Showing 129001 words to 132000 words out of 375662 words
Chapter 44 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx
kira Safiya.
Safiya ta shigo kanta a kasa tana kallon
yadda kafafuwanta suke nutsewa a cikin
carpet din falon da ta kasa tantance da me
aka yi shi. Kamar da katifa kamar kuma da
gashin rago.
Ta durkusa daga nesa da su ta gaishe da
Hajiya, Hajiya tace mata "ya sunan ki?" Tace
"Safiya" Hajiya ta kalli ciwon da yake kafar
Safiya tace "ya akayi kika ji ciwo haka
Safiya?" Safiya ta dago kanta tana kallon ta
tace "kusa na taka guda biyu, lokacin da
nake kokarin tono yaruwata da katangar
dakin mu ta fada mata".
Duk hajiyoyin biyu suka bude baki, thinking
about the trauma, dan itama Hajiya Kyauta
bata san yadda mutuwar Sauda ta kasance
ba, Hajiya Maryama tace "ina yar'uwar taki
take to yanzu? An fito da ita?" Safiya tace
"ta mutu. An fito da gawarta daga karkashin kasa, sal aka sake mayar da ita aka binne a
kasan wata kasar a makabarta" suka sake
yin shiru baki daya, sai kuma Hajiya ta sake
tambaya "mamanki fa? Me ya faru da ita?"
Safiya tace "Baba Hadiza, Mota ce ta kade
ta, sanda take gudu zata cecemu ni da
Sauda daga hannun Dauda" suka sake yin
shiru, safiya ta kara cewa "Dauda din yayan
mu ne" ba tare da sun tambaye ta ba,
Sai Hajiya Maryama taji tana son jin cikakken
labarin Safiya, ta tambaye ta, ita kuma ta
bata labari tiryan tiryan a yadda rayuwar ta
ta kasance tun daga kan abinda ta sani na
labarin auren iyayen ta har zuwa rasuwar
Alhaji Haladu da kuma tragedies din da suka
biyo baya.
16
1:15 AM
Bata san tana kuka a labarin nata ba sai da
ta gama taga audience din nata suna share
hawaye sannan ta share nata ita ma. Ta
cigaba da magana "so nake in samu hanyar
da san zamu jari in fara sana'"a, shine naje
grin Hajiya Kyauta ita kuma tace min zata
kawo ni nan in yi aikatau sai in tara kudin da
zan yi jari dasu, Hajiya dan Allah ki dauke ni
aiki, zanyi miki aiki sosai kuma zan ringa
girmama mutane yadda ba zaki kore ni ba, in
na tara kudi sai in gina wa Baba Hadiza
masallaci in roki Allah ya gina mata gida a
aljanna da ladan masallacin". Hajiya ta sauko daga kan kujerar da take ta
durkusa a gaban Safiya tace "zan dauke ki
aiki kinji? Kuma ba zan kore ki ba ko da kinyi
laifi, in kinyi laifi zanyi miki fada in baki
tarbiyya kamar yadda uwa ya kamata ta
bawa yar ta tarbiyya. Kin zama yata daga
yau kinji? Ina fatan nima Allah zai gina min
katon gida a aljanna da ladan rikon da zanvi
miki"
Hajiya Kyauta ta share nata hawayen tace
"Amen Hajiya. Dama nasan zaki karbe ta.
Banyi tunanin kowa ba sai ke. Allah ya dubi
niyyar ki ya baki ikon sauke wannan babban
nauyin da kika dauka" Hajiya tace "Ameen.
Ke ma Allah ya baki ladan taimakon da kika
yi mata da zuciya daya. Da baki dauko ta ba
da yadda zuciyar ta ta bushe din nan
gudawar zata yi ko da kuwa an daura mata
auren ne, kuma kinga da ba'a san hannun
wanda zata fada ba".
Ta juya gurin Safiya tace "zan dauke ki aiki,
zan ke baki albashi kamar yadda bake bawa
sauran yan aikin gidan nan, zanyi hakan ne
saboda ki samu ki cika burin ki na gina wa
mahaifiyarki masallaci da gumin ki, amma ba
zan rike ki a matsayin yar aiki ba, zan rike ki
a matsayin yata, Kuma ina so ki saki jikin ki,
duk wata magana da kika san zaki iyayi da
Baba Hadiza ki zo kivi da ni, in wata shawara
kike nema ki zo gurina, duk wani abinda ya
shige miki duhu ki tambaye ni, duk wani abu da kike bukata ki tambaye ni. Kinji?" Safiya
ta gyada kai tana share hawayen ta, rabon
da ayi mata magana with motherly concern
irin haka tun Baba Hadiza tana da rai, hakan
yasa ta tuna irin yadda take missing
mahaifiyar tata.
Daga nan sai Hajiya ta dauki wayarta ta yi
kira, "Sa'adatu zo ina neman ki". Jimawa
kadan sai ga daya daga cikin yaran da aka
kora dazu ta fito daga ciki ta zauna a kusa
da Hajiya tace "Hajiya ganj" Hajiya tace
"ga
yar'uwa kun samu ke da A'isha, ta zama
kanwar u daga yau" Sa'adatu ta kalli Safiya
ta a yatsina fuska tace
"Hajiya yar'uwar mu
kuma? Ji nake sabuwar yar aikin da aka
kawo miki ce?" Hajiya tace "shi dan aiki ba
mutum bane ba kenan? Ba zai zama dan
uwa ba? So nake kuje ku samar mata kayan
sawan da suka yi muku kadan a cikin kayan
ku, da duk sauran kayan da kuka san zata
bukata kafin in fita in siyo mata. A dakin ku
zata zauna tare da ku saboda ina son ku
kula min da ita, duk abinda tayi ba dai-dai
ba ku gyara mata har ta gane ta saba da irin
rayuwar nan. Kin gane?"
Sa'adatu ta ce "eh" amma daga ganin
fuskarta kasan bata ji dadin maganar ba,
Hajiya ta kara sa da cewa "saura kuma kije
kiyi tayi mata wannan fadan naki da baya
karewa". Ta juya kan Safiya tace "wannan kanwata ce
uban mu daya sunan ta Sa'adatu, daga
yanzu ta zama yayarki. Zata ke kula dake
kamar yadda yaya zata kula da kanwarta. Sai
dai tana da fada" ta karashe maganar cikin
tsokanar Sa'adatu da har lokacin take zaune
fuskar ta a bace. Hajiya tace "ku je ki nuna
mata dakin ku.
Ta juya gurin Hajiya Kyauta tace "to sai
kuma a bani yar aikin"
Sa'adatu ta mike Safiya ta bi bayanta
hannunta rike da ledar da hotan su yake ciki,
wannan ledar ita kadai ce abinda Safiya ta
shiga da shi gidan Hajiya.
Wani dan corridor suka bi sannan suka yi
kwana, sai suka tarar da kofofin dakuna
guda biyu da kuma toilet a tsakiya. Sa'adatu
ta bude kofa daya ta shiga sai Safiya ta bita
amma sai ta tsaya a bakin kofa kanta a kasa.
Babu abinda bata so a rayuwar ta irin a
wulakanta ta, ta kuma lura kamar yammatan
suna da wulakanci. Kallon dai suke cigaba
da yi a dakin a tvn dakin. Daya yarinyar tana
zaune a kan gado, Lawisa tana zaune a
kasa,
6
3
1:15 AM
Sa'adatu ta zauna akan kujerar dakin tace
"Fati ga bakuwa nan inji Hajiya, tace zata
zauna anan a wajen mu. Kuma zata zama kanwar mu" wadda aka kira da Fati ta kalli
Safiya sannan tace "yar'uwar ku ce?"
Sa'adatu tace "ni dai ban san ta ba, ban san
a ina ta samo ta ba, tace kuma mu bata
kayan sawa da abubuwan bukata" Lawisa da
take zaune a kasa tace "yar aiki ce fa, na
ganta tare da wannan matar da tazo"
Sa'adatu tace "ina ruwan ki? Bana hanaki
muna magana kina saka mana baki ba?
Tashi ki fita?"
Lawisa ta taso saura kadan ta bangaje
Safiya sai ta bata guri ta wuce. Tana nan dai
a tsaye Sa'adatu ta bude wardrobe din dakin
ta fara debo kaya tana ajiyewa akan dago,
sai data bata kaya sunfi set goma, har da
mayafai da hijabs, sannan ta bude drawer ta
bata sabulun wanka, tooth brush da paste,
da kuma man shafawa da roll on da turare.
Ta tsaya tana kallon ta sai ta kalli Fati tace
"kuma fa kyakkyawa ce. Gyara kawai take
bukata" Fati ta kalle ta ta tabe baki tace
"fatan dai ba nan dakin zaki ajiye ta ba. Sai
dai ki kata can dayan dakin" Sa'adatu bata
ce komai ba ta saka hannu ta kwashi kayan
tace "debo sauran mu tafi" Safiya ta debi
sauran kayan suka fita suka shiga dayan
dakin. Ta lura kamar dakin ba'a amfani da
shi kamar wancan, amma kuma shima
exactly kamar wancan din yake, Sa'adatu ta
ajiye kayan akan dago tace "ga kaya nan na
baki, ki zuba a cikin wardrobe din nan ki ki zuba a cikin wardrobe din nan ki
ringa sakawa, ga kuma kayan gyaran jiki
suma na baki, kin iya amfani da su?" Safiya
bata ce komai ba sai Sa'adatu ta nuna mata
yadda zata yi amfani da komai, sannan ta
nuna mata yadda zata kunna kayan
electronics din dakin, sai kuma suka fita ta
nuna mata yadda zata yi amfani da toilet,
daga nan ta mayar da ita falo.
Sanda ta koma falo already Hajiya sun gama
maganganun du da Hajiya Kyauta, Safiya ta
fahimci Hajiya ta dauki Jamila aiki itama a
gidan, amma instead of cikin gida da aka
shiga da ita sai aka hada Jamila da Dije,
matar da suka gani a waje, ta tafi da ita
bangaren yan aiki mata.
Hajjya ta tambayi Safiya in ta samu duk
abinda take bukata, Safiya tace "ta bani
kaya masu yawa, Nagode sosai Allah ya kara
arziki" Hajiya tace "Ameen. Tana da kirki ai
da kyauta, sai fada fal cikinta" Sa'adatu ta
tura baki tana kunkuni.
Daga nan suka yi sallama da Kyauta da
sauran yaran, Kyauta tayi mata alkawarin
duk sanda ta shigo Abuja zata je zuwa tana
ganin ta, Ta tsaya tana kallon su har suka
fita daga gate sannan ta juya ta koma ciki, A
lokacin Safiya tana da shekaru goma sha
hudu a duniya, dai dai da shekarun Baba
Hadiza sanda aka aura mata Alhaji Haladu. A hankali Safiya ta fara adjusting to rayuwar
gidan duk da dai ba xata ce babu challenges
ba amma tana jin dadin changes din sosai.
Ita kadai take kwana a dakin da Sa'adatu ta
kai ta, and all the nights she misses her
mother and siblings, wishing suma rayuwa
ta basu irin wanna damar ta kwanciya a irin
wannan gadon da kwana cikin ac a
lafiyayyen dakin da baya zuba ballantana ya
fada a kansu. Kullum ita take fara tashi a
gidan, kafin kuma mutan gidan su tashi ta
gyara duk inda take da access to, tun daga
dakin da take kwana har falo har kitchen da
duk wani daki da ya ke bude ko da kuwa
babu kowa a ciki. So take ta nuna wa Hajiya
irin gwanintar ta dan Hajiyar ta san bata yi
kuskuren daukan ta aiki ba. Satin ta daya a
gidan Hajiya ta dinka musu sababbin kaya
ita da Jamila, sai dai na Safiya yafi na Jamila
yawa.
Ta lura su Sa'adatu suna zuwa makaranta,
kullum da safe zasu tashi su shirya, Dije zata
hada musu breakfast su ci tare da wasu
samari biyu suma data fahimci rikon su ake
yi a gidan, in sun gama driver zai kai su
school, ita kuma zata je ta gyara musu dakin
da suka kwana a ciki sannan ta wanke toilet
din da suka yi amfani da shi,
Farko ta samu challenges kafin ta iya aikin gidan, sai da Dije ta zauna tayi mata bayanin
yadda ake yin amfani da komai sannan ta
iya, a hankali kuma har ta kware. Ta fahimci
cewa Fati yar kanwar mai gidan ce, ita kuma
Sa'adatu kanwar matar gidan.
9
4
1:15 AM
Ta kuma fahimci cewa daga mai gidan har
matar gidan yan kasuwa ne kwararru dan
har sunayin muamala sosai da kamfanonin
kasashen waje.
And she wished that one day she will be like
them....
Jinin su yafi haduwa da Sa'adatu akan Fati,
saboda Sa'adatu tafi fada amma tafi son
mutane, Fati tana da rainuwa musamman da
ta kara fahimtar cewa da gaske Safiya ba
yar uwar Hajiya bace ba.
A gurin Hajiya ma kuma tana samun kulawa
ta musamman dan ko da yaushe in dai suka
hadu sai ta tambaye ta "kin ci abinci? Akwai
abinda kike so? Ki ringa yin bacci sosai kina
hutawa ko kya samu ki dan yi kiba, ga
Sa'adatu nan sai hawa take kamar fulawar
da aka saka wa yeast". In Sa'adatu taji haka
sai ta kara kumbura,
Ranar nan tana dakin da su Sa'adatu suke
tana yi mata tsifa, sun kulla kallo a tv suna yi
ga wayoyi ana ta chatting da kawaye ana ga wayoyi ana ta chatting da kawaye ana
shirya irin hidimar da za'a yi a birthday din
wata kawar su da yake zuwa soon. Hajiya ta
shigo ta tsaya a bakin kofa tana kallon su
tana kuma jin irin hirar da suke yi ba tare da
sun ga shigowar ta ba. Sai da suka gama
sann6ta karasa shigowa ta kuma kama fada.
"Kun ganku yaran nan sai kunyi wa kanku
fada fa. Rayuwa ba zata tafi muku yadda
kuke so a haka ba. Ku baku da tunanin
komai sai na jin dadin duniya? Ya kamata
ace zuwa yanzu kun fara tunanin yadda
zaku ke juya biyar tana komawa goma.
Rayuwa bata da tabbas. Kamata yayi ace
kun fara tunanin wata sana'ar hannu ko wani
kasuwanci da zaku iya fara wa tun kafin ku
gama secondary school. Hausawa sunce da
zafi zafi ake dukan karfe"
Sai duk su biyun suka kwashe da dariya
"haba Hajiya, wacce sana'a ce zamuyi ne
wai? Sai kace wasu maza" "mu kam ai sai
dai a nemo a kawo mana. Soft life kawai"
Hajiya ta bude baki "soft life? Kawai dai
kuce min cima zaune na tara a gida na. To
Allah ya sawake muku. Amma dai sai kun
sake tunani tun kafin lokaci ya kure muku,
Ko irin dan cin cin din nan ne da zobo ku
ringa yi mana kuna tafiya da shi makaranta
kuna siyarwa" Sa'adatu tace "cin cin fa kika
ce Hajiya? Haba dai! Wuce nan mana""Safiya dai bata ce komai ba har Hajiya ta
fita, sai data gama tsefewa Sa'adatu kitson
ta sannan ta fita tana neman inda Hajiya
tayi, a falon ta na sama ta same ta waya da
dealer din da zai kawo mata abayas. "A
sabon shagona zan saka su, kaga kuma
zuwa nan da two weeks nake son bude shi.
Dan Allah kar saba min alkawari".
Safiya ta zauna a kasa sai da ta gama wayar
sannan ta kalle ta cikin kulawa tace "Safiya?
Kina bukatar wan abu ne" Safiya ta gyara
zama tace "maganar sana'a da naji kina
yiwa su Sa'adatu. Kina gain nima zan iya
yi?" Hajiya ta gyara zamanta tace "ba su
Sa'adatu nake yiwa maganar sana'a ba, har
da ke kema, gabaki dayan ku nake yiwa. Da
akwai sana'ar da kike gain zaki iya farawa
yanzu?"
Safiya tayi shiru tana tunani sannan tace
"a
garin mu dai tun bayan rasuwar Baba ni da
Baba Hadiza muna yin awara da kuma wake
da shinkafa muna siyarwa, ban sani ba ko
anan zasu siya?" Hajiya ta dan yi shiru tana
tunani sai tace "gaskiya bani da tabbas din
zaki yi cinikin wake da shinkafa anan, Amma
ina saka ran zaki vi na awara tunda abin
sha'awa ce." Ta sake yin shiru sai kuma tayi
murmushi tace "kin san wani abu. I have a
plan for you. Ki rubuta min duk abinda kike bukata na yin sana'ar awara ni kuma zan
siyo miki. Zaki iya yin aikin dahuwar awarar a
can filin baya, sai mu aika duk makota zan
kuma yi miki talla a gun customers dina, sai
a ringa sakawa a robobi ana aikawa ko'ina"
Safiya tayi murmushi tana jin dadi "Nagode
Hajiya, Nagode sosai " hajiya tace "and that
is not all, zan bude sabon shagon da zan
ringa siyar da fabrics na mata, da sauran
ado na mata, zan dauke ki aiki a matsayin
sales girl din shagon, zan hada ki da
yarinyar da already na riga na dauka sai kuyi
akin tare ki koyi harkar yadda ake gudanar
da business" Safiya tayi shiru tana kallon ta
tace "amma Hajiya already kin riga kin
dauke ni aiki anan gidan ai, ko kora ta kika yi
daga akin gidan?" Hajiya tace "ban kore ki
ba kuma ba zan kore ki ba, ko baki san ana
yin aiki biyu a lokaci daya ba? And also
concerning aikin gidan nan, Dije tace min
kusan komai ke kike
14
1:15 AM
yi, maybe shi yasa har yanzu kika gagara yin
kiba, daga yau na ware miki aikin ki,
bedroom dina da nan falon su kadai ne naki.
In kika yi kika gama sai ki tafi zaman shagon
ki, in kin dawo da yamma sai ki dafa awarar
ki, are you up to the task?" Safiya tayi shiru
dan bata gane karshen ba, Hajiya ta
maimaita mata "zaki iya yin hakan?" Da sauri ta gyada kai "zan iya Hajiya, sosai ma".
And that was how it began.
Ana bude shagon Safiya ta fara aikin zaman
shago, kullum da assuba tana tashi zata hau
saman Hajiya, dama kuma Hajiya ba'a dakin
ta take kwana ba tana dakin Alhaji. Dan haka
dakin nata bashi da datti gyaran sa babu
wahala, cikin kankanin lokaci Safiya take
gamawa sannan ta sauko ta gyara nata
dakin tayi wanka ta shirya taci abinci ta debi
na rana ta tafi shago. A can take wuni sai
la'asar take dawowa gida sannan tazo ta
dora dahuwar awarar ta. Ta kan dafa da
yawa wani lokacin ta yi freezing sai take
daukowa tana soyawa ana zuwa ana siya
daga gida gida. Yadda take cinikin awarar
har mamaki yake bata. Tana kuma diyar da
danya, idan mutum yafi so ya soya da kansa
a gida. Har a shago idan customers sunzo
takan yi musu tallan awarar ta, daga baya
sai ta fara soyawa tana tafiya da ita shagon
ma tana siyarwa a can.
Da lokacin albashi yayi Hajiya ta lissafa
kudin albashin ta na aikin gida ta bata a
hannunta, Sannan ta sake lissafa kudin
albashin zaman shago ta sake bata, Sai ta
tsaya tana kallon kudin kawai dan dai ita
bata taba gain kudi masu yawan wadannan
ba. A garin su ko masu aikin gwamnati jin suna daukan wanna kudin. Ta tashi ta je ta
dauko kudin ribar awarar ta da take tarawa
ta kara su akan albashin nata. And the first
thing that came to her mind was wacce
hanya zata bi ta juya wadannan kudaden su
kawo mata wasu?
Maman