Showing 21001 words to 24000 words out of 123375 words

Chapter 8 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt

Abba ya yi saurin tare numfashinta, “Sai _me? Idan kin ganshi rungume da ita nace sai mene? Kuma ina son ki gane, kin taba fuskar yaron nan na Karshe! Sultan ya wuce mari a yanzu sai dai nasiha. Kai Sultan zo ka wuce dakinka. Allah ya yi maka albarka yasa ka gama da duniya lafiya. Maza ka wuce.� Sultan ya juya kawai yana jin dacin furucin mahaifiyarsa akansa. Ya maimaita Kalmar zina tafi a Kirga. Hakan yasa ya kasa barci. Tunanin ya yi nesa da Nasreen da iyayensa suka darsu a zuciyarsa. Ita kuwa Nasreen ta lashi labbanta da suka yi laushi ya fi a Kirga. Tunanin Sultan ya ci gaba da gallabanta. A haka har barci barawo ya sace ta Washegari suka shirya zuwa Makaranta, a lokacin Sultan ya jima da barin gida. Akan hanyarsu ta dawowa ne aka tare direban su aka cunkusa su a wata mota. Nasreen dai tana rungume da Nawfal bakinta bai fasa addu’a ba. Wani irin Kunci ya ziyarceta, Yanzu mutanan nan ina za su kaita? Ita dai damuwarta kada a rabata da dan uwanta. Da zarar ta tuna da Sultan Sai taji wasu hawaye suna kwaranya. Nawfal dai ko Kwakkwarar motsi ya kasa yi. Tafiya ake yi tun suna sa ran sauka har suka sadakar da kwanakin su a duniya ya Kare. Sai wajen Magriba aka bude Kofar mota aka cillo su waje sannan suka Kara gaba. Nawfal ya dubi Nasreen cike da tausayawa ya ce, “Nasreen kin ga wata duniyar suka ajiye mu. Yanzu ina zamu dosa?� Nasreen ta ce, “Duba ka gani akwai jama’a a garin?� Ya dudduba ya ce, “Daji ne wurin babu wasu jama’a. Amma zo mu Kara gaba ko zamu sami abinda zamu ci.� Haka suka yi gaba babu wanda suka samu sai wata mai siyar da abinci da take shirin rufe wurinta. Nawfal ya fara magana, “Sannu. Don Allah wani gari ne nan?� Matar ta dube shi ta ce, “Ku kuma daga ina haka? Wannan garin Katsina ne Kankia. Me ya kawo ku nan?� Nawfal ya dan yi shiru, “Wallahi wasu ne suka sato mu suka kawo nan. Don Allah ina Zamu sami makwanci? Sai ki daukeni aikin wanke-wanke kina ba mu abinci, ° Matar mai suna Amina ta nuna masu Kofar shagonta wanda akwai rumfa, “Sai dai ku dinga kwana a nan domin ba zan iya baku makwanci ba, kun san duniyar babu amana. Ita wannan makauniya ce?� Ya dan durkusa, “Mun gode _ sosai. Makauniya ce� Ta dan tausaya masu, sannan ta cire zanenta daya ta basu ta ce, su lulluba. Har ta tafi ba ta daina waiwayarsu ba. Ita kuwa Nasreen umartar Nawfal ta yi da ya samo masu ruwa suyi alwala. Bayan sun yi alwala ne suka raba dukkan sallolin da ke kansu sannan suka dan rabe. Nasreen tana jin yunwa, amma kuma ta kasa gayawa Nawfal yunwa take ji, saboda kada ya shiga damuwa. Shi kansa yunwar yake ji amma ya kasa furtawa. Can ya tuna da awaran da ya siyo daga Makaranta don haka ya ciro jakarsa ya fitar, a lokacin ne kuma Nasreen ta jiyo Kamshi da fara’arta ta ce, ““Nawfal menene wannan kuma?� Sai da ya kai bakinta ta gutsura sannan ya bata amsa, ““Dazu ashe na siya wara na manta ne. Zai ishemu mu ci.� A nan suka cinye warar, Nawfal ya dibo masu ruwa suka sha. Cikin dare dukkansu suka kasa barci saboda azaban cizon sauro. Shi dai Nawfal sai korarwa Nasreen Sauron yake yi. Ga kwanciyar Kasa, ga cinnaku, ga sanyi da ke ratsa su. Nasreen ta dinga kuka ba tare da ta bari Nawfal ya sani ba. Can ta yi magana a hankali, “Nawfal waye zaiyi .mana haka? Me yasa za a raba mu da danginmu?� Nawfal ya girgiza kai, ‘“‘Nasreen idan kina tunanin su Abba danginmu ne ki daina tunanin hakan. Da wahala idan ba tsinto mu aka yiba. Rannan naji Umma suna magana da wata Kawarta take cewa Deedi ne ya rakito mu, ya kawo masu masifa cikin gida. Amma tabbas! Mu ba “yan gidan bane. Ya zama dole mu mance duk wani jin dadi, mu fuskanci abinda ke gabanmu. Mu koyi zaman wahala mu koyi nema da kanmu, mu koyi maraici, tunda dama mu din marayu ne. Idan muka ce zamu yi ta zama a gidan nan watarana Umma za ta sa ashana ta Kona mu. Kin ga ta nakasa maki idanu, yanzu haka ita ta sa,a kawo mu nan, Don Allah Nasreen mu mance gidan nan mu jure dukkan gwagwarmayar nan watarana sai labari.� Nasreen ta gigice da kalaman Nawfal, don haka ta bashi labarin yadda suka yi da Sultan a daren jiya, ta ci gaba da cewa, “Yanzu Nawfal mu dauka ba mu hada komai da su Abba ba, idan muka barsu munyi masu adalci? Wane hali yanzu su Deedi suke? Sun raine mu tsawon shekaru goma sha bakwai, yau don mun yi fushi sai mu guje su? Da wannan zamu saka masu kenan Nawfal? Ya kamata muyi tunani.� Nawfal ya ce, “Nasreen bamu yi laifi ba idan muka yi hakan. Zamu bi su da addu’a wanda duk nisan inda muke zai je ya same su. Maganar kuma babu aure a tsakaninki da Deedi ya dai fada maki hakanne domin baya son ki damu da lamarinsa, yana hango tashin masifun da zaki iya shiga ne idan har Umma tasan akwai soyayya a tsakaninku. Don Allah mu mance baya mu fuskanci gaba.� Nasreen ta fitar da kukanta fili, wanda har yasa zuciyar Nawfal ya karaya, “Nawfal ka yi min addu’a domin na fada cikin hatsarin son Deedi. Ba zan iya raba kaina da irin wannan soyayyar ba, domin bansan lokacin da ta shige ni ba.� A lokacin wani Katon sauro ya cije ta ta kai wa kanta duka, Nawfal ya share hawayensa ya ce, “Zan taya ki da addu’a insha Allahu komai zai zama labari.�Www.bankinhausanovels.com.ng A can garin Kaduna kuwa, Sultan yana Office ‘ya ga kiran mahaifiyarsa, abin ya ba shi mamaki domin ba zai tuna ranar da ta kira shi ba. Ya dauka da Sallama tun kafin ya gaisheta ta fara magana, “Sultan su Nasreen ba su dawo daga Makaranta ba, ko kuna tare ne?� Mikewa ya yi tsaye kafin ya ce, “Umma ban gane ba? Ina shi direban yake?� Umma ta tabe baki, “Babu direba, babu su Nasreen. Allah ya sa ba wani gantalin aka wuce ba.� Sultan ya katse wayar kawai ya hada ‘yan sanda suka fita a cikin motarsu. Kai tsaye hanyar Makarantar suka nufa, a nan suka sami direba a yashe, ga mota a gefe, haka mutane sun fara taruwa. Shi ya fara sakkowa daga motar ya tallabo Direban, Sumewa ya yi don haka yasa a kawo masa ruwa ya watsa masa, gabansa yana tsananta faduwa. Yana farfadowa ya ce, “Ina su Nasreen? Ina suke!� Ya daka masa tsawa. A gigice yake magana, “Yau na shiga uku! Wasu suka zo a farar mota suka tafi da su.� Sultan ya shake dircban nan jikinsa yana rawa, “Idan wani abu ya sami su Nasreen ina tabbatar maka sai na kashe ka! Ka gaya min da su waye ka hada baki aka sace min su? Gaya min waye ya turo ku?� Sultan fa ya haukace, ya fita hayyacinsa. Da Kyar ‘yan sandan nan suka Kwaci direba, sannan suka sa shi a baya tare da wani dan Sanda aka samu aka lallaba Sultan ya shiga motar gidansu dan sanda ya shiga ya wuce da shi gida. A lokacin Abba ya dawo, don haka ya Karaso gaban Abba jiki asanyaye. “Abba..� Ya ja sunan mahaifinsa, ya kuma kasa furta komai. Sai dan sandan nan ne ya korawa Abba “bsyani Da Karfi Abba yake Salati. Sultan kuwa ya kasa magana, sai idanunsa da sukayi jazir kamar gauta. Jikinsa har rawa yake yi. Ita kanta Umma yadda taga yaron nata ya sauya a lokaci guda yasa jikinta mugun sanyi.,,Gaba daya suka shiga falo, Abba ya baiwa dan sandan umarnin a bi ko ina a sanya cigiyarta. Kafin ka ce me? Gari ya dauka an sace “yan biyu mace da namiji, Sultan ya zauna a kujera jikinsa asanyaye babu Kwari, Haduwarsu kawai yake tunawa a jiya, ya kasa magana ya kasa duban Abbansa. Shi kuwa Abba tashin hankalinsa ya ninku da ya tuna bai sauke Katon nauyin da ke kansa ba. “Sultan nayi kuskure mai girma! Ban barka ka samu kyakkyawar zama da Nasreen ba.� Dukkansu suka dube shi cikin rashin fahimta. “Sultan Nasreen matarka ce, matarka ce aka sace � ta. Na hada aurenku domin ganin ka sami daman rike amanar Saudat da kyau! Yau sai gashi ka rasa matarka. Ban sani ba ko kasheta akayi, idan kuwa tana da rai za ta yi ta yawo da igiyar aurenka akanta.� Ba Umma ba, hatta Sultan sai da maganar tayi masa girma. Damuwarsa ta sake ninkuwa. Daman Nasreen matarsa ce? Da , yasan matarsa ce me Zai sa jiya/ya gaya mata irin wannan kalaman? Rintse ido yayi yana jin | kamar mahaifinsa bai kyauta masa ba. Umma kuwa tunani take yi a zuciyarta me yasa batasa a kashe Nasreen ba kawai ta huta? A fusace ta mike, “Allah na gode maka da aka saceta. Ashe so ta yi ta kanainaiye min gida? Kana nufin Nasreen ita ce matar Sultan? Amma dai Alhaji ka gama cutata. Da inga wannan baKar ranar � gara inga ranar mutuwata. Ita Iyamin da Sanin ai suna da ‘ya’ya maza, Me yasa basu aura masu
6/5/22, 10:28 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚*






CHAPTER 8






*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*






A JIYA MUN TSAYA


Sultan nayi kuskure mai girma! Ban barka ka samu kyakkyawar zama da Nasreen ba.� Dukkansu suka dube shi cikin rashin fahimta. “Sultan Nasreen matarka ce, matarka ce aka sace � ta. Na hada aurenku domin ganin ka sami daman rike amanar Saudat da kyau! Yau sai gashi ka rasa matarka. Ban sani ba ko kasheta akayi, idan kuwa tana da rai za ta yi ta yawo da igiyar aurenka akanta.� Ba Umma ba, hatta Sultan sai da maganar tayi masa girma. Damuwarsa ta sake ninkuwa. Daman Nasreen matarsa ce? Da , yasan matarsa ce me Zai sa jiya/ya gaya mata irin wannan kalaman? Rintse ido yayi yana jin | kamar mahaifinsa bai kyauta masa ba. Umma kuwa tunani take yi a zuciyarta me yasa batasa a kashe Nasreen ba kawai ta huta? A fusace ta mike, “Allah na gode maka da aka saceta. Ashe so ta yi ta kanainaiye min gida? Kana nufin Nasreen ita ce matar Sultan? Amma dai Alhaji ka gama cutata. Da inga wannan baKar ranar � gara inga ranar mutuwata. Ita Iyamin da Sanin ai suna da ‘ya’ya maza, Me yasa basu aura masu


ZAMU TASHI


ba? Allah ya kara nesanta su da mu, yasa ko a lahira haduwar ta yi wuya.� Hafsat ta mike ta ce, “Tabdijan! Nasreen matar Yaya Sultan? Allah ka tsaremu da hada zuri’a da shegu. Allah ya ga abinda ya gani.� Haidar ya mike yana fadin, “Af yanzu sai a nemo wata matar amma dai ba Nasreen ba.� Sultan bashi da Karfin furta komai, sai idanu da yake bin su da shi. Haka Abba ya kasa magana, ya tabbata yau zai yi barcin wahala na rashin ‘yan biyun da ya Kwallafa ransa akansu. Yaran suna da matuKar shiga rai. Sultan kuwa tunda ya duKar da kai bai sake motsawa ba. Shiru-shiru babu wanda ya sake yin magana hakan yasa mahaifinsa ya tsargu. Yana dago shi yaga baya motsi hakas yasa Abban sake gigicewa ya Kwala masa kirs yana girgiza shi. Umma da su Hafsat suka fito 8 guje. Ganin baya motsi yasa Umma ta dora hannu akai tana ihu. Haka ma Hafsat. Shi kanshi Haidar sai da ya yi Kwalla domin suna son? Yayansu fiye da komai, kawai hudubar uwarsu suke dauka. ) Cikin Kankanin lokaci aka isa da shi asibiti. Umma ta rike keken da ake gungura shi,


tana bin nursis din Abba ya fincikota daga jikin keken yana huci, “Ina ruwanki da shi? Dama kina sonsa kika ganshi a cikin wani hali kika sake tura shi ciki? Ashe kina sonsa kike watsa masa kalaman batanci? Idan Sultan ya mutu ke kika kashe min da kuma ba zan barki ba, dan sai nayi shari’a da ke. Salma ina matukar zarginki akan bacewar yaran nan. Yau da ina da hujja a hannuna da babu abinda zai hana ban kai ki Kara ba. Amma a juri zuwa rafi.. Abba ya koma gefe kawai yana sharar Kwalla. Ya sani, ya sani duk inda Nasreen suke suna cikin mawuyacin hali. Ya fi tausayawa rayuwarsu fiye da ta dansa. Umma kuka take yi sosai, ba don danasani ba, sai don halin da danta yake ciki, Sultan yana farfadowa ya zubawa mutanen cikin dakin idanu. Tabbas ya tabbata ba mafarki yake yi ba kamar yadda yake fata ba. “Abba angano inda su Nawfal suke? Abba a ina za su kwana? Wa zai dubi maraicin su ya basu abinci? Wa zai taimaka min ya yi aikin lada ya kula min da su? Abba a ina zan samo su? Shi kenan rayuwarsu Nasreen ya tafi kenan? Me ya sa ba ka gaya min Nasrecn matata ce ba? Da ka
gaya min da na gaya mata Kalmar da take ta dako ta ji daga bakina. Da ban yi mata Karyar babu aure a tsakanin mu ba. Da na bata kulawa a matsayinta na matata ko da sau daya ne tak! Abba ba zan taba sararawa wanda ya yi min wannan yankan Kaunar ba.� Abba ya zura masa idanu yana kallon yadda Sultan ya fita hayyacinsa a wuni guda. Shi ya san Sultan zai shiga halin da ya fi wannan ma, akan su Nasrecn. Sunkuyawa ya yi yana shafa kansa, “Sultan kai ba yaro bane, bare in ce har yanzu baka gama tantance menene Kaddara ba. Kana da hankalin tantance baki da_fari. Rayuwarmu bata tafiya a dai-dai dole sai jarabawa ta dinga ratsa mu. ‘Insha Allahu Nasreeri za ta dawo ku ci gaba da rayuwa a matsayin miji da mata. Kada ka mance Nasreen RUBUTACCIYA ce, tun tana cikin mahaifiyarta take haduwa da Kaddara, har yanzu tana rayuwa. Dole duk inda Nasreen take ta dawo domin bata da wani wurin da ya wuce nan gidan. Ka kwantar da hankalinka mu dage da addu’a.� Lumshe idanunsa ya yi yana tunanin a wani hali suke a yanzu? Wasa-wasa sai da Sultan ya yi kwanaki biyar yana jinyar kansa. Ko da ya dawo gidan ma sai ya koma yi masu yajin magana. A take ya kira su Mahbub ya gaya masu komai, hakan yasa dukkansu suka baro aikin su suka iso wurinsa. Barr Tajuddcen ya fara magana kamar kullum, “Sultan akwai sarkakKiya a_ cikin wannan lamarin. Ta ya ya hakan zai faru? Ta ya ya za a sace Nasreen da dan uwanta? Dole mai wannan aikin yana kusa da kai ne. Nasreen -matarka ce? Daman da ita Abba ya daura maka aure? TirKashi! Abin akwai sarKaKiya.� Haisam ya karBe da cewa, “Ko dai mahaifinsu ya gano akwai ‘ya’yansa a gidanku ne? Zai yuwu sai kawai ya aiko a sace su.�
Aslaf ya girgiza kai, “Ni ma tunanin da nake yi kenan, idan ba haka ba waye zai sace su?�� Mahbub ya girgiza kai, ““A’a mahaifinsu bai san da zaman su ba, bana jin shi ne zai yi wannan aikin. A dai sake bincike.�Ashmaaan ya dago yana duban kowa, har anfidda rai zai yi magana, sannan ya tanka, “Ku natsu sosai ku dubi maganar Mahbub, Idan har mahaifin nasreen yasan suna raye, ba zai bari su kawo wannan shekarun ba, zai aika a yi farautar ransu kamar yadda ya yi na uwarsu. Amsar wanda ya aikata hakan yana wurin Sultan domin kuwa shi ne yasan mutanen da take takun saKa da su.� Khamis ya dan murmusa ya ce, “Dadina da kai kaifin basira dan mutan Sudan. Maganar gaskiya ba mahaifinsu ba ne ya yi aikin nan, wanda ya aikata laifin nan makusancin Sultan ne, na kurkusa. Sultan kayi sakaci gaskiya. Yaran da suke dauke da abubuwa masu rikitarwa, za kabar su kara zube? Kana da irin matsayin nan a hukumance amma kake barin ~wani lagwanin direba ya jasu zuwa Makaranta? Ai yaran nan tsaro suke bukata. Ka mance na yi irin wannan sakacin aka tafin min da mata? Ka mance Ashmaan ya yi irin wannan gangancin aka kusa kashe masa mata? Daga Karshe me ya biyo baya? Dabararsa ta Kwace shi, da ya dauke matarsa ya turata London. Shi Mahbub da ya fimu dabara, ai hada matarsa ya yi da ‘yan sanda ya kuma sanya doka mai tsanani akanta. Yanzu dai menene abin yi?� Al-ameen ya ce, “Aikin gama ai ya gama. If not da gidajen daya daga cikin mu ya kawota aka boyeta har a gama bincike, mu zaKulo masu laifukan. Yanzu maganar bincike a kan wadanda suka yi kisa dole a dakata tunda shaidun sun Bace. Kawai mu mayar da hankali wajen nemanta.� Sultan ya girgiza kai, “Mahaifiyata ce kadai ta tsani Nasreen da dan uwanta tsana mai tsanani. To kaina ya kulle ko ita ce za ta sanya ayi hakan domin nisanta su da mu? Sai kuma wani dan iska da ya taba zuwa wai yana sonta Wai sai ya aure ta. A lokacin bansan andaura mana aure ba, zafin da mahaifina ya dauka ya bani mamaki. Su dai nake zargi.� Barrister Tajuddeen ya danyi rubutu ya -. dago yana duban Sultan, “Sorry to say Sultan, Umma ita ce asalin suspect! Amma kuma tafi Karfin mu gaskiya. Sai dai mu bi komai a hankali har Allah ya warware mana ‘wannan tashin hankali. Sannan zamu sa malamai suyi ta sauka suna addu’a. Allah ya bayyana maka matarka da dan’uwanta,�
Gabadaya aka amsa da Amin. Sultan ya dan shafi sajensa ya ce, “Zan bar garin nan. Ba zan iya zama a cikin gidanmu ba, sai in ga kamar zan ga Nasreen. Yarinyar da bata ganin gabanta ya za tayi rayuwa a wurin da babu tattali? Ba zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login