Showing 45001 words to 48000 words out of 65973 words

Chapter 16 - HAMRA'UL YAZEEDA by Nusaiba Alkamawa book 1.doc

07 Oct 2025

1045

a ha?ura,shi mufeen din ko haule ko abuwa abashi za suyi na'am dashi sai a Waura auren dashi dama nasan takwara da kyar zata iya yarda da auren shi sbd mufeen Win da ya nuna mata mugunta ahto ni dai gaskiya na faWa naga kana zazzare min idanuwa Inna ta gama faWa tana kallon mufeed din ganin yana mata wani irin kallo.

____Shi kuwa Mufeed Win sanda Daddy ya furta za' haWa auren shi da Hamrat ji yayi tamkar ancaka masa mashi a kirjinsa san da kuma yaji hamrat din ta ce bata son shi yaji matu?ar dad'i kamar ya zuba ruwa a ?asa yasha, yayi tawa Allah godiya acikin zuciyarsa," yanzu idan a kace Hamrat zai aura ya zai yi da ranshi ina zai kai rigimar hamrat kuma baza ta taSa girmama shi ba amatsayin mijinta sbd ta riga da ta raina shi tabbas hamrat tana da matu?ar kyau wanda shi tunda ya ke arayuwar sa bai taSa ganin wacce tafi Hamrat kyau ba duk da kuwa yawan kasashen wajan da ya ke zuwa kuwa ,amma duk da kyanta bazai iya auren taba tunda Daddy ya soma haka gwarama tun wuri ya tafi London ya huta.

******
Daddy ya so wannan haWin ya yi sbd a ?arfafa zuminci,zumincin nasu yadaWa ?aruwa duk da kuwa alhmdllh kansu a haWe ya ke yaso Hamrat ta yarda da auren mufeed sbd zai ri?e ta da amana ba tare da ya cutar da ita ba yasan halin Mufeed ya kuma san na Hamrat Win,shi Mufeed mutum ne mai sanyin hali bayason damuwa bashi da faWa sannan bayason raini,ita kuma Hamrat yarinya ce rigimammiya me tsiwar tsiya da faWa shiyasa yaga da cewar abun tunda ba a haWa zafi da zafi ba, ko kuma sanyi da sanyi ba, sbd za a kwari juna anfiso agauraya.

Dan haka ya ce "to shikkenan mamana anfasa, kowa nan gaba yaje ya nemi wanda ya ke so ni kuma zan baku dan bazan muku auren dole ba ,Allah yayi muku albarka ."amen su momy suka ce, Hamrat da mufeed suka sauke wata ajiyar Zuciya atare.

"Daddy nan gaba ko ma wacece na yarda kazaSa min ita zan amsheta hannu bibbiyu.

Mufeed ya faWa sbd ya faranta masa rai ganin kamar ya shiga cikin damuwa, kuma kar daga baya a sanja shawara ace ya auri Hamrat Win shiyasa ya yi saurin faWan haka dan gwara abashi wata akan hamrat din nan me shegiyar tsiwar tsiya kuma yasan mahaifin nasa bazai zaSa masa abinda zai cutar da shi ba,"sannan Daddy Dan Allah ka yarje min da naje London domin na aiwatar da wasu business Dina na cen.

Daddy cikin jin daWi ya ce "masha Allahu naji daWin maganar ka kuma insha Allahu baza kayi kukan zaSen da zanyi maka ba kuma na yarje maka kaje London Win idan yaso ka na dawowa Sai ayi auren naka in kuna lokacin Allah yasa kun daidaita da Hamrat din Toh yanzu dai zaku iya tafiya.

****
Duk suka mi?e banda Inna Dan Sai da suka ?ara tautaunawa sannan tabar part Win dadyn .


Reader's zanso Jin wane Sangaren kuka fi so acikin wannan labarin?.


Akwai tambayoyi da za ayi agame da littafin nan duk wanda ya amsa yana da kyautar card

Ana page 25 za agudanar da gasar.

Ta Wannan number zaku iya samuna
0902 890 3887


More comment more typing

Comment .


HAMRA'UL YAZEEDAH



Labari da rubutawa
Daga
Nusaiba Alkamawa


Tiktok at
NUSAIBA ALKAMAWA

YouTube at NUSAIBA ALKAMAWA

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
=ت? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=ت?
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?


Page =???=??? 24


*Khalil*

______?ara shiga wanka yayi ya shirya cikin shigar shadda aikuwa tayi masa kyau sosai,yana fita suka kusan cin, karo da yaya mufeed.


"Irin wannan cin kwalliya haka Ina zuwa ?"

*****
Sosa ?eya yayi kamar bazai faWa ba, sai kuma yaga gwara ya faWa sbd bai saba ?arya ba,kuma sannan baya taSa Soyew yaya Mufeed sirrin sa," zanje gurin yazeedaty ne tana son ganina.

____Tsuke fuska yayi "wai kai bana raba ka da yazeedan nan ba sai kace ita ce autar mata, to kayi gaggawa ka rabu da ita, yanzun kaje kuyi sallamar ?arshe yana gama faWan haka yayi tafiyarsa.

*****
Shi kuwa Khalil mamaki ne ya gama cika sa taya zai iya barin masoyiyarsa?

Bayan duk bugun zuciyarsa, soyayyarta ?ara hauhawa ta ke, gwara yaje ko Allah zai sa mahaifin nata ya ha?ura,wata zuciyar ta ce" amma me yasa ta ke son ganin ka da gaggawa haka?

Da wannan tunanin ya shiga mota ya ?auki hanyar zuwa gidan su yazeeda.


______Yazeeda tana gama wayar da khalil ta dafe kanta sbd tsananin ciwon da ya ke mata,wai shin ma taya zata iya faWawa khalil su rabu?sam kalmar rabuwar ma bata da daWin faWa ko abaki amma ba yacce na iya zanbi umarnin Daddy.


****
Khalil yana isa ya kirata awaya hijab Win ta kawai ta Wauka, tayi waje ?irjinta yana dukan uku _uku tana zuwa ta tarar da shi a parlourn ba?i .


_____Shima anashi Sangaren duk gaba Waya ba yajin dad'i shi kanshi yaga yanayin fuskarta ba sanda yasa ba ganinta , abaya ba.


____Jiki a sanyaye ta tura ?ofar Falon jikake ras_ ras gaban ta ya yanke ya faWi, dafe ?irji tayi gami da zaro ido tuni jikinta ya hau Sari yana karkarwa. da kyar ta iya sallama ta nufi inda yake,

Yana zaune akan matsakai ciyar kujera yayin da ya kifa kansa a ?asa wasu zafafan hawaye na Wiga, akan kwayar idanuwansa,cikin sar?a??iyar muryarta da ke fita dakyar ta ce "my Lov" da sauri ya Waga mata hannu alamar dakatar wa, rass gaban ta ya ?ara faWuwa a karo na biyu, Wagowa yayi ya zuba mata rinannun idanuwansa da suka sauya kala zuwa ?arshe, tabbas duk wanda yayi arba dashi a wannan halin sai ya tausaya masa sabo da tsabagen tsagwaron azabu da suke ratsa zuciyarsa.

___ girgiza kai Yazeeda ta shigayi, cikin wata da kusashshiyar murya mai cike da zallar raWaWi da ?una ya ce "Lo.... lo..." kasa maganar yayi saboda wani azabebben kuka da yaci ?arfinsa, cikin tashin hankali Yazeeda ta ke cewa "don Allah ka faWa min meye damuwar ina ji ajikina wata rayuwa mara daWi zamu shiga!!!" tana gama faWin haka ta rushe da kuka, cike da jarumta ya ?o?arta ya ce "Lokaci.... yayi... da zaz zamu ha?ura da junan mu...." cak kukan da Yazeeda ta ke ya tsaya sabo da razani da tashin hankali zaro ido tayi ta dafe ?irji tana haki, mazajen idanuwansa da suka koma tamkar garwashi ya zuba mata domin gazgata mata, Yazeeda tayi mutuwar zaune ta kasa motsa koda Wan yatsanta Waya ne, sai wasu masifaffun a zababbun hawaye dake kwaranya daga idanuwanta,


Cike da tausayawa ya ce "kiyi ha?uri ki koyi rayuwa babu ni a tare dake, duk da na sani ni ba lallai na iya gudanar da rayuwata ba keba," girgiza kai Yazeeda tayi ta rushe da wani mashahurin kuka mai tsuma zuciya cikin muryar kuka ta ce "yanzu shike nan rabuwa zamuyi shike nan burinmu na zama ma'aurata ba zai cika ba?", wallahi ina sonka ba zan iya jure rashin ka daga gareni ba, kaine rayuwata farin cikina kaine komai nawa,taya zan rayu babu numfashi atare dani. karka manta kaine numfashi na, ba zan iya rayuwa ba kai ba ka taimakeni duk da nasani ba laifinka bane baka da laifi ha?i?a kana azabtuwa da soyayyata ban sani ba koya rayuwarka zata kasan ce bayan rabuwarmu ban damu da gushe war farin cikina ba amma ina so naka farin cikin ya Wore na har abada Khalil ka yafe min ?addara ta raba mu!!!!!!!" ta ?arasa maganar tana ?ara dur?ushewa a wurin,

Tabbass Khalil da Yazeeda suna cikin wani hali na mutuwa ko rayuwa


Khalil yana so yayi magana amma ya kasa ji yake kamar zai mutu zuciyarsa wani tsalle ta ke tana bugu ji yake kamar zata faso ?irjinsa ta fito, Yazeed ta murmusa hawaye na zuba ta ce "Allah sarki Yaya Khalil ka nuna kulawarka a kaina ka nunamin hanya me kyau ka nunamin so da ?auna na gaskiya da amana Allah baiyi nice zan zamo matarka ba, sai ha?uri Allah ya bamu ha?uri da juriyar rashin junan mu" tana gama faWin haka ta ciro wani kyakkyawan zoben azurfa a hannunta, tana kuka ta kama Wan yatsan shi ta zira masa, ta ce "wannan shine zoben da mahaifina ya bani, ni kuma na sadaukar dashi wakai,!!!" wani zazzafan zoben ta ?ara cirowa ta dam?a masa a tafin hannunsa ta ce "ga zoben da ka bani a matsayina na masoyiyarka, yanzu kuma gashi soyayyar ta rabe sabo da haka ga shinan," ta ?arasa maganar tana murmushi tana girgiza kai hawaye na zuba acikin idanunta,tashi tayi ta nufi hanyar fita, dafe ?irjinsa yayi yana razga kuka yana kiran sunanta da cewa "Yazeeda karki tafi ki barni, bazan iya rayuwa batare dake ba wallahi ina sonki so na har abada

Nayi tunanin duniya zata bani dama dayawa tayarda zan baki kulawa fiye da yadda kike zato
amma ?addara tana shirin rabani dake duk da bansani ba ko zamu sake samun wata damar anan gaba amma zanyi amfani da damar da nake da ita yanzu na zubar da hawayena ko nasamu saukin abunda ya addabeni ki yahkuri domin mafarkin mu yakasa cika ta dalilin sana'ata da nasan wa?a za tai sanadin rabuwarmu da ban fara ba
to yanzu zantafi kuma ina fatan zakiyi kokarin mantawa dani acikin rayuwarki duk danasan abune mai matukar wahala amma shine zai sa ki tsira da lafiyarki
yafaWa yana me cizon dan yatsansa idon sa cike da kwallar da takasa zubar da hawaye."



Tafiya tafara don batason ya fara tafiya a idanunta shiyasa gwara ita tatafi.

" Yaze........" kasa ?arasa maganar yayi sabo da Aman jini da ya shigayi nan ta ke ya faWo daga kan kujerar yana Waga mata hannu alamar ta tsaya, haka kawai taji bugun zuciyarta ya ?ara tsananta ta juyo, zare ido tayi tana da fe ?irji wata gaggarumar ?ara ta ?walla yayin da taga Khalil ya daina motsi, luuuu tabi ?asa ta faWi a sumee .....


*Hamrat*

Hamrat taji dad'i da dady bai tilastata ba akan ta auri mufeed sam bata sonshi SBD mugune ba shiri suke ba inda wani Daddy ya bata zata karSesa hannu bibbiyu harma tayi masa godiya sbd dady ubane sam baya bambantata da yayansa yana nuna mata kulawa sam bata tashi da kukan maraici ba sbd dady ya sha re mata hawayenta .

Haka ta nufi ?akinta ta kwanta tana nunanin soyayyarsu da Uncle Hameed wani irin zafafan hawaye ne suka fito daga cikin kwayar idonta.


Comment.

*HAMRA'UL YAZEEDAH*




*STORY And WRITTEN*

BY

*NUSAIBA ALKAMAWA*



Tiktok at
*NUSAIBA ALKAMAWA*

*PAGE =???=???* 25


Na sadaukar da wannan page Win, ga duk wani masoyin littafin nan Wato Hamra'ul Yazeeda much Love =ؕ?=??

_________________________


*Aunty*

Shuru -shuru Aunty ta ji Yazeeda bata dawo ba, tun bayan fitar da ta yi da Khalil yazo, wani tunani ne ya Warsu azuciyarta, da sauri ta tashi ta nufi parlourn ba'ki ,tsayawa cak tayi kamar karta shiga, sai kuma wata zuciyar ta ce 'Gwara dai ki shigan.'

"D'aga ?ayattacen labulan da ke Wakin ta yi, da kutsa kai bakinta Wauke da sallama, amma shuru ba a mayar mata da martani ba,can ta hango hijab Win Yazeeda a malale A ?asa da sauri ta nufi wajanta tana zuwa taga Khalil da Yazeeda akwance gefe Waya kuma ga jini nan duk ya Sata wajan.

cikin razani ta kalli shi bakinshi, jini yayi dama-dama abakin nashi.


******
?irjinta na dukan uku_ uku gaba Waya duk tabi ta gama tsorata cikin fitar hayyaci, ta kwala wata uban ?ara ta na Waga Yazeeda,ganin babu numfashi atattare da ita kumatunta ta ke ta Sawa tana ambaton sunanta amma ko gezau .


_______Ajjiye yazeeda ta yi ta koma gun Khalil,nan ma ta ga baya numfashi saka hannu aka tayi tana sumbatu ruwan hawaye kuwa duk ya gama jika idanuwanta.


Gate man ne ya shigo da sassarfa jin ?aran da Aunty tayi yana shiga ya tarar da wannan tashin hankali, yana wa Aunty magana amma shuru saboda gaba Waya ta kidime,tunaninta baikai ga takirawo wani ba domin akaisu asibiti ko Allah zai sa basu rasun ba ,gate man bai yi wata -wata ba ya fara Waukan Yazeeda yana kwala wa idi driver kira idi ya amsa masa ya taho da sauri ya buWe masa mota ya sakata agidan baya. Idi sai tambayar abinda ya same ta yake gateman ya ce shima dai bai sani ba, sannan ya taimaka mishi sukaje suka d'auko namijin, suka saka khalil amotar suka wuce asibiti darect emergency aka wuce dasu

Dama sunsan asibiti inda Alhaji yake zuwa tare da iyalansa.


*****
Cen gida kuwa Aunty sai da taji ?arar tashin motarsu, sannan ta dawo hayyacinta Cikin kuka ta koma parlourn nata, ta Wauki waya ta dannawa Daddyn Yazeeda kira, ta wassafa masa abinda ya faru ya ce mata gashinan ahanyar dawowa gidan,yanzu zai ?araso sai su wuce asibiti,ta ce masa" To" sannan ta katse wayar, tana musu addu'a Allah yasa ba mutuwa sukai ba idan basu rasu ba Allah ya ta shi kafaWunsu da gaggawa.


____Cikin ?an?anin lokaci ya ?araso bayan sunyi waya da idi driver,yana isa Aunty ta fito babu shiri suka nufi asibitin,suna isa darect wajan Doctor suka nufa Doctor ya ce,
"Ansamu Yazeeda ta farfaWo amma khalil ne dai har yanzu shuru amma dai suna iya kacin bakin ko?arinsu na ganin ya farfaWo .


____Azuciyar zuciya a tare suka sauke su kace yanzu zasu iya ganinta?

Doctor ya ce a'a sai dai Zuwa gobe dan allura sukai mata sbd ta samu hutu domin sunbatun da ta ke na tana so taga Khalil.

Doctor ya cigaba da cewa su bashi number iyayen Khalil saboda ya sanar musu da halin da Wansu yake ciki sai a sannan Aunty ta tuna sbd shaf ta sha'afa Allah ya,sa ma, tana da number Hamrat Dan Yazeeda ta,taSa aran wayar ta ta ta saka no Win Hamrat Win ta kirata ashi.


Wayar ta Wauka cikin Sa'a kuwa taga number Hamrat din danna kira tayi .


******
Hamrat kuwa na kwance abun duniya duk yabi ya isheta ta rasa meke mata dad'i gaba Waya tunanin Uncle Hameed ne ke kunshe acikin zuciyarta.

____?arar wayarta ta jiyo, Waukar wayar tayi taga wata bakuwar number( Dan Lokacin da yazeedan ta kirata batayi serving ba)kamar ba zata Waga ba sai kuma ta Waga.

Daga Wayan Sangaren taji anyi sallama

"Assalamu alaikum"
.cikin sanyayyiyar muryar ta ta amsa da "wa'alaiki ssalamu" .


"Fatan dai ina magana da Hamrat?

"Eh itace" .

____"Yauwa Auntyn yazeeda ce, cikin mamaki Hamrat ta ce "la Aunty ashe kece ina yini ya bestyn tawa ta ke ?

"Ta na asibiti tare da khalil kifaWawa mahaifinsa cewa khalil ya yanki jiki ya faWi yanzu dai likito ci suna kansa suna ?o?arin bashi kulawa.

****
Ras haka taji ?irjinta ya bata, cikin zaro ido haWe da razabi ta ke tambayar Aunty wane asibitin ne ?

" Aunty ta faWa mata.
Aikuwa basu shiri Hamrat ta nufi ?akin momy tana tunanin ta inda zata faWa mata, momy ta ga Hamrat dai bata cikin hayyacinta ta ke tambayarta abunda yasameta?

*
aikuwa ta wastsafa mata abinda ya ke faruwa
Momy cikin kiWima ta nufi part Win Daddy ta faWa aji masa nan suka shirya harda Inna suka nufi asibitin.


____Suna zuwa suka tarar da su Aunty azaune, tambayarsu suka fara meya same shi Aunty dai ta ce musu batasan komai ba, kawai ta dai zo ta taradda dasu akwance.

* babu shiri suka nufi wajan likitan suka faWa masa sune mahaifan khalil Doctor yace "Ya kamu da ciwon zuciya da kuma na damuwa. Daddy yace abasu dama su fitar dashi ?asar waje Doctor yace babu damuwa.


____Nan dai Daddy ya kamalla mishi komai, Mufeed ne me jinya sai kuma Hamrat ta zata tafi karo karatu, akwai wani abokin Daddy acen agidan shi zata zauna nan da kwana uku ne tafiyar nasu.


Hamrat tayi-tayi abarta ta gana Yazeeda, amma likita ya hana haka suka kwana asibitin ba tare da sun ga marasa Lpyn ba Sangaren khalil daban dana Yazeeda.



A kwana na biyun ne aka barsu suka ga Yazeeda amma bata magana sai iya kuka Hamrat ta so sunyi magana sabida ta faWa mata damuwarta amma ina Yazeeda ba magana ba zata iya ba haka nan Hamrat tabar wajan yazeeda rai duk babu dad'i .

_________Bayan sun gama komai na tafiyar, tafiyar ta kasance dama yau ce, airport suka nufa su momy ce masu rakiyar bayan an cajesu suka nufi wajan jirgin, kasa suka shiga kujerarsu a jere su uku wato khalil mufeed Hamrat khalil har yanzu jikin dai babu dad'i dan yana jin jiki jirgi yana tashi Hamrat ji ta ke duk tsoro ya da baibayeta kamar ta saki ihu, salati ta fara sannan tsoron ya ragu azuciyarta mufeed sai tsaki yake yi ganin Hamrat na neman ta kunyata shi .

*London*
_____Suna sauka wata zukekiyar mota ta Wauke su ,darect sai asibiti bayan ankai khalil Wakin shi aka fara dubashi sannan Mufeed ya nufi inda Hamrat zata zauna shima dai agidan zasu zauna idan khalil yaji sau?i.


Yazeeda sai da tayi sati asibiti sannan aka sallame su haryanzu batace wa kowa ubban aunty takaraci maganar yazeeda bata tankanta har aunty tayiwa Doctor magana akan ko wata matsalar ta same ta doctor yace babu komai kawai dai batayi niyyar maganar vane .


Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar da yazeedat cikin kunci da begen masoyinta kullum tana cikin daki ita kadai sam batasan wani ya rabeta Daddy yayi rarrashin Aunty ma haka amma yazeeda taki ji kullum cikin damuwa take hakama kodayaushe cikin kuka take Saida aka dauki wasu kwanaki sannan tadaina kukan kuma tarage damuwar hankalinta kuma ya fara karkata ga inda zata fara Film sai tunanin take ta yacce zata fara gashi batasan kowa ba aharkar kuma batasan inda zata nufa ba .



Su Daddy ko da yaushe suna waya sunajin jikin khalil Alhmdllh an fara samun cigaba dan yafara warware wa Daddy yace ko ansallame su ma a asibitin kada su sake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login