Showing 69001 words to 72000 words out of 123375 words
Chapter 24 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt
Ko a gida ko a Office ko a kasuwa, ko a cikin hawan idi, ko a filin sukuwa ko kuma a cikin taron jama’a da yawansu ya kai iya adadin buhun gero, inhar jan Gwarzona zai gifta, jinina zai motsa alamun farin cikina yana kusa da ni. Bare kuma a gidana,
a gidan nawa ma a cikin tsakiyar falona, a falon nawa ma a kusa da ni. Sannu da zuwa mijina, ba irina mai sonka za ka boyewa kanka ba. Me ka samo mana ne?�
Yarinyar kullum sake rikide masa take yi, a hankali ya Karaso ya karbe turaren wutan, ya dauketa cak! Sai cikin dakinta yasa key ya rufe. Tana girgiza masa kai, sai dai bai kai cikinta ba, domin cike take da kewarsa sosai. Suna nan kwance sun lula wata duniyar, suka ji Kwankwasa Kofa. Nasreen ta gigice tana son yin magana, ya sake hade bakin su wuri guda, hakan ya hanata furta komai, sai gabanta da ke faman bugawa da Karfi. A hankali ya yi mata magana “Ki natsu ki kwantar da hankalinki da muijinki kike tare ba kwarto ba. Bansan dalilin da yasa Umma ta zo ta sa mana Katon lullubi ba a tsakanin mu, bayan tuni Allah ya yaye mana wannan Katon hijabin, ya bani dama inyi abinda na gadama da ke domin ke matata ce. Yau a dakin nan zamu kwana ni da ke, na bar sake raba makwanci da ke Nasreen, Ni kadai nasan wahalar da na sha da baki kusa da ni a kwanakin nan biyu. Ki daina tsoro kin ji?� Gumi ne ke tsattsafo mata a kowani irin bugun Kofa da
Hafsat take yi. Bata damu ba, ba ta kawo komai a ranta ba, ta juya abinta.
Ta dubi Umma tace, “Rufe Kofar ta yi. Kina ganin makiran yarinyar nan? Tun ranar da kika rabata da Yaya kullum kwanan kuka take yi.�
Umma ta tabe baki, “Karshen rufe Kofa ta zo ta koremu ne daga gidan. Ita da Sultan sai dai ta hango wata da shi amma Wallahi ba dai ita ba. Sai naga ta inda dangantakan musulunci da rashin addini suka hada hanya.�
Zakiyya ta dubi wayar Umma da ke Kara � ta ce, “Umma, Abba ke kiranki.� Umma ta harari wayar cike da bakin ciki. Dallah ja can ki bani � wuri ba zan dauka ba. Ya addabeni da azaban kira kamar tsohon makahon da ya rasa gane hanyar gida.� Zakiyya da Hatsat suka yi dariya suka tafa. Nasreen da ta lume a cikin wata duniya, ta kasa ko da motsa hannunta ne. Shi kansa ya fahimci yadda ya wahalar da ita, tausayinta ya kama shi, da ace bai dau alKawarin ba zai amshi hakkinsa ba, har sai idanunta sun bude yau da ya nunawa su Umma shima namiji ne cikukke mai lafiya. Haka ya tashi kafin ya tafi
ya manna mata sumba, sannan yace“I love you Wife.�
Ta kasa magana sai motsa labbanta da ta yi ta mayar masa da martani. Ya gane abinda take nufi don haka ya jawo bargo ya rufeta, ya fice tare da jawo mata Kofar. Jin kansa yake yi kamar sabon ango, dukkan Kuncin da yake tare da shi, ya kau, sai murmushi yake saki abinsa. Umma da Zakiyya da Hafsat suka bi shi da kallo cike da mamaki.
Hankalin Umma idan ya yi dubu to ya tashi, “Kai da kake barci yaushe ka fito ka shiga dakin Nasreen? Me kaje yi a dakinta?� Tambayar taso ta bashi dariya, sai ya kirne kawai yana murmushi, “Umma don na shiga dakin Nasreen kawai sao a ce min me naje yi? Naje inkai mata waya Nawfal ya addabi Abba sai an bashi Nasreen. Sai na sami dakin a rufe. Da Kyar ta bude Kofar tana magagi wai barci take yi, ni kuma na fito na Kyaleta zuwa anjima sai insake kiransa suyi magana. Ta gabanku na wuce na shiga, abin mamaki babu wanda ya kula da ni. Hira ta yi dadi kenan. Ke Hafsat dauko min fura a frij da Cup.�
Yana maganar tare da gyara zama, haka yaki yarda su hada idanu da mahaifiyarsa domin , ya sani tana kallon Kwayar idanunsa ta gama gano shi. Domin idanun a lumshe suke sunyi jazir, ga wani irin kasala da yake fama da ita. Yana nan zaune yana shan furar, Nasrcen ta shigo tana bin bango. Yana son zuwa ya Karaso da ita, idanun Umma yana kafe akansa. Ta laluba ta zauna tana gaida Umma cikin yanayinta na sanyi. Babu wanda ya amsa mata, don haka_ tayi shiru tana wasa da ‘yan yatsunta. Babu wanda ya yi maganar Kamshin Sultan da ke fita* daga jikin Nasreen, amma kuma zuciyarsu a cike suke. Sultan ya mike, ya Karaso gabanta ya kama hannunta ya manna akan kofin furar sannan ya ce, “Gashi ki shanye ragowata.� Nasreen ta yi murmushi ta kafa kofin a baki, shi kuma ya sha mur kawai ya wuce ciki. Umma_ ta yi shiru tana nazarin irin wannan farin cikin da Sultan yake ciki na menene? Zakiyya ta dubi Umma tana son yin kuka, Umma ta harareta, hakan yasa ta dake kawai. Cikin dare kowa yana barci, Sultan yana kwance tsakiyar gadonsa ya kasa tsaida KwakKwarar tunani. Ya Kosa su sami appointment kamar yadda Al-ameen ya gaya
masa, su bar Kasar nan. Sauko da Kafafunsa ya yi yana jin zai bi shawarar da zuciyarsa take gaya masa. A hankali ya fice zuwa dakin da Nasreen take kwance kusa da Hafsat. Sai da ya wuce Ummansa a falo tana kwance a nan, da alamun yau a wurin take jin kwana. Nasreen ma idanunta biyu, tana jin motsi ta ji Kamshinsa ta rufe idanunta tana Salati a zuciyarta, ta tabbatar yau zai tona mata asiri. Dauke numfashinta ta yi a lokacin da ya dauketa cak! Tsoro sosai ya _ Shigeta, za ta yi magana yasa bakinsa ya hanata maganar. Sai da ya tabbatar da ta yi _ laushi sosal, sannan ya fice da ita. Yana kusa da � mahaifiyarsa ya ji motsinta, hakan yasa ya dakata har sai da ya tabbatar da ba tashin za ta yi ‘ba, sannan ya wuce abinsa. A tsakiyar gadonsa ya shimfideta ya dora kansa a bisa kafadarta, “Nasreen..� Ya kira sunanta cikin wata murya wacce bata san yana Boye da irinta ba. Ta kasa amsawa sai ma sake tattaro natsuwarta da ta yi akansa. Hannunta ya kama ya tura a cikin gashin gansa kafin ya fara magana, “Nasreen, ina shan wahala a sakamakon rashin ki kusa. A baya nasha wuya, a zatona Karshen wahalar ta zo? Ashe yanzu aka fara? Ki
gaya min ta inda zan iya ci gaba da zuba idanu, ganinki ma yana neman ya gagareni. Sai inje wurin aiki ban saki a idanuna ba, idan na dawo zan ga kowa zaune a falo amma banda ke Nasreen. Don Allah ki dinga daurewa kina yakice dukkan wata kunya kina fitowa nima in ganki kin ? Gobe ki shirya zan gayawa Umma zan kai ki asibiti a duba idanunki za ki ga likita kin ji? Yi min alKawarin za ki biyo ni.� Tana jin sonsa kamar ta faso Kirjinta ta ciro Son ta nuna � masa don ya fi gazgata ta. Ta rasa ta yadda zata
iya yi masa bayanin irin abinda take ji a cikin zuciyarta a sanadiyyarsa. ,
A hankali ta yi magana, wanda da ba don yadda ya tattaro natsuwarsa akanta ba, da babu abinda zai ji, “Na amince Deena, duk abinda ka yi dai-dai ne, ina jin tsoron Umma ne shi ya sa, kuma ta ce min in daina zama a falo. Ban san me na yi wa Umma ba bata sona Dee, ban san me zan yi wa Umma in burge ta ba, ban san mene ne musababbabin wannan tsanar ba, don Allah ka sanar min dalilin ka gaya min idan laifi na yi mata zan ba ta hakuri.�
Ta fara fitar da hawaye, ya sa hannunsa ya dauke hawayen yana sake duban ta, “Ba ki yi wa
Umma komai ba, ban san mene ne dalilin da ya sa Umma take gwada maki irin wannan tsanar ba, kamar ba jininta ba.�
Nasreen ta girgiza kanta, “Ka daina zolaya ta da irin wadannan maganganun Deee, tuni na yi hankalin bambance fari da baki, na sani, da ni da Nawfal ba jininku ba ne, ba mu da wata alaka da ku, na sani akwai wani boyayyen labari mai matukar muni a tsakanin mu da gidan ku, ban sani ba, ko tsinto mu aka yi. Sai dai idan na tuna kalaman Abba da yake cewa tun muna ciki kake dawainiya da mu, haka kai ma kana yawan gaya min tun muna ciki kake son mu, sai indimauce, inrude ina neman wanda zai buda min wannan sarkakKiyar da ke faruwa. Don Allah ku sanar da ni abubuwan nan domin infahimta. Su waye lyayena?
‘““Wacce Kaddara ce haka a jikinmu da har Umma take tsananin Kyamatar mu? Da gaske mu din haihuwar Karkashin mota ce? Ko kuwa wata Hausar ce daban? Ka gaya min wacece ni? Kai kadai za ka iya bude min komai kai tsaye. Ban taba tunanin tambayarka ba ne, saboda ina tsoron jin irin amsar da za ka ba ni, ko kuma irin yadda za ka daukenwac
6/10/22, 09:54 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚*
CHAPTER 5
*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*
MUN TSAYA
A hankali ta yi magana, wanda da ba don yadda ya tattaro natsuwarsa akanta ba, da babu abinda zai ji, “Na amince Deena, duk abinda ka yi dai-dai ne, ina jin tsoron Umma ne shi ya sa, kuma ta ce min in daina zama a falo. Ban san me na yi wa Umma ba bata sona Dee, ban san me zan yi wa Umma in burge ta ba, ban san mene ne musababbabin wannan tsanar ba, don Allah ka sanar min dalilin ka gaya min idan laifi na yi mata zan ba ta hakuri.�
Ta fara fitar da hawaye, ya sa hannunsa ya dauke hawayen yana sake duban ta, “Ba ki yi wa
Umma komai ba, ban san mene ne dalilin da ya sa Umma take gwada maki irin wannan tsanar ba, kamar ba jininta ba.�
Nasreen ta girgiza kanta, “Ka daina zolaya ta da irin wadannan maganganun Deee, tuni na yi hankalin bambance fari da baki, na sani, da ni da Nawfal ba jininku ba ne, ba mu da wata alaka da ku, na sani akwai wani boyayyen labari mai matukar muni a tsakanin mu da gidan ku, ban sani ba, ko tsinto mu aka yi. Sai dai idan na tuna kalaman Abba da yake cewa tun muna ciki kake dawainiya da mu, haka kai ma kana yawan gaya min tun muna ciki kake son mu, sai indimauce, inrude ina neman wanda zai buda min wannan sarkakKiyar da ke faruwa. Don Allah ku sanar da ni abubuwan nan domin infahimta. Su waye lyayena?
‘““Wacce Kaddara ce haka a jikinmu da har Umma take tsananin Kyamatar mu? Da gaske mu din haihuwar Karkashin mota ce? Ko kuwa wata Hausar ce daban? Ka gaya min wacece ni? Kai kadai za ka iya bude min komai kai tsaye. Ban taba tunanin tambayarka ba ne, saboda ina tsoron jin irin amsar da za ka ba ni, ko kuma irin yadda za ka daukeni a matsayin butulu wacce ta
ZAMU TASHI
kasa godewa Allah da irin baiwar da ya bani, wajen suturtani a cikin gidanku, ya yi min baiwar ilimin addini da na boko.�
Sultan idan hankalinsa ya yi dubu to ya tashi, ya jima yana tsoron zuwar wannan ranar domin ba shi da cikakken amsar da zai iya ba ta, haka har yanzu ba ta yi girman da za ta iya daukar tashin hankali irin wannan ba, ya so ne sai komai ya natsa sannan ya dauke ta zuwa gun dangin mahaifiyarta. Haka yana tsoron ya gaya� mata ta tada hankalinta wajen neman ubanta, wanda a yanzu bai san wanene wannan uban ba.: Sai da ya tattaro dukkan natsuwarsa sannan ya ja dogon hancinta, wanda kullum ya hadu da ita sai ya taba, “Nasreen na san idan na rantse maki za ki yarda da ni ko? Wallahi ba a KarKashin mota aka haife ku ba, ina kika taba jin an haihu a KarKashin mota? Kuma kina da uwa kina da uba kina da dangi kamar kowa. Ina jiran mutane su gama abubuwan su ni kuma a lokacin ne zan ba kowa kunya, zan dauko mahaifinki ki gan shi har ku zauna kusha hirarku. Don Allah kada ki sake yi min irin maganar nan kin ji?�
Babu musu ta daga kanta, “Na ji, don Allah ka yafe min don Allah. Insha Allahu, ba zan sake yin maganar ba.
Sai da yasa hannunsa ya warware gashinta. da ta tubke sannan ya ce, “Ba ki yi min komai ba, haka yin maganar da kika yi, ba zaisa ince maki butulu ba, har abada kin gama min komai da kika zauna a matsayin matata. Ki Kara haquri watarana sai labari.�
Ba ta yi magana ba, domin sakon da yake tura mata suna cin nasarar isowa inda ake bukatar su iso. Sun yi nisa a wata. duniya suka ji bugun Kofa hakan yasa ta. Kankame shi.
Ya zame kansa ya mike zai je ya bude, ta kame shi ta mayar da shi Kirjinta da yake sake gigita shi, ta yi magana a hankali, “Za ka bude kofa a yanayin da nake ciki?� Sai yanzu ya dawo da dubansa jikinta, ta dan haskem fitilar ya fahimci abinda take sufi, don haka ya mayar mata da kayanta a natse kamar ba shi bane ake buga masa kofa da Karfin tsiya. Ya maidata ya kwantar ya jawo mata bargo, sannan ya kashe wutar dakin gaba daya ya dawo duhu. Yana budewa Zakiyya tana kokarin cusa kanta a cikin dakin. Ya kalleta tare da yamutsa fuska yana
* kallon su Umma da Hafsat da duk suka yi cirkocirko, “Umma lafiya kuwa? Me ke faruwa ne?�
Umma ta tabe baki, “Yau sai Nasreen ta bar gidan nan. Ashe yawon dare yarinyar nan take fita?� Sultan ya bata fuska, “Haba Umma ki dinga kyautata zato a gun dan’adam. Me ya faru kuma?�
Umma ta ce, “Idan Nasreen ba tana tare da kai bane, to babu ita a cikin gidan nan.�
Sultan ya zaro idanu kamar gaske, ya kuma nuna tashin hankalinsa a fili, hakan ya sa dukkansu da suke zargin Nasreen tana tare da shi * suka kauda tunanin, “Nasreen ta fita a gidan nan? Kuma anduba ko ina? Kai babu yadda za a° yi ta iya fita bayan ga “yan sanda. Mu je gurin su din.�
A Kaggauce suka fice, Umma tana jin dadi a ranta ta riga tasan Karshen zaman Nasreen ne yazo a gidan, domin ita zarginta ya koma ko tana tare da daya daga cikin ‘yan sandan ne?�
Suna ficewa Nasreen ta laluba ta nufi Kitchen, ta laluba ta tara ruwan zafi a famfo ta tsaya shiru gabanta yana fadiwa da Karfi. Tunani ne fal a cikin cikinta, haka kalaman Umma da ta ji suna ta yi mata yawo a tsakiyar kai, tana
mamakin yadda Umma za ta dinga cewa tana bin maza, tana dangantata da Zina, wannan abun yana matuKar yi mata ciwo. .
Sultan ya tsaya a gaban daya daga cikin ‘yan sandan wanda idanunsa biyu ya ce, “Kun ga Nasrcen ta fitonan?�
Ya girgiza kai ya ce, “Oga sir, ina nan zaune ban tashi ko‘ina ba, babu wacce ta fito nan.
Kawai Sultan ya juya yana cewa, “Anya Nasrcen ta bar gidan nan a tsohon daren nan? Babu mutumin da zai iya fita a gidan nan ba tare da izinina ba, bare kuma ficewar dare, ai da na sallame su domin sun zama marasa amfani. Mu koma ciki a sake duba bandaki ko wani wurin.�
Hafsat ta yi carab ta ce, “Har bandakin na duba babu ita.�
Banga komai ba, suka dawo falo yana . magana da Karfi, “Yanzu ina Nasrccn taje? Lallai idan ya tabbata ta fitan, zan kuwa bata mata rai. Ko da kuwa nan da Gate ta je. Yarinyar da bata iya dogon tafiya ita kadai shi ne za ta fice?� Nasrcen ta saki ajiyar zuciya, sannan ta dan kwarawa Kafarta ruwan zafin da ta dibo, duk da babu zafin kirki sai ta fasa Kara, hakan yasa
Sultan yayi hanyar kitchen da sauri har ya riga su shiga. Yana zuwa ya riketa sosai a jikinsa, kasancewar akwai Kamshin turarensa a jikin Nasreen Umma tana iya ganewa suna tare shi ya sa ya yanke hakan. Gabadaya aka shigo ana leken Kafafun da take ta wash! Wash!!
Sultanya dubi� Hafsat ya ce, “Ke kawo min gishiri. Haba Nasreen na fara gajiya da : lamarinki, kina’sane da ba gani kike yi ba, amma � sai ki dinga zuwa inda za ki ji ciwo don ki bar ni . da wahala ko? Me ya sa:ba za ki tashi Hafsat ta kawo maki ruwan zafin ba?�
Hafsat ta murguda baki tace “Kuma � Yaya idonta biyu*lokacin, ashe ta sadada ta fita.�
Sultan ya dago yana dubanta cikin takaici, “Cewa na yi ki:samo.min gishiri.�*
Nasren ta fara fitar da hawayen bakin cikin yadda Umma bata taba kamata da wani ba, amma take dangantata da zina. Bayan ta sani shaidar zina a musulunci abu ne mai matuKar wahala. . .
Umma da Zakiyya suka dub juna cike da farin ciki yau Sultan ya taba ‘yar Gold. Da kansa ya shafamata gishirin kadan don yana sane da ba konewa ta yi ba. Yana dago ta ya ce.
“I love you wife.� A hankali ya yi maganar babu wanda ya ji sa ita da aka fada dominta.
Sakon ya ratsa ta har ta saki murmushi cikin hawayen ta motsa labbanta. A wurin duk suka aika wa juna sako wanda a zahiri babu wanda ya gani haka babu wanda ya fahimta, duk wayewar da Umma take kirawowa kanta.
� A falo ya ajiye ta ya dubi Hafsat ya ce, � “Ke, hado mata tea.� Babu musu ta wuce ta hado tea, ya mika mata tana sha. Bayan ta sha fiye da � rabi ne ta ajiye a nan.