar tata ta kasance, she never lost
hope, She kept her head high and she
achieved fiye da yadda tunanin mai tunani
zai tunano masa, Na ajiye hoton. And so will
1
Na dago kai ina kallon Hassan da ya saka ni
a gaba yana kallo kamar zai yi kuka nace. a gaba yana kallo kamar zai yi kuka nace
*karfe nawa ne dinner din Safina?" Yayi
mamakin tambaya ta amma sai ya kalli
agogo yace "7pm dai suka saka a kati.
Though sunce babu African time dan a yau
za"a kai amare bayan dinner din" na
tambaya "amare?" Yace "eh, su biyu ne ai,
akwai sister din mijin yaya Safina, tare aka
hada auren nasu" "Mufida" na fada a
hankali, yace "kin san ta ne?" Ban ce komai
ba sai na dafa gado na mike. Shima ya mike
da sauri yana kokarin rike ni. Nace "Okay.
Let's get ready kar mu makara" ya bude ido
"kar mu makara zuwa ina? Mu mun fasa
zuwa ai tunda Daddy yace mu zauna da ke.
Ke ma baki fa da lafiya ba zaki iya zuwa ba"
na kirkiro murmushi nace "dan inje dinner
din nan na taho tun daga Germany da sabon
yanka a cikina, bana jin akwaí abinda zai
hana ni zuwa",
17
11
7:46 PM
Na shiga toilet na tsaya ina kallon kaina a
madubi, saí a lokacín na kara fahimtar
abinda twins suke nufi da suka ce I looked
terrible dan da gaske I really looked terrible.
Idona ya kara fadawa kasa ya kuma loosing
all the light da suke cikin sa, fatar idon ta
yamushe tayi baki, fatar lips dina ta bushe
har tana neman tsagewa, ba zan iya tuna
rabon da in shafa mai a bakina ba, ko a
sauran jikina, Na tuna da da a gurina babban
abu mai muhimmanci shine skin care routine
dina, bana taba yadda inyi missing. Amma
yanzu da rayuwa ta nuna min shege banga
na fahimci komai ma guri yake samu. na fahimci komai ma guri yake samu.
Sanitary pad din jikina na chanja na sake
gyara kaina sannan na fito nace musu "na
shirya, ku zo mu tafi" suka kalli juna sannan
suka kalle ni, Hussein yace "yaya dinner ce
fa. Kuma dangin angon nan naga manyan
mutane ne sosai. It is going to be
extravagant ....." Na yafa mayafi na nace "ba
zuwa zanyi dan in burge kowa ba, zuwa
zanyi dan inyi wa yar uwata murnar sabon
auren ta. Wanda yaga ni ko shigata basu yi
masa ba sai dai ya rufe idon sa".
Doguwar riga ce a jikina ta yadi. Rigar aunty
Hajjo ce ta bani na saka da zamu taho
saboda tana da girma sosai kuma yadin
yana da laushi ba zai ke min famin ciwo na
ba. Rigar duk ta chukwuikuye saboda zaman
jirgi. Dankwalin rigar na daura a kaina na
rufe dankararren gashina da na manta rabon
da in taje shi. Sai kuma wani mayafi da ko
kadan bai shiga da yadin ba dana dora a
kafada ta.
Ganin basu da niyyar tashi mu tafi sai na
wuce su na ce "in kun gama ku same ni a
waje", A parlor na zauna ina jiran su, Esther
ta zo da sauri ta kunna min tv da ac, ni duk
basu dame ni ba, so nake inyi sauri inje in
aiwatar da abinda yake raina, Wajen 7:30
suka fito, still da alamar basa son inje, na
mike tsaye "kun gama?" Suma basu chanja
kayan jikin su ba, Hussain ya sake kokarin
hanani fita "yaya bedrest fa aka baki" ban
amsa ba nayi hanyar waje, sai kuma na dawo. amsa ba nayi hanyar waje, sai kuma na dawo
da baya nace musu "a ina ne gurin? Akwai
gatepass a hannun ku? Na iya mota ai zan
iya kai kaina in ba zaku kaini ba".
A dole suka fito muka shiga mota muka tafi,
sai da muka yi nisa nace musu "kar ku gaya
wa Daddy naje" basu ce komai ba.
Muna zuwa mukayi packing a inda aka
tanada, na zauna a mota ina kallon mutane
suna ta shiga gurin, ga kida har ya fara
tashi. Sai na rufe ido na ina kokarin karfafa
zuciyata. Yau zan ganshi. Amma a matsayin
mijin wata. A matsayin mijin Safina. Yayin da
ni kuma nake matsayin matar wani. Matar
Mukhtar. Sai da naga alamar gurin ya cika
sosai sannan nayi karfin halin fita daga
motar, tunda na fita naji alamar jiri yana
neman dibana amma na daure dan bana son
twins su sani, na taka a hankali naje har
bakin kofar na bayar da katin da twins suka
bani sannan na shiga. A gurin muka rabu da
su su suka tafi bangaren maza ni nayi na
mata. Dama abinda nake so kenan. Ina
kallon security din yana bina da kallo, maybe
ya dauka almajira ce, Daga can karshe na
samu guri na zauna saboda bana son wanda
ya sanni ya ganni, Duk da dai nasan a yadda
nake din nan ba kowa ne wanda ya sanni zai
gane ni ba, A haka har guri ya gama cika aka
fara gabatar da event, Ina ji aka yi
announcing zuwan iyayen su Muhammad da
Mufida, suka shigo cikin isa da burgewa.
Sannan aka shigo da iyayen angon Mufida,
suma suka wuce, sal iyayen amaryar. suma suka wuce, sal iyayen amaryar
Muhammad, wato Safina, Mommy ce a gaba
da yan uwanta suna take mata baya, nayi
ajjiyar zuciya, wato ta baro mijin nata a
asibiti ta taho dinner. Daga nan kuma sai aka
y announcing shigowar angwaye da amare.
Na mike tsaye daga inda nake ina hango
kofar da zasu shigo ta cikin ta. Su
Muhammad ne a gaba. Ido na fuskarsa ta
fara gani. Yayi kyau iyakacin yadda dan
Adam ya kamata yayi kyau. Gefensa ga
yayata nan Safina, taci kwalliya ta ajin
karshe, fuskar ta dauke da murmushi idonta
a kasa kamar mai jin kunyar mutanen gurin.
A bayan su abokan Muhammad ne, most of
which na sansu, da kuma kawayen Safina,
gabadayan su na san su. Kowannen su cikin
kwalliya ta alfarma kuma cikin farin ciki. A
raina nace gabakidayan su munafukai ne,
tun daga kan Muhammad din har zuwa kan
securities din gurin, duk munafukai ne.
25
14
7:46 PM
Sai naji a raina ina fatan ina ma dai ginin
gurin ya rushe ya fado a kan mu gabaki
dayan mu mu mutu kowa ya huta.
Ina na tsaye har suka je suka tsaya a
tsakiyar fage, aka ringa kiran iyaye suna yi
musu ruwan kudi, daga inda nake ina hango
yadda Mommy take watsi da kudi. Kudin da
ba ita ta nema ba, Sai da aka gama aka ce
suke su zauna. And those minutes daga
shigowar su zuwa zaman su, zan iya cewa
are one of the most terrifying minutes of my. are one of the most terrifying minutes of my
life.
Suna zama aka yi announcing shigowar
Mufida da angon ta. Nan da nan sai hankalin
mutane ya koma kansu. I took my chance.
Burina shine in hargitsa bikin ba tare da nayi
calling attention din mutane zuwa kaina ba,
not that I care about mutane, but bana son
Daddy ya sani. Bana son yasan komai.
Na bi ta gefen mutane har sai da na wuce
inda mutane suke zazzaune. Ina jin jiri yana
dibana amma na cigaba da daurewa. Daga
inda nake ina hango Muhammad da Safina
akan kujerun da aka tanada saboda su.
Idonsa yana kasa yana daddanna wayarsa,
ita kuma tana magana da wata kawarta
Husna. Na taka a hankali na tafi inda suke
idanuna a kansa, zuciya ta tana jera duk irin
zagin da ta iya tana yi masa. "Munafiki.
Mayaudari. Maci amana" sai dai kuma kiran
tasa zuciyar take yi, so take ya amsa, so
take ya dago ya kalli cikin idona ya gaya min
dalilin da yasa ya auri yar'uwata.
Tamkar wanda tasa zuciyar taji kiran tawa,
sai ya dago idonsa a lokaci daya suka fada
cikin nawa. Ina kallon sanda wayarsa ta
zame daga cikin yatsun hannun sa ta fadi
akan carpet din gurin. Ya mike tsaye a
hankali kamar wanda ake jansa da zare. Na
cigaba da tafiya idona a cikin nasa har sai da
naje na tsaya a gabansa tsakanin mu bai fi
taku daya ba. taku daya ba.
Sai a lokacin Safina ta ganni, ta zabura
kamar wadda aka watsawa wuta. Na dauke
ido na daga cikin nashi na mayar kanta nace
"hello dear sister. Na taho daga Germany
nazo nan gurin musamman dan ke, dan inyi
miki HML. Happy Married life to you" na
mayar da ido na kansa, har lokacin ni yake
kallo da idon da ban san yadda zan
kwatanta shi ba. Nace "and Happy married
life to you too".
Sai na juya a hankali na sauka daga kan
stage din, doing everything in my power dan
ganin na hana kaina faduwa a gurin, bana
son Daddy ya sani. Wata kofa na gani a kusa
da stage din, kamar masu rabon abinci ne
suke fitowa daga ciki. Nayi sauri na shiga, na
wuce su suna ta hidimar su, na ga wata kofa
na sake shiga sai na ganni a waje, kamar filin
bayan gurin ne. Na tsaya ina tsakar
numfashi da sauri dan in samu in daidaita
bugun zuciya ta,
Ji nayi an finciko ni da karfi an juyo dani,
saura kadan in karasa shidewa, Muhammad
na gani a tsaye a gaba na fuskarsa da yana
yin da ban taba ganin ta cikin sa ba, yanayin
da ba zan iya kwatantawa ba, EPISODE EIGHTEEN
15
> 5
3
owner
2
7:43 PM
Safiyya
Episode Eighteen: New Couples
Paid advert
*Contact Bojuwa HERBAL'S for all your*
*kayan mata for*
*Amarya*
*Uwargida*
*Bazawara*
*Mai jego*
*Saiwowin sanyi gangariya da na dahuwar
kazar sababi har da na tattabaru da ciccibi
all from Chad.*
*Kayan gyara masu kyau