Showing 231001 words to 234000 words out of 375662 words
Chapter 78 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx
/>
kulawa sosai. Sannan lokacin da Mukhtar ya fara cewa yana so na ta nuna amincewar ta da maganar dan har irin alkunyar nan ta fara nuna min ta surukai.
Da na ki karbar soyayyar sa, a bar gidan
su, sai dangantakar mu ta ragu sosai and I
did not blame her, babu uwar da zata so
ace ba'a son danta. But I thought she will
get over it with time. Sai kuma gani da
ciki, cikin shege, and sai kuma na zabi
Mukhtar din a matsayin wanda zan aura
to cover the cikin shegen da nayi. I think
kowacce uwa will do abinda Umma tavi ko
ma fiye da haka. Na fahimce ta. Wannan
kuma ya saka bani da grudges
whatsoever on her. And then uncle Ahmad. Uncle Ahmad bayan Daddy bani da wani father figure
kamar sa. Babu kuma wand aya
hidimtawa dukiyar Ammie da Daddy
kamar shi. He spent his entire life yana
aiki a karkashin su though not free tunda
duk abinda ya ke da shi daga gare su ne
but he gave it his best, Ita kuma dukiya
tana da zaki, mutane kadan ne zasu so
rabuwa da ita bayan sun dauki shekaru
suna juya ta. Wannan shi yasa ya nuna
goyon bayan saga aure na da Mukhtar
tun a karon farko, wannan kuma shi yasa
har a last zaman da muka yi ya ke cigaba
da kokarin cusa min Mukhtar din dan yana gain aure na da Mukhtar zai saka ya cigaba da juya dukiyar kuma ko babu ransa to dansa da jikokin sane akan
dukiyar, in babu raina ma sune zasu gaje
ni. Amma kuma bashi da hannu a cikin
abinda Mukhtar din yayi. Nayi kokarin dawo da hankali na kansu, har lokacin suna ta tafka rigima da
Mukhtar, na lura cewa ba karamin maruwa
fuskar Mukhtar tayi a gurin Uncle Ahmad
ba dan fuskar har tayi ja ta fara kumbura,
amma da yake ba shi da kunya still bai yi
shiru ba. Na juyar da kaina gefe na daina kallon su.
Na dauka uncle Ahmad zai cig6da
dagewa a kan abar aurena da Mukhtar, sai
kuma na lura cewa yanzu ya fahimci
hakan ba mai yiyuwa bane ba ya hakura.
And by submitting his resignation letter
yana nufin ya sallama komai ya kuma
hakura da komai. Da gaske uncle Ahmad huce haushin sa yake yi akan Mukhtar, dan bayan marikan
da yake zuba masa har da kafa ya saka ya
ke dukan sa. Ni dai sai na mike tsaye nayi
cikin gida na barsu anan. Na gama kuma
da wannan shafin. Ban yafe wa Mukhtar
ba kuma bana jin zan yafe masa. Amma na bar shi da Allah, na kuma san hukuncin da zai yanke masa yafi wanda alkali zai yanke masa idan na kai shi court.
Maman Maama✍🏻
Ina yan soyayya? Next post zamu tabo
muku Malam Muhammadun ku insha
Allah. Allah ya sa kar ya bada ku kuma😅[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Safiyya❤️🩹
Episode Forty Seven : The Decision
*Free baking master class*
I'll be sharing delightfully delicious
recipes including how to make soft and
fluffy doughnut for *free* it's completely
free A-Z
Click the link below to join
Females only
https://chat.whatsapp.com/
DN5w2VPGPhE0gf3700F9k0
0704248974
Zan koyarda snacks kala 8 kyauta
acikinsu akwai yadda zakiyi doughnut me
laushi da dadi classes dinnam kyauta ne
daga farko har karshe
Danna wannam link kiyi joining
Mata kawai
Or contact
07042486974
To be added
https://chat.whatsapp.com/
DN5w2VPGPhE0gf3700F9ko
Safiyya.....
Ranar kwana nayi banyi bacci ba ina saka
da warwara, a fahimci abinda Daddy
yake nufi, amma sai dai kuma fahimtar ta
sa ta toshe min hanyar da na biyo kuma
na kasa ganin wata hanyar da zata bulle
da ni xuwa destination dina. Na tashi nayi
sallah na gaya wa Allah bukata ta na roje
shi ya bani mafita tunda dai ni bani da ita.
Sai wajen asuba na kwanta akan sallayar
nayi bacci, bayan anyi sallah na tashi nayi
sallah sannan na koma kan gado na
kwanta bacci mai nauyi ya dauke ni.
Ban farka ba sai da rana tayi sosai. Na
tashi nayi wanka na shirya ina jin kaina
yana yi min ciwo duk kuwa da cewa nayi
bacci mai nauyi amma na san damuwa ce
ta saka min ciwon kan. Na dauko waya ta
ina dubawa sai na ga sako daga Abdul
yana yi min mitar bana neman su sai in
sun neme ni "munyi fushi" ya turo tare da
hoton Junior ya bata rai ya turo baki, Sai
na samu kaina da yin dariya, He looks so
cute and innocent and doesn't deserve all
this, Na shafa fuskar sa ta cikin wayar sai
nace a hankali "hey you, It is going to be
okay. You are going to be okay, I promise"
Nayi replying Abdul tare da tsokanar sa
ina tambayar sa labarin amarya. Sai kuma na tashi na tafi part din Daddy dan gaishe
shi. Ina shiga na tarar da shi a falon sa
tare da Mustapha suna gwada wani
machine da aka siyo masa da zai taimaka
masa wajen zama da tashi ba tare da an
rike shi ba. Na zauna a gefe ina kallon su.
Mustapha might be a bad person but he
takes care of Daddy and I am greatful to
him for that.
Sai da suka gama sannan na karasa gurin
sa na gaishe shi sannan nace '
"sai yanzu na tashi. I slept in" ya zauna yana haki
saboda movements din da yayi sannan
yace min "maybe baki yi bacci da dare ba
ne ba ko?" Na sunkuya da kai nace "haka
ne Daddy. Ina ta tunani ne. I am still not
sure what I will do" yace "kin ci abinci?"
Na girgiza kai "no, shigowa nayi da ma mu
gaisa sai inje inci abincin" yace "good. Sai
kuma yayi shiru ya kwantar da kansa tare
da rufe idonsa,
Har na fara tunanin tashi ina gain maybe
bacci ya dauke shi sai kuma na ga ya
bude ido yana kallona yace "na taba baki
labarin siblings din Ammien ki?" Na gyara
zama, ina son labarin Ammie ko a gurin
waye ballantana a gurin Daddy, A gurin sa
da sauran mutane na hada labarin ta.
Nace "wanne labarin da ga ciki? Na yadda
suka yi sanadin rasuwar baba Hadiza da su Sauda ko kuma na yadda suka biyo ta
nan suka takurawa rayuwar ta?" Ya girgiza
kai yace "na abinda ya faru da su bayan
rasuwar ta" nace "Daddy you never talk
about anything related to rasuwar Ammie.
Labaran ka duk na sanda tana raye ne ba
ka taba bani labarin lokacin rasuwar ta ko
abinda ya far bayan rasuwar tata ba".
Yayi shiru yana kallon tv amma ba wai tvn
yake kalla ba. Ya dan jima sannan yace
"tabbas yan'uwa Safiya sun tsane ta ita
da yan'uwan ta, tsanar da har ta kaisu ga
aikata abubuwa da dama wadanda suka
zama sanadiyyar da Safiya ta rasa kowa
nata. Sannan kuma sai Allah ya daukaka
ta fiye da yadda bata yi tunani ba, fiye da
yadda suma ba su taba mafarki ba, and
they came back, zuciyoyin su still cike da
tsanar ta, they threatened her life, suka
kira ta da juya, suka kuma bita da
mugayen maganganu na sharri".
"A lokacin a irin daukakar da Safiya take
da shi idan da taga dama zsta iya batar da
su a duniya baki daya, idan da taga dama
zata iya kai su kara ta lissafo irin
abubuwan da suka aikata mata and she
can get a good lawyer da zai iya rufe mata
duk wanda yake da hannu a cikin abinda
ya same ta. But she didn't do that. She said sanda ta shiga gidan su yaga yadda Allah ya mayar da su ita kuma ta ga yadda Allah ya mayar da ita sai ta san
cewa Allah has already fought her battle
for her. Bata bukatar revenge. Ya riga yayi
mata. Amma sai ta ja jikinta daga gare su
dan gujewa sharrin su. Ko sanda suke
zuwa gidan nan. A cikin gidan nan sun
taba gaya mata ido da ido cewa tunda ita
juya ce bata haihuwa suna jira be ta mutu
su ci gadon ta. She could have sue them
a lokacin, but she didn't. She said taga
abinda Allah yay musu wancan karon,
wanna karon ma shi take jira yayi mata
komai. She just took some protective
measures and leave them with God".
"And then she died"
"Washegarin da ta rasu suka zo gidan
nan, Bus guda suka yo shata daga Kura
suka taho mazan su da matan su, yara da
manya, Sanda suka zo aka gaya min sai
nace a barsu su shigo, Na saka aka basu
dakuna biyu, maza aka basu daya a waje
mata kuma aka basu daya a cikin gida,
Amma tun a lokacin sai suka tayar da rigimar su dakunan ta suke so a bude musu a sama su a dakin ta zasu sauka. Lokacin kina ta koke koken ki na neman
mahaifiyar ki Sa'adatu da sauran mutane
suna ta fama da ke amma su ko a kin su.
Hajiya ta san ba alkhairi ne ya kawo su ba
dan haka ta hau saman ta rufe dakunan ta
rike key a hannun ta. Shikenan sai rikici.
Suka kafa maganganu na rashin mutunci
da izgilanci suke yiwa Hajiya, Sa'adatu
kuma da sauran mutane suka shiga ciki,
sai rigima ta tashi a gidan gaisuwa"
"Ni ina can ina cikin matsananciyar
damuwar abinda ya faru naji hayaniya. Ina
ji dama na san sune. Nan take na kira
police suka zo suka kwashe su
gabakidaya suka tafi dasu. Sai da suka
kwana a can. Ahmad ne yayi ta zirga-
zirga sannan daga baya nace a sake su
amma kar su dawo min gida. Su barni inji
da abinda yake damuna".
"Suka tafi din, amma basu hakura ba
ranar sadakar bakwai sai gasu sun dawo,
Mutane sun taru ana yi mata sadaka da
adduoin neman rahamar ubangiji amma
tun daga bakin gate suka fara zage zage,
wai suna so suga uban da zai hana su
shiga gidan, ai gidan ma yanzu nasu ne, ai
ance musu dama gidan tane kuma su ne magadan ta dan haka sun zo karbar gadon su. Har nayi niyyar sake kiran police sai Alhaji Nasir ya hana ni. Ya aika
aka shigo da su ya zaunar da su yace su
zauna avi mata addu'a tare da su sannan
sai a saurari maganar da suka zo da ita".
"Aka gama zaman addu'a aka tashi. Suka
sake zama da Alhaji Nasiru suka gaya
masa sun zone karbar dukiyar da ta mutu
ta bari, har da list din su a hannu na
abubuwan da aka gaya musu ta mallaka.
Alhaji Nasiru ace babu komai dama ai shi
gado Allah ya riga ya raba shi. Su je su
samo malamin da zai raba gadon sai su
zo a raba a basu. Suka ki tafiya, dan
sunce ko kudin motar da zasu koma kura
basu da shi jira suke sai an basu su samu
na mota a ciki, Alhaji Salisu ya sama musu
gurin zama, sannan ya nemo alkalin da zai
raba gado ya kawo ya hada su dashi,
sannan ni kuma aka ce in bayar da abinda
ta bari wanda za'a raba".
"Ban je gurin ba dama nace ba zan je ba,
sai na tura barrister Umar da sauran
lawyers din ta suke managing affairs dinta
suka je, suka gabatar da lissafin
abubuwan da ta mutu ta bari wadanda
suke nata. Wadannan sun hada da
wadansu daga cikin kayan sskawarta, sauran tarkacen irin na mata, da kuma kudin da yake cikin account din ta. Ko mota bata da ita. Nan take sabuwar
rigima ta rikice dan ma Allah yasa na gaya
wa barrister su tafi da security dan babu
abinda ba zai iya faruwa ba. Ai kam dai
ance Dauda wuka ya fitar yace sai ya illata
barrister Umar".
"Nan take suka shigar da kara Court akan
an cinye musu gadon yar'uwar su data
mutu ta bar musu. Zama daya aka yi wa
shari'ar alkali ya kori karar tunda basu da
hujjar cewa wadannan kadarori da suka
lissafa nata ne. Dan ga takardu lawyers
din mu sunje da su da suke nuna duk
kadarorin nan naki ne ba nata bane ba.
Daga nan suka sake kai kara kotun
musulunci. Sunce waccan kotun kafurci
ake yi a ciki. A wannan zaman court din
ne naje, na kuma yiwa alkali bayanin duk
abinda Safiya tayi sanda tana da rai kuma
cikin koshin lafiyar ta. Ta baki kyautar komai da ta mallaka kuma ke ce kadai yar ta a duniya. Na kuma nuna masa abinda ta mutu ta bari a matsayin
nata. Sannan nace ni da ke mun yate
gadon Safiya, abinda ta bari din mun bar
musu su rike"
"A take alkali ya tabbatar musu da cewa
Musulunci ya yarda da abinda Safiya tayi,
dan haka abinda na nuna musu din shine
kawai abinda za'a raba a matsayin gadon
ta, sannan kuma yace ni da ke musulunci
bai bamu damar cewa mun yafe gado ba,
ba'a yafe gado, dole sai an bamu sai dai
in an bamu mu bayar in bama so"
"Still sai suka tayar da rigimar wai ai kayan
sakawa kadai na fito da su banda kayan
daki, su sun san cewa kowacce mace
tana da kayan dakin ta a gidan mijinta dan
haka sai na fito da su gado da kujeru da
sauran su ai suma kayan ta ne. Ni kuma
na san sanda na sayi gidan nan na saka
aka zuba komai a cikin sa, tabbas safiya
ta sai abubuwa itama amma ba ma
zanniya ware abinda ta siya da wanda na
siya ba dan haka nace su zo su dauka.
Ahmad yana ta bala'i nace ya barsu suzo
su dauka. Na zo gida na kwashe duk
abinda na san mai daraja ne kuma ta baki
tun tana da rai, irin su gwala-gwalai da
manyan suturu da designer perfumes din
ta duk na adana a bangare na, Duk abinda
yake bangaren ta kuma nace azo a dauka,
Hatta carpet da labule ba'a bari ba sai da
suka cire, Hatta cutlary set sai da suka
dauke daga kitchen. Cokali basu bari ba,
Har da mugunta, abinda aka ga ba zai
dauku ba sai a fasa shi. Ban ce komai ba
dan ni ta kaina nake yi. Duniyar ma ta fita daga kaina ballantana kayan da suke cikin
ta. Suka kai alkali aka yiwa kaya kudi aka
fitar da nawa da naki sauran aka basu. Ni
dai ban sake komawa court din ba.
Abinda aka bamu ma nace da Ahmad yaje
yayi sadaka da su Allah ya kai mata ladan
kabarin ta. Daga lokacin naji gidan gabaki
daya ya fita daga kaina ba zan iya cigaba
da zama a cikin sa ba. It holds a lot of
good and bad memories for the both of
us dan kema a lokacin kamar kinfi kukan
neman ta in muka shigo gidan. A lokacin
ne na yanke hukunci komawa Kano da
zama to ease the pain for us".
Yayi shiru yana hutawa, idon sa yayi ja,
har yanzu mutuwar Ammie tana damun sa
sosai and I couldn't imagine going
through the pain of loosing her at the
same time kuma da wannan bacin ran na
yan'uwan ta. Ga kuma ni da na saka shi a
gaba da rigima kullum.
Muka cigaba da yin shiru sannan nace
"Daddy to ba ka gaya min ba" yace "ban
gaya miki me ba?" Nace "sanda zaka fara
magana kace zaka bani labarin abinda ya
faru da su bayan rasuwar ta. Menene ya
faru da su?" Ya dan yi gyaran murya yace
"a labarin da aka bani, Tun a gaban alkalin
da ya raba gadon suka fara rigima akan
abinda aka basu, matan suna ta zabar
kayan sakawa daga cikin kayan da suka samu. Sai babban su, Yaya Malam, ya kwace komai daga hannun kowa yace su bari sai sun je gida sai suyi nasu rabon.
Ya dauko shatar motar diban kaya aka
kwashe duk kayan aka zuba a ciki, cash
din kuma ya karba ya rike a hannun sa, su
kuma suka shiga mota suka koma Kura
gabakidayan su"
"Daga baya Jamilu dan marigayiya Hajiya
Kyauta, shi yake bani labarin abinda ya
faru da su. Yace bayan sun je gida suka yi
ta jiran motar kaya tazo shiru shiru mota
bata zo ba. Tun suna tunanin matsala
motar ta samu a hanya har suka fara
tuhumar yaya Malam akan inda kaya suka
makale, da farko yayi ta basu uzurirruka
masu cike da karaiyayi. Daga baya bayan
an debi tsahon lokaci ba tare da kaya sun
zo ba sai suka hada kai suka je gidan sa
suka ritsa shi suka ce lallai sai ya fadi inda
kaya suke, a nan ne yaga babu sarki sai
Allah sai yace musu kaya dai ya siyar da
su, kudin kuma ya biya lawyer din da ya
dauka ya tsaya musu a court, kudin
hannunsa kuma da su ya biya kudin
shatar motar da suke je suka dawo da
kuma motar da aka dauki kayan, Dan haka
babu wani abu da ya rage wanda zai basu”.
"Wannan maganar ta bata musu rai sosai,
a take Dauda ya cire wuka ya soka wa yaya Malam a kahon zuci, a take ya fadi ya mutu, yan sanda kuna suka kama Dauda, bayan anyi shari'ar sa sai aka
yanke masa hukuncin daurin rai da rai". Ya sake yin shiru yana kallon expression din fuska ta. Ban taba tunanin wannan ne abinda ya faru da su Dauda ba ban kuma taba damuwa da lallai sai na san wani abu
a game da su ba. Lallai Allah mai yawan
hikima ma a cikin dukkan al'amuran sa.
Daddy yayi murmushi yana lura da yadda
labarin ya taba ni sai yace "ina fatan kin
gane abinda nake so ki fahimta a cikin
wannan labarin. When you leave all your
battles in God's hand, God will fight all
your battles for you. Za kuma ki samu
justice din da baki taba zata ba,