Showing 15001 words to 18000 words out of 65973 words

Chapter 6 - HAMRA'UL YAZEEDA by Nusaiba Alkamawa book 1.doc

07 Oct 2025

1046

tazararmu shekara daya ne " hakadai sukaita tsokanarta .

Waheed kuwa sai satar kallonta yakeyi harta shige gida bayan tashiga gida ne su Waheed sukayiwa Asiya sallama suka nufi mota.

har sunshiga mota saikuma Khamis yafito hannunshi da wata farar leda katuwa .

Ya kwankwaso kofar get din ,maigadi yana buWewa ya mika masa Leda yace" Dan Allah baba kabawa Asiya.

"baba mai gadi yace to" Khamis yazaro kudi yabawa baba mai gadi " baba mai gadi yadunga yiwa khamis godiya.

Khamis yatafi " yana tafiya baba mai gadi yakaiwa Asiya sakonta " bayan yatafi ta bude tana dubawa taga sarka ce mai Dan karan kyau ta gold kirar Dubai Asiya sabida tsabar murna batasan sanda tafara cewa ba ,"wow my Dear Thank you Thank so much I really love you my lovely khamis.

Saida suka je gidansu khamess sannan Waheed yaWau motarsa yanufi gida .


Hajiya saratu kuwa taje gidan aunty ,aunty tajata PART Winta.

Bayan sunzauna angabatarwa da Hajiya saratu abincin ciye_ ciye bayan taci ta koshi sannan suka fara shawarwari .

Aunty tace" Hajiya Sarah Amira fa tazo ma tana part Win waccen matar bansan manufar dakike da shi akan ameerah ba .

Hajiya saratu tace aure yakamata mu hada Waheed da Ameera ta wannan hanyar CE kawai zamu samu abinda mukeso" .

AUNTY tace wai tsaya hajiya aure dawa wace Ameeran? Hajiya saratu tace Ameeran ki mana" Aunty tace taya kike ganin zan hada Ameera jinina da Wan makiyyata karfa ki manta Ameera yar kawuna CE kuma muna ji da ita taya zan hadata aure da Waheed mutumin danafi tsana kuma Dan kishiyata".?

" hajiya saratu tace daWina dake kenan ?in bin shawara kinsan mene ma,anar yin haka?" to yakamata kisan cewa ta wannan hanyar CE kawai zamu iyayin ya?i da hajiya Nafisa dakuma yaranta .

" Aunty tayi murmushi tace to ?awata inajinki" hajiya saratu tace yauwa kawata kinsan meye hikimata tayin hakan?

Aunty tagirgiza akai alamar a'a .

"inason mu haWa Ameera da wahid aure ne Domin musamu cikon burinmu da mukayi shekara da shekaru muna son cikashi ta wannan hanyar na tabbatar zamu samu cikon burinmu hajiya saratu tacigaba da magana ,.

" abinda za,ayi shine dolene sai kin sakko kin lallaba kishiyarki ta amince da aurannan sannan zaki cusawa Ameera son aurennan Domin karta bamu matsala" Aunty tayi Dariya tace kawata inajinki to me zamuyimusu"?

_______ hajiya saratu tace idan muka haWasu aure zamu bari har sai ta samu ciki ta haihu daga nan saimu kashe alhaji da Waheed ta ruwan sanyi wato zamusa azubamusu guba acikin abin shansu su duka ukun harda kaninsa bayan mun kashe su saimu haukata hajiya Nafisa tabi Duniya shikenan Dukiya ta dawo hannunmu.

Suka she?e da dariyar mugunta.

_WAHEED_

Waheed yana cikin cin abinci adaining area yaji karar takalmi ?waras, kwaras,kwaras,yana juyowa yaga itace kallo daya yayi mata ya Wauke kansa daga inda take ita kuwa farin cikine ya mamaye zuciyarta aranta tace wow ya Allah ka mallakamin wannan bawan naka tana ?arasawa tace" la yaya abinci kakeci Sata rai yayi yace Eh ?arasowa tayi tace yaya xanci shidai wahid yana mamakin hali irinna Ameera ace mace sam batada kamun kai aransa yace kai wannan mijinki yashiga ukunsa tashi yayi yabarmata gurin ya haye sama Dakin momy, yana hawa ya tarar da safwan akan cinyarta yanata shagwaba bai kulashiba yafara gaishe da momy ta amsa sannan suka cigaba da hirarsu duk Dai Rabin hirar da takeyi masa akan yayi ?o?ari yayi aure CE.

*HAMRAT*
Afirgice tatashi daga barcin tana ambaton sunan Allah tare da addu'ar tashi daga bacci ,gumi duk yagama ji?ata babu shiri tashiga toilet tayi wanka tadauro alwala sannan ta fito tayi sallah ,aikuwa tana idarwa ,tadauki littafin zuciyarta tana bugawa na irin abunda tagani a amafarkin ,rubutawa tafara.

More Comments more typing.
`~HAMRATU'L YAZEEDAH~





_Na_
```NUSAIBA ALKAMAWA```
( ```AUNTY NUSY)```



**PART TEN* 10


___________

********
Har sun mi?e uncle hameed yacewa yazeeda yanasan mgn da ita, komawa tayi tazauna ita kuwa hamrat fita tayi takoma hostel dinsu.

"gyaran murya uncle yayi tare da cewa," nasan zakiyi mamakin tsayar dake da nayi,but abinda zance miki daman gskia tunda naga aysha naji tana burgeni daga baya kuma nagane ashe ba 'iya burgeni take ba sonta nake.

_____,kuma bazan iya sanar da ita ba,taimako daya nakeso kimin inaso kisanar da ita.


* dagowa Yazeedat tayi ta kalleshi tace "ba matsala uncle hameed,zan mata magana Insha Allahu,tana faWar haka ta mike tafita.


___________,nannauyan ajiyar zuciya yasauke, tare da Waukan wayarshi yadanna kiran mom dinshi,ringing biyu ta daga, daga chan Sangaren naji ance "hello my son."

_________cikin son mahaifiyar tashi yace,mom barka da rana, murmushi mahaifiyar tashi tayi tace na kiraka bakai picking call ba.


"shagwaSe fuska yayi kamar tana ganinsa yace "mom wllh inayiwa Walibai lesson ne shiyasa banyi picking ba.

" okay yanxu dai saura kwana nawa kadawo?

"mom kinsan sai anyi mus??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????u hutu tukunna.

"Amma my son kasan dad dinka ya matsu kadawo dan yazaSama yarinyar dazaka aur.......

"what? Mom bangane mai kike san faWa ba dan Allah mom kidakatar da dad da wannan abin, kumama daman ma na kirakine nasanar dake nasamo matar dazan aura, amma dole saita gama school tukunna.


____________hmm my son kenan kasan dai dad dinka kaifi Wayane magana Waya yake tunda yabaka daman kafito da mata baka fito da ita ba,yace shizai fitoma dakanshi tunda kayi biris da maganar tashi, ka,Wauka wasa yakema.


"amma mom..dakata nidai bazan shiga maganannan ba idan kadawo kwayi maganar.

_______,tana gama fadar haka takatse wayarta,dafa kanshi yayi yana busar da iska mai zafi daga bakinsa tare da furta ya Allah, Allah ka karkatomin da hankalin dad ya fahimceni.

**********

?angaren yazeeda kuwa! tana shiga taga hamra, ?arasowa tayi ta zauna kusa da ita tace" aunty tashi inason magana da ke mi?ewa HAMRAT tayi ta fiskance ta.

" nan yazeeda ta kwashe duk abin da sukayi da uncle Hamid ta faWa mata, tunda yazeeda ta fara magana hamrat ta sunkuyar da Kai tana wasa da hannun ta, zuba mata ido YAZEEDA tayi ganin tayi shiru batace komai ba.

" taSata tayi aikuwa firgigit ta dago dara_ daran idanunta ta sauke su akan yazeeda .

",tunanin me kike besty naga kinyi Shuru?

" murmushi hamrat tayi tace Sis Yazeedat ni ban San me zance Miki bane shiyasa ki kaga nayi Shuru.

" murmushi yazeeda tayi tace babu matsala dama kawai yace na sanar dake ne.

______ ,nan dai suka canja wani hiran da sauri hamrat ta tashi tana fadin kai ni !!!! Na manta ban shigar da haddana ba .

________wasa_ wasa yau hamrat tayi wata biyu a makaranta a wata na uku ne Yazeedat tace mata za azo visiting dinsu, murna wajan hamrat ba'a magana ta matsu taga innarta da yaya mufeed da kuma yaya Khalil,dan tayi missing din su.

_________Hamrat ta Kara kyau ta Kara girma tsantsar kyawun da Allah yabada ta ya Kara fitowa, dan Yazeedat tana ?ara wayar da ita dan yanxu hamrat ma ta iya turanci ba laifi dan principle din makaranta ma yace za 'a musu jumping saboda ?okarin da suke da shi.

" Za a maida su ss one uncle hameed ya sanar da shugaban makarantan maganar son hamrat dayake shima shugaban makarantan ya yarda Amma yace kar suyi soyayya da zetaSa musu karatu.


" shima kuma ya yarda ya sanar da Yazeedat Yan da sukayi da shugaban makarantan ranan da hamrat taje leason din bayan sun gama leason Win ne yace Yana son magana da ita gyara zama tayi tana fuskantan uncle hameed Win Amma kuma bata Kalli fuskarsa ba kanta a sunkuye yake tana wasa da zara_ zara yatsun hannunta.


" tsintar muryanshi tayi cikin sexy voice dinshi yafara dacewa,nasan abin da zance Miki Yazeedat ta sanar dake zan ?ara mai maita Miki ne saboda kiji daga bakina sai kinfi gamsuwa *Aysha* cikin wata sanyayyar muryan shi ya kira sunan ta ita kanta sai da taji tsikan jikin ta ya tashi !!! Taji sunan ya ?ara mata daWi ba kamar yanda mutane suke faWa ba katse mata tunani yayi da cewa tun farkon fara ganin ki naji kin kwanta min a Rai maganar gaskiya Ina sonki so na hakika Wanda kuma nake fata mu kasance tare da juna na har abada insha Allah wato ma'ana Ina son auren ki inhar kin bani dama hakan .


"shuru tamai bata ce mai komai ba.

" ganin haka yasa yayi murmushi yace nasan bazaki bani amsa ba Amma nabaki lokaci Ina sauraron amsa daga gare ki Yana gama fadan haka yace zaki iya tafiya.

" jiki a sanyaye ta fita shi kuma binta yayi da ido har ta fita ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya karajin sonta na Kara karuwa a cikin zuciyan sa.


______ itako hamrat tana fita bata tsaya a ko ina ba sai dakin su tana shiga taji karan ruwa alamun Yazeedat tana wanka zama tayi a bakin gadon su tana tunani Yazeedat ce ta fito daga wanka daure da towel a jikin ta.

" Kiran sunan hamrat ta farayi ganin ta mata shuru ne alamun tayi nisa a cikin tunanin,.

"matsawa tayi wajen da take zaune taSata tayi firgigit tayi ta dawo da kallon ta kanta tace besty, uncle hameed ne ya tareni da maganar da kika faWa min.

" murmushi yazeeda tayi domin ta gane kan zancen, tace to ke kuma me kika ce?

"Hamra Tace " ba abin da nace masa, kisan dai bazan iya cewa komai ba Ina tsananin Jin kunyar uncle hameed.


"Yazeeda tace"kawai ki amince kinga mutumin kirki ne.

"Hararar wasa HAMRAT ta jefe ta dashi tace "watakam kina goyon bayansa ,ai shikkenan na amince .

Rungumeta yazeeda tayi tace" kai Nagode ?awata aikuwa xanje masa da babban albishir.

*****

Yau takama ranar zuwa visiting kowa sai Woki yake hamrat sai murna ake Amman yazeeda kam, bawani murna da take SBD nata iyayen ba zuwa xasuyi ba Amman aike kam tana sha akai_ akai.

Hamrat tunWazu take ta faman jiran zuwansu inna ,wata ?alar mota ce me kyau ta Kunno Kai parking sukayi hamrat xai zubawa motar idanu take domin duk motar datazo wucewa saita kalleta koxata ga su inna aikuwa akayi Sa'a taga yaya khalil yafito yasha shadda ba?a dayake farine ba?aramin kyau kuwa tayi masa ba .

_______Da gudu hamrat tayo kan khalil ta rungume shi inna dasu Dady da mommy suka fito.

Kan inna hamrat takoma," ta rungume ta tana kukan shagwaSa itama inna ganin jikar Tata tana hawaye itama saita fashe da kukan, rungumeta su mommy sukai suna aikin rarrashinta.

____Shi kuwa khalil tsareta yayi da ido ganin tayi kyau sannan kuma ta?ara girma kamar ba ita ba.


Yazeeda ta?araso wajansu tagaishe su aikuwa Dady da inna harma da ita Saida sukaji wani shok alokaci guda .

"Amsawa sukai.

"Hamrat tace inna ga ?awata Yazeedat Yazeedat tayi murmushi itadai familyn birgeta yayi .


"Inna tace ayya ?ar albarka Allah yayi wa rayuwar ki albarka inna tafaWa haka cike da son yarinyar haka kawai taji yarinyar ta shiga ranta.

Yaxeedat ta amsa da "amen" ,sannan HAMRAT ta nuna mata yaya khalil tace to ga yaya khalil nan da kikejin labarinsa agurina.

Murmushi Yazeedat tasakar masa wanda ya?ara xautar da khalil.

Aikuwa yau naga yaya khalil duk da kuwa ba bakon fuska bane ba waye baisan fasihin mawa?in nan ba, ina kuma yaya Mufeed ?.

______Sai asannan ne ma hamrat ta tuna dashi, nan tafara waiwaye da taga dai bata ganshi ba tace inna ina kuma yaya Mufeed shi baizomin ba .

Dady yace ai Mufeed bayama kasar gaba Waya da dashi xamuzo abokin faWan naki.

Murmushi hamrat tayi tace to muje nabarku atsaye SBD murna .

Aikuwa suka tafi bayan sun sauke mata kaya iri_ iri abinci ne abinsha kayan ciye_ ciye suturu duk dai gasu nan.



Hamrat tabasu labarin irin yacce Yazeedat ta kula da ita sosai aikuwa su Dady suka yabawa kokarin ta wani abun mamaki sukaga Yazeedat tana ?anayi da hamrat ?adan .



*******
?arasawa sukayi suna tafe suna hira hamrat na li?e da inna sunsha hira kuwa uncle hameed ma yazo sungaisa dasu yagabatar dakanshi awajan daddy,aikuwa hamrat tasha tsokana harda daddy shima tsokanarta yayi hamrat kuwa saidai tasunkuyar dakai tayi murmushi.

" mommy sai yaba kokarin Yazeedat take yadda takara gyara mata hamrat,gashi takara kyau sosai dan wanda yasan hamrat ada bazaice ita bace yanxu dan sai yanxu tsantsar kyan hamrat yakara bayyana.

" shikuwa Khalil saida yasan yadda yayi ya amshi number Yazeedat


"?ammata sukaita zuwa wai ganin Prince Khalil shikuwa sai haWe rai yake SBD karsu wuce gona da iri sukaita masa magiya akan suWau hoto hakan nan yadaure sukai hoto wannan yana tafiya wannan yana zuwa daga karshe zama yayi hamrat tabasu hakuri sannan suka tafi suna yaba kyansa ashe duk a hoto da suke ganinshi axahiri yama fi kyau sosai.

______shikuma daddy yayaba da hankalin uncle hameed Kuma yasan mahaifinshi sosai dan mahaifinshi bakaramin mutum bane,hakadai sukaita shan hira kuma sun kawowa hamrat kayan karatu sosai har sukaxo tafiya dakyar aka SanSare hamrat daga jikin inna dan hamrat tace ita saita bisu tafasa karatun saida suka mata wayo dacewa jibi zasuzo su Wauketa yanzun ta shirya kayanta,sannan ta yarda, itama Inna kuka take,haka dai suka tafi hamrat tashige dakinsu takwanta tana rera kuka dakyar yazeeda ta lallaSata tayi shiru.

_________bayan komai ya lafane yazeeda tace" besty yau dai naga Prince yaya Khalil da inna saura yaya mufeed,tabe baki hamrat tayi tace wannan mugun ina zaki ganshi kuma kinsan bamu shiri dashi shiyasa,chemin yake yar qauye nikuma banasan yana chemin haka.


" murmushi yazeeda tayi tace ai shiyasa nagodewa Allah dabai xoba shiyasa nakeso kifi haka wayewa sosai yadda idan yaganki bazai ganeki ba .

",ai daman sis yazeeda bazai zoba koda yana nan ba zuwa zaiba,SBD ba?in ranshi ma baxai bari yazo ba .

Murmushi Yazeedat tayi "tace kawai Allah ya kyauta ,ashe Prince khalil da nadade ina sauraro ina mugun son wakokin shi sosai ashe yayan kine shine baki taSa faWa min ba nidayake bansanshi a fuska ba kawai da muryarshi nagane.

Auf to Ni kuma sainai tacewa yayana mawakine kawai dai tunda yanzu Kinga xahiri ai shikkenan ko.

hakadai sukaita hirarsu.



******
_________ haka rayuwa ta cigaba da tafiya hamrat da uncle hameed sunyi mugun sha?uwa hakama bangaren Yazeedat da prince Khalil soyayya sukesha kamar babu gobe.

" yanxu yazeeda da hamrat suna SS two mlmai da dalibai babu wanda baisan aysha Ibrahim da Yazeedat khalil ba ,danko ta Sangaren kokarinsu ma a,sansu dan idan suka shiga class basa taSayin hausa suda kaga sunyi hausa saidai idan suna wajan kwanansu.


______yau takama za'afaraiwa su Yazeedat exam sosai suka duku fa da karatu dan Wannan exam din tashiga SS three ce, sun maida hankali sosai da haka har suka kammala exam kowa zai kama hanyar gidansu dan daman hukumar makaranta tasanar da iyayen yara kowa yazo yadauki yarsa ambasu hutu.

************
?angaren dady kuwa suna zaune suda Khalil da mommy daddy yacewa Khalil yaje yakira masa mufeed yaje yaWauko hamrat daga makaranta,tashi yayi yashiga part dinsu, bedroom Win mufeed yanufa ganin kofar abude yasa yatura kofar yashiga,,ganin mufeed kwance ya rufe kanshi da blanket yasa ya?araso da sauri, yaya mufeed mai yake damunka?

Yatambaya yanamai yaye blanket din jin zafi yayi,radau ajikin Mufeed Win,dakyar mufeed yanuna mai inda zai Wauko mai magani, da sauri yatashi yaduba drawer din yadaukomai maganin tare da ruwa da sauri yataimakamai yamike yaballomai mgn yabashi tare kwantar dashi yalullubeshi.


"yafita dan sanarwa da Dady cewa yaya mufeed baida lpy ,Yana ?arasawa parlour'n dady, yacewa dady yaya mufeed baida lpy,jinjina kai daddy yayi yace,amma dai yasha mgni ko?

"yatambayi Khalil,eh dady saida nashiga nabashi ."ok to Allah yakara sauki, daman abinda yasa nace kakiramin yayanka sonake yaje yaWaukomin mamana daga school,amma yanxu kaikaje kaWaukota kabimin mamana ahankali dankai idan kasami mota gudu kake da mutum.

"sosa kai Khalil yayi yace daddy bazanyi gudu da itaba,yana fadar haka yamike da farin cikinsa don daman yadade baiga yazeeda ba yanaso yaje yaganta,shiryawa yaje yayi tukunna yafito yayiwa daddy da mommy sallama sannan yafita, yana isa mkrntr yayi parking .

Wannan ?aronma ?anmata sukai mai ca akan yabasu number wayar shi,har saida yabasu sannan suka tafi .

_______hango hamrat yayi atsaye da akwatinta,fitowa yayi aikuwa hamrat ganin yaya Khalil yasa ta?araso da murnan ta," yaya Khalil tundaxu naketa jiranka harma anxo antafi da bestyna,tafaWa cike da shagwaba.


"murmushi Khalil yayi yace haba little kanwata kinsan da yaya mufeed ne zaizo daukarki but baida lpy ne shiyasa akace ninaxo,yana fadar haka yana samata akwatinta a kijerar baya.

_______ shiga tayi gaba shima yazagaya yashiga mazaunin driver ,tada motan yayi suka tafi suna tafe suna hira har suka karasa gidan yayi parking,yana tsayar da mota hamrat tafita da gudu tayi part din inna girgiza kai kawai Khalil yayi yana ganin yarintar hamrat haryanxu da sauran ta .


******
tun daga parlour take kwalawa inna kira,Inna dake bacci taji muryan takwararta kamar a mafarki,mi?ewa take kokarinyi dai_dai sanda hamrat taturo kofar faWawa tayi jikinta tana fashewa da kukan shagwaSa.

"itama innar kamar jira take tafashe da kuka,tura kofar Khalil yayi yagansu sunata sharSar kukansu, shikuwa Khalil maizeyi idan ba dariya ba, ganin yana dariyane yasa suka daina kukan suka zubamai ido.


"saida yayi dariyarsa mai isarsa tukunna yatsagaita,turo ?aramin bakinta tayi cikin shagwaSa tace,"kai yaya Khalil kaida zaka rarrashemu sai kuma kaita mana dariya?

",sorry kanwata abin nakune yakeban dariya.',innace tace rabu da dannema yaushe kika dawone takwara yanxu nadawo daman yaya Khalil bai fada miki yau zandawoba?


"inda yafadamin ai bazan zauna ina bacci ba,shidai yaya Khalil hucewa yayi yana musu sai anjima,bayan fitarsa inna tace waini takwara maikike shafawane naga kin chanja gaba daya kinyi kyau harkinfi lokacin da mukazo kyau Allah yasa dai ba abinda ?ammata suke yiba kike ba ,benishin ko?


" murmushi hamrat tayi nan tace a'a wllh inna Allah yayi min tsari dayin bleaching ai Kinga ba haske nayi ba kawai skin Winane yagyaru menene kuma sikin???

"kai inna inbaki iya faWan abuba kawai kiyi shiru nan tabata lbr yadda akai da kuma hidimar da Yazeedat tayi,aikuwa inna sai sawa Yazeedat albarka take,saida suka sha hira sosai tukunna hamrat tayi toilet dan watsa ruwa tana fitowa tanufi mirror tatsara kwalliya dudai bawani abin tashafaba amma tayi kyau sosai riga da wando tasa kirar pakistan ta yafa gyalan kayan,bakaramin kyau hamrat

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login