Showing 135001 words to 138000 words out of 375662 words
Chapter 46 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx
ya samu
gida ya kama musu rent anan Abuja dan
baya son ya rabata da kasuwancin ta, shima
kuma yanzu yafi mayar da hankali akan
shagon sa na nan Abuja, na kanon mostly
kaninsa Ahmad ne yake handling.
Suma kuma su Hajiya Maryama da Alhaji
Nasir sunyi namijin kokari wajen zubawa
Safiya kayan daki na fitar kunya, yayin da
Sa'adatu ta shiga ta fita ta tabbatar cewa
bikin ya tsaru ya zama very unique and
classy babu wanda zai kushe sai dai idan
hassada ce yake yi.
3
2
9:04 PM
Safiya ta so ta fitar da kudi ta yiwa kanta
gata, amma Hajiya Maryama tace babu
abinda zata yi wa kanta "wannan auren da
zamuyi miki shine last gatan da zamuyi miki,
daga wannan karon kin bar hannun mu
kuma bama fatan ki dawo. Kin koma hannun
mijin ki, amma still ina son ki sani cewa
muna nan anan gidan babu inda zamuje a
duk sanda kike bukatar wani abu ko wata
sharawa ki zo muna maraba lale da ke".
Safiya tamkar ya take a gurin Hajiya
Maryama. In har ba maganar kuka taba yi da
ita ba ba zaka san ba uta ta haife ta ba. Duk
wasu harkokin ta ita take dorawa akai. Duk
inda zata je da ita take zuwa. Ranar nan ma
da zata je gidan ambassador Muhammad
Dikko, da ita taje,
Anan gidan Alhaji Nasiru aka daura auren
Safiya, shine waliyyin ta. Da dare kuma aka
kai Safiya gidan mijinta. A lokacin tana da
shekaru ashirin da biyar a duniya, A ranar
Safiya tayi kukan da rabon da tayi irinsa tun
kafin zuwan ta Abuja. Kukan rabuwa da
Hajiya da kuma Sa'adatu, ta yiwa Hajiya Safiya ta so ta fitar da kudi ta yiwa kanta
gata, amma Hajiya Maryama tace babu
abinda zata vi wa kanta "wannan auren da
zamuyi miki shine last gatan da zamuyi miki,
daga wanna karon kin bar hannun mu
kuma bama fatan ki dawo. Kin koma hannun
mijin ki, amma still ina son ki sani cewa
muna nan anan gidan babu inda zamuje a
duk sanda kike bukatar wani abu ko wata
sharawa ki zo muna maraba lale da ke".
Safiya tamkar ya take a gurin Hajiya
Maryama. In har ba maganar kuka taba yi da
ita ba ba zaka san ba uta ta haife ta ba. Duk
wasu harkokin ta ita take dorawa akai. Duk
inda zata je da ita take zuwa. Ranar nan ma
da zata je gidan ambassador Muhammad
Dikko, da ita taje.
Anan gidan Alhaji Nasir aka daura auren
Safiya, shine waliyyin ta. Da dare kuma aka
kai Safiya gidan mijinta. A lokacin tana da
shekaru ashirin da biyar a duniya. A ranar
Safiya tayi kukan da rabon da tai irinsa tun
kafin zuwan ta Abuja. Kukan rabuwa da
Hajiya da kuma Sa'adatu, ta yiwa Hajiya
kuma adduoin da sai da suka saka ita kanta
hajiyan kuka tare da duk wanda yake gurin,
A haka Hajiya ta rungume ta ta kaita dakin
mijinta tana matukar jin dadi a ranta, ita ta
san Safiya a gurin ta investment ce,
investment din da ba a duniya zata samu
ribar sa ba, a lahira ne,[07/01, 10:42 pm] +234 906 816 1960: A big sorry to those that waited for
Safiyya yesterday
owner
A big thanks to those that checked up on
me
Some things cannot be explained.
21
6:49 AM
Safiyya
Episode Thirty One: The Legend
Safiya became very emotional tun da aka
kaita gidan miji, tun daga kukan rabuwa
da Hajiya kuma shikenan sai ta zarce
kullum kuka ta bar ango da aikin rarrashi,
amma shi ya fahimci zuwa lokacin ba wai
auren take yiwa kukan ba ko kuma
rabuwa da Hajiya ba, loneliness ne yake
damunta, tana missing din familyn ta
sosai. Ta koma kullum sai ta yi hirar su,
kuma da ta fara sai hawaye, Adam ya
fahimci abin nata har da survivors guilt, a
zuciyarta tana feeling guilt na cewa su
sun mutu ita kuma tana raye, and she is
living the life that idan da ace suna raye
ba lallai ne ta samu wannan rayuwar ba.
One week after the wedding ya tashi da
safe ya neme ta a dakin su ya rasa, yayi ta
zagaya gidan yana neman ta sai can ya
samo ta a backyard dinsu tana zaune a
kasa ita kadai tana kallon flowers din
gurin, ya je ya zauna a kusa da ita ba tare
da yace mata komai ba. Sun jima a haka
sannan ta juyo tana kallon sa da idanunta
da suka kumbura saboda kuka tace "da
kai aka je Kura ko su Baba ne suka je su
kadai?" Yace "da ni aka je" ta juya ta
cigaba da kallon flowers din sannan a
hankali tace "ina so zan je. In ka yarda".
Ya saka hannu ya jawo ta kan kafadarsa
sannan ya zagaye ta da hannunsa guda
daya yace "of cause we will go in kina son
zuwa, just tell me yaushe kike so muje" ta
kara kwanciya a jikinsa tace "jibi" suka
saka yin shiru zuwa wani lokaci sannan
yace "I saw the rooms, na ga dakunan da
suka fadi. Kasar tana nan har yanzu" tace
"I want to see it".
Kwana biyu bayan nan suka dauki hanyar
Zamfara da sassafe, dan tun kafin asuba
tayi suka fita sai a hanya suka tsaya suka
vi sallah. Su kadai kuma babu wanda suka
gaya wa. The drive was joyous as well as
emotional for Safiya saboda tana jin dadin
companion dinta amma kuma tafiyar tana
tuna mata tahowar da tayi zuwa Abuja
over 11years ago, a hanya hirar da kawai
take bashi, ranar har da hirar Baba and
the little she can remember about him musamman irin soyayyar da ya nuna mata
ita da yan'uwan ta. They talked about
yadda irin auren Alhaji Haladu da Baba
Hadiza yake random a cikin al'ummar mu
da kuma yadda irin auren yake affecting
zumunci a tsakanin yan gida daya. It is
halal tabbas, amma wata halal din ana
barin ta ko dan kunya da abinda zata
haifar nan gaba. Wani ma sai yayi retire,
da kudin gratuity dinsa zsi je ya auro yar
karamar yarinya ta zo kuma ta fara
haihuwa bayan sun gama girma matansa
kuma sun manyanta, sai kuma yazo ya
biye mata yayi ta yarinta yana bakanta ran
matansa da yayansa, wannan kuma sai ya
kara hura wutar kiyayyar amaryar da
kuma yayanta a zuciyar wadancan. A
karshe ya mutu ya bar baya da kura.
Su kuma yayan da aka haifa basu da laifi,
amma a karshe sune suke paying price
din abinda ba su suka siya ba.
Karfe 10 na safe a Gusau tayi musu, anan
suka tsaya suka samu wani eatery suka ci
abinci sannan suka dauki hanyar Kura.
Few minutes after that suna garin Kura,
Tun da suka shiga yayi slowing down yana
tafiya a hankali ita kuma tayi shiru tana
karewa garin kallo, nothing much has
changed tun barinta garin, except for few
houses da taga an gina an ld wadansu an
sake musu fasali zuwa na zamani amma babu wani major change a garin, dan haka
tar take gane hanya tiryan tiryan har kofar
gidan su.
Abinda ta fara gani shine tarin kasar da ta
kasance ita ce dakin da tayi spending
most of her childhood in. She could still
feel the moist, dark and suffocating
nature of the rooms, their laughter
together ita da kannnenta da Baba
Hadiza, sheshshekar kukan su idan suna
cikin bakin ciki, ta rufe idonta tana tuno
sound din kukan Khadijah sanda bata da
lafiya "Baba Hadiza ki kaini asibiti bani da
lafiya". Ta bude idonta tana jin echo din
hun Sauda a lokacin da mota ta kade
Baba Hadiza.
Ta juya da sauri ta kalli gurin, a idonta
tana gain gizon sanda motar ta daki
Baba Hadiza ta tashi sama sannan ta fado
kan kwalta. Ta tuna da yadda jini ya ringa
fita daga kan ta, yadda jinin ya jika ta ita
da Sauda. Ta bude tafin hannun ta tana
kallo, kamar mai kokarin gain jinin a jikin
hannun.
Adam ya saka hannun sa cikin nata yana
kallon yadda hawaye yake bin fuskarta
yace "kina so mu koma?" Ta girgiza kan ta
"no" sai ta cire hannun ta daga cikin nasa ta bude kofar ta fita.
Sai a lokacin ta lura da cewa mutanen
unguwar kusan kowa da yake gurin a
lokacin motar ta su yake kalla, irin anga
bakuwar mota ta tsaya kuma ba'a san
waye a cikin ta ba. Ta juya tana kallon inda
suke suyar awarar su ita da Sauda, a kofar
gidan makota, saboda basu isa su yi a
kofar gidan su ba.
Ta taka a hankali zuwa kofar gidan ta
shiga soron, yana nan shima yadda ta
sam shi sai dai ya kara lalacewa, katangar
duk ta tsatstsage, rufin ya taho zai fadi sai
itace aka saka aka tokare shi. Langa
langar da aka saka aka raba soron gida
biyu babu ita, haka jakankunan kayan su
da ta bari a wajan babu su suma. Daga
dukkan alama soron ma ba'a amfani da
shi yanzu dan dakunan su da suka fada
kuma ba'a gyara ba sun saka gidan ya
zama bashi da takamaiman mashiga.
Ta shiga tsakar gida tana bin gidan da
kallo, daga dakin da yake farko, dakin da
nan ne inda yake na Baba Hadiza sanda
Alhaji Haladu yana da rai, dakin da a ciki
aka haife ta taga wata mata da bata sani
ba ta fito ta a kallon ta "'baiwar Allah
lafiya? Daga ina?" Bata amsa mata ba ta cigaba da bin gidan da kallo.
Babban abinda ya ja hankalin ta a
chanjawar da gidan yayi shine bedroom
din Inna Sa'ade da taga ya rushe shima.
Sabon dakin da aka yi mata ginin bulon
siminti aka jingina shi a jikin nasu na kasa
har yayi sanadiyar lalacewar nasun kuma
yayi sanadiyyar rayuwar Sauda, shima ya
fadi, kuma daga alama ya jima shima da
faduwar, amma kuma kamar nasu shima
ba"a gyara gurin ba yana nan a bude, sai
ginin kasa da aka yi aka toshe kofar
tsakanin cikin dakin nata da falon ta.
Safiya ta wuce matar da har yanzu take yi
mata magana ta doshi kofar falon Inna
Sa'aden, kafin ta daga labule taji murya a
bayan ta, muryar yayanta Dauda "ke
wacece ne wai ana ta yi miki magana kinyi
wa mutane shiru?" Ta juyo da sauri ta
sauke rinannun idanun ta akan sa, ya ja da
baya kadan kamar wanda yayi gamo,
"Baba Hadiza?" Ya fada, sai kuma ya
chanja "Safiya?"
Bata amsa masa ba sai ido da take binsa
da shi. Muryar sa tana nan yadda take
bata manta ta ba, ta tuno sanda yace "ina
uwar ta ku? Ko bata dawo daga yawon
karuwancin ba?" Amma kuma kamannin
sa gabaki daya sun chanja, ya rame ya sirance yayi baki, kana ganin sa ka ga
wanda shaye shaye yayi wa kamun mutu
ka raba.
"Lantana! Lami!" Ya fara kwalla kiran
sunan yayyen su wadanda suke yaya ne a
gurin Inna Gaje. Lami ta fito daga dakin
Inna gaje da sauri tana gyara daurin zani.
"Kai lafiya kake min irin wannan kiran
mafarautan? Ba dai zan baka rancen wani
kudin ba dan. .
...." Sai kuma ta tsaya tana
kallon Safiya.
"Safiya" ta kira ta direct
"Safiya ke ce haka? Ke ce a gidan nan?"
Safiya ta tuno ta sanda take zazzagin
Baba Hadiza tana kuma kokarin dukan ta
a dai dai lokacin da aka dauki gawar Alhaji
Haladu. Ta kuma tuno ta sanda suke yi
musu watsi da kaya a waje suna cewa sai
sun bar musu gida, Baba Hadiza tana ta
kuka tana bin su tana rokon su.
Ta juyo sosai tana kallon ta ta kira sunan
ta ita ma "Lami" duk kuwa da cewa Lamin
da haife ta dan tana da yaya sa'annin ta.
Sai kuwa Lami ta rafka salati "jama'a ku
fito. Safiya ce a gidan nan jama'a. Ashe
tana raye. Jama'a ku fito ku ganta dan in
tabbatar ba gamo nayi ba" Dauda yace
"gani nima ina ganin ta kuwa? Wanne irin
gamo? Zamuyi gamo ni mu biyu?" Ta
watsa masa kallon banza "kai dalla can,
kai me idon ka yake gani in banda kwaya?
Ina kiran mutane masu hankali ne su zo su
taya ni gani" nan take sai masifa ta kaure a tsakanin su.
Safiya ta wuce su ta shiga dakin da take
ta hari tun da ta shigo gidan. Sai dai tun
da ta daga labule taji dakin yana wari,
wani wari kamar warin mushe. Ga duhu
tamkar dakin su na da saboda tagogin
dakin duk a rufe suke. Sai da ta dan jima a
tsaye a gurin sannan idon ta ya washe, a
lokacin ne ta ga mutum a kwance a kan
katifa a tsakar daki.
14
6
3
6:52 AM
Sama sama take jin murya tana kiran
sunan ta "Safiya? Safiya ke ce? Safiya" ta
durkusa a gaban halittar da take kwance
a gabanta tana kallon ta. Ta rame ta
motse ta yamushe, Inna Sa'ade ce.
Kafafuwanta duk guda biyun babu su an
yanke su. Daga jikin ta da kuma katifar da
take kwance a kai ne warin yake fitowa.
Sai dai bakin ta yana nan tas, kuma daga
dukkan alamu tana cikin hayyacin ta.
"Safiya daki na ne ya fado min ina kwance
ina bacci, kafafuwana duk duka kakkarye
sai da aka yanke su, Balarabe yayi
hatsarin mota ya mutu, sauran yaya na
duk sun gaji da kulawa da ni suna can
gurin matayen su, Sai Dauda shi kuma
babu abinda yake sai shaye shaye, komai nawa ya sace ya siyar ya sayi kayan shaye
shayen sa..
..." Ta cigaba da magana non
stop, kamar neman wanda zata yiwa
magana da ma take yi, kamar ta jima ba ta
yi magana da kowa ba.
Safiya ta mike tsaye ba tare da ta ce mata
komai ba ta doshi kofa. Sai da taje bakin
kofa sannan inna Sa'ade ta sake kiran
sunan ta "safiya"Safiya ta dakata sannan
ta juyo tana kallon ta, tace "ki godewa
Allah da Sauda mutuwa tayi ba ta zama iri
na ba. A wani lokaci mutuwa rahama ce,
ni yanzu neman ta nake yi taki zuwa".
Har ta koma tsakar gida ana cigaba da
rigima tsakanin Lami da Dauda. Ta wuce
su again ba tare da tace komai ba ta shiga
dakin Inna Gaje. Tana zaune akan
tabarma ita kadai tana ta maganganu
kasa kasa, har Safiya taje gabanta ta
durkusa bata san ta je ba, kuma Safiyan
bata gane me take cewa ba. Maganganu
kawai take yi marasa ma'ana. Ga tsufa ita
ma ta koma kamar tsumma. "Da yazo ya
dauki kazar sai suka tafi cikin ruwan
sama, kuma saniyar bata da ilimi, Allah dai
ya tona asirin takalmi, Amen Ameen"
Safiya ta mike tsaye tana cigaba da kallon
ta sannan ta saka hannu biyu ta share
hawayen fuskarta ta juya ta bar dakin.
Tana fita Lami ta sske kokarin tarar gabanta, ta lura yayan lamin suna zagaye
da ita, da alama zawarci take yi. "Safiya
ina kika je tsahon shekarun nan. Munyi ta
neman ki bamu same ki ba. Mun dauka
ma ba kya duniya" Dauda yace "ina taje
kuwa in banda yawon duniya, namiji ne fa
yanzu ya kawo ta a katuwar mota, a ina
Safiya zata samu shiga irin waccan motar
in dai ba yawon duniya take yi ba?" Lami
tace "dalla yi mana shiru, ka kalle ta mana
ka gani? Ko dan shaye shaye ya toshe
kwakwalwar ka. Bata yi kama da abinda
kake fada ba, kama take yi da matan
masu kudi. Ka sani ko mijinta ne? Ko aure
ta yi? Safiya kiyi min magana mana ina ta
yi miki magana".
Still Safiya bata ce komai ba, ta wuce ta
tsakiyar su taje ta hau ta kan kasar da
shekaru suka saka ta zaizaye ta zama
bata da yawa, ta fita daga gidan ta koma
mota inda ta bar Adam.
Yana tsaye a jikin motar yana kallon cikin
gidan, daga dukkan alamu hankalin sa
ba'a kwance yake ba, yana gain ta fito
yayi ajiyar zuciya sannan ya bude mata
kofa ta shiga ta zauna a dai dai lokacin da
yaya Malam ya kawo kai yana kokarin
shiga gidan, ya tsaya yana kallon motar
daga alama bai gane wacce ta shiga cikin
motar ba, Safiya ta bishi da kallo, yana
nan kamar yadda ta san shi, ssi dai
shekaru da suka karu akan na da, sai
kuma shekarun suka saka taga yayi mata
kama da baban su. Ta rufe ido tana
kokarin tuno wa da fuskar Baba, suna
kama sosai da yaya Malam, ta bude idon
tace da Adam, "Drive, please" ya taka
motar a dai dai lokacin da yaya Malam ya
gane ta yace "Safiya?" Amma bata amsa
masa ba kamar yadda bata amsawa kowa
a gidan ba.
Gidan Hajiya Kyauta tayi masa kwatance
suka je, Hajiya Kyauta tayi murnar ganin
su sosai dan dama bata samu zuwa bikin
nasu ba saboda bata jin dadi sosai. Suka
zauna suka yi hira da ita sannan suka ci
abinci. A lokacin ne take bawa Safiya
labaran abubuwan da suka faru a gidan
su, yayan ta Balarabe wanda Inna Sa'ade
take ji da shi a cikin yayanta ya mutu, ita
kuma kasar da ta kashe Sauda ita ce ta
lalata nata ginin na zamani sannan babu
zato babu tsammani dakin ya fado mata
ita ma cikin dare, abinda yayi sanadiyyar
kafafuwanta biyu duk sai da aka yanke su.
15
8
4
6:52 AM
Ita dama bata da yaya mata, yaya mazan
suka fara jinyarta kamar gaske daga baya
duk kowa ya kama gabansa sai Dauda da
yayi aure yanzu yake zaune a asalin dakin Baba Hadiza. Su sauran yayan daudan
suke aikowa kudi wai ya kula da
mahaifiyar ta su, shi kuma sai ya cinve
kudin. Hatta fitsari da bahaya a lokuta da
dama sai dai tayi su a kwance.
Inna Gaje on the other hand tsufa yazo
mata da