Showing 24001 words to 27000 words out of 65973 words

Chapter 9 - HAMRA'UL YAZEEDA by Nusaiba Alkamawa book 1.doc

07 Oct 2025

1026

abinda yake damunsa, daddy yace" insha Allahu za,ayi maganin matsalar.

****
---------waheed baisan Wanda yake kansa ba har zuwa dare bai farka ba, kasan cewar anyimasa allurar bacci shiyasa har yanxu bai farkaba.

******sai cikin dare ya farka momy tashiga toilet Dan yin alwala zatayi sallar nafila.

"**" Ameera ce akusa dashi domin ita tunda aka kawoshi take cikin tashin hankali har zuwa yan xun daya farka.

_______ da kiran sunan Allah ya farka, Ameera ta matso kusa da shi tafara yimasa sannu ,kai kawai ya d'aga domin baya kaunar ganin Ameera ko kadan sabida gani yakeyi ita ce silar faruwar komai inda ba,a bashi itaba to da tuni sahibar sa zai aura wato Jidda a gaskiya ji yake kamar bazai ta'ba son wata ba bayan Jidda jiyakeyi kamar duk matan duniya Jidda duk tafisu.


________To bayan waheed yashafe kwana biyu a asibiti, daddy ya damu akan a sallameshi sabida saura kwana biyu bikinsa hakan kuwa akayi bayan an sallameshi sun dawo gida suna falo suna hira daddy yace" my son waheed yace" na,am daddy" daddy yace "inka gama cin abincin inason ganinka waheed yace" to daddy bayan ya gama yabi daddy part dinsa bayan sun zauna daddy ya kalli ,waheed cike da tausayawa yace" my son inason na tambayeka wani abu kuma banaso kayimin 'karya duk nasan ba halin kabane, nafiso ka gayamin gaskiya .

Waheed yace" to daddy insha Allahu in nasani zan gayamaka gaskiya. daddy yace" Waheed inason ka gayamin menene yake damunka da har yasaka ka kwanta a asibiti harda ciwon zuciya?

Waheed ya d'ago da kansa fuskarsa tayi jawur jijiyoyin kansa duk sun tashi, idonsa yayi jawur kamar garwashin wuta cikin damuwa yace".
______daddy wlhi inason ta baxan iya rayuwa babu ita ba wlhi daddy itace rayuwata.

_____ cikin rashin fahimta daddy yace" wace ita? "Waheed cikin sanyin murya da sarewa yace" daddy sunanta Jidda agidan kawun khamis take, yar kawun khamis ce.

daddy yace"waheed ,waheed yace na,am daddy.

daddy yace" inason kabani labarinta " waheed yace" to daddy ,atake waheed ya gayawa daddy inda yasanta da kuma iyaka abinda yasani akanta wanda khamis yafada masa, saida waheed,yagama bawa daddy labarin sannan daddy yace" kana da tabbacin zata soka kuma kanada tabbacin bata soyayya da wani?
yakamata dai kaje ka tabbatar tukunna nikuma nayimaka alkawarin indai babu wanda take so kuma tana sonka babu abinda zai hana na aura maka ita.

______ cikin farin ciki waheed yace" to daddy amma kuma ya maganar Ameera?

" Daddy yace" maganar Ameera tananan kawai na barka ne kagama farin cikin ka ne sena gayamaka, maganar auren Ameera tananan kuma baza,a daga ba nanda kwana biyu za,a aura maka aure kamar yanda muka tsara nayi maka alkawarin ana gama bikinku da sati daya za,a fara maganar Neman auren ita yarinyar da kakeso yanxu dai kafin bikinka yakamata kanemi yardarta sannan kuma waheed , kaji tsoron Allah kayi adalci a tsakanin matanka karka zalunci koda daya daga cikinsu karkaga kafi son waccan kafifitata to hakika ranar lahira zaka tashi tsagin jikinka yana shan yayye sannan inason kabar maganar Neman aurenka amatsayin sirri inyaso daga baya kowa yasani.

Waheed yaita yiwa daddy godiya sannan yatashi garau dashi kamar ba shine Mara lpy ba yanufi part dinsa yana shiga ya tarar da Ameera aciki rike da net.

- karasowa yayi baicemata komaiba yazo zai wuceta ,tace" yawwa yayana ,waheed yace" na,am tace kaga wannan net din zeyimin kyau tafada tana kara net din a wuyanta.

Cikin ya'ke yace" yayimiki kyau mana cikin farin ciki tace" yawwa yayana Dan Allah zaka rakani unguwa?

- cikin rashin fahimta yace "inafa kenan? Ameera tayi wani farr da ido sannan tace saloon mana, yace OK zan rakaki.

cikin jin dadi tace "yawwa yayana bara naje na shirya waheed yace" haba Ameera kina gani ko gama warkewa ban gamayiba zakice na rakaki inda zaki jirani zuwa gobe to amma in sauri kikeyi kina iya tafiya.

Cikin yake tace" babu komai ai yayana zan jira ai kai za,ayiwa kwalliyar aranta kuwa tace zaka shigo hannu ne


matsowa kusa dashi tayi, tace" yauwa yayana inaso yau muyi hira akan yadda rayuwar aurenmu zata kasance, sabida inaso muyi rayuwa mai dadi mai cike da farin ciki hade da soyayya.

" cikin takaici yace" to naji amma Dan Allah yanxu kitafi kaina ciwo yakeyi .

_____tace to, Yaya amma aranta bataso hakan ba amma babu komai yakusa shigowa hannu, Dan yanda takejin tasha gyarannan saitayi masa yanga ma.

kai kuji karfin hali irinna Ameera ko hakan zata kasance oho=؃?nidai nace kubiyoni kuji yacce zata kaya.

_______bayan ta tafi tashi yayi yashiga toilet bayan ya gama wanka ya Dakko Riga da wando jeans da T- shit yasaka Wando blue T- shit din kuma red ce tayi kyau sosai sai faman kamshi yakeyi ya taje sumar gashinsa sai faman kyalli takeyi, key din motarsa ya dauka Darect gidansu khamis ya wuce .

_____bayan sun gaisa da momyn khamis yayi part din khamis din, khamis yana cikin yin waya shida Asiya yaji ana knocking .

Katse wayar yayi ,ya tashi yaje yace "waye? Waheed yace" nine abokina ,khamis, cikin mamaki ya bude yace" abokina harka warke jiya fa nadawo daga dubaka amma harka fara fita?

* haushi ne Yakama waheed yace" kodai na juya ne? cikin sauri yace "a,a abokina zomu shiga daga ciki.
__ yana shiga suka zauna waheed ya kwashe duk abinda ya faru tun daga rashin lafiyarsa har dalilin dayasashi rashin lpy, dakuma alkawarin da daddynsa yayimasa khamis ya nisa sannan yace "abokina hakika nima naso ka auri Jidda sabida Jidda yarinya CE mai hakuri,ga tarbiyya gata da hankali, amma inajin tsoron abinda zai biyo baya kasan fa momy bata sani ba.

______ waheed yace" Dan Allah abokina inason kabar hango mana matsala ,Dan Allah katashi muje, kashirya.

Khamis yace" to abokina Dan jirani ban wasu yan mintina, khamis yafito a shirye tsab dashi yaci shadda ash colour, yayi masa kyau sosai.

- bayan sun isa harabar gidan suka tarar da momy Dama khamis ya fadawa Asiya Don haka bayan sun gaishe ta khamis yace" momy Asiya tana ciki ne?

***
yafada yana Sosa kai momy tace "tana ciki khamis yasake cewa momy Jidda fa? cikin mamaki momy tace.

_____Jidda kuma kodai tsokanar taka daka saba zakayi ne? Khamis cikin jin kunya yace" a,a .

"momy tace "tana ciki tana kicin tanayiwa daddy girki wai yau so take tabashi mamaki da iya girkinta, tama hanani nayiwa mijin nawa girki.

- cikin bar kwanci takeyin maganar dukansu suka kwashe da Dariya.

** shikuwa gogan namu ya Dada jin dad'i da akace tanayin girki koba komai ya huta da cin nagida Dan yasan yan matan yanxu ba kowace budurwa ce ta iya girki ba.

_________________
________ to bayan sun shiga sungaisa Asiya tasa aka kawo musu abinci.

******
su khamis sai faman santi sukeyi, bayan sun gama cin abincin ,khames yasa Asiya tayiwa momy magana Dama tsakaninsa da momy akwai fahimta suna wasa da Dariya sosai itada khamis din ,momy macece mai son raha da barkwanci da hakuri wasa da Dariyarta har yarantama tare sukeyi.

____ Allah bai bata da namiji ba yara biyu Allah yabata wato Asiya da Jidda tsakanin Jidda da Asiya babu tazara sosai Jidda yarinya ce mai hakuri dason jama,a sabanin yar uwarta Asiya da batasan hayaniya bayan sun kebe da momy.

khamis ya gayawa momy abinda yake tafe dasu sannan yacewa momy waheed zaiyi aure kafin Jidda yayiwa momy bayannin komai akan abinda daddyn waheed yace agame da auransa.

" momy ta gamsu da bayanan da khamis yaxomata dashi sannan tayaba da hankalin waheed da kuma tarbiyarsa.

____ Don haka tace" zata gayawa daddynsu abinda ya gayamaka inyaso seya gayawa khamis abinda suka yanke din.

to bayan sunxo tafiya seda Asiya da Jidda suka rakosu har bakin mota waheed jiyake kamar ya Dauke Jidda ya gudu da ita tsabar irin sonda yakeyi mata.

- khamis yacewa Asiya yakamata mubasu guri su dan gaisa kinsan abokin nawa fa bai iya soyayyaba.

Khamis ya fada cike da zolaya.

********** bayan su khamis sun basu guri waheed ya dago cike da murmushi yace" da farko dai sunana waheed Ibrahim, mahaifina Dan kasuwa ne inada kannai guda uku dakuma kanwa guda daya amma yanxu bata nan zanyimiki bayaninta daga baya.

****
sannan ni Doctor ne ina aiki ne a NTB Mahaifiyata tanada abokiyar zama sannan saura kwana biyu a dauramin aurena na fari .

____a gaskiya Jidda bazan boyemiki ba na kamu da sonki da kuma kaunarki shin nima kina sona?

----- cikin jin kunya ta rufe fuskarta da tafin hannunta Wanda yasha Jan kunshi.

" ai a take waheed yaji ya kara sonta komai nata yana burgeshi tsinto maganar ta yayi tana cewa" to matar dazaka aura fa ?ai nasan kana sonta ko?

" mamaki abin yabashi duk bayanin da yayimata bata rikeba saina aurensa mata kenan akwai kishi ya tabbata idan Ameera taji zai kara aure mutuwa ce kawai bazatayiba katse masa tunani tayi ta hanyar cewa kayi shiru, kodai nayi laifi ne?

" da sauri yace" a,a itama inasonta kowacce da matsayinta agurina sake tambayarta yayi yace''
Jidda kina sona? juyowa tayi ta kalleshi sannan tace............

Comment and share
*_HAMRA'UL YAZEEDA_*


BY *
*_NUSAIBA ALKAMAWA_*


Tiktok* AT NUSAIBA ALKAMAWA

YouTube _NUSAIBA_
*ALKAMAWA*

*PART 13* and 14




___________________________________________
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
=ت? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=ت?
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?
____________________________________________

_________________________________Juyowa ta yi ta kalleshi,sannan ta ce "to Allah yabamu zaman lafiya. tana gama faWi ta yi ciki da gudu, alamun jin kunya.

____ bayan sunyiwa Asiya sallama suka nufi gida a hanya khamees ya bawa Waheed number Win Jidda, bayan ya sauke khames ya nufi gida

*****

byan waheed ya koma gida ya sauya kayan bacci ya Wauko phone Winsa, ya kira wata number , wajen sau uku ya na kira ba'a 'Wauka ba sai da ya fidda rai sai kuma ya ji ?arar shigowar sa?o ya na dubawa ya ga ansaka please yi ha?uri zanzo gareka,

murmushi ya yi, sannan ya juya baya ya kwanta after 5m ya sake kira sai da ta kusa katsewa sannan aka Waga, wata sassanyar ajiyar xuciya ya yi, ya ji daddad'ar muryarta ta da ki kunnensa, ha?i?a Jidda tana saukar masa da nutsuwa ko da tunota ya yi,

*******
sallamarta ya amsa mata sannan ya ce "Hi baby hope you are Fine.?" ta ce "wallahi am fine and u.?" "Ya ce fine My happiness." sunan da ya fad'a ya yi matu?ar burgeta, a haka suka cigaba da hirarsu mai cike da ban sha'awa

******Waleeda******

_____Cikin sauri Walida ta ke tafiya, ka na ganinta kasan a firgice ta ke, da gudu ta ?arasa gida domin ta je tafad'i abinda idanuwan ta suka gani, da ya yi mugun firgitata, batare da tayi sallama ba ta kutsa kai cikin gidan tana kwala kiran, Mama! Mama!.



-Abinda ta ga maman tana yine ya dakatar da ita da ga kwala kiran sunan Mama da takeyi, cikin sauri ta fito daga Wakin tana hawaye wato abinda tagani d'azu da ya yi mugun firgitata baikai kwatan kwacin abinda idanuwanta sukayi tozali dashi yanzo ba, wa'iyazubillah!

********
Tunanin halin da Iyayenta suka jefa kansu a ciki ta keyi, tambayar kanta ta farayi, "shin wai dama haka Iyaye suke kasancewa ko kuma iya nata iyayen ne kawai suke a haka? abinnan ita kanta tasan babu kyau aikatashi bale kuma Iyayenta da suka haife ta, tunda ita ta san aikata abin nan babu kyau to ta ya za'ace su basu sani ba, tasan cewa sun fita hankali da tunani, ga ilimi dai-dai gwargwado suna dashi amman sunsan cewa Allah ya haramta yin hakan, kiran da ta ji ana yimata ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula,


"Waleeda yaushe ki ka dawo? ya kuma ki ka zauna anan.?" Katse Maman Walida ta yi ta hanyar cewa, "Mama wai dan Allah bazaku daina wannan banzar Wabi'ar da ku ka Waukarwa kanku ba? wallahi Mama nagaji da wannan halin naku, idan har baza ku dai na ba, ina mai tabbatar muku da cewa zan gudu daga garin nan, na huta da ba ?a?en maganganun da mutane suke yimin na rasa mai ya sa ku ke aikatawa bayan kunsan babu kyau ta ?arshe maganar cikin zubda hawaye,



Wata uwar ashar da naji sai da ta sa al?alamina faduwa da taimakon Khadijah da ta mi?lmin ya sa har nake ci gaba da baku labarin, amman abinda ya fi bani mamaki shine, Walida tana tsaye babu alamar ma zagin ya shige ta domin ta saba jin fiye da hakan a gurinsu, fita soron gidan tayi, tabar mahaifiyar ta a wajan don ta ga yau kuma me Yaya Waleed ya yi?

"tana ?arasa fitowa ta ga police ya ri?esa da karfi, shi kuma sai banka musu uwar ashariya ya ke me had'e da muzurai, tsabar takaicin da ni ke ciki ya sa na kasa magana sai ruwan hawaye da yake shatata a cikin kwayar idanuna zuwa kan kumatu na kamar an bude fanfo na bakin cikin halin da family na suka jefa kansu aciki;



"Kai ku sakar min yaro mana, sai a biya ku kudin ku." cewar Mama da ta fito hannunta ri?e da sigari tana zu?a, Baba ne ya shigo a hargitse domin har anje majalisar su ankai masa rahoto, "Ku sakar min yaro, ku faWi nawa ne kuWin ku a biyaku." Waya da ga cikin police Win ne ya ce, "Alhaji kayi hakuyri, amma maganar bazatayu anan ba, dole sai munje police station ,saboda munanan aikinsa ya yi yawa a wajanmu, shi ya sa mai gidanmu ya ce mu taho da shi, saboda munanan aiyukan sa ya ci ace ya na gidan yari, amma saboda alfarmar da muke muku ne yasa hakan bai faru ba."


Bud'ar bakin Mama sai cewa ta yi, "ohh ni Maimunatu akace ku faWi nawa ne kuWin ku a biya ku, amma kunawa mutane wani zance daban." Waya da ga cikin police Winne da ya fara fusata, ya ja hannun Yaya Waleed ya turasa cikin mota, sannan ya ce "malamai kawai ku samemu a station." ci kin sauri Waleeda ta sha gabansu, idanunta na zubar da hawaye ta kalli Yaya Waleed, "Yayana ina fatan da ga wannan laifin bazaka sake aikata wani laifin ba, ina ro?on Allah ya shirya mana kai." ci ke da tsanin bacin rai Waleed ya ke kallonta, "kinga Malama da kata, ai garani sau dubu akanki, badon ke ba da tuni *IYAYEN MU* sun zauna lafiya amma duk wannan halin da suka tsinci kansu a ciki kece sanadi." ya na ?o?arin ci gaba da magana ya ji anja motar basu tsaya ko ina ba sai a police station,


*********
Ni kuwa cikin mutuwar jiki na Webi y'ammatan kafafuwana na koma cikin gida, kalaman Yaya Waleed na min yawo a ciki kwakwalwata, duk da ya saba faWamin irin haka, amma ni bansan abinda na yi musu b??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a, da Yaya Waleed ya ke ce wa duk ta sanadiyata IYAYEN MU, suka tsinci kansu a haka, kuma inna tambaye sa ya fad'amin sai ya ?i gaya min, suma Iyayena inna tambaye su basuson gayamin,



hayaniyar Iyaye na naji suna zage_ zage akan tafiya da Yaya Waleed da akayi, a kullum tunani na shine ta ya zan gyara su Mama, kullum cikin yi musu addu'a shiriya ni ke, Allah ya shirye su ya kuma ganar dasu gaskiya, kiran sallar da naji anayi ne ya sa na tashi, na je na d auro alwalla sannan nayi salla, na daWe akan sallaya inawa Iyayena addu'a sannan na ta shi, fitowa na yi na ga su Baba a zaune babu alamar ma zasu tashi suyi salla, wucesu na yi na fita domin na je na Wauko Fatima da ga gidan Hajiya Baba, can ni ke kaita domin banaso Fatima ta dinga zama a gida, domin gudun kar Iyayenmu su koya mata irin dabi'ar su, shiyasa ni ke kaita can idan zanje aiki, idan na dawo kuma na je na Wauko ta,




Lissafi na fara yi yau kayan nawa nayi? saboda alkawarin da na yiwa fatima domin ba tada mantuwa yanzu zata samun daru, indai ban siya mata ba,

- tsayawa na yi a ?ofar gidan, shagon Hajiya baba na siya mata duk abinda na yi mata alkawari harna haWa mata da indomie da bobo domin zuwa makaranta, domin su Mama babu abinda suke siya mata, dan inta sune ma kartaje makarantar, bayan na gama siyayyar na shiga gidan bakina dauke da sallama, amsamin sukayi cikin murna Faty ta zo ta rungume ni,

_______nima cikin farin ciki na rungume ta, cike da kewarta ita kaWaice wacce zan kalla na ji daWi kama hannunta na yi, sannan nazauna, aikuwa ina zama ta ce" min "Aunty ina al'kawarina.?"

" Hajiya Baba ta ce" to Fateema kyadai bari mugaisa ko.?"

" Murmushi na yi na ce "ai indai Faty ce sai ka bata hankalinka zai kwanta."
Ungo, na mi?a mata aikuwa da murnar ta, ta karSa, tana min godiya, Baba kuwa kallon mu ta ke cike da sha'awa ita ba ta ta'ba ganin irin soyayyar ya da ?anwa irin tamu ba,


*******
Gaisheta na yi ta amsa cikin fara'a, hira muka fara sama_sama sannan na tashi na ce mata zamu tafi gida domin akwai aikin da nekeso na yi, ta ce na bari sai anjima.

murmushi na yi mata kawai na ce mata ai zandawo gobe, kama hannun Faty na yi, na yiwa Hajiya sallama muka kama hanyar zuwa gida,


______mu na isa na tarar da mama a kan tudun ko far gidan,tana waya da alama wayar mai muhimmanci ce, girgiza kaina na yi ina jin takaici, wai ace Mahaifiyata ce haka, duk wanda ya zo wucewa saiya ganta, gashi kuma bawani kayan arziki bane ajikinta,


Wuce ta mukayi, muka shiga cikin gidan

Amman me???

Yaya waleed na tarar tsakar gidan, banyi mamaki ganinsa ba, saboda duk sanda aka kama shi baya kwana ake sakinsa, saboda manyan mutanen da baba ya ke huld'a dasu,

bance masa komai ba na yi wucewata , saboda na ga yana muzurai don ina masa magana zai huce haushin sa a kaina.

'Dakinmu na shiga na yiwa Fateema

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login