Showing 1 words to 3000 words out of 375662 words
Chapter 1 - SAFIYYA Book Complete Hausa Novels Maman Maama.docx
[07/01, 10:41 pm] +234 906 816 1960: ❤🩹*Safiyya*❤🩹
*By*
*Maman Maama*
Daga marubuciyar:
Maimoon
A'isha Humaira
Diyam
Tagwaye
Jidda
And now..... Safiyya
*Episode One: Bon appetite!*
Breakfast is Served💔
Bismillahir Rahmanir Rahim
Ina rokon Allah ya bani ikon rubuta alkhairi, ya hana ni rubuta sharri.
Assalamu alaikum dearies ❤️
Fatan munyi azumi da sallah lfy. Allah ya karbi ibadun mu ya sa muna daga cikin yantattun bayin sa Ameen.
So, kamar yadda nayi alkawarin rubuta Safiyyah after sallah, gashi nan zanyi kokarin cikawa 😁. Ku dai ku taya ni addu'ar Allah ya bani ikon cikawar. Lol
Believe me, dama nayi niyyar yi ne on an impulse, sai daga baya kuma na fara cewa "anya kuwa?" But then na riga na fada muku and duk sanda nayi magana ina matukar kokarin ganin na cika ta, sai dai when it is beyond my control, as nobody is perfect. So, we will try insha Allah, but you will have to be patient with me idan an samu rashin update akan lokaci, ina so ku saka a ranku cewa ina iyakacin kokari na.
Kamar yadda na faɗa, littafin Safiyya hopefully zai zo a matsayin free tun daga farkon sa har karshen sa insha Allah, depending on in mun samu sponsors at least twenty, ku kuma readers ina rokon alfarmar ku bada haɗin kai wajen showing support to the sponsors dan suji dadin cigaba da siya muku littafin Safiyya kuna karantawa, idan babu sponsors, littafin Safiyya zai koma paid after the free pages.
I hope we will enjoy this journey tare da Safiyya and Gidado, it is going to be rough 😁, but I promise you a smooth landing.
*Him*👳🏻
"Tell me you love me" yaji muryar ta ta daki dodon kunnen sa kamar a yanzu ne take yi masa maganar. Ya saka hannayen sa biyu ya toshe kunnuwansa sannan ya rintse idanun sa da karfi amma sai ya zama kamar kara clearing vision and hearing dinsa yayi. Abinda ya manta shine daga cikin kansa muryar take fitowa ba daga surrounding dinsa ba. A idonsa yana ganin fuskarta, as clear as the moon when it is full. A zaune a cikin motarsa, fuskarta dauke da murmushin da ya kasance tamkar maganin dukkan damuwa a gare shi, idanuwan ta cike da soyayyar sa.
"Tell me you love me" ta fada tana saita camera din wayar ta a fuskarsa, ya saka hannu daya ya kare fuskarsa yana murmushi. "Stop it!" Ya ce cikin muryar dariya, she giggled sannan ta chanja angle din camera din zuwa inda bai kare ba a fuskarsa. "Ka fada mana to, why are you shying away from a simple question. Do you love me?"
Ya bude fuskarsa yana kokarin frowning amma ya kasa, baya iya bata rai in dai yana tare da ita. Ya jingina kansa a headrest din kujerar motar yana kallon camera din tata yace "do you need to ask?" Tace "of cause. I want to hear you say it" ya lumshe ido ya bude yace "what is with the camera then?" Tace "as evidence. I want to record you say it sannan in ajiye as evidence yadda idan nan gaba ka ce baka so na ina da shaidar da zan shigar da karar ka zuwa kotun masoya".
Yayi dariya sosai yana kokarin ture camera din tata amma sai ta matsar away from his reaching hands, ta ce "confess! Say you love me" ya ajiye hannunsa ganin bata da niyyar bashi wayar yace "common! Why do I have to say it? Me yasa ke ba zaki fada ba sai ni?" Ta daga gira tace "because I say so... Kuma duk abinda nace ina so shi nake samu. Now I want you to say you love me". Ta karasa cikin turo bakin shagwaba.
Yayi ajjiyar zuciya "you are impossible Piya. Me zan fada miki ne wanda baki sani ba?" Tace "that you love me?" Yace "you already know that ai, you just enjoy.... enjoy.....en.." ta karasa masa cikin kwaikwayon muryarsa "you enjoy teasing me " sai kuma ta yi dariya. "You are right, na san dama ba fada zaka yi ba. I only wanted to see that" ta fada tana nuna fuskarsa, ya shafa fuskar kamar mai neman wani abu yace "see what?" Tace "your face is red my dear. You are blushing" ta karasa tana sake wata dariyar.
Yayi ajjiyar zuciya "Piya! You are...." "Impossible" ta karasa masa tana sake kwaikwayon sa. Ya harare ta "stop that" ta maimaita "stop that" ya fakaice ta ya zare wayar daga hannun ta sannan ya juya camerar zuwa fuskarta. Tayi saurin rufe fuskarta da hannayen ta biyu tana dariya, yayi zooming screen din yana karewa kyawawan fingers dinta kallo. "wa na kama?" Ya fada cikin tsokana, "now, tell me you love me" ta bude fuskar ta harare shi tare da murguda baki a lokaci daya, yayi murmushi "in dai har da gaske rashin kunyar kike ji da ita ki fada min inji. Say you love me" ya karasa yana rage murya can kasa. Ta fara laluben handle din kofar. "Ni ka bude min kofa. Ni hostel zan shiga" yace "kin isa ma, ai yau sai kin fada. Kuma inyi recording din ki in ajiye, in munyi aure mun haifi yara sai in nuna musu yadda maman su ta mutu a kaina" ta juya ido "wai ma, wa ya gaya maka haka?" Yace "I know...I just know. Tun ranar da kika fara gani na you just couldn't stay away from me, kinga dan farin bafulatani kin rikice, kince in ba ni ba sai rijiya" tayi dariya "ranar da na fara ganin ka, loving you was the last thing on my mind. Bana jin ma nasan menene love ɗin " yace "huh? Shi yasa kika bar seat din ki kika dawo nawa? Admit it Piya, you were attracted to me" ta juya idonta "shi yasa naga tun daga ranar duk inda nayi sai ka bini, bita zai zai" yace "tabbas, and this is just the beginning, duk inda kika je sai na biki. Naji na yarda ni bita zai zai din ne. Kuma nan gaba zan zama 'mijin kafin ta ce'"
Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, tana jin nauyin idanuwansa a kanta, ya sauke wayar tare da yin ajjiyar zuciya yace "Please Piya, I think it is about time ki kaini gurin Daddy, har yanzu baki gama jan ajin ba wai?" Ta dago kai suka haɗa ido "sai ka lallaba ni kuma ka bani cin hanci" ya gyara zama yana shafa aljihunsa sannan yace "whatever you want, just say it, kin san cewa I can give the world to you idan da tawa ce. I can go to the ....to the..." "End of the earth " ta karasa masa, yace "yeah, right, I can go to the end of the earth for you if you want me to" ta danyi murmushi tana kallon hannun ta, da alama hankalin ta ya fara tafiya wani gurin daban kamar yadda ta kanyi a duk lokacin da yayi mata maganar aure, absent mindedly tace "but earth doesn't have an end, it is spherical" yace "I don't care. Kin dai gane me nake nufi ai. I can do anything for you" bata ce komai ba sai ta juya kanta tana kallon waje, yayin da shi kuma ya rage ido yana kallon ta kamar mai tunani sai yace "but how do you do it?" Ta juyo tana kallon sa tace "do what?" Yace "finish my sentences. You always seem to know abinda yake raina tun kafin in fada" ta danyi kyakkyawan murmushin ta idanuwan ta suna reflecting tarin soyayyar sa da take cikin zuciyar ta tace "because I am your soulmate".
****. ****. ****. ****. ****
"I am your soulmate" yaji muryar ta tayi amsa kuwwa a cikin kwakwalwar sa. Kansa yake ji kamar zai tsage gida biyu. Ya saka hannu ya dafe goshin sa amma kuma sai yaji ciwon kamar a tsakiyar kan yake, amma kuma kamar ba ciwo ba, kamar wuta ce ake hurawa a cikin kan nasa da zafin ta yake saka gumi tsiyayowa daga cikin gashin kansa zuwa fuskarsa zuwa sauran jikin sa.
Ba ciwon kan ne ya fi damunsa ba, ciwon da zuciyarsa take masa ne yafi addabarsa. Wani irin zafi take yi masa mai kama da ƙaiƙayi , gashi tana lullube a kirjinsa dan haka babu damar sosa ta. Ya saka daya hannun ya dafe zuciyar tare da yin ajjiyar zuciya da niyyar rage azabar amma sai yaji tamkar kara kaikayin yayi. Dama wannan shine heartbreak din da ake faɗa, wannan azabar shine abinda yan social media suke wasa da shi har suke kiransa breakfast? Amma lallai duk wanda yayi wasa da wannan to bai taba shiga irin wannan yanayin ba ne ba. Bai taba jin yadda ake ji ba, ba'a taba yi masa abinda aka yi masa yanzu ba.
She was his life. For years, bai taba hango future dinsa ba tare da ita ba. Bai taba ko da tunanin cewa zata iya rabuwa da shi ba because she lead him on, ta nuna masa soyayyar da bai taba tunanin akwai algus a cikin ta ba. Ya gama shirin komai na auren ta. Ya gama plan din komai. A mind dinsa har yayan da zasu haifa yayi picturing din su da kuma irin soyayya da kulawar da zai basu. Gidan da zasu zauna ya gama shi tuntuni. Ita kawai yake jiya, green light kawai yake jira daga gare ta and then suddenly bayan tayi tafiya ta dawo she came to his office da katon ciki a jikin ta and said
"I am married. I have been married for years. I am sorry"
And then she said "it was all a misunderstanding. I never thought you love me. You never said you love me da na gaya maka cewa I am married ".
"Damn it!" ya fada da karfi tare da mikewa tsaye kamar wanda aka yiwa allura. Sai kuma ya dafa bango sannan ya koma ya zauna, bai san ya akayi ba sai ya samu kansa da murmushi. "Ka zare Muhammad" ya fada wa kansa "ta haukatar da kai. Shi kenan ta ka ta kare. Yanzu ma gashi nan kana magana da kanka" sai kuma ya daki goshinsa da tafin hannunsa "damn you" sai kuma ya sake yin wani murmushin. May be haukan will be a blessing. At least in ya haukace gidan mahaukata za'a kai shi ayi tayi masa alluran bacci har karshen rayuwar sa. Then he wouldn't have to think about her. Then he wouldn't have to miss her, miss her smile and laughter, miss the feeling of blood rushing through his body whenever he gets close to her, miss the feeling of excitement whenever his phone rang and he saw her name "Piya❤️".
He already miss tsokanar da take masa, tana enjoying tsokanar sa sosai saboda sunan kakanta ne dashi, she used to say "Malam Muhammadu dan fulani, ka ga yar kyakkyawar budurwa shine ka gudo daga riga ka zo ka makale mata"
To ko wannan ma tsokanar ce?
Yaji wani irin hope ya ratsa zuciyar sa . Cikin sauri ya fara neman wayarsa har yana zubar da wasu daga cikin takardun kan desk din, ya dauka da sauri yayi dialing number din ta sannan ya saka a speaker, a ransa yana karanto addu'ar da bai ma san addu'ar menene ba. Wayar ta shiga amma har ta gama ringing ba'a dauka ba. Ya kira daya layin nata shima ya gama ya katse bata dauka ba. Sai ya kuma kiran na farkon
"The number you are trying to call is not available at the moment....." Ya katse. "Damn it!" Ya sake kira, still the same response. Wani bangaren na zuciyarsa ya fara gaya masa cewa blocking dinsa tayi. "she just blocked you guy" ya fada a fili. "she blocked me" ya maimaita da karyayyar zuciya.
Ba wasan bane ba kenan. Ba mafarki bane ba kuma. Da gaske ne. Da gaske ne abinda tazo ta gaya masa yanzu. Abinda ya gani a jikin ta yanzu.
But how can that be? How evil can she be? Ta yaya zata kasance mai aure through out all zamantakewar su? Ta yaya zai kasa ganewa?
"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun"
Ya fada a fili. He told her that he hates her amma kuma few minutes later babu abinda yake son gani a duniya sama da ita. Babu abinda yake so sama da ita. Babu kuma abinda yake ƙi sama da ita.
Is that even possible?
****. ****. ****. ****. ****.
*Her* 🧕🏻
Nayi kokarin dora thumb dina a ignition amma sai na kasa saboda yadda hannuna yake rawa. Na rike hannun da daya hannun da niyyar bashi support amma sai suke rawar a tare. Sai na hada su duk biyun na rungume a kirjina tare da jan dogayen numfashi sau uku ta hancina ina saki ta baki na da niyyar calming nerves dina down ko dan na samu damar driving zuwa gida, dan na tabbatar idan nayi driving a halin da nake ciki to kuwa akwai matsala ba karama ba, but part of me didn't care about matsala, a percentage of that part even hoped for matsalar, amma nasan in dai har matsalar da nake fata ta faru bisa ganganci ko son rai na to zan hadu da ubangiji na dan shine ya bani rai kuma shi kadai ne yake da ikon karbar ran nawa.
Na sake attempting kunna motar, ta tashi sannan na saka ta a drive na dauki hanyar fita daga school ɗin, a raina ina tabbatar wa da kaina cewa wannan shine ganin da zanyi wa makarantar na karshe kamar yadda na yiwa Muhammad kallon karshe a yau. Absentmindedly na dinga driving ɗin, a hankali kamar mai shiga daki, ba tare da na damu da motocin da suke ta yi min horn a baya na ba, da yawan su in sun gaji da horn din sai su yiwa kansu hanya su zo su wuce ni a guje tare da jeho min kallon banza wanda ko kaɗan bai bata min rai ba. Ni yanzu naci dubu sai ceto.
A hanya naga restaurant din da na kawo Muhammad last birthday dinsa, ranar da ta raba mu rabuwa ta har abada. Na tuna maganar da ya gaya min a lokacin.
"Wata shekarar ba zata zagayo ba Piya in sha Allah sai da ke a dakina" nayi murmushi cikin yarda da hakan "insha Allah" ya bude ido "da gaske? Da gaske kike kin gama jan ajin?" Na lumshe ido na bude tare da langwabar da kai ina kallon sa "zaren nawa naga yana kokarin tsinkewa. Besides, na ga alamar ba zaka iya rayuwa babu ni ba". Yace "exactly. Ba zan iya rayuwa babu ke ba".
Na dauke idona daga kan restaurant din ina kokarin cire tunanin ranar daga raina. In dai har na cigaba da tunanin ranar to ba zan iya karasa wa gida ba, maybe sai dai a karasa da ni.
Ina tsayawa a bakin gate, tun kafin inyi horn mai gadi ya bude gate din, nasan dai ya gaishe ni amma banji me yace ba sai kawai na gyada masa kai na shige ciki. Addu'a daya da take raina ita ce Allah yasa kar in hadu da kowa har sai na shiga dakina, bana son ganin kowa a lokacin, bana son kowa ya ganni a halin da nake ciki dan bana son tambaya.
Sai dai addu'a ta bata karbu ba, ina yin packing naga Yaya Mustapha shima yayi packing a kusa da ni. Na rufe ido na "ya Salam, not him, not now please God" amma ita ma addu'ar bata karbu ba dan yana fitowa daga motar sa direct window na ya taho, ina kallon sa through tinted glass dina ya tsaya ya gyara zaman hular kansa da kuma collar din rigar sa sannan yayi knocking glass din. Na rufe ido na tare da jingina kaina a jikin kujerar motar, "ya Rabbi" na fada a hankali "ya Rabbi give me strength" sannan na kashe motar na bude kofa da sauri na fita.
"Fiyya" ya fada yana kokarin haɗa ido da ni. "Ina kika je haka? Daddy ya tayar da hankalin kowa a gidan nan yana neman ki" sai kuma yayi shiru yana karewa fuska ta kallo "are you okay? Are you crying?"
Tambayar da yayi min ce ta saka na shafa fuskata sannan na kalli hannun, ni kaina ban san kukan nake yi ba sai lokacin na fahimci tun daga school nake kuka har gida. Ban ce masa komai ba na zagaye shi na wuce, har na shiga ciki ina jin idanun sa a kaina.
"God Please... Allah dan Allah.... Allah kasa ba shi bane ba. I cannot take it idan shine".
Sai dana dan tsaya a bakin kofa ina karewa parlor kallo ina lissafin ta inda zan bi yadda ba zan haɗu da kowa ba, duk da cewa ma dai gidan babu mutane sosai dan zuwan mu kenan gari jiya kuma gobe zamu sake barin gari. Kuma babu ma'aikata sosai a gidan tunda ba a garin muke da zama ba.
Babu kowa da na gani, dan haka na fara tafiya a hankali making sure ban making sound ba har na kusa hawa stairs, a lokacin ne naji muryar Esther. "Madam? Are you okay?"
Na runtse ido na tare da kokarin goge hawayen fuska ta amma ina gogesu wasu suka yi replacing din su. Wannan yasa ban juya na kalle ta ba nace cikin muryar da naji kamar ba tawa ba "I am fine. Don't let anyone enter my room" da haka na cigaba da hawa sama ina jinta tana cigaba da wata maganar da ban fahimci me tace ba.
Ina shiga dakina na tura kofa na murda lock sannan na jingina da jikin kofar, a hankali kuma sai na zame na zauna a gurin