Showing 15001 words to 18000 words out of 123375 words

Chapter 6 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt

yayi magana, “Kada ki damu, akwai zaman da zamu yi da abokaina akan wata matsala, don haka zanyiwa Dr. Aslaf magana, akan idanunki zai bamu shawarar Kasar da ya kamata mu tafi da ke sai a duba idanunki. Idan ba haka ba, waye zai aurar min Nasreen dina a haka?� Wani irin tafiya ta yi mai kama da tafiyar barci. Ga iska yana Kara kada su. Tana murmushi tana magana kamar wacce ta sha wani abin maye, “Deena, zan zauna tare da kai ba zan auri kowa ba.� Dagata ya yi saboda da gaske ya gane tana cikin wani yanayi. “Tashi muje Office dina.� Girgiza kai ta yi, “Ina son indauwama a nan wurin. Kamshin filawowin suna sanya min nishadi da sanyi a zuciyata, wanda rabon da in ji � hakan na jima. Dee wani abu ke tsaya min a Kirji yana min zafi sosai, ko nasha ruwa baya wuce wa.� Wannan Karon tausayinta ya kama shi, Nasreen ta yi Karama da yawa da shiga irin wannan yanayin, “Ki dinga addu’a Nasreen kin ji? Mu je Office dina akwai abinda zan dauka.� Da isar su Office din, “yan sanda suka taso ° suna sara masa, shi dai yana rike da hannun Nasreen. Gaba daya mutane idanunsu akan Nasreen yake, wani ma cewa ya yi koda take makauniya zai iya aurenta inhar Oga zai ba su ita. A kujera ya ajiyeta, a lokacin ne kuma aka gaya masa wani case ya ce, a shigo da matar a gurguje. . � Tana shigowa tana bayani bai dago daga abinda yake yi ba bare ya dubeta, “Yallabai mijina ne ya zaneni,� Yana rubutunsa ya ce, “Me kika yi masa har ya duke ki?� Ta share hawayenta ta ci-gaba da magana, “Ya musuluntar da ni ne, ya raba ni da kowa, ya ce min addinin musulunci shi ne addinin gaskiya, nasha wahala da iyayena har na rabu da su, na zabe shi da addininsa. Amma tunda na aure shi kullum sai ya yi min gori akan addininsa, kullum idan na yi kuskure sai ya ce min matsalar tubabbe kenan. Yallabai ina son a raba aurena da shi, zan koma addinina, ko dan inhuta da gorinsa da na ‘yan uwansa.� Tun bayan da ta ambaci ta koma addininta ya ajiye rubutun yana dubanta. Damuwa ce shimfide a fuskarsa. Har yaushe musulman mu za suyi hankali? A hakan wasu suke son jawo wadanda basa addininsu su dawo addinin su? Bai yi magana ba, har sai da ya gama nazari sannan ya ce ta fada inda za a ga miinta. Ta kwatanta ‘ya bada umamnin a je a kawo masa shi yanzu. Ya dubi matar ya ce, “Amma kafin in ce komai, daina daukar musulunci haka yake. Musulunci abu ne mai sauki da kuma dadi. Idan kina cikin musulunci zaki sami hanyoyin warwarewar matsalarki, wanda ina ganin baki bi hanyar bane shi ya sa kike dan samun matsala. Haka kuma mu a cikin addininmu akwai jarabawa, da Allah yake yiwa bayinsa. A Karkashin jarabawar nan zaki sami hanyar shiga Aljannah. Misali a cikin Alqur’ani akwai waraka a ciki. Ko malamin da ya musuluntar da ke bai gaya maki hakan ba?� Sunkuyar da kanta Kasa ta yi ta ce, ‘“Malamin ya yi min bayani. Amma bai gaya min musulmi zai lya yiwa wanda ya aro addininsa gori ba, haka bai gaya min akwai duka a cikin sharuddan aurenku ba. Ina zuwa Islamiyya har yau ban ji inda malaman ta ce ana gorin addini ba.� Sultan ya rintse ido yana kallon rubutun suna komawa kamar yashi. Saudat! Ita ta fado masa arai. Mahaifiyar Nasreen da Nawfal. Tasha gori akan addininmu amma kuma tana rike da mu. Hatta mahaifiyarsa har yau tana yi wa su Nasreen gori akan addinin da Saudat ta aro. Sultan ya girgiza kansa, “Hakane, haramun ne ma musulmi ya ci zarafin dan uwansa musulmi. A cikin addininku akwai na banza akwai na kirki, haka muma a cikin addinin mu, akwai irin hakan, Amma mu ba mu gorin addini, haka kuma ke kin fi shi rashin zunubi, saboda kin tuba kin musulunta. Addinin musulunci akwai dadi idan kika natsu a cikinsa. Dokokin mu basu da tsauri. Haka a KarKashin wannan auren da kike son a raba zaki shiga Aljannah. Haka ina son ki zuba ido ki gani, tun aduniya Allah zai saka maki, akan mijinki idan har da gaske yana zaluntarki. Shi Allah baya barin azzalumi. Kada zuciyarki ta yi rauni kawai dan namiji yana cuzguna maki, ki dauka irin taki jarabawar kenan. Idan Allah ya dubi zuciyarki ya tabbatar a wadace take da imani, da son addininsa, sai shi kuma ya saka maki. Kada ki ce wai sai kin ji dadi sannan zaki yabawa addinin musulunci.� A lokacin kuma aka shigo da Bala mijin Karima. A Kasa yasa ya zauna yana aika masa da mugun kallo mai cike da tsana. “Ka san wannan ko?� Ya nuna masa Karima da hannu. “Yallabai na santa matata ce, shekarun mu uku da aure da ita.� Sultan ya dinga jinjina yayi wuri ta fara fuskantar matsala, “Ta ce tana son a raba aurenku, saboda kana dukanta, don haka zan tura ku kotu, daga nan zaka amshi irin naka hukuncin.�
6/5/22, 10:27 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚*






CHAPTER 6






*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*




A JIYA MUN TSAYA


tsauri. Haka a KarKashin wannan auren da kike son a raba zaki shiga Aljannah. Haka ina son ki zuba ido ki gani, tun aduniya Allah zai saka maki, akan mijinki idan har da gaske yana zaluntarki. Shi Allah baya barin azzalumi. Kada zuciyarki ta yi rauni kawai dan namiji yana cuzguna maki, ki dauka irin taki jarabawar kenan. Idan Allah ya dubi zuciyarki ya tabbatar a wadace take da imani, da son addininsa, sai shi kuma ya saka maki. Kada ki ce wai sai kin ji dadi sannan zaki yabawa addinin musulunci.� A lokacin kuma aka shigo da Bala mijin Karima. A Kasa yasa ya zauna yana aika masa da mugun kallo mai cike da tsana. “Ka san wannan ko?� Ya nuna masa Karima da hannu. “Yallabai na santa matata ce, shekarun mu uku da aure da ita.� Sultan ya dinga jinjina yayi wuri ta fara fuskantar matsala, “Ta ce tana son a raba aurenku, saboda kana dukanta, don haka zan tura ku kotu, daga nan zaka amshi irin naka hukuncin.�


ZAMU TASHI


Bala ya shiga yayyanka idanu, “Yallabai a yi min afuwa, sharrin shaidan ne ba zan sake dukan ta ba.� Sultan da zuciyarsa ke zafi, ya dubi Copral Ya ce, “Na tsani mutum ya aikata laifi da gangar yace sharrin shaidanne. Har yaushe musulmin Kwarai zai dinga barin shaidan yana shigowa cikin rayuwarsa, yana wanzar masa da sharri a cikin gidansa? Don Allah dauke min shi ka hukunta min shi har sai ya bani tabbacin shi ne shaidanin.� Bala ya gigice yana bayar da hakuri hakan yasa Sultan sake watsa idanunsa akansa, “Gaya min sharrinka ne yasa kake dukan matarka, kake yi mata gori akan ta aro addininka ko kuwa har yanzu na shaidan ne?� : Bala ya ce, “Yallabai sharrina ne kuma nayi kuskure.� Sultan ya ajiye biro yana dubansu, “Malam Bala musulunci bai yarda miji ya dinga dukar matarsa ba, domin ba ankawo maka ita bane domin ka dinga dukanta ba. Musulunci bai yarda da gori akan komai ba, bare har akai ga gori akan babban abu, wato addini.


Musulunci bai yarda mumini ya dinga tauye hakkin iyalansa ba. Kai hakkin wani ma a waje haramun ne bare akai ga hakkin matarka. Yanzu kasa matarka ta hada mu gaba daya tana yi mana kudin goro, tana kallon malaminka da ya musuluntar da ita a matsayin mugu, tana kallon iyayenka da ‘yan uwanka a matsayin mugaye. Daga Karshe sai ta ji ta tsani musulunci tana neman ta koma wancan addinin da ka sameta a cikinsa. Bayan kai da kaje za ka aureta baka ji lokacin da malaminka ya ce hakkinka ne ka yi mata duka, da gori ba. Malam Bala ka ji tsoron Allah. Ka sani sai Allah ya saka mata, kamun Allah kuma ba.irin kamun mu bane mu hukuma. Kurkun Allah ba irin namu kurkun bane. Ka kiyaye abubuwan nan, za ka fi Karfin gidanka, cin matarka, shanta, rashin lafiyarta kaucewa gaya mata munanan kalamai. Domin kalamai wannan idan kana gaya mata su marasa dadi zaka wayi gari kalamanka su kasheta. Idan kuma kaima jahili ne ba ka san ilimin addinin musulunci ba, ka dauko ‘yar jama’a ka aurota kana yi mata koyarwa irin na jahilai don Allah kaje ka nemi ilimin addinin nan, kada kayi mana asarar mutum daya daga cikin musulunci. Ka � ka kare hakkin matarka, da mutuncinta. Ina son Copral ka tafi da su, a kawo min malamin da ya daura aurecn da kuma wanda ya musuluntar da ita. “Ni Office dina idan anzo irin wannan case din sai na bi diddigi naji dalilin da yasa ake hakan. Idan mutum ya yi alKawarin gyarawa bai gyara ba, ina da hukunci kala-kala da zai sa mutum ya gyara ba don yana so ba. Bana daukar shirme. Haka bana barin a ci mutuncin mata! Domin ita mace ta wuce komai, sai da ita za ka sami natsuwa, ita ce ta dauki cikinka tana amai, tana kasa barci cikin dare saboda laulayi, a hakan za ta girka maka abinci, ta kai maka ruwan wanka. Tana renon cikinka tana renonka. Idan ta tashi haihuwa, ta kai sati tana naKuda. Wata ko nan take mutuwa, ko shekara ba za a yi ba, za ka Karo wata. Idan ta tsallake ta Haifa, ta shayar ta lura da lafiyarsa. Idan bai da lafiya ta zauna cikin dare tana nemo dabara, kai kuma kana can kana barci. Ta wanke masa kaya ta wanke naka. Mace dai ita ta kawoka duniya ita ta reneka. Shi ne don rashin hankali ka rasa abin wulakantawa sai ‘ya mace? Ka tambaya wane ne Abdullahi Lukman! Bana daukar irin wannan shirman.� Jikin Bala da Karima ya yi matuar sanyi, hakika D.P.O dinnan na daban ne, yasan hakkin dan adam. Ya dubi Nasreen yaga hawaye shimfide a fuskarta. Hankalinsa ya tashi don haka ya taso ya dawo kusa da ita, yasa yatsa yana dauke hawayen. “Nasreen menene? Waye ya bata maki?� Fuskarta dauke da murmushi ta ce, “Babu wanda ya bata min. Ina godewa Allah ne da nayi sa’an dan uwan mahaifiya mai sanin ya kamata. Allah kadai yasan wahalar da mahaifiyata tasha kafin ta kawo ni gidan duniya. Allah ka sakawa mahaifiyata. Allah kasa mahaifina bai wulaKanta min ita ba. Daga Karshe Allah ya saka maka da renonmu da kayi tun muna cikin tsumma.� Sultan ya mike ya dago ta, Zuciyarsa take gaya masa ya rungumeta, Don haka ya mayar da ita Kirjinsa ya rufe da hannayensa, Sannu a hankali natsuwa ta ratsa su, Nasreen ta sake lafewa a Kirjinsa tana sakin ajiyar zuciya. Da kansa ya ga dacewar ya janyeta, ya kamo hannunta suka fice. Mansur da ya gama kallon hotunan Nasreen ya zuKo tabarsa yana fesarwa a fuskar su Hajiya Ladidi. Hajiya Salma ta Kufula don ta tsané rashin tarbiyya, za ta yi magana, Hajiya Ladidi ta matse mata hannu, dole tayi shiru suna ci gaba da kallonsa, “Hajiya wannan yarinyar ta hadu. Soyayyar Karya kuke son in nuna mata, amma a zahirin gaskiya ni sonta nake yi da yaske. Kuma Wallahi! Wallahi!! Sai na aure ta da Karfin tsiya. Wannan ai kalata ce. Hajitya ku bar kudinku wannan da kudina zan aureta.� Hajiya Salma da Hajiya Ladidi suka yi ‘murmushin jin dadi. Abu kamar wasa soyayyar Nasreen ya mamaye ko ina na zuciyar Mansur, wanda har ya kasa hakuri ya shirya cikin shigar kamala ya je gidan da sunan hira. . A falo Hajiya Salma ta tare shi, ta kuma turo Naareen. Gaba daya ya shagala wajen kallonta, kwafsi daya ne, matsalar idanu, amma shi sannan babu shi a zuciyarsa, babban burinsa ya mallaketa ko ta halin KaKa.��Wanene kai? Me kake nema a wurina?� Sai da ya shafi sajensa kafin ‘ya ce, “Sunana Mansur. Sonki nake yi, kuma Wallahi sai na aureki.� “Ni kuma bana sonka, ka tafi tun kafin Abbana ya zo ya sameka anan.�Www.bankinhausanovels.com.ng Mansur ya mike yana tunkarota. A lokacin Abba da Sultan suka sawo kai. Da Karfi Abba ya ce, “Innalillahi wa inna ilaihirraji un.� Wani irin jiri ya nemi ya kwashe shi ya riKe jikin bango, yana sake watsa idanunsa akan Mansur. Tuni Nasreen ta mike a gigice tana cewa, “Abba Wallahi ban san shi ba, ban taba jin ko muryarsa ba, Umma ce ta ce dole sai na zo, amma ban san shi ba. Ka yarda da ni Abba ba zan yi maka, Karya ba. Ta sake rushewa da kuka.� _ Shi kuwa Sultan ya rasa dalilin da yake jin zai iya shake Mansur ya mutu har lahira. Don hakane ya wuce Abba ya shake shi, wanda duk Karfi irin na Mansur ya kasa Kwatar kansa daga irin rikon da Sultan ya yi masa. Idanunsa suka firfito waje. Umma da su Hafsat suka rugo a guje sakamakon jin Kakarin Mansur, Umma ce ta Kwace shi, sakamakon marin da ta dauke Sultan da shi, tana wani irin huci, “Sake shi mara mutunci kawai, Ina ruwanka idan saurayi ya zo wurinta? Ko za ka hanata aure ne? lyye Nace aure za ka hana tayi Nine nan nayi masa izini tunda ya ce yana sonta da aure, ai ba jiKata zamu yi mu sha ba, dole za ta yi aure.� Abba dai yana tsaye Kafafunsa duk sun yi sanyi. Sai yanzu ya sami ikon yin magana, “Kai zo ka fice min daga gida tun kafin ka yi nadamar haukan da kake shirin yi. Idan na sake ganinka a gidana zan yi maka mafi munin wulakanci. Nasreen share hawayenki baki da laifi. Laifin wancan ne, kuma zan dau mataki.� Ya fada yana nuna Umma da yatsa. Mansur har ya kai bakin Kofa ya waiwayo ya kafe Nasreen da idanu, “Ina nan dawowa in aureki matata. Zan aureki ko da kuwa wannan ne abu na Karshe da zan yi in mutu.� Sultan ya nufo shi, ya riKe wuyan rigarsa, “Za ka mutu kuwa! Idan wannan bai zama abu na Karshe da za ka yi ka mutu ba, zai zama ganganci na Karshe da za ka yi ka bakunci lahirar. Idan ka san da gaske kai mara kunya ne, anjima ba sai gobe ba, ka sake taka Kafafunka a Kofar gidan nan. Fice!� Ya tunkuda Kyayarsa zuwa waje. Ya koma kawai ya zauna a kujera ya yi tagumi yana kallon mahaifiyarsa. Abba ya nuna ta da yatsa ya ce, “Ke ce ajalina Salma. Idan na fadi na mutu ke ce sila.� Hajiya Salma ta ce, “Oh ni kada ka sa min sharrin kisa. Yarinya dai dole za ta yi aure. Kai kuma lafiya kake kallona kamar tsohon maye? Ko dukana nima za ka yi ne?� Mikewa ya yi kamar zai fita sai ya ji muryar Haidar yana cewa, “Gaskiya Abba ka tsani Umma da yawa, idan ba haka ba, menene a ciki don Nasreen ta yi soyayya? Duk kuka tashi hankalinku kamar kun kama ta da kwarto? Kuma…� Sultan ya juyo ya watsa masa idanu tare da mika dan yatsansa alamun gargadi. Hakan yasa Haidar hadiye kalamansa, domin bai san cewa bai fita daga falon ba, da babu abinda zai sa shi tofawa. Sultan ya kama hannun Abbansa suka fice kawai. Shi dai Abba a ranar ko barcin kirki bai yi ba, wani tunani ne a cikin zuciyarsa da yake tunanin irin kuskuren da zai iya tafkawa, inhar ya zubawa Umma idanu ta Sauya masa tsarinsa a kan yaran. Haka acan dakin Sultan ya kasa barci, sai tunani fal cikinsa. Dole ya koma dakin Nasreen tana kwance cikin bargo, yasa hannu ya yaye bargon. Abinda ya ganine yasa shi saurin rufeta yana ambaton dukkan addu’ar kariya daga fadawa _ tarkon shaidan. Motsinta ya ji ta tashi ashe ba tayi barci ba, tana KoKarin yaye bargon ta rungume shi, ya dakatar da ita ta ta hanyar rike bargon. Sai a lokacin ta tuna da irin kayan da ke jikinta, don haka ta shiga laluben hijabinta. Shi ya dauko ya taimaka mata tasa. “Nasreen! Me yasa kika fito wajen dan iskan nan? Don Allah Nasreen ki taimakeni inrike amanar da mahaifiyarki ta bani akanku. Na yi mata alKawarin zan iya, ki taimake ni in mutu ba tare da antambayeni yadda na rike amanarku ba. Na kasa barci Nasreen, ina da abubuwan ci gaba da nasa a gabana, amma saboda ku na kasa aikata komai, ina son in aurar da ke, Nawfal ya kama aikinsa, sai insamu nima inKarasa ayyukana. Za ki taimaka min nima burikan nan nawa su cika?� A gigice take magana, “Wallahi Dee ban san shi ba, ka yarda da ni. Ina dakina Anti Hafsat tazo ta yi min jagora muka je falon. Ya ce yana sona, nace bana sonsa. Ajiyar zuciya ya Kwace masa, yaso a daren ya shiga dakin Hafsat, sai kuma ya canza tunani. “Allah ya yi maki albarka koma ki kwanta kiyi barci.� Babu musu ta koma ta kwanta, amma kuma bata sakar masa hannun ba, Zuba mata idanu ya yi yana jin wasu abubuwa suna sake canza mazauni a cikin jikinsa. Yana jin_kansa kamar ba shi ba, Dayan hannunsa yasa ya mayar da gashin kanta baya da suke Kokarin | rufe mata fuska. A hankali ya matso sosai ya bata fake a goshi. Wannan lamari yasa Nasreen nutsewa wata duniya. Wanda har bata san lokacin da ya zare hannunsa ya fice daga dakin ba. Dakin Nawfal ya leKa ya same shi zaune akan dadduma yana Sallah. Ibadan yaran yana burge shi, ya sake. gode. wa Allah da, dukkan abubuwan da ya dora su akai babu wanda suka kuskure masa; A hankali yayi maganar da ya ratsa kunnuwan Nawfal. Nawfal kada ka mance ni a cikin addu’arka. Haka, kada ka mance da mahaifiyarka.� Ya sa kai ya wuce, Dakin Hafsat

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login