Showing 30001 words to 33000 words out of 65973 words

Chapter 11 - HAMRA'UL YAZEEDA by Nusaiba Alkamawa book 1.doc

07 Oct 2025

1031

jikinta,suna isa kuwa sunyi sa,a, su malam suna cikin rumfa suna karatu, har suka wuce basu kula da su ba suna shiga Hajiya jimmai tana dama koko taji sallamarsu ta amsa cikin sakin fuska.

* Maimuna ta wuce Wakinta ta kwanta batare da ta kula hajiya jimmai ba bare ta gaisheta.

Gaisheta su Yahaya sukayi ta amsa cikin sakar musu fuska harda basu gurin xama,ta cigaba da abinda ta keyi suna cikin hira malam ya shigo ya same su.

Suna hira yayi sallama suka amsa Sannan ya samu guri ya zauna malam yayi gyaran murya yace,

" yyauwa Yahaya ina son yin magana da kai"
Yahaya ya ce.
"toy malam ina jinka malam yayi gyaran murya yace.
" Dama akan maganarka ne Da Maimuna"
ras haka gaban su Yahaya ya fadi,kardai ace Malam yasan abunda suka yiwa yar tasa,Malam ya cigaba da magana.
"Na yanke shawarar haWaku aure kaida Maimuna munyi magana da kawunka Insha Allahu ranar juma,a mai xuwa yau ya rage saura kwana biyar kenan Za'a d'aura auren,zaku zauna a gidana na gangare kafin ka samu naka. Don haka sai kaje kafara shiri nidai sadaki kawai nake bukata."
Tunda ya fara maganar Yahaya yaji tamkar ana kwaWa masa guduma." Mama ce ta tashi cikin tsiwa da masifa irin ta tsofaffi tace.

"Wallahi malam baka isa ba ta ya zaka aurawa yarinyar ka almajiri kuma mara gata bashida komai wlhi bazata saSu ba kam 'Yata sai me kudi da gata Wanda ya gaji arxiki gaba da baya ba fakiriba."


****
Cikin fushi Malam yace "Rufe mana Baki jimmai." makut kuwa tayi sbd tasan Malam Bai iya fushi ba Amman Bata daddara xuba musu harara ba.

Maimuna tana ciki tana jinsu godiya ta yiwa Allah sannan ta tashi tace" Allah nagode maka ya Allah ka rifamin Asiri."

jitayi malam yana cewa tana ina maimunar?

Tashi Maimuna tayi ta fito ta samu guri ta zauna ta ce "Baba gani kallonta yayi yace" Maimuna kinasan ki gama da duniya lpy?"



?aga masa kai tayi tace" Eh baba." Baba yace "To ina son ki kasance ?ata gari mai yiwa iyayenta biyayya, gurin yayi tsit hajiya jimmai kuwa tama rasa mai xatace kawai ta tashi tabar gurin.



*******
malam ya cigaba da cewa "Maimuna nan da kwana biyar zan aurar dake kuma Wanda zan baki ba wani bane face Yahaya ."Maimuna ta ce, "To Baba Allah ya sa hakan shi ya fi alkhairi ji sukaji ance" ba ameen ba...........?

Mama ce ta fito taji Maimuna tana cewa Ameen tayi carab tace ba Ameen ba .


_______Kallon Allah Wa dai kawai Malam ya bita dashi domin a sabo yaci ace yasaba da halin Matar tasa ,yayi fadan yayi nasihar amman duk abanxa ,har yanzu Yana mata addu'ar shiriya .

shikuwa Yahaya Duk ya rasa me yake yi masa dad'i tashi yayi yace" malam ni zan wuce gurin aiki isha Allahu zanyi kokari iyaka iyawata naga nasamu koda hayar gida ne tunda naga a kudin hayar gidan hayi ake wasu bukatun azumi Dana sallah malam yace "haba Yahaya karka damu kanka kaje kafara shiri kawai yace "to ngd .

Dauda ma bin bayansa yayi ,Maimuna ma ta tashi tashiga d'aki, Malam ya cigaba da lazimin sa ,mama kuwa sai faWa take ta inda tashiga batanan take fita ba Amman yayi mata banxa .

Kai Da yagaji da maganar tata ma tashi yayi yabar mata gidan .


Ba irin huWubar da uwar Bata yiwa Maimuna ba akan ta bijire umarnin mahaifinta, Amman fir Maimuna taki yarda sbd tana matukar son Yahaya a cewarta daya daga cikinsu ne ya dace daya aureta Amman ita kokaWan Dauda baiyi mata ba ,shiyasa tazaSi Yahaya,domin su rufawa juna asiri.

______Haka mahaifiyar tata ta ha?ura Amman cikin xuciyarta bata so, taso ace Maimuna ta auri Mai kuWi yacce itama kanta xata huta haka dai ta xubawa sarauntar Allah Ido.


Haka aka Waura auren Yahaya da maimuna aka kaita gidan mahaifinta Wanda ya basu su xauna
Sunci amarcinsu balaifi Yahaya Yana kula da Maimuna,tana cin abu mai kyau,Amman ?alubalen da tafara fuskan ta shine,babu daman yabarta ta fita ita kaWai sai yace" bai yarda da ita ba ,ko Kuma yaga Dauda yaje gidan sa baya nan sai labari yaji to a ranar fa babu xaman lafiya saboda acewar sa daga Dauda har Maimuna bai yarda dasu ba ,haka Maimuna xata sha kukanta ta more,tana nadamar abinda yafaru da ita ,gashi dai sune suka fara saninta a matsayin Wiya mace Amman bai yarda da ita ba ,illar bawa saurayi budurci kenan.



"Kuma bakowa bane ya jani a wannan matsayin ba face,mahaifiyata Nima Kuma na biyewa kwadayi da son zuciya.


____Yahaya ya fara sauyawa Maimuna dama ashe, da dokin amarci ne yanzu kuwa ta zama yar gida ,kullum suna cikin faWa itama da yake Maimuna wajan rashin kunya ba daganan ba yasa duk abinda ya faWa mata sai ta mayar masa shi kuma abin ana ?ara Kona masa rai, shiyasa yake ?ara jibgarta tun Bata ramawa har itama tafara ramawa Amman me ?

_____sai Yahaya yafara mata horo da yunwa ,anyi musu sulhu Amman Ina abun sai ?ara gaba yake yi idan takai ?ararsa gurin mahaifiyar ta kuwa dariya take mata, kota ce ta ka she aurenta taxo ta auri mai kudi,akwai ranar da take faWawa Maimuna haka, shi kuma Malam yana bakin ?ofa yana jinsu aikuwa cikin fushi ran maza ya Saci,yace" idan ta kuskura tabi maganar mahaifiyar ta kuwa zai sallamata wa duniya ita .

*******Aikuwa tun daga Jin furucin mahaifin nata yasa ta nutsu ta daina Waukar maganar mahaifiyar tata .

Wannan kenan!!.



Na cigaba ko na tsaya ??

Godiyata gare ku masu yimin sharhi in Godiya da ?warin gwiwar da kuke bani =?
?>?p?

Karku manta daga
_NUSAIBA ALKAMAWA

_Ne_Plx comment and_ _share_
*hamra'ul yazeeda*



*BY NUSAIBA*
*ALKAMAWA*

Wattapad :*nusaiba alkamawa*

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
=ت? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=ت?
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?


*PAGE* 17


________ A haka rayuwata cigaba da tapiya Maimuna da Yahaya dai zaman ha?uri sukeyi da junansu inda Yahya yanzu kasuwan cin sa ya cigaba yanzu har fita yake yi yana shigo da kayan maye daga waje.

Yahaya yanxu shima ya fara shaye-shaye ta dalilin Dauda abokinsa da wasu mutane da suke haWuwa suna rabawa manyan mutane, kayan maye yanzu Yahaya har Club yake zuwa, haka ya sai wani madaidai cin gida mai kyau yana da mota a yanzu ga kuma baby's dinsu shida Dauda wanda acewar su abokanan shanawarsu ne.

* Dauda har yanxu bai yi aure ba yace "shi matan waje sun ishe sa, ana haka, Allah yabawa Maimuna ciki, ta haihu lpy yaro yaci suna Waleed .

***
Kwanci tashi yaron wajen Yahaya ya fara wayo don haka Yahaya ba kasafai yake dukan Maimuna ba, don da, abu kaWan idan tayi masa sai ya fara dukan ta, tun Maimuna tana kai ?ararsa wajen malam har ta daina sabida indai ta kai ?ararsa sai malam ya kirawo shi yayi musu nasiha, wanda hakan nema yasa Yahaya yake ?ara suburbuWarta, yake yin abinda yaga dama.


____ yanxu Yahaya har ?ammata yake kawo mata cikin gida in tayi magana sai yayi mata dukan tsiya.

* wataran ma haka zai fita bai bata kudin abinci ba.

* wata rana yahaya yaxo da abokin sa, mai suna Zakari, Zakariyya yaga Maimuna ya yaba da surar da Allah yayi mata don haka ya nuna kwaWayinsa afili,ya shai dawa Yahaya.

________yahaya ya amince masa da bu?atar akan cewa shima zai bashi matarsa ya Wana (wa iyazibillahi ya Allah ka tsaremu daga faWa wa Sharrin zina>?2?Amin)
haka kuwa akayi Yahaya ne yafara mu,amala da matar Zakariya sannan daga baya yabashi damar yin amfani Da Maimuna.

***
Maimuna tana cikin bawa Waleed abinci, Yahaya da abokinsa suka shigo haka Yahaya babu kunya babu tsoron Allah ya shai dawa Maimuna abinda yakawo xakariyya gidan.


Da farko kin amincewa tayi amma Da taga zai yi mata irin dukan daya saba ciki kuwa harda saki haka yasa ta amince sbd idan ya sake ta ba wanda zai iya auren ta a haka.

Cikin kuka tace "na Amince".

******
Yahaya ya ?auki Waleed ya fita dashi haka ta naji tana gani xakariyya ya keta mata mutuncin aure a ranta ji take yi kamar ta mutu ta huta, Zakariya saida yayi amfani da ita wajen sau uku saida ya tara mata gajiya, azaba kuwa babu irin wacce bata shaba bayan ya kammala Yahaya ya ajiye mata Waleed suka fita, tun daga wannan ranar Zakariya yazama tamkar mijin Maimuna kullum sai ya sadu da ita hakama Yahaya kullum sai ya nemi matan banxa har giya yana sha Maimuna, kuwa idonta ya DaWa budewa ta zama abar kwatance Domin kuwa Maimuna, A yanxu itama zamu iya cewa tabi sahu sau biyu Zakariya yana yi mata ciki tana zubarwa, sai ya zama na ita da Yahaya sun mai da gidansu gidan karuwai kullum sai ya kawo ?ammata .


haka itama tana kawo duk gardin da taga dama gidan suyi shaye-shayensu da zina ce-zina censu a haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya.





________malam kuwa labari ya isar masa akan abinda aka ce masa ?arsa tana aikatawa a lokacin daya kirawota ya bayyana mata abinda ake cewa, ta karyata.


************
Malam Dai kullum cikin yada masa da magana akeyi hakan nema yasa yau ya yanke shawarar zuwa gidan yar tasa Batare da sanin taba, bayan malam yaje masallacin juma,a yadawo ya wuce gidan Maimuna, bayan yaje yatsaya a kofar gidan yana ta faman yin sallama amma shiru ba'a amsa ba .

******
yana tsaye sai yaga Wizi ya fito daga gidan ya mi?a masa hannu sukayi musabaha malam yacewa Wizi

Dan Allah bawan Allah masu gidan suna ciki?

" Wizi da Maimuna ta gama Sata masa rai saka makon saurayin ta da yazo ta shareshi cikin jin haushin maganar yace" kai! Dalla tsoho karka cika min kunne in kaima kwarton ta ne to ka shiga wata ?ila idan kana da kudi ta kula ka .

"yana gama faWan hakan ya juya, yabar Malam A Daskare a wajen .

yana tsaye yana fargabar abinda zai tarar Dan yanzu ya fara tsorata da lamarin yar tasa Malam Daya gaji da tsayuwa kawai yayi shahada yashiga yana shiga mai zai gani?

Maimuna ce zaune akan cinyar babson tana shan wiwi ta nannaWe takarda sai faman zuka takeyi Malam tuni tsayuwa ta fara gagararsa kafafunsa suka kasa ?aukan sa ji kake kummm Malam ya yanke jiki ya faWi da sauri suka juyo Domin su harga Allah basu kula da shigowar sa ba cikin sauri Maimuna ta tashi da gudu tayi kan Malam tana kuka tana jijjigashi jitayi baya numfashi cikin tashin hankali tayiwa babson magana.

tace" Don Allah babson ka taimaka mu kaishi asibiti wlhi baya numfashi babson da yaketa faman zukar shisha dinsa ya tashi yace kamashi mu fita dashi Musashi a mota kamashi sukayi suka sakashi a mota sukayi asibiti dashi emergency akayi dashi ana bashi taimakon gaggawa amma ina da kyar suka samu likitocin suka samu numfashinsa Amma da oxygen yake shakar numfashi .

malam saida yayi kwana biyu kafin aka samu ya farka malam yana farkawa da sunan yarsa ya farka Mama ce agurinsa da kyar yacire oxygen din yace" maimuna, Mama cikin kuka tace" bara na kira wo maka ita .


*******
cikin sauri taje wajen ma, aikata Waya daga cikin su ta kirawo mata Maimuna kasan cewar Maimuna ta bawa matar number din ta koda za,a bu?aci wani abun na kudi.

______maimuna ta naji ance ya farka tayi sauri ta shirya.

ta shirya waleed ta nufi asibitin tana zuwa ta tarar Malam yana wani irin tari sai da yaji ma yanayin tarin sannan yayi mata alama da tazo tana xuwa yace" maimuna kiji tsoron Allah Duk abinda kike yi yana kallonki kuma yana jinki Don Allah ko bayan raina kiyi min alkawarin ko ba yanzu ba ko nan gaba zaki dena wannan saSon Allah da kikeyi cikin kuka tace baba...........



_______ insha Allahu zan Daina , Malam da jin hakan ya rafka salati rai yayi halinsa innanillahi wa inna ilaihi raji,un kullu nafsin za ikatil maut Malam ya riga mu gidan gaskiya sai dai muce Allah yajikansa yayi masa rahama yasa in tamu tazo mu cika da imani da kyakyawan karshe Ameen.

* ya Allah kaji?an malam ba,a dau wani lokaci ba aka gama cike-ciken da za,ayi aka basu gawar malam Domin suje suyi masa sutura, A gaskiya tunda nake ban taSa ganin mutumin da yayi jama,a irinta Malam ba,anyi Jana,izarsa a babban masallacin malam ja,afar da yake Dorayi babba.

* bayan ankaishi makwancinsa haka akaita karbar gaisuwa masu kudi sunata kawo sadakar abinci da ruwa, ahaka har aka gama zaman makoki, bayan rasuwar Malam Maimuna tadaina yin zina Amman bata fasa yin abinda takeyi ba na xuke _xuke Mama tayi faWan amma a banza Abinda Maimuna takeyi yasa mama hankalinta yayi mugun tashi, ni kuwa nace duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwan kan duka.

_____ bayan rasuwar malam Da shekara Waya Maimuna bata fasa yin abinda take yi ba mama tayi faWan amma a banza Abinda maimuna take yi yasa mama Dole tasa gidansu a kasuwa tasiyar dashi anan unguwarsu Maimuna tasamu gida tasiya mai Waki biyu da katon tsakar gida Sun raba ?an sauran abinda malam yabari ciki kuwa hadda gidansu Wanda yasaka yan haya sun siyar dashi sun raba kudin kasancewar Malam bashida yan uwa shi kadaine, wannan kenan

_________ Kwanci tashi babu wuya agurin Allah haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda abubuwa da Dama suka faru ciki kuwa hadda kama Su Dauda da akayi shida abokan kasuwancin sa da ogansa, Allah ne yatemaki Yahaya alokacin banda shi aka ?ebo kayan bayan binciken da ?an sanda sukayi ne sun tabbatar da abinda ake zarginsu Don haka aka mi?asu gidan yari da wa,adin da aka diba musu, to tun daga wannan lokacin Yahaya ya fara rasa kuWi yau ya sai da wannan gobe ya saida wancan hatta motarsa saida yasiyar da ita da yaga ya rasa mafita sai ya koma bi???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n abokansa yan siyasa yana yi musu dilar ?an mata suna biyansa.


* da akwai wani lokaci da Yahaya ya kaiwa sanata wata yarinya wacce bada Amincewarta ba bayan sanata ya gama Sata yarinyar tayi kokarin tona masa asiri ya kasheta.

tundaga lokacin Yahaya yake tsoron kai wa wani ?ammata Don haka ya yanke shawarar Neman aikin yi, cikin sa,a kuwa yasamu aiki a abuja ta hanyar wani abokinsa, aikin shine zai dunga kai yara makaranta yana ?akko su ,gidan alhaji jameel Musa kenan inda yake dawo wa gida duk karshen sati.

To yahaya baya nuna Dabi,arsa ta asali yana Soyewa idan zai kula yan matansa sai ya koma kano yakeyi sabida kar alhaji jamel ya kore shi alhaji jameel yana da matansa guda biyu , Hajiya aunty sai Hajiya momy, Hajiya aunty ita ce uwar gida.

Sannan hajiya momy ita ce amarya, yaran alhaji jameel su uku ne banda yaransa maza guda biyu da suka rasu a yanxu haka, hajiya momy tana da wani cikin" wannan kenan bayan Yahaya yakai yara makaranta ne yake dawowa kasan cewar anbashi Daki a gidan inya dawo ne yake siyo kayan bushe- bushen sa ya shiga Wakinsa yasha abinsa babu Wanda ya lura da hakan a gidan.

Wata rana, Hajiya aunty tana Neman Wanda zai binne mata Abu a gidan seta yanke shawarar Neman Yahaya Direba, tana shiga Wakin ta sameshi yana ta shaye-shayensa Yahaya yana ganinta yafara bata hakuri tayi shiru tunani takeyi aran ta, wannan Damace a gareta. Yahaya yana cikin bata hakuri yaji ta bushe da Dariya.


* mamaki ne ya kamashi" ji yayi hajiya aunty tana cewa karka Damu Dama wani aiki zan baka.

tabashi kudi tace" yaje ma?abarta ya binne mata , Yahaya kuwa ya karSa yayi tafiyar sa yana fita ya yanke shawarar ya wuce kano tunda kuWin data bashi zai isheshi yadawo a yau yanaso yashana da ?anmatan sa Don haka ya ?akko wayarsa yakira alhaji yasanar masa cewa matarsa CE ba tada lpy.


* alhaji jameel mutum ne mai karamci da hakuri da tausayawa na kasa dashi shi yasa duk Wanda yayi aiki a ?arkashinsa yake jin dadi, alhaji yace" masa to yagaishe su zaisa a ?akko su, Yahaya yanajin haka yaji dadi sosai Don haka abinda hajiya tabashi ya binne ma bai binne ba yabarshe awajen yayi tafiyarsa.

*******
to bayan Yahaya ya tafi Alhaji da kansa yaje ya ?akko yaran nasa daga school bayan sun dawone suka tarar da hajiya momy tana nakuda hankalinsa yatashi a take ya Dakko mota asabe mai wanke- wanke ta taimaka masa suka kaita asibiti sunata faman zarya kimanin mintina talatin da kaita cikin ikon Allah ta haifi kyakkyawar yarinyar ta mai kama da Alhaji sak yarinyar har tafi sauran yaran kyau duk kyansu da ake gani sai aka ga ashema su ba kyawawa bane Alhaji jameel ya ?auki babyn bayan an sallamesu yana rike da ita har suka isa gida suna zuwa yayi mata huWu ba da sunan maifiyar sa wato aishatul humaira Amma za suna kiranta da haneefa wannan zaSin Brothers dinta ne tunda aka haifi haneefa suke bata kulawa har faWa sukeyi wajen Waukarta wannan kenan.

_______
bayan kwana hudu da haifar haneefa kowa a gidan yana sonta banda hajiya aunty wacce ta ?auki karan tsana ta ?orawa haneefa acikin kwanaki hudu da haifarta Yahaya ma tunda ya ?auki yarinyar yaji tashiga ransa sosai.



Share and comment
*_HAMRA'UL YAZEEDAH_*




*_STORY And WRITTEN_*
by
*_NUSAIBA_ _ALKAMAWA*_
( *Aunty Nusee* )

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
=ت? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=ت?
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?



WhatsApp no 09028903887

*Page

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login