Showing 276001 words to 279000 words out of 375662 words

Chapter 93 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx

10 Oct 2025

7926

/>
Madam. I am just happy that you are in a good mood today. Kwana biyu baya duk fuskarki babu smile" nayi murmushi "someone put a smile on my lips early this morning, and I am going to hold on to it har dare" ta danyi dariya tana tafa hannu "wonderful. I am so glad madam. Zanyi zaman daki. Please take me with you" na bude ido "I said someone, ya akayi kika san namiji ne?" Tace "I know love when I see it, and you madam are in love"., Nayi murmushi kawai bance komai ba.

A lokacin naji alamar wani ya shigo gurin, naga kuma Esther ta gyara fuskarta sannan ta tashi tsaye tana gaishe da wanda ya shigo din. Na juya na ga Mustapha sai na dawo da ido na kan abinci na na cigaba da ci. Ya karaso ya zauna Esther ta fara hidimar zuba masa abinci, ya kalle ni na dago kai nace "goodmorning" yace "how are you?" Ban amsa ba na cigaba da cin abinci na amma ina jin idonsa still a kaina sai yace "ci ba kiba dai inji hausawa sun ce asarar abinci ne" dariya ta kusa ta kwace min sai na mayar da ita, hakan ya sa na kusa kwarewa, Esther ta bar shi ya dawo gurina ya zuba min ruwa ta miko min, na karba na sha nagode mata nacigaba da cin abincin still ba tare da nace masa komai ba.

Yana cigaba da kallo na yace “why are you laughing?” Na danyi kokarin bata rai nace “dariya kuma? Waye yake dariya” yabata rai “wai da” nakara kokarin danne dariya ta na cigaba da cin abinci na. Esther tagama zuba masa ta juya ta fita ta barmu mu kadai. Yafara cin abincin sa yana kallo na har lokacin sai kuma yace “akwai maganar da nake so muyi dama fiyya. I have been thinking of a way to get you alone Amma na rasa, kin san yanda kike yanzu, kin zama hukuma sai lallashi” na gyara zama na tare da daukan cup din coffee na ina karasa shanye abinda yake ciki, na daga gira nace “wacce maganar ce knan ?” Yayi ajiyar zuciya “maganar ai guda daya ce. It is about us. I don’t know why you are still shying away from the truth, chasing a dream that will mever come true” na ajiye cup din ina jin raina yana baci nace “haryanzu dai ban gane maganar ba. Kace about us. Wacce magana ce about us” yayi shiru yana noticing changing yanayin fuska ta yace “kin sani ai” na mike tsaye nace “akwai maganganu da yawa da na sani about us Mustapha, maganar sanda kake cin zalina a bayan mutane sanda muna yara idan na kai kara kuma Safina tayi karya ta kare ka? Ko maganar sanda kayi ta trying to sexually assault me in then threatened me cewa idan na fada sai kayi da gaske?" Ya mike tsaye, jikinsa gabakidaya yana rawa idonsa kamar zai fado kasa dan tsoro yana kalion hanyar shigowa gurin "shishsh, me kike cewa Safiyya? Me ya kaio wanna maganar kuma?" Nace "ban gama ba ai, akwai wata maganar kuma, maganar sanda bayan mun girma kake shiga dakina a dukkan opportunity da ka samu and begging me to let you do

it ko da sau daya ne" ya tako da sauri zuwa gabana yay kokarin rufe min baki da hannunsa, fuskarsa cike da toro, na matsa baya da sauri na kuma cigaba da magana, "you told me babu wanda zai sani, you told me ko na fada babu wanda zai yarda, I had to find a way to protect myself from you Mustapha, Saboda kai

komawa nay kamar yar daba, duk dakin da na zauna ina ajjye da wuka a gefe saboda kai, har yau akwai wuka a dakina saboda in kare kaina daga sharrin ka. You traumatized my childhood, and you traumatized my nights at my teenage Na kasa gaya wa Daddy saboda maganar tayi min nauyi, na kasa gayawa Mommy dan mahalfiyar ka ce kuma ba lallai ta yarda ba kamar yadda kace. But maybe this is the right time to tell them, Maybe in na fada musu a yanzu

zasu fahimci dalilin da yasa na zarge ka akan abinda ya same ni. Kuma zasu fahimci dalilin da yasa nace bana son auren ka" ya sake kokarin rufe min baki, na juya da sauri na dauki wuka a cikin set din kanana wukaren da suke jere a cikin shelf din da take bangon dining room din "the next time you touch me will be the

last time you have a hand".

Ya yi taku biyu baya yana kara lekawa cikin parlour sannan ya juyo yana kallona. '"na riga na baki hakuri ai Safiyya. Me kike so in yi miki ne kuma? Kuskure ne da rudin kuruciya da kuma sharrin shaidan kuma babu wanda yake above mistake. Kuma ai banyi ba ko? To me yasa ba zaki yafe ki manta maganar ba? What do you want from me?" Nace "kaje ka gaya wa Mommy da Daddy cewa ka janye maganar aure na. In baka fada ba ni kuma zan gaya musu dalilin da yasa ba zan aure

ka ba" ya fara jujuya kansa "Safiyya. Wannan maganar ai ba ta kai wadda za'a fasa aure saboda ita ba. I promise you ban taba yi ba, a kanki ma kuskure ne da rudin shaidan, I mean you are very beautiful and we live together and I was young and hot blooded. But that doesn’t mean….” Na katse shi “I don’t care about shaidan and all his sharri stuff. Kai kayi min laifi kuma kai nake hukunta wa by not marrying you. I may forgive you but I can't marry you. Make them understand that or I will”.

Yayi shiru muka cigaba da tsayuwa muna Kallon juna. A lokacin ne muka ji shigowar Mommy, tun kafin ta shigo parlour muryarta ta karade gidan da Fada, Ya juyo yana kallona da sauri yace "I will do it, just don't talk about this again" ya fita da sauri ya taffi gurin ta. Nima fitowa nayi daga dinning din na tsaya akan steps din da ake takawa daga parlour kafin a shiga dinning din ina kalion kofar shigowa pariaur.

Mommy ta shigo mayafin ta a hannu tana zazzaga fada "ban taba ganin mahaukaciya, marar zuciya a duniya irin wanna yarinyar ba. Da ace bata kama da

ni tsaf zance chanja min ita akayi a asibiti. Ta yaya za'a yi ni yadda nake da wanna zuciyar amma ace ita tata kare ya dauke?" Mustapiha da yake kokarin

daidaita yanayin fuskarsa yace "Mommy lafiya? Ke da waye haka?" Hassan daya biyo ta a baya da jakarta yace a hankali “ita da yaya Safina”.

lta kuma Mommy tace "ni da wa kuma in banda waccan shashashar kanwar ta ka? Wai yarinyar nan ance za'a sallame ta yau na tashi da sassafe na tafi dan mu taho gida tare amma budar bakin ta wai ita

gidan mijinta zata koma, Ko a ina mijin yake? Dan wancan fitsararren yaron dai ba miji bane ba. Kuma wallahi ni da ita ne" ran Mustapha ya baci "kuma Mommy kika barta ta tafi baki babballata a asibitin ba?" Mommy tace "bar ni da ita. Bar mishi aikin

nayi. Jira nake yi yayi gunduwa gunduwa da ita ya watso ta waje kuma na gaya mata wallahi ba zan koma asibiti zaman jinyar ta ba sai dai ta tafi Katsina wadanda suka aura mata shi suyi jinyar ta a can.

Haka kawai yara suna nema su haukata ni. Wannan yaron ya zamar min annoba a cikin gidan nan wallahi. Ya mayar min duk yaran sun zama mahaukata. Daga safinan har Safiyya da nake ganin kamar tana da hankali".

Jin ta ambaci sunana sai nayi saurin yin baya zan koma inda na fito. Ban san ta ganni ba sai ji nayi tace "ina zaki je? Dawo nan" na juyo na dawo cikin falon na

gaisheta "good morning mommy" tace "wanne morning din? Wacce Mommy din? Yaushe rabon da ki gaishe ni a gidan nan?” Nace "Mommy al ba kya nan ne shi….” Tace kin san bana nan ne? Na tabbatar baki sani ba kuma baki neme ni ba saboda ke yanzu kin zama yar kanki ko? Ba'a isa ayi miki fada ba sai ki dauki fushi da mutane. Ina daukan ki me hankali

ashe kema shashasha ce irin Safina. To wallahi bari kiji in gaya miki, abinda kike nema will never happen. Babu ta yadda za'a yi miciji ya sare ni a kafa daya kuma

in sake mika masa daya kafar. In zaki dawo hankalin ki ma ki dawo tun kafin lokaci ya kure miki. Shashasha". Sai na juya nayi hanyar stairs. Tace "ai ba ce miki nayi na gama ba" na juyo na dawo amma sai na zamu guri na zauna danna fahimci ba yanzu zata gama fadan ba. Ta kuwa cigaba yin abinta. Ni dai na zauna

kaina a kasa, ina yi ina kallon agogo ina lissafin lokacin meeting dina yayin da ita kuma ta cigaba da juye fadan ta a akaina.

Allah ya taimake ni sai ga Dr Ma'aruf ya shigo, shigowar sa ce ta saka tayi shiru ta amsa gaishe ta da yake yi sannan ya zauna ya miko min wata takarda yana yi min bayanin bills ne na dukkan expenses din da aka kashe a wanna karon da kuma kudin machines din da akayi order. Na dudduba tare da sauke ajiyar zuciya nace "same account da wanda na tuna muku last month?" Yace "eh" Na mike nace okay, zan hado maka da salaries dinku for this month, shikenan sai mu gama dasu. Yayi murmushi "that will be good. Thank you"

A haka na samu na zame na hau sama kamar zuwa zany in yi transfer din amma kawai sai na ajiye takardar nayi kwanciya ta na rufe idona. I knew I have achieved something with Mustapha amma kuma

maganar komawar Safina gidan Muhammad tana neman dagula lamari na. Ba wai na saka ran ba zata koma ba ne ba amma kawai da najinta koma din sai naji kishin ya motsa. Ni kaina ban san yadda

za'a yi wannan lamarin ba. Na dai san kawai cewa ina son Muhammad. Ban kuma saukowa ba sai da na gama dukkan meetings dina da na gabatar online. Ina gama wa na rubuta wata takarda na tura e-mail din Uncle Ahmad sannan nayi refreshing na saka riga da

skirt na atampa na daura dankwalin atampar sannan na saka mayafi na kuma feshe jikina da turaruka masu tsada na fito.

Dakin Daddy na fara shiga. A zaune na same shi Dr yana ta yi masa wasu bayanai shi kuma yana gyada kal alamar fahimta, Na zauna sai da suka gama sannan na karaso na gaishe shi, Ya amsa min, yanzu

muryar ta fito amma can kasa, Nayi murmushi, Dr yace "jiki alhamdulillah, Kar ki damu kinji?" Na gyada kaí tare da kara matsawa kusa da Daddy na rike hannunsa nace "Daddy zan fita, Zanje gidan uncle

Ahmad. Yanzu zan dawo insha Allah", A idonsa naga alamar yaji dadin magana ta, sai ya danyi mun murmushi kadan, Ina fita daga parlourn a na dauko shades a cikin jaka ta na saka a idona, Ina fita

harabar gidan naga guards dina sun tashi zasu tafi gurin motasu sai na kira su da hannu na, suka karasa and I said "I don't feel like driving today" da sauri daya ya koma ya kawo motarsu zuwa inda nake,

daya kuma ya bude min baya na shiga sai ya zagaya ya shiga gaba kusa da dan uwansa muka tafi, A hanya na gaya musu address din inda zamuje, gidan uncle Ahmad, Na dauko waya ta na a duba naga missed calls from Muhammad amma sai na share shi,

Haushin sa nake ji duk da bai yi min komai ba. Amma kuma sai nayi amfani da lokacin wajen saving number din sa da sunan da yake kai tun da "Pyar💕”na kuma bata lokaci wajen zaban hoton sa a cikin hotunan sa da nayi retrieving na saka akan number din sa, na kuma zabi ring tune mai dadi mai cike da kalaman

soyayya na saka masa, sai dai still da ya Kira ni ban dauka ba. A raina nace *kaje Matarka tana gida tana jiran ka*.

A kofar gidan uncle Ahmad muka tsaya muka yi horn aka bude gate muka shiga, amma sai na zauna a mota nace su tambaya suji ko mukhtar yana ciki, suka

dawo suka ce baya nan sai na fita sannan nace musu idan ya dawo kar su barshi ya shiga ciki har sai na gama na fito.

Ina shiga cilkin parlour da sallama naga Umma ta fito daga Kitchen. Sai kawai ta tsaya tana kallona. Na cire shades din idona na durkusa na gaishe ta. Ta amsa still fuskar ta da mamakin ganina sai nace "Umma ina su Salima, ina Uncle?" Sai ta kalli dakin Salima sannan ta juya ta kalli hanyar part din uncle Ahmad amma still

bata de komai ba. Sai na mike tsaye nace *Umma uncle din yana kusa? Zan iya ganin sa?" Ta dan gyara fuskarta tana kokarin cire mamaki daga cikin ta tace

"bara inyi masa magana. Salima tana cilki zaki iya shiga" nace "zan shiga, bara in ga uncle tikunna".

Sai ta juya ta shiga part din uncle Ahmad da sauri, Ina nan zaune sai ga Yaya ya shigo, nay kokarin gaishe shi sai naga yayi min kallon banza ya wuce yana cewa

*dama ke kika ajiye mana wannan bakar motar da wadannan bakaken mutanen a kofar gida kenan" ban ce masa komai ba sai ya shige dakin Salima. Yana shiga sai ga ta ta fito, ta tsaya a bakin kofa tana

kallona kamar yadda nima nake kallon ta. *Fiyya" ta fada a hankali. Na dan yi mata murmushi "hello Salima" ta karaso cikin falon tana murmushi itama. Kafin ta zauna uncle Ahmad ya fito tare da Umma. Na

mike tsaye cikin girmamawa sai da ya zauna sannan na zauna nima a kasa, Umma ta zauna a gefensa tana kallo na fuskarta da expression din self pity. Na

gaishe da uncle, ya amsa min idonsa a kasa sai nace "'Uncle dama zuwa nayi in tuna maka da cewa Daddy ba shi da lafiya. You should be with him. He misses

you. Na san kuma kaima kana missing dinsa" yayi shiru sai kuma yayi magana muryarsa tana rawa "me zance masa idan naje?" Nayi sauri nace masa "kace masa ya jiki? Sai kuma ku cigaba da maganganun ku yadda kuka saba" duk muka yi shiru sai na sake cewa "tun kafin ku san zaku same mu kuke tare, you shouldn't be apart because of us" Umma tace "haka ne. Nima na gaya masa, Kin gan shi nan kullum yana kwance a daki cikin damuwa. Amma insha Allah zai je in an jima* nayi murmushi nace "ke ma ya kamata kije Umma, Kera ai kanwar Daddy ce. Ya kamata kema ki je ki ga jikin sa zaiji dadi.

Ban jima sosai ba saboda babu abin magana sosai., Sun kasa sakin jiki suyi min magana sai na mike nace zan tafi, amma sal na kalli Salima nace "ki zo mu tafi tare Salima. In sun je in an jima sai ku taho tare" ta juya ta kalli Umma sannan sai ta koma dal da sauri ta dauko mayafin ta ta fito. Sai da zan fita nace da uncle Ahmad "uncle na tura maka sako email dinka. I will appreciate a response as soon as possible. The management misses you.

Tare muka koma gida da Salima. Muna ta hira sama sama sai dai daga dukkan alama ita ma tsintar kalimomi take yi wajen yi min magana, Mostly akan lafiyar Daddy take min tambaya ina amsa mata. Tayi magana akan wayata da take ta hasken kiran da Muhammad yake ta jera min. ana ta kiran ki fa* na kalli wayar "share shi kawai" "shi?" Tace tana murmushi, nayi murmushi kawai bance komai ba sai ta dau wayar tawa da wani kiran ya shigo ta amsa ta saka a kunnen ta, na dago kai tare da bude ido ina kallon ta cikin mamaki. Sai naga tayi dariya tana rufe bakin ta da hannun ta sannan tace ba ita bace ba. Kanwar ta ce" eh muna hanya ne, naga kamar kayi laifi ne kana ta

Kira ank dauka shine na taimaka maka na dauka* *okay to gamu nan karasowa" ta fada dai dai lokacin da muka sha kwanar shiga layin mu. A take na hango motar Muhammad a tsallaken gidan mu. Na juya

ido na sannan na dauko shades dina na mayar dasu ido na nace da driver din ya tsaya a waje, muna tsayawa Muhammad ya bude motarsa ya fito ya tsaya a gaban ta tare da saka hannayensa a cikin aljihun

sa. Na cigaba da zama a motar ina kallon sa, yayi kyau sosai cikin dinkin shadda ruwan toka mai duhu, rigar mai kananan hannaye ce wadda ta fito da damatsen hannunsa da naga sun kara girma fiye da

yadda na san su, Fatarsa tana kyalli, iska tana kada yalwataccen gyararren gashin kansa. Salima ta taba ni sannan tace min a hankali "he is hot" nayi murmushi

sannan na bude kofa na fita, a tare security din suka fito sai nace musu su wuce ciki kawai,

I purposely cat walked toward him. Irin tafiyar da na tabbatar ta karasa susuta sauran tunaninsa. Sai dai yadda ya zuba min ido ya saka naji ina kamar zan fadi

amma na samu da kyar na karasa inda yake. Ya danyi gyaran murya yace "you look stunningly beautiful. You took my breath away", Sai na daga gira na dauke

kai gefe daya. Ya zagaya side din da na juya fuska ta tare da hade hannayensa a guri daya yace "ban san laifin da nayi ba. Whatever it is. Na dauki laifin 100 percent and I am sorry" na murguda masa baki sannan na sake dauke kaina "ni gida zan shiga yanzu" yace "not


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login