Showing 237001 words to 240000 words out of 375662 words
Chapter 80 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx
da motar yace
"welcome back to Nija" gidado yayi ajiyar
zuciya yace "home sweet home" sai dai
kuma a ransa bashi da tabbas din how
sweet the home will really be for him.
Al'ameen ya dan kalle shi yace "you look
good, you look really good, har wata kiba
naga kayi fa, and with that skin dole ka
nuna baka san rana ba" gidado ya dan
daga hannunsa yana kallon skin din
sannan ya tabe baki yace "change of
weather, just take me home kaji? Ka kaini
inga rabin rai na ko na san na dawo
Nigeria" Al'ameen yace cikin tsokana
"kaga angon Safina wanna doki haka?
ana ta missing amarya ko? Tunda ka bata
rabin ran ka mu babu komai zamu raba
the other half din" Gidado ya jefa masa
wata harara yace "Safina kuma? a'a ba
Safina ba Sa'adatu" Alameen yace
"wacece kuma saadatu? Kar dai kace min
new catch kayi" Muhammad yayi dariya sosai sannan yace "uwar safina nake nufi, sunanta Sa'adatu" Al'ameen yayi dariya shima yace "wallahi baka da kirki
Muhammad, warta fa kace, yanzu sunan
sirikar taka kake ambata kanka tsaye?"
Muhammad ya daga kafada yace "kai ka
jawo mata, why will you say she is my
rabin rai?" Alameen yace "then who is
your rabin rai? Am sure you are not
talking about that married girl k0? Ko har
yanzu bamu wuce gurin ba?" Muhammad
yace "I was talking about Mama. Mama is
my rabin rai please. And don't mention
that girl's name. let the sleeping dog lay"
Muhammad Alameen bai ja maganar ba
kamar yadda gidado ya bukata, sai suka
koma hirar humaira da sauran family
members, daga nan kuma suka yi maganar various businesses din su da yadda suke adjusting to their
responsibilities.
Ana bude musu gate mama ta bude kofa
ta tsaya tana kallon su har suka yi packing
suka fito a tare, Gidado yana fadada
murmushin sa yace "Mamana" sannan ya
karasa inda take da sauri ya rungume ta,
gabaki dayanta iya kirjinsa ta tsaya.
Alameen ya karaso sai ta saki Muhammad
tana amsa masa gaisuwar sa tare da
tambayar sa lafiyar Humairah, bai amsa
ba ya sunkuyar da kai yana shafa keya
cikin nuna jin kunya, mama tace "Allah dai
ya sauke ta lafiya, Allah ya sauke su lafiya baki daya" Alameen ya amsa a hankali sannan yayi musu sallama yace zai koma office, Mama tayi kokarin ya shigo yayi
lunch amma yaki yace sauri yake yi.
Suna shiga ciki Muhammad ya zauna
akan kujera cikin nuna gajiya tare da fara
unbuttoning shirt din jikinsa, "akwai zafi
mama" mama ta karo karfin ac sannan ta
zo ta zauna tana kallonsa fuskarta cike da
farin cikin yanayin da ta ganshi a ciki "you
look good Muhammad. I was worried ko
baka samun abinci kana ci sosai" yayi
murmushi "ba sosai nake cin abincin ba
fa, ina ta missing abincinki, kawai dai ina
samun bacci ne sosai and the weather
there is good. Shine kawai. Ina abba?"
tace "yana office shi da Haidar" ta kalli
agogo "but they will soon be on their way".
Yaran gidan suka fara hidimar ajiye masa
kayan ciye ciyen da mama ta tanadar
masa. Ya zuba drink a cup yana tasting
sanyin sa sai yace da daya daga cikin
yaran "get me ice, saurj" mama tace "kai
dai kana son sanyi, ka sha ruwan sanyi ka
sha kankara kayi wanka da ruwan sany"
ya danyi murmushi bai ce komai ba. He
sometimes feels as if his blood is too hot
shi yasa yake cooling din sa down. Abu
mai sanyi yana calming dinsa kuma baya
saka shi ciwo.
Aka ajiye bowl of ice din a gabansa tare
da diba aka zuba a cikin drink din da
already ya riga ya zuba a cikin cup, ya
dago kansa suka hada ido da mai zuba
masa ice din. Ta sha kwalliya kamar ranar
ne zaa kai ta gidan miji. Jikinta sanye da
doguwar riga ta shadda da ta sha aikin
stones sai kyalli take yi, fuskarta with all
the make up possible, daga dukkan alamu
ma gidan kyalliya taje musamman aka yi
mata kwalliyar aka kuma daura mata
dankwalin kanta, hannayenta sun sha
both bakin lalle da ja. Fuskarta dauke da
murmushi.
Ta miko masa kofin tare da cewa "sannu
da zuwa" ya karba, amma maimakon ya
sha sai ya ajiye akan table din gabansa
tare da cewa "yauwa, sannunki". Ya juya
gurin Mama "Mama bara inje inyi sallah
tukunna" tace "gaskiya kam, kar ka ci
abinci jikin ka yayi nauyi ka kasa tashi.
Jiya na saka aka gyara maka dakin ka
dama. Yana bude" ya wuce da sauri zuwa
dakin nasa.
A can ya shiga toilet ya watsa ruwa ya
chanja kaya zuwa jallabiyya da wando
sannan yayi sallah azahar da laasar din da
yaji already an fara yi. Sai kuma ya dawo
falo, mama bata nan sai safina a zaune ta
dasa wa hanyar da zai fito ido, yayin mata kallo daya ya dauke kai yana jin gabansa yana faduwa, ta chanja, she looked a bit like abinda baya son ya ambata ko da
kuwa a zuciyarsa ne, she cannot be. It is not possible. Amma shi ya san cewa it is very possible kawai yana so yay denying ne to protect his heart. Ya dauki wani cup din, ignoring wancan da safina ta taba, ya sake zuba ice sannan ya zuba drink a kai ya zauna yana
jujjuyawa a hannunsa har sai da yayi masa
sanyin da yake so sannan ya daga ya
shanye ya kuma hada wani ya ajiye. Ta
sauko daga kan kujerar da take kai zuwa
gabansa tace "me za'a zuba maka?
Akwai.... " Ya katse ta "I know menene
akwai, so just shut your hole please. And
please get out of my site ina son zama da
family na" ta gyara zaman ta a gabansa
tace "I am your family" ta shafa marar ta a
hankali tace "we are your family" ya mike
tsaye yana jin kamar yayi ball da kayan da
suke gabansa. "goddammit" ya fada a
hankali, almost inaudible dan yasan ko da
wasa mama taji yana yin zagi sai ransa ya
baci.
A lokacin abba ya shigo, haidar yana
binsa a baya da briefcase a hannunsa,
duk su biyun suka saki murmushin ganin Muhammad, ya juya gurinsu shima yana
kirkirar murmushi duk kuwa da yadda
hankalinsa gabaki daya yake a tashe. Ya
je ya rungume abba sannan kuma ya
russuna ya gaishe shi, ya rungume haidar
shima, haidar yana kare masa kallo yace
"amma bread kake ci a can ko? Naga
kamar wanda aka saka maka yeast?
Mama da ta fito daga sashen ta da charbi
a hannunta jikinta sanye da hijab, daga
alama sallah tayi tace "tubarkallah". Abba
yayi dariya shima yana jin dadin ganin dan
nasa yace "zai zazzage ne ai, akwai aiki
da nake ta tara masa yana nan yana jiran
sa"
Safina da take zaune a gefe ta gaishe da
abba ya amsa mata tare da tambayar ta
jikin ta, bata ce komai ba ta sunkuyar da
kai tana murmushi, Haidar ya fara
tsokanar ta "yau da ya dawo, tagumi ya
kare. Nace wannan ciwon nata har da
rashin yaya" ta dan harare shi cikin wasa
amma bata ce komai ba sai mama tace
"kinyi sallah kuwa safina? Dan miji ya
dawo kuma sai ki zauna ki saka shi a gaba
kina kallo ba zaki je kiyi sallah ba?" safina
ta mike da sauri ta shiga wani daki da
yake cikin falon.
Suna zama sai ga mufida ta shigo gidan
da gudunta, tazo ta rungume Muhammad tana dariya, ya daga ta daga jikinsa hana murmushi, yana kin dadi a zuciyarsa "yar autar Mama, ke da nace miki zan zo har gida ina same ki?" Ta bata rai "da zaka
tafi ma cewa kayi zaka je muyi sallama
kuma ba ka je ba. Shi yasa naki jiran ka
yanzu" yace "ayi hakuri, nayi niyyar zuwa
wallahi sai abubuwa suka duke min
hankali, sai da na shiga jirgi na tuna" tace
"zanyi hakurin but I need one more
squeeze" ta fada tana kara rungume shi.
Bayan Mufida ta gaishe da kowa sai suka
hadu gabaki daya suka tafi dining suka
fara zuba abinci, tun kafin su fara ci sai ga
Safina ta dawo, fuskarta tana nan da
kwalliyar ta, tana shiga gurin Mufida tace
"hey in law! I was about to ask about you
sai na manta" Safina tace "nayi fushi ai.
Tunda kinga yayanki ai dole ki manta da
ni'" Mama ta juyo tana kallon Safina tace
"Safina wannan fuskar kuwa kin wanke
ta? Ta yaya kika yi alwala da wannan
kwalliyar?" Safina ta dan yi murmushi
nervously "Mama nayi, ai ba zata fita ba
dama" Mama ta girgiza kai "ai kuwa dai in
bata fita ba alwala ba tayi ba. Ki koma ki
wanke ta tas ki sake alwala ki sake Sallah.
Ai ya ga kwalliyar taki" Safina ta dan bata
rai "Mama nayi alwala kafin inje kwalliyar
fa" Mama tace "tun safe kenan? Alwala
tun safe har la'asar ai ya kamata a hakura da ita ko?" Safina ta juya ta koma ciki,
Mama ta gyara zaman ta tana cigaba da
zuba wa Abba abinci. Haidar yayi dariya,
Mufida tace "Mama kin ba da Safina a
gaban Haidar, a gaban kuma mijinta"
Mama tace"ga Abban ku nan a zaune
shima ai. Dole mu gyara mata mata
tarbiyyar ta ai, ko mijin nata ne yayi ba dai
dai ba dole a gyara masa ballantana ita,
she will soon become a mother, idan babu
tarbiyya ai mun shiga uku baki daya".
Muhammad ya kware da abincin da yake
ci. Abba ya zuba masa ruwa ya mika
masa, ya karba ya sha amma still yaji
abincin ya tsaya masa a makogwaronsa
ya ki wucewa, wani zafi yaji jikinsa ya
dauka. Ya fara panning fuskarsa da
hannayensa sai ya lura kowa na gurin shi
yake kallo. Abba yace "lafiyar ka kuwa?"
Muhammad ya sake daukan cokalin ya
debi abincin yace "lafiya lau.
I am not feeling good ne kawaj" Mama
tace "kace lafiya lau kuma kace you are
not feeling good, Wanne ne kenan? Kar fa
mu je ko heat stroke zaka samu dan tun
dazu kake complain din zafi" Haidar ya
mike tare da kara karfin ac sannan shima
ya tambaye shi "are you okay Yaya?" Muhammad ya kirkiri murmushi tare da gyada kai, yana jin babu dadin yadda duk suka shiga damuwa lokaci daya saboda
shi.
"It is okay. I am okay yanzu" ya fada yana
sake kai lomar abinci bakinsa duk da
waccan lomar har lokacin bata wuce ba. A
zuciyarsa ya san abinda duk wadannan
maganganun suke nufi amma ya kasa
barin kwakwalwarsa ta yarda. Mama tace
"'in ka cigaba da jin zafin dai kayi magana
aje asibiti, tun kafin abun ya zama babba"
ya gyada kai kawai tare da kokarin cigaba
da cin abincin da yake gabansa.
Sunanan zaune Safina ta sake dawowa, ta
wanke fuskar tas yanzu, daurin dankwalin
ma daga dukkan alama an kwance shi an
sake, Mama tace "yauwa, ko ke fa, yanzu
har kinfi kyau ma" ta danyi murmushi tana
sunkuyar da kanta kasa, Mama ta nuna
mata kujerar kusa da Mufida daga right
dinta tace "zauna to ke ma kici abinci, tun
safe banga kinci komai ba kina ta
kwalliya" sai ta zagaya ta zauna a left din
Mufida, kujerar da take kusa da
Muhammad. Ta zuba abinci ta fara ci,
yana jin idanunta a kansa amma bai ko
kalli inda take ba, he tried as much as he
can to not ruin the moment for his family.
Suka yi ta hirar su suna bashi labarin gida
yana basu labarin can. Bayan sun gama
kuma sai suka sake dawowa falo ya zauna
yana ta yiwa Abba bayanin tarukan da
yayi attending da matsayar da aka samu a
tarukan and what they mean to their business.
Suna nan tare har magrib, suka je suka yi
sallar suka sake dawowa suka cigaba da
hirar su, zuwa lokacin Muhammad ya dan
ware, trying not to look at side din da
Safina take zaune duk kuwa da cewa yana
jin yadda ta zuba masa ido a jikin sa.
Daga baya sai ga mijin Mufida yazo
daukan ta, shima ya shigo yayi joining
hirar ta su, sai kuma suka yi dinner tare
sannan Abba yace kowa ya zo ya tafi
gidan sa. Mufida ta fara tsokanar Safina
"Safina ki kara wa Mama ko sati biyu ne
mana" Mama tace "ina fa, ta tafi gidan
mijinta ya cigaba da jinyar a can. Tun dazu
dama na saka an kai yan aikinta gidan dan
su gyara musu kafin su tafi"
Babu kunya sai ga Safina ta jawo akwatin
kaya ta fita da su waje, tana ganin
Muhammad ya tashi kuwa tayi wa Mama
sallama, dama Abba ya riga ya shiga ciki,
ya fita ta riga Muhammad din shiga motar
ta zauna, maybe tana tsoron kar yayi
mata irin na ranar nan. Ya tsaya yana kallon ta kawai a ransa yana tunanin da ace daya motar tana nan da ita zai je ya shiga yayi tafiyar sa ya barta anan ya ga
yadda zata yi. Amma kuma Mama tana
tsaye a bakin kofa tana kallon su, yayi
sallama da su Mufida ya zo ya shiga
motar yana bata wuta Mama ta leko tace
"ka tafi a hankali fa, ban da gudu, kai a
guje dama kake driving dinka sai kace dan
tsere" yayi murmushi "to Mama, ba zanyi
gudu ba" tace "Allah ya sa" ya ja motar a
hankali suka fita daga gidan, amma ana
rute gate ya fige ta a guje saura kadan
Safina ta hantsula, tayi sauri ta gyara
zamanta tare da saka seat belt.
Suka fara tafiya da farko in silent, Allah
Allah yake yi suje gida ba tare da tayi
magana ba ballantana tayi confirming
abinda yake suspecting. Har ya fara
murnar ba zata yi ba sai kuma tayi din "ya
hanya?" Yayi kamar bai ji ta ba ya kara
gudun motar sa, sai kuma tace "you run
away, gashi kuma ka dawo" ya dan daga
kafarsa ya juyo yana kallon ta yace
"excuse me? Me kika ce?" Ta maimaita
"cewa nayi ka gudu, gashi kuma ka dawo"
yace "ban gane na gudu ba? Gudun me
zanyi? Run away from what?" Tace "you
run away from me" yace "and why will I
do that?" Tace "because you found out
that you cannot resist me. Shi yasa ka gudu"
Sai da ya danyi karamar dariya "you are
delusional. You and I know that that thing
that you think happened…….." Ta katse shi
"that I think happened? Kana nufin bai
faru kenan ba. Kana nufin I imagined it?
Okay wanne bangaren nay imagining the
first round or the second" yaji kamar yaje
ya jefa su a rami gabakidaya su mutu
kowa ya huta. Yana girgiza kansa cikin dacin rai yace "I wanted to not talk about it now, amma
tunda kin kawo topic din let me spell it out
for you. Na farko I did not run away from
you or from anything, na riga nayi
planning tafiya ta before that thing you
think is something happened. So idan
kina tunanin it means something to me ki
daina, it means nothing, you mean
nothing and will never be anything to me.
Abu na biyu kuma mafi muhimmanci
shine ni da ke gabakidaya mun san cewa
what happened that day wasn't natural,
you did something to me, I don't know
what amma ke kin sani kuma you are
going to tell me one way or another. Me
kika yi min?" Ya fada almost shouting.
Tayi kokarin matsawa daga kusa da shi
yadda ransa ya baci gani take kamar zai
kai mata duka.
"'Ba zaki fada ba?" Ya sake yi mata tsawa.
Ta rufe fuskarta da hannayenta da suka
sha lalle tace "ni banyi maka komai ba. Ni
babu abinda nayi maka". Yayi horn a bakin
gate mai gadi ya bude masa kofa ya shiga
da motar yaje yayi packing ya juyo yana
kallon ta "Ke munafuka ce Safina. Baki da
gaskiya ko kadan. Kin aikata abinda kika
aikata and you have the guts to spill out
trash from that hole in your face kina gaya
min maganar banza? You did something
to me ke ma kin sani, you thought idan
naje gadon ki I will fall in love with you ko?
Haka kike tunani? To abinda baki sani ba
shine what you did made me hate you the
more, made me despise you the more,
your gutter behavior and your trash of a
body disgust me. I am going to find out
what you did and I am going to use it as a
pass to my freedom from you". Ya bude
motar ya fita sannan ya buga kofar motar
da karfi.
Part din sa ya wuce, sai daya bude ya
shiga sannan ya tuna bai fito da kayansa
daga mota ba, ya juya ya fita ya tarar har
lokacin tana zaune a mota tana kuka. Ya
fito da kayansa ya ajiye ya bar mata nata a
ciki. Mai gadi yazo da sauri ya gaishe shi
ya dauki kayan ya wuce ciki. Sai a lokacin ta fito daga motar, ta tsaya tana kallon sa suna magana da mai gadin, yan aikin ta biyu da cousin dinta da suke gidan suka fito ta bude booth ta basu kayan ta suka
shiga da shi cikin gida.
Sai da ya gama yiwa mai gadi magana ya
juya zai tafi sannan ta kira sunansa
"Muhammad" ya dakata amma bai juyo
ba. Ta karasa bayan sa ta tsaya sannan
tace "I am pregnant" still bai motsa ba
ballantana ya juyo ya kalle ta. Ta cigaba "I
wanted to tell you tun kana can, amma ba
ka daukan waya ta ba ka duba messages
dina. At least idan banci albarkacin
soyayyar da nake yi maka ba ai ya kamata
yanzu in ci albarkacin abinda yake ciki na"
Ya yi gaba, pretending kamar bai ji abinda
ta fada ba amma ransa tafasa