Showing 39001 words to 42000 words out of 123375 words

Chapter 14 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt

kuma yaki amincewa a sanar da kowa. Wannan lamari yasa Justina kwanciya ciwo har sai da aka sake shi.


“Bayan ya fito ne ya yi ta neman hanyar da zai sake ganin Justina, amma abin ya faskara, domin ko Makaranta anhanata zuwa. Ni na nake kai mata wasika idan ya rubuto sai ta bayar da amsa inkai masa.


Justina ta rame ta lalace amma kuma iyayenta basu tausayawa mata ba. Babanta ma cewa ya yi gara ta mutu da ya ganta tana cikin musulunci. Rana ta Karshe ne, ta gudu, taje ta sami Sani. A ranar ma ni na raka ta. Ya kama hannayenta a karo na farko ya ce, “Justina daga yau sunanki Saudat kin ji? Zan dauke ki in kai ki wurin wani babban Malami domin ya musuluntar da ke, ki daure komai zai zo mana da sauKki kin ji?� Babu musu ta amince masa, suka je wurin malamin ya gaya mata dokokin shiga musulunci ta ce, ta yarda. Sannu a hankali ya mayar da ita gidansu, ba tare da ansan ta fita ba, ta koma tana yin addininta a Boye haka duk lokacin da za su hadu da Sani ni nake hada yadda haduwarsu za ta kasance. Sani ya taimaka sosai wajen koyawa Justina _abubuwan addininsa.


. “Da yake yarinya ce mai Kwakwalwa nan da nan take kwashe dukkan bayanansa. Har aka zo gabar aure. Ya tabbatar mata da zai aureta, zai dauketa ya kaita wajen


babban yayansa. Haka suka shirya suka tafi wajen Yayansa. Sai dai ya Boye masa sauya addinin da ta yi zuwa nasa, kasancewar yasan halin Yayan akwai tsauri da Kin addinin da ba nasa ba. Don haka yasa Alkhairi ya nuna masa zai tura a nema masa aurenta. Sai dai suna fita daga gidan yayan yasa aka bi bayan su, har aka gano komai akan Justina.


“Da aka gayawa Yayan hankalinsa ya ~ tashi jin cewar ba addininsu daya ba, amma kuma da yake yana da irin nasa burin sai ya � share ya bar zancen. Justina taje ta nemi gafarar iyayenta tace masu ba za ta Kara ba. Hakan yasa suka amince da ita, suka Kyaleta ta ci gaba da zuwa Makaranta. A hanyar dawowarmu ne aka sace mu da ni da ita aka sanya mu a cikin mota sai wani gida. A nan wurin mutumin nan ya yi wa Justina fyade. Tana kuka aka dauke mu aka dawo da mu inda aka dauko mu. Justina ta yi kuka, ta yi kuka kamar ranta zai fita.


Ni nake ta ba ta haKuri, na kuma gaya mata ta kira Sani ta gaya masa komai, sai ta ce min, “Nora kin san waye ya yi min haka? Yayan Sani shi ya aikata min haka. Ba zan iya gayawa Sani ba, ko na gaya mashi ba zai yarda ba. Ya gaya min Yayansa malami ne. Me yasa zai yi min haka? Yanzu Nora ya zanyi?� Na ce mata ta yi_ shiru ta bar maganar. Abu kamar wasa sai da yayan


“Sani yasa aka sace mu sau uku yana biyan buKatarsa da Justina.�


* Al-ameen da ya yake jin sunan Justina din yana Bata masa rai ya dubeta ya ce, “Anti pls kira ta da Saudat dinta.�


Kowa ya gyada kansa don sun fi gamsuwa da Saudat din fiye da Justina.


Nora ta gyada kanta ta ci gaba da magana tana hawaye, “Ana haka kawai sai ga ciki. Ta shiga tashin hankali da bayyanar cikin nan, haka ta gaya min ba za ta iya zubarwa ba, domin angaya mata hukuncin wanda ya zubar da ciki tamkar ya kashe rai ne. Babu yadda ban nuna mata irin matsalar


da za ta iya shiga ba, amma taki amince wa maganata. A lokacin da iyayenta suka ankare sai suka yi mata dukan tsiya suka koreta, ni na boyeta a gidanmu nasa aka nemo Sani ta fito tana kuka ta gaya mashi komai, sai ya gaggaya mata magana, ya zazzageta ya kuma ce-bai yarda fyade akayi mata ba, taje ta nemi wanda ya yi mata ciki � amma kada ta sake tunawa da wani mai suna irin nasa. RoKon duniyar nan mun yi � wa Sani amma yaKi taimaka mata. Ita kuma ta Ki gaya masa wanda ya yi mata hakan, sai � take ganin wannan wani al’amari ne mai girman da bai kamata yaji ba. Da farko a gidan mu ta fara zama, iyayena suka koreta shi ne tabi titi. Saudat tasha wahala a duniya, ta koma bara, tana samun abinda take ci, duk da hakan tana nan a cikin musulunci kullum da dogon hijabinta. Har sana’ar wankin mota ta yi domin ta dinga samun abinda za ta ci. Daga baya ne da mutane suka ankare da cikin jikinta shi ne musulmanku suka tsaneta, suka sa ta tsani


duniyar gaba daya. Hakan yasa ta je har gidan Yayan Sani, ta bada sako a ba shi. Wannan lamari ya daga_ hankalin Yayan Sani har ya aiko mata da barazana. Haka ta ci gaba da renon cikinta cikin wahala da Kuncin rayuwa, shi kuma ya ci gaba da farautar rayuwarta, har Allah ya bashi ikon cimma burinsa na ganin ya kasheta. Wannan shi ne abinda na sani a kan Saudat! Idan an gaya maku wani labarin


. sabanin wannan to Karya ake yi, wanda na gaya maku a yanzu shi ne gaskiyar.� �


Sultan ya sauke ajiyar zuciya ba yadda ya kamata ba. “Kinsan waye Yayan Sanin? Kin taba ganinsa? Me ya sa ya kafa maki doka yake bibiyar rayuwarki?��


Ajiyar zuciya ya Kwace mata ta ce, “Ban taba ganinsa ba, ban san shi ba. Duk abubuwan da yake yi yana turowa ne. Kamar lokacin da aka kashe Justi� Ku yi haKuri aka kashe Saudat. Sai aka ce ba a ga gawanta ba, haka ba asan me ya biyo bayan kasheta da aka yi ba. Shi ne yake zargin ta


gayawa wani ne kamar yadda ta yi ta aiko masa da barazana akan cikinta, da kuma cewar za ta tona masa asiri. Anduba kayanta babu wasu hujjoji, don haka aka biyoni gida akayi bincike a gidana aka ga babu komai,__, daga nan aka yi min gargadi da za a iya kasheni idan har na kuskura na fada wani abu. Iyayen Saudat sunyi kuka, sun so ko gawanta su samu, sun yi danasani. Yanzu haka Babanta yana kwance yana fama da ciwon zuciya, saboda rashin ‘yarsa. Amma ni har yanzu ban taba ganinsa ba, ko


� gunansa ban sani ba, ku yarda da ni ba zan yi maku Karya ba.� Sultan ya bugi bango da Karfi yana jin
babu ma amfanin wannan tatsuniyar. “Shi . Sanin ya za a yi mu gan shi?�
Girgiza kanta ta yi, “Ban san yadda za a yi mu ganshi ba, amma akwai abokinsa wanda shi yake hadamu da shi a duk san da muke son ganinsa, zan je innemo shi sai ya gaya mana inda za mu je mu ganshi.�


Sultan ya gyada kai yana dubanta, “Za mu mayar da ku gidanku, zamu sa ‘yan sanda su kula da shige da ficenku. Ina buKatar sanin inda zan je inga Sani a kwana biyu kacal. Kada’ki wuce hakan. Maganar miliyan dayanku da muka yi maku alkawan ‘yan sandanmu za su tafi maku da kudin sai kuyi amfani da su. Ya zama dole mu gano


wanene azzalumin da ya aikatawa Saudat fyade ya kuma aika aka kasheta.� Sai da aka fice da su kafin suka zubawa juna ido da alama sun rasa mafita.


Ashmaan ya fara magana yana duban su, “Zan watsa hotunan Saudat a duniya, zan rubuta muna neman wanda ya kasheta, akwai kyauta mai tsoka. Bayan nan da wasu kwanaki zan watsa hotunan Nasreen da Nawfal in kuma ambatar babban kyauta ga duk wanda Allah yasa ya gansu.�


Mahbub ya dube shi a tsanake, “Mene ne fa’idar yin hakan?�


Aslaf ya zare glas din idanuns *a yana sake duban Ashmaan,
6/9/22, 09:31 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 2🦚*




CHAPTER 4




*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*







MUN TSAYA


Sultan ya gyada kai yana dubanta, “Za mu mayar da ku gidanku, zamu sa ‘yan sanda su kula da shige da ficenku. Ina buKatar sanin inda zan je inga Sani a kwana biyu kacal. Kada’ki wuce hakan. Maganar miliyan dayanku da muka yi maku alkawan ‘yan sandanmu za su tafi maku da kudin sai kuyi amfani da su. Ya zama dole mu gano


wanene azzalumin da ya aikatawa Saudat fyade ya kuma aika aka kasheta.� Sai da aka fice da su kafin suka zubawa juna ido da alama sun rasa mafita.


Ashmaan ya fara magana yana duban su, “Zan watsa hotunan Saudat a duniya, zan rubuta muna neman wanda ya kasheta, akwai kyauta mai tsoka. Bayan nan da wasu kwanaki zan watsa hotunan Nasreen da Nawfal in kuma ambatar babban kyauta ga duk wanda Allah yasa ya gansu.�


Mahbub ya dube shi a tsanake, “Mene ne fa’idar yin hakan?�


Aslaf ya zare glas din idanunsa yana sake duban Ashmaan, “Idan kayi hakan


ZAMU TASHI


Ashmaan za a sami matsala. Wanda muke nema zai gane magana bata mutu ba, daga nan zamu fara wasan buya.�


Al-ameen ya girgiza kai ya ce, “Tabbas zai iya ankarewa da muna nemansa, ko ya gudu, ko kuma ya sanya mu fara farautar juna.�


Haisam ya ce, “Zai fi kyau mu fara gano wanene Sani? A ina za mu gan shi?� Barrister Tajuddeeen idanunsa yana kan Laptop da alama shi ba zai yi Korafin ba. Sultan ya zare glas ya ce, “Abinda Ashmaan yake fada akwai alamun hakan za a yi. Yanzu lalube muke yi a duhu, a yanzu ne za a fara wasan. Kawai ya gudu a cikin daji mu kuma muyi farautarsa. Idan muna binsa a boye zamu ci gaba da samun matsaloli, gara yasan muna nemansa, ta hanyar guduwarsa ne za mu iya gane shi.�


Ashmaan ya ce, “Very good mutumina. Hasashena kenan. Idan muka sa hoton Saudat zamu yi amfani da kalamai wajen jawo hankulan jama’a akan abinda ke
faruwa, daga nan hankalinsa zai tashi, zai fara farautar Anti Nora. Ita ce macen da yake da tabbacin inhar hukuma ta gana da ita, kashinsa ya bushe. A lokacin da za a kaiwa Nora farmaki, mu kuma mun dauke su daga wannan wurin, haka yaranmu za su yi ta kula da motsin kowa. Tarko zamu kafa masa insha Allahu zamu kamo shi. Amma idan aka ce a nemo inda Sani yake, amsar ita ce babu wanda yasan a wacce duniyar Sanin yake ciki a yanzu. Kun ga ashe wahala za mu ci gaba da sha, har mu ji mun


gundura da abin. Ku bar min wannan aikin @ hannuna ni na san yadda zan yi. Sai mu dage da addu’a domin ba a fara ba, yanzu dai za a fara wasan.�


Wannan bayanai na Ashmaan da Sultan ya gamsar da kowa haka kowa a wurin ya jinjina wa kaifin tunanin su. Haka suka tashi taron kowa ya kama gabansa.


Dukkan abubuwan da Ashmaan ya tsara, ya tsara su ne tare da taimakon Sultan, cikin ikon Allah aka_buga bayani akan


mutuwar Saudat, yadda aka kasheta, da kuma yadda ake neman Nora, da kuma wanda ya yi kisan, ganin Nora kadai ne zai Sa a gano waye ya yi kisan nan. Hankula sun tashi, yanayi ya sauya, wurare sun canza Haka sun dauke Nora da mijinta, Abin mamaki da al’ajabi sai gashi anshiga an sace Nora da mijinta, a lokacinne ‘yan sanda suka ci nasarar kamo wanda yaje da ninyar yin kisan. Sai dai yin hakan ya Kara tada hankalin wanda ya aikata wannan . mummunar aikin. Haka Karin jin dadinsa bai bari wadanda ya tura sun san fuskarsa * ba, bare har a ambaci sunansa a Police Station. Wahalar duniyar nan sun sha a � wurin Sultan amma babu takamaiman bayani. Wannan abu ya Kara jefa Sultan a cikin dogon tunani. A kwanaki biyun nan babu ranar da ba zai yi mafarkin Nasreen �. dinsa a cikin wahala da masifa ba. A cikin garin na Kaduna Sultan ne tsaye yana , Karewa gidan su kallo da har sun mance da � wata Nasreen da ta yi rayuwa a cikin su.
Yana shiga ya sami babu kowa, don haka ya kwanta, wani irin barci na babu gaira babu dalili ya kwashe shi.


A Katon falon da shigowarsa kenan ya samu. Ya sami Abban zaune a falo ya Kurawa tv idanu, ita kawa Umma sai aikin masifa take yi, tana yi tana Karawa.


Cike da mamaki ya shigo falon, sai ya dubi Umma sai kuma ya dubi Hafsat da take kuka kamar ranta zai fita. “Yauwa gara da Allah ya kawo min kai, ba zan iya ganin wannanr tashin hankalin ba.�


Abba ya dube ta cike da _ takaici, wanda hakan ke nuni da idan ma asirin ake banka masa, to Allah ya kubutar da shi, “Kada ki kuskura ki sa min da a cikin shirmanki da ‘ya’yanki. Ba su ba ne ‘ya’yan so? Alhamdulillahi. Tun yaran nan suna Kanana nake gargadinki da ki daina zagin ~ ‘ya’yan wasu, amma kika sawa kunnenki auduga kika toshe. Ke baki son mazinaci ko? Kin tsani zina ko? ‘Ya’yan zina ba su isa su zauna a cikin gidanki ba, har sai da kika kora su suka bi duniya. Yau ga ‘yarki da dan zina a cikinta, kuma Wallahi! Babu mai zubar da cikin nan sai an haife shi. Haka babu matakin da zan dauka ‘yarki ce ki yi duk yadda kika gadama da ita. Daman ‘ya’yan so ai Karshen su kenan.�


Sultan da yaji wani irin jiri mai Karfi ya shige shi, ya fada cikin kujera cikin wani irin jiri wanda bai san lokacin da ya zauna din ba. Yana ta kallon Hafsat na kallon tsoro da firgici. Hafsat ta Bata wayonta, amma bai ga laifin kowa ba, sai laifin mahaifiyarsa. Mace ce mai tsananin son kanta, sai Allah ya nuna mata ishara tun a gidan duniya.


Yana son ya yi magana Abban ya daga masa hannu. “Babu ruwanka ban kuma yarda kayi magana ba, ka zuba masu idanu su Karata can. Ai kaf zuri’arsu babu mazinaci, don haka babu wani yaro da ya isa ya aikata zina a gidan Hajiya Salma.�


Sultan ya mike ya dinga kifa mata mari yana Kwallo da ita, domin ji yake gara ya kashe ta da ya ga irin wannan abin kunyar. Firgigit ya farka daga irin barcin da yake yi, jikinsa duk ya jike da gumi. Idanunsa ya watsa a kan Hafsat wacce ita ta zo tashinsa.


A dimauce ya ce “Ke zo nan. Uban me kike jira baki fitar da mijin aure ba? So kike sai kin gama zama Mama a gida kafin ki yi aure?� Hafsat ta turo baki tana mamakin nawa take da har za ta yi aure yanzu?


Shi dai Sultan ya kasa dawowa hayyacinsa da irin mummunar mafarkin da ya yi akan Hafsat. Haka sai kallon cikinta yake yi kamar mai son dole sai ya tantance cikin gareta ko kuwa sharrin mafarki ne? Tirkashi! Duk ranar da Hafsat ta yi cikin shege babu ko tantama kashe ta Umma za ta yi ta huta. Ya fi kowa sanin yadda Ummansa ta tsani zina, ko da yake tsanar Zina a jinin zuri’ar Umma yake, kaf dinsu ba su Kaunar mazinaci ya matso inda suke, shi ya sa kullum a cikin tsaftace kansu suke.


Nasreenn ta farka cikin dare tana ja da baya, haka hawaye masu yawan gaske suke zuba daga idanunta. Tabbas ta ji hannayen wani a jikinta, amma kuma ba ta san ko wane ne ba, sannan tana da tabbacin Mansur baya gidan, hasalima yayi mata sallama da zai yi tafiya. Idan wani ne ya shigo ina masu tsaronta? Lalubawa ta yi tana neman Nawfal bata ji shi ba, ga hucin mutum a dakin,


Cikin kuka ta fara kwala kira, “Nawfall� Ji ta yi an toshe mata baki, ta yadda baza ta iya Kwacewa ba. Tashin hankali ya sake bayyana a bisa dakalin fuskarta. Da Karfi ta daddage ta ingice shi ta yi hanyar waje da gudu, sai dai bata sani ba, ta doshi bango ta buga kanta da karti. Tsananin azabar da ta tsirga mata yasa ta ja da baya, duk da haka bata daina Kofarin ficewar ba.


Hannunsa yasa ya dawo da ita baya, yana Kokann banKadeta, Tana son yin ihu babu dama haka kuma karfinta ya soma


Karewa. Mutumin da ke kwance akanta yaji anbuga masa wata sanda, mai girma da kauri. Da Karfi ya rike kansa sannan ya dago yana mazurai.


Nawfal ya zaro dukkan idanunsa, “Mansur! Kai ne? Kai da ka yi tafiya yaushe ka dawo har kake KoKarin kashe Nasreen? Innalillahi wa inna ilaihirraji un. Nasreen Mansur ne yazo yake son nakasa maki rayuwa. Ai na gaya maki mutumin nan baya sonki amma kika nuna min Karya nake yi. Ga shi ai shi yake baki wahalar nan.�


Nasreen ta shafi goshinta da yake mata radadi, “Nawfal ai Mansur baya garin nan ya akayi ya dawo? Mansur baka sona ka fitar da ni daga wannan gidan Wallahi na gaji.�


Mansur ya dan shafi kansa. “Kin gane ko? Kawai ina can ne aka yi min waya wai kuna son ku gudu ku bar gidan nan, ni kuma � da na ankare sai na shammaci kowa na dawo. Abin mamaki sai na sami kuna nan, Shaidan ne ya rinjayeni a kan ki Nasreen ke
6/9/22, 09:41 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 2🦚*






CHAPTER 5





*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*





MUN TSAYA


Hannunsa yasa ya dawo da ita baya, yana Kokann banKadeta, Tana son yin ihu babu dama haka kuma karfinta ya soma


Karewa. Mutumin da ke kwance akanta yaji anbuga masa wata sanda, mai girma da kauri. Da Karfi ya rike kansa sannan ya dago yana mazurai.


Nawfal ya zaro dukkan idanunsa, “Mansur! Kai ne? Kai da ka yi tafiya yaushe ka dawo har kake KoKarin kashe Nasreen? Innalillahi wa inna ilaihirraji un. Nasreen Mansur ne yazo yake son nakasa maki rayuwa. Ai na gaya maki mutumin nan baya sonki amma kika nuna min Karya nake yi. Ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login