Showing 18001 words to 21000 words out of 65973 words

Chapter 7 - HAMRA'UL YAZEEDA by Nusaiba Alkamawa book 1.doc

07 Oct 2025

1026

tayi ba kuwa kamar kasaceta ,kallon inna tayi tace "bara taje Sangaren mommy,adawo lpy inna tace mata,. Ta amsa da Amin sannan tafita parlour'n mommy ta nufa ganin mommy tana lazimi yasa ta salallabo tabayanta ta rufe mata ido itakuwa tasan kowace hakan yasa tace yata takaina saukar yaushe?",dariya hamrat tayi tace ya'akai kika ganeni mommy?",uhmm taya bazansan kebace ai nasan yau zaki dawo kuma naganeki da wannan kamshin turaren naki,zama hamrat tayi jikin mommy tace mommy na kinwuni lpy,?"lpy qlau hamrat ya karatu?, alhmdllh mommy, nan dai itama sukaita hirarsu, mommy ce tace hamrat kije kigaida yayanku yana part dinsa baya jin dadi.


"kai mommy kinsan dai halin yaya mufeed yanxu ina zuwa zaimin muguntar daya sabamin,girgiza kai mommy tayi tace koda yana miki mugunta yakamata ace kinje kin dubasa kinga yayan kine.

",turo ?aramin bakinta tayi tare da mikewa ,ta nufi part dinsa bedroom dinsa tanufa dai_dai time din da take bude kofar shima dai_dai time din dayake fitowa daga toilet,daure da towel a west dinshi dayan kuma yana tsane kyakkyawan laulausan Sakin gashinshi daya danyi tsayi kadan.

________,jin anturo kofarshi yasa yajiyo dan ganin wane dan rainin hankalinne zai shigo masa kai tsaye, dan yasan su momy basa masa haka .

",ita kuwa hamrat tun lokacin data ganshi ahaka gabanta yafadi tayi saurin juyawa baya.

" takowa yayi cikin tafiyarsa ta isa da takama yatako inda take chafko lallausan bakin gashinta yayi,ya ce Wacece ke?


___________ Tatsinkayi daddadan kuma sanyayyar muryanshi, kwallace tafara taruwa a idanunta sbd azabar zafin data keji akanta Dan rikon da yayi mata bana wasa bane ,ganin kamar bai gane taba yasa taki juyowa,n..i ni sunana rahama yar kawar mommy ce ita tace nazo na duba ka ance bakada lpy, yaji murya mai zaki yadaki dodon kunnanshi,kawar da tunanin yayi ta hanyar cewa kuma sai akace ki shigomin daki kai tsaye babu knocking ko?

"Dan Allah kayi hakuri,tsaki yasaki yanamai sakinta yajuya,itakuwa saurin fita tayi tana haki saida ta tsaya ta daidaita nutsuwarta tukunna takama hanyar komawa,.

______Sangaren mommyn takoma,ganin bata parlour'n yasa ta ?arasa bedroom dinta ganin ta tayi zaune kan bed dinta tana danna waya.


",karasowa hamrat tayi ta rumgume mommy tare da fadin mommy naje na dubashi, murmushi mommy tayi tace koke fa yata, yauwa mommy bara naje gun innata Kuma inason ma naci abinci,tana fadar haka tafita bata jira amsar da mommy zata bata ba,ita kuwa mommy murmushi kawai tayi ta cigaba da abinda take,part din inna tahuce tana shiga ta tarar da abincin ta zama tayi tanaci,har inna tazo tazauna akujera.

" murmushi hamrat tayi,ganin tana ci tana murmushi yasa inna cewa, waini takwara murmushin me kike kodai Wan hameedun kike tunawa,uhm inna wlhi yaya mufeed ne yaban dariya shiyasa kikaga inata zuba murmushi,tsuke fuska inna tayi tare da shirin mikewa ,yasa hamrat cewa inna ina zaki?


zanje wajan mufeen mana nasan harya fara takura miki daga dawowarki shiyasa gwanda naje na feeceshi.

haba inna nifa bafa wani abin yamin ba,nan dai hamrat tabawa inna lbrin abinda yafaru Wazu da mufeed,itama inna abin yabata dariya tace kaji dan nema aikuwa bazamu fadamai kinxoba.

" Wlhi kuwa inna karki faWamai har sai yagane da kanshi Dan banama so muhadu yanzu, Khalil ne yashigo rike da waya ahannunshi mikawa hamrat wayan yayi tare da fadin uncle din kune,karSa tayi tahuce daki,shikuwa zama yayi suka fara hira da inna,ita kuwa fadawa tayi kan bed tana fadin hello habiby ,nannauyan ajiyar xuciya yasauke yana fadin meyasa dakika sauka baki ari waya kin kirani ba kinsan halin dana shiga da banji muryan kiba tunjiya,shagwabe murya tayi" sorry habiby wlhi jiya wayan bestyna babu charge kuma yau dana dawo yaya Khalil yana saukeni yafita bai dawo ba sai yanxu dakai kirana.

",uhm shikenan to amma dai kinje fani wani halina rashin jin muryanki ,bazan ?ara ba masoyi, fatan kaje gida lpy ya mom and dad fatan Suma suna lpy,lpy qlau ya inna da mommy kinsamesu lpy?,lpy qlau habiby .

____nan dai sukaita hira daga baya yace zaizo jibi,da haka sukai sallama,yana kashe wayan yami?e yafaWa bathroom Dan yawatsa ruwa sannan yaje Kiran da dad dinshi yake mai.


_________ bayan yafito yadau farar jallabiyarsa yasa yafeshe jikinsa da perfumes mai sanyin kamshi,yana gamawa yanufi Sangaren mom dinshi yana shiga dakin yatarar da dad tare da Mom dinsa sai kanwarsa sapiyya Dake zaune kusa da Mom dinta dayake itace auta, zama yayi kan luntsu meman carpet tare da gaisar da iyayennashi cikin girmamawa amsawa sukai suma cikin sakin fuska , yaya hameed inayini? ,sapiyya tagaida yayannata, "murmushi yayi yace lpy lau auta ya school, Alhamdulillahi, dad ne yayi gyaran murya tare da fadin daman nakira kane inaso nacema nazabama matar da zaka aura.


cikin kaduwa hameed "yadago idanunsa baidai ce komai ba dan aqa'idar dad dinshi idan yana mgn bayasan acemai uffan harsai yagama mgnr.

" So natona naga babu wacce tadace dakai sai safnah,tun bayanxuba take sonka amma kake Biris da ita kuma nabaka dama kafito da wacce kakeso amma kaki yanxu kuma nagama yanke hukunci,idan kanada mgn zaka iyayi,Wago da idanunshi yayi wanda suka fara chanja launi,dad daman abinda yasa nadawo inaso nasanar dakai nasamo matar da zan aura,.

"amma babana maiyasa tun tuni danace kafito da ita baka fito da itaba sai yanxu kuma kasan dai bana mgn biyu, cuz kasan dai babanta amininane bazai yuhu mungama mgn dashiba kuma yanzu nazo na chanja.


", Yana fadar haka yamike yayi Waki,dawo da kallon shi kan Mom yayi tare da fadin mom dan Allah kisa baki wlhi Mom inason hamrat bazan iya rabuwa da itaba.


"girgiza kai mom tayi kasan my son duk abinda za'ace dad dinka bazai chanja mgn ba tun asali kai kayi sakaci dakaji mgnrshi da bazaima haka ba nasan ba son safnah kake ba,amman bayadda zakai.


________,itama tana fadar haka ta mi?e suka nufi daki tare da autarta sapiyya,shima mi?ewa yayi jiki babu kwari yanufi part dinsa yanajin kanshi nawani irin sara mashi.


" yana shiga yafaWa bed tareda dafe kanshi dake barazanar rabewa gida biyu.




Comments and share
*_Hamra'ul Yazeeda_*



Na
_*nusaiba alkamawa*_
(Aunty nusee )


Wattpad nusaiba *alkamawa*

Tiktok nusaiba _alkamawa_

YouTube nusaiba *alkamawa*

*Part* 11


_______Bayan kwana biyu .

********
?arar waya ne ya tashi hamrat daga baccin ranar da suke, domin Yazeeda yau ta kawo mata ziyara da yake yau sunsha aiki, shine suka kwanta domin huta gajiya.


*****
sunan uncle Hameed ne yafito Saro_ Saro akan screen Win wayar .

?aga wayar tayi Tace" Allah sarki my King yau bansamu lokaci ba,duk yau banji daddadar muryar kaba.

" duk tana faWan haka ne azuciyarta afili kuma ta amsa wayar tashi,cikin sanyayyiyar Muryar Tata tace "hello" .


Daga Wayan bangaren akace, haba my Queen kinsan dai kinsani cikin damuwa koh!.


_______Turo Wan Karami bakin ta tayi tace "Allah baby Nima nashiga damuwa sosai ,bamu fito da wuri ba daga kitchen shiyasa .

Na matsu naga kyakkyawar fuskar nan taka.

"murmushi yayi yace" karki damu my Queen na kusa dawowa dady ne ma yarike Ni shiyasa bandawo ba. " murmushi tayi tace" ai gwara da dady yayi ma haka kadunga zumunci.


"Aransa kuwa cewa yayi, hamrat kenan baki san me yasa dady ya hanani tafiya ba bansan meyasa dady bayason auren kiba .

Magana take masa Amman yatafi duniyar tunani,baby? hamrat takara ambatar sunanshi da dan karfi.


____Firgigit yayi ya amsa tace" wai tunanin me kake ne inata maka magana naji shuru?.

Murmushi yayi yace" hmmn my Queen kenan inaso nafada miiki wani abu da baki sani ba .


"Ohk baby, inajinka.

Shiru yayi nadan wani lokaci kamar bayasan maganar yace" narasa taya xanmiki wannan bayanin my Queen.

Hamrat ta?ara ?asa da murya tace "haba King karka damu kasanar dani komene.


Uncle Hameed ya sauke wata ajiyar zuciya sannan yace" my Queen dadyna bayason aurenmu dake .

*******
Take taji gabanta yafadi.


Yacigaba da cewa lokacin yayyin mahaifina da sukaje dady baiSoye musu komai ba yace "ke yar Wan uwansa ce marainiya ce ke,kinsan harkai aure bawani boye_boye suna dawowa suka sanar da dadyna shine ya kirani akan cewar danme zanje in dauko wa kaina wata yar kauye marainiya wai yana da yar friend dinsa da yake son hadani da ita yar gata wacce tafiki komai.

Nikuma nadage akan cewar kece zaSina da ke kadai zan iya rayuwa, shine dady yamareni yanzu haka fushi yake dani.


_____Hamrat ta jinjina kai wani abu mai Waci yatsaya mata a ma?ogaro da kewa tayi tace masa "King kenan wannan aiba matsala bace kasani da kai zanzauna kuma watarana insha Allah dady sai yayi alfahari da auren namu Sannan muma mudage da addu'a .


Uncle Hameed nan take yaji soyayyar hamrat ta daWa karuwa acikin zuciyarsa yaji dadin maganar Tata .


Yace" gaskiya my Queen Babu abinda zance ma Allah sai godiya daya hadani dake, ke tadabance acikin mata .

Kamar yadda kake na daban acikin maza koh? cewar hamrat nan dai suka cigaba da hirar soyayya tare da tautaunawa akan yacce xasu billowa dady ya amince da auren nasu cikin sauki har sukai sallama.


Hamrat ta kwanta akan gado kwalla na tsiyaya akan kyakkyawar fuskar nata ahaka har YAZEEDAH tafarka daga baccin ,tace bestyna lpy what happened?

Hamrat ta zaiyane mata komai yacce sukai da uncle Hameed,nan Yazeeda tashiga rarrashinta tana mata nasiha har Allah yasa ta shawo kanta tadaina kukan.


To aranar hamrat haka ta yini babu walwala har yazeeda ta koma gida.



Yau hamrat tashirya tanufi gidansu yazeeda wanda yaya mufeed ne yakaita SBD bin umarnin dady.

Tana zuwa bayan sunsha hira yazeeda taja HAMRA'U suka nufi shopping .

Basu suka dawo gida ba sai wajan hudu suna dawowa kai tsaye bedroom din Yazeeda suka wuce saida hamrat ta?ara watsa ruwa, sannan itama Yazeeda tashiga ta watsa, suna fitowa ko mai basu shafa ba suka saka kaya suka nufi parlour .

Babu kowa a parlourn don haka Yazeeda tace su wuce kitchen Saida suka ci abinci sannan Yazeeda tafara nunawa hamrat abubuwa na kitchen din harda yimata practice.

"Hamrat kuwa sai mamakin Yazeeda take babu abinda bata iya ba na girkin zamani dana gargajiya duk kudin su yazeeda hakan baisa mahaifin nata sangartataba.

Aikuwa basu suka kammala girke _girken ba sai wajan karfe biyar sannan suka koma daki yazeeda ta dauko wani katon gidan hotuna ta ajjiye agaban hamrat .

Hamra'u tace ke" ko gajiya bakyayi to wannan fa ?

Yazeeda ta zauna ta bude saiga wasu hotunanta tana jinjira,da hoton kakannin ta nawajan uwa da hoton kaninta wanda yarasu tana bude hoto nagaba kirjin hamrat yabada wani ras haka kawai taji jikinta yayi sanyi da taga hoton wani mutumi.

Yazeeda tace "wannan shine mahaifina besty hamrat cikin yake tace" Masha Allah ashe shine dadyn namu ina kuma auntyn ?


Yazeeda ta?ara bude wani shafin tace "wannan itace aunty mahaifiyata kenan hamrat ta kalli matar haka kawai taji matar bata kwanta mata arai ba, cikin yake tace ayya Allah yakara masu lpy da tsahon rai .


Yazeeda tafurta"amen .

Hamrat dai taga hotuna sun?i ?arewa tace "besty kinga ankusa kiran sallah ko, arufe hotunan haka .

Yazeeda tace" kinsan Allah tunda nadauko sai kin ?arasa ganin kuwa .

Ai kuwa Saida aka kira sallar magrib sannan Yazeeda ta ajjiye domin sungama gani .


Suka tashi sukai alwala sukai sallah sannan Yazeeda tace" besty Bara naimiki kwalliya.


Hamrat tace' wa zakiyiwa kwalliyar bayan an jima za a zo daukata. Yazeeda tace" nidai Saina Miki haka Yazeeda kuwa tadauko makeup kit tazauna ta tsarawa hamrat kwalliya me kyau.

Karkuso kuga yacce tayi mugun kyau ,abunka da me kyau kuma aka ?ara da wanka ita kanta sai yaba kyan da tayi ,ta,ke Yazeeda ma sai santin kwalliyar Tata take .

"Itama shiryawa tayi Sannan suka nufi parlour.

Tarar da wata mata sukai azaune da gudu Yazeeda taje ta rungume ta tana me murnar dawowar ta, aunty yaushe kika dawo kuma shine ko kifada min .

Cikin soyayyar ?artata aunty tace  ai dama haka nace surprise dinki zanyi shiyasa nayi zamana a parlour nace ina jiran fitowar taki, murmushi Yazeeda tayi tace aikuwa kinyi surprised Dina aunty ga ?awata sunanta hamrat itace wacce nake baki labarinta.


-Cikin fara'a aunty tajiyo da nufin taga hamrat din turus ta tsaya da mamaki shinfide afuskar tata, takasa rike abin acikinta, tace ah Yazeeda yanaga kawar taki kuna Wan kama ne ?

Hamrat data matso kusa da ita tace" aunty ai idan aminantaka takai aminantaka ana kama da juna sosai, tafada haka tana me gaida auntyn.


"Aunty ta amsa babu yabo babu fallasa .

Aunty tace" Yazeeda da ina zakuje da naga kunfito, aunty,hamrat zanraka parking space. "au tafiya zatayi tadanjirani ina zuwa .

Yazeeda tace''to .

"aunty ta nufi daki tadauko wa hamrat kayan gyaran gashi da kuma tsala_tsalan abaya guda uku tamika mata hamrat takarba tana mata Godiya.

Wayarta taji tana ringing sunan yaya mufeed yafito Saro _Saro akan screen din wayar.

Tana daga wa yace "tafito yana waje yana jiranta.

Yazeeda tace "kice yashigo agaisamana , hamrat tace ''sauri yake ne hamrat ta,fadi haka ne dan tasan bashigowar zaiyi ba .

Yazeeda tace "ok tashi muje na gaishe sa.mikewa sukai aikuwa suka hango zabgegiyar motar sa, nufar motar sukai.


Yazeeda ta gaishe sa ya amsa babu yabo babu fallasa.

Yazeeda tace "to besty Allah yasaka da alkhairi kigaida su momy da inna, "duk zasuji cewar hamrat.

Yazeeda tace "yanzu kenan sai a skul zamu kara haduwa eh wllh cewar hamrat.

Yazeeda tajuya ta koma gida. ita kuwa hamrat ta bude gidan baya zata shiga.

Ta tsinkayi muryarsa yana faWin "wakika mayar driver dinki?

"Gidan gaba tabude kawai tashiga dan tasan tujarar yayan nata .

Sunfara tafiya mufeed ya kalleta yace" ina kuka je ?

Dago kanta tayi ta kallesa sannan tayi ?asa da kai tace "babu inda mukaje.

"Kee bansan shirmen banza babu inda kukaje shine kikayi kwalliya?to wa kikayiwa kwalliyar ?.

Banza tayi masa sbd taga tambayar tasa ta rainin hankali ce .

Kee ba dake nake magana ba ?yafada cikin tsare gida .

Wllh naga ranar da zaki ?ara cewa zaki fita.

'',nikuma Saina fita ba.

"Ke wai yaushe kika raina Ni nidama banyarda da wannan fitar naki ba nasan akwai abinda kuka shirya.

"Ai dai Allah yana kallona idan ma sharri kayi min.

Kewai ubanwa yake miki sharrin? Yasa ka hannu yabige mata bakin.

Idanuwanta yaciko da kwalla tace" kuma Allah zaisakamin.

"Kewai babu damar mutum yayi miki faWa saikin mayar da martani? yayita masifa haryagaji yayi shuru.

Yanayin parking tabude murfin motar tayi ficewarta ta tsinkayi muryar nasa yace" ke ubanwa kika ajiyewa kayan ko Ni zandauko Miki ?.

Komawa tayi ta dauko ,ta wuce parlour.

Sallama tayi duk nacikin Wakin suka amsa mata .

Khalil yace" oyoyo sis ?ake kawai tayi dan yaya mufeed yagama Sata mata rai kusa da inna taje tazauna .

Inna tace" keda waye naga kamar fuskar ki babu walwala?.

Aikuwa kamar jira hamrat take ta fashe da kuka .

Hankali inna inyayi dubu to ya tashi babu shiri kuwa ta rungume jikar Tata tana fadin wa yaSata Miki rai?

"Hamrat cikin sheshshekar kuka tace" ba yaya mufeed bane ba yadokeni harda cewa zai ?aryani.

Tana cikin fadan haka daidai lokacin yashigo.

Inna tace" wai me yarinyar nan tayi maka ne kabi ka tsane ta, to wllh Allah saiya sakamata.

"Mamakine yacika mufeed ganin irin sharrin da hamrat tayi masa ita kuma inna tabi kai tazauna.

Khalil yazaro handkerchief daga aljihun shi yami?ata.

Hamrat ta karSa ta share hawayenta.

Mufeed ranshi ya?ara Saci, babu damar mutum yayi mata faWa sai abin yazama Magana zai wuce kenan ,ya tsinkayi muryar dady yana cewa "mufeed dawo kazauna.

Dawowar yayi yazauna.

Dady yace" wato maganar inna ce taSata maka rai koh!?

"A'a dady kawai dai bacci nake jine.

"Dan Allah mufeed kadunga saita zuciyarka kudunga yawaita salatin Annabi s a w .

Inna tace "aikuwa akwai wata addu'a ta sanyayya rai zomuje nabaka kaita karantawa kaji Wan albarka.

"Khalil yayi murmushi aransa yace" inna kenan ayi faWa a shirya .

*******
Inna da kanta taja hannun mufeed din suka nufi dakin tadauko tabashi, kamar basu ne Wazu arana ba.

Dady yace" inna wanda yace zai shiga tsakaninsu kunya zaiji.

Dariya inna tayi tace" ai Ni daman muguntar dayake wa hamra'u ne yake haWani dashi amma ai mufeen na hannun dama nane .

_____Dariya khalil yayi yajuyo ya kalli hamrat yace "kanwata baki bani labarin my wife Wina ba.

Saurin rike baki,hamrat tayi dariya taso kwace mata tace" yaya khalil agaban dadyn?

Dady yace" ai kema hamrat kinsan Khalil bakunya ne dashi ba ,dadai mufeed ne shine zeji kunyar fadan haka, Bara mutashi mubashi guri ,saiki bashi labarin matar tashi daya faWa .

Mikewa yayi yanufi dakinsa itama inna tabi bayan dan nata .

Bayan sun tashi ne hamrat ta ?ara gyara zama tace "yanzu dai bestyna tace wllh bataji dadi ba daba kazo ba kuma tace tana gaida ka .

"Murmushi khalil yayi yace "Allah sarki my wife nayi missing dinta.

To yanzu dai baki mana saurayi acen ba ?

TaSe baki tayi tace" hmmn wani kanin auntyn Yazeeda sukazo da abokan sa daga shigowa parlour munje gaishe sa wani daga cikin abokan yawani tsuramin idanuwa waishi bash .

Tafadi hakane SBD yaya mufeed yaji haushi dan bayason tadunga kula samari .

"Murmushi khalil yayi yana wani satar kallon yaya mufeed dan yaga reaction dinsa aikuwa yaga yawani haWe rai yana danna waya.

Yaya mufeed ya tashi yabar musu dakin.

Bayan yafita ne Khalil ya kalli hamrat yace,"HAMRA'U Yakamata kidainawa yaya mufeed rashin kunya kinga ba sa'anki bane ba ke bakisan

Irin Soyayyar dayake nuna Miki lokacin Nima banfi shekara goma sha daya ba kinmin rashin kunya adalilinki.

Saida yadukeni abinda baitaSa minba kenan ,dan Allah kidainawa yaya mufeed rashin kunya ko yanzu da bakwayin shiri kidunga tuna irin soyayyar daya nuna Miki abaya, kuma ina da tabbacin haryanzu yaya mufeed yana sonki kawai dai rashin kunyar dakike masa ne yake jawowa kuke faWan dashi,kuma kinsan yaya mufeed bayason raini.

"Ita kanta jikin hamrat din yayi sanyi itama kanta tasan da irin soyayyar daya nuna mata abaya kuma ansha bata labarin haka amma yanzu maimakon itama ta mayar da alkhairi Amman sai akasin haka.

"Amma watarana shi yake kulani yayyita min masifa babu abinda namai, nikuma Bazan iya hakuri ba Saina mayar da martani Amman yanzu in Allah ya yarda zandaina koda ya kulani Bazan sake mayar masa da martaniba.

Murmushi Prince Khalil yayi yace tnk U my sis yanzudai abinda za ai kije ki kwanta gashi yanzu jibi zaku koma skul .

Toh yaya Saida safe Allah yakaimu .

"Amen"
Tana shiga part din nasu ta cire kayan ta tashiga toilet daman inna tayi bacci bayan ta fito tasaka kayan bacci sannan itama takwanta


Washegari kuwa dady yasa khalil suje da ita suyi siyayyar makaranta,aikuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login