Showing 99001 words to 102000 words out of 123375 words
Chapter 34 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt
kuma ya bi jirgin da ya yi booking ya koma Abuja cike da damuwar rashin Nasreen. A can gida bayan Umma ta gama waya da .Sultan Zakiyya ta fito tana waKe-waKe saboda ta ji lokacin da Umma take waya da Sultan, kuma ta kira shi yaKi dagawa, don haka ta fito da rashin mutuncinta. Kafar Umma ta take da Karfi
Umma tasa Kara, hakan yasa Hafsat fitowa da. tana duban Umman. Jin irin sayin da take yi wa Zakiyya ne ta fahimi abinda ke faruwa, don haka ta dora mata tafi a fuska tana huci. “Ke uwata ba sa’arki ba ce. Butulu kawai mun yi maki rana kin yi mana dare. Ki bar ganin ana Kyaleki wawuya wai idan an tambaye ta wai tana da ciki, bacin mun san komai babu komai a cikin. Ai shi ciki ba a Karyarsa domin nan da watanni uku dole ya bayyana kansa.� Zakiyya ta yi kukan kura za ta shako Hafsat
Hafsat ta nuna ta da yatsa, “Idan kika yi tsautsayin kwatanta hakan zan baki mamaki, don Wallahi sai kin koma gida kin yi jinyar kanki. Kada kuma ki ce ban gaya maki ba.� Dole Zakiyya ta dakata da abinda ta yi ninya, ta koma daki tana kuka ta gayawa uwarta, hakuri ta bata ta ce ta barsu tana nan tana sabon shiri akan su. Sultan yana isowa gida ya sami Umma ta gama shiryawa tsaf tana zaman jiran Sultan. Yana ganin abinda ke faruwa ya dubi Umma cike da mamaki ya ce, “Umma ina za ki je?� Umma ta fara hawaye ta ce, “Sultan ni zan tafi. Zakiyya ta ci mutuncina a gidan nan, haka
kaima baka dauke ni a matsayin uwa ba. Zan koma gun mijina na tabbata shi kadai yake sona ko da kuwa nayi wani mugun abu ne.�
Zakiyya ta fito tana taunar cingam, ta dubi Sultan ta mika masa takarda fara Kar da biro, “Ka sake ni ba zan iya ba. Kuma cikin nan zubar da shi zan yi. Ba zai yuwu wasu can su dake ni baka ce komai ba, haka Salamatu ta ce za ta kai hannu jikina. Dubi fuskata Hafsat ta mare ni.� Sultan ya dubi fuskokin kowa ya tabbatar da ba Karamin abu akayi ba. Ya riga yasan Zakiyya ‘yar dambe ce ta Karshe don haka kome za a ce ta yi ba zai musa ba. Yana son fara ba Umma hakuri domin zuwanta Kaduna wani tashin hankalin ne da zai hana shi samun natsuwa. Haka yasan Ummansa tana iya tsine masa akan dai kishiyar da za ta tarar. Don haka ya durKusa yana roKonta kada ta koma yanzu, ta bari ya sami natsuwa agun aiki a lokacin sai ta koma. Da Kyar ya shawo kan Umma, ita kuwa Zakiyya dubanta ya yi ya ce, “Wace ce kuma mai sunan da kika ambata?�
Ta dube shi sosai ta ce, “Wai Salamatu? Ga ta nan a gabanka.� Sultan ya mike cike da fusata zai yi kanta, Umma ta girgiza kai, “Kada ka taba ta ka barta da halinta, zan je Kadunan har gidan uwarta. Kuma ni ba ni ta kira kai tsaye ba, uwarta Ladidi ta kira. Shashasha wacce bata san ciwon kanta ba.� Zakiyya ta juya ta tafi tana taunan cingam da Karfi yana bada wani sauti. Shi dai Sultan yana gama lallaba Umma ya zayaya ya kira Abba ya kwashe komai ya gaya masa, Abba ya saki ajiyar zuciya yace“Sultan ka Kyale ta ta dawo nima ina son dawowar nata, � gara tasan komai ta yi abinda za ta yi kowa ya daina fargaba. Idan muka jure babu shakka zai zo ya wuce. Dole duk boye-boyenka watarana za ta sani. Zakiyya kuma kayi ta hakuri da ita ita kanta wataran sai ta yi danasani.�
Sultan ya amsa yana cewa, “Abba ko za ta zo ba zan bar ta ta dawo yanzu ba, ina cikin damuwa abubuwa duk sun Kwace min. Ga Office dina ina fuskantar barazana akan wani Case na fyade da aka yi wa wata ‘yar yarinya, so suke su bani kudi saboda kada sunansu ya baci, ni kuma naki karbar kudin, shi ne da su da Ogana suke aiko min da barazana. Kankat daga can sama gargadi ake yi min. Ni kuma na yi alkawarin ko wannan ne dalilin cire kakina sai na dau mataki a kansu.� Abba ya jinjina kai, “Hakane Babana Allah ya taimaka ya dafa maka. Ina Kara gargadinka da ko ni mahaifinka ka kama da aikata dokan da ta sabawa aikinka, ka kama ni ka hukunta ni daidai da laiifina. Allah ya yi maka albarka.� Sultan ya ji dadin furucin mahaifinsa haka yana samun natsuwa ne a duk lokacin da ya sanya masa albarka. Haka suka sauke wayar sannan ya nufi cikin gida wurin Zakiyya. Bai wani sha wahalar lallashinta ba, domin ya gaya mata ya daina lallashin mace, hakan yasa ta yi tunanin ko asirin ya yi sanyi ne? Dama kuma asiri sai dai ka dora, amma aikinsa kwana arba’in ne kawai, ya tashi aiki. Tunda Zakiyya ta riKe shi a daki ta hana shi fita, hankalinsa yana kan su Nasreen, haka yana kallon kiran waya da lambar waje, mai dauke da +44 ya tabbatar da Code din London ne don haka ya ki dauka ta gagare shi. Tafiyar awa shida da minti kusan arba’in da uku ya kawo su Kasar London. Kai tsaye aka
nufi da su shahararren Hotel din Marriot Hotel wanda babu nisa a tsakaninsa da eye Centre din da za ayi mata aiki. Tana jin Naufal da Jidda suna santin wurin amma ita babu idanun da za ta gane haduwar wurin, sai dai ta shaki iskan Kasar. Kai tsaye suka nufi gun Abokinsa Dr. Sadiq da ya iso da kansa yana murmushi.
Bayan sun gaisa ne ya dubi Nasreen ya ce, “Ita ce patient din namu? Al-ameen ya amsa masa, sannan suka shiga ciki. Jidda tana tare da Nasreen, Bayan sun gama cin abinci Jidda ta ce, “Wai don Allah ina kika samu wannan Kamshin ne? Tun a Najefiya nake son tambayarki. Idan kin zo da shi dan sammin in je dakin Abban ~ Muhsin nasan zai ji dadinsa.
Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Wallahi ~ Yumnah ta bani a lokacin da na je gidanta, shi ne Dee ya ji Kamshin ya matsa sai da.aka basa lambar Jafar din ya yi tattaki ya tafi har Zaria, yasa Kanwar Anti Fatima Dan Borno ta je ta siyo masa, da yake ance ita kanta Anti Dan Bornon acan take siyayyan duk wasu Kamshi da take amfani da su. Idan kika je ma za ki iya haduwa da ita taje nata siyayyan.� Jidda ta zaro idanu ta ce, “Ko dai agunsa ne Anti Bintu take siyan kayan Kamshin jiki da na gyaran fata? Ita ma daga Zaria ake sako mata a mota.�
Nasreen da hankalinta gaba daya yake gun Sultan ta ce, “Shi ne ma, shima a Sabon garin Zaria yake, wai kafin akai Police Station. Kuma ya riga ya yi sunan da kowa ya san shi. Yanzu haka Yumnah ta ce min idan na dawo za ta ba ni wani sirri da ta siya a wurinsa, wai ba kowa yasan sirrin ba. Karin abin burgewa talaka ma zai iya zuwa da kudinsa kadan ya mallaki abinda yake so. Bari in dibar maki ki je za ki ba ni labari.�� Jidda ta ce, ‘“‘Lallai ma Yumnah wato so sone son kai ya fi. Yanzu duk yadda nake da ita bata kawo min wannan na gwada ba?�
Nasreen ta miko mata, kai tsaye ta fada wanka ta fito ta goga man ta shafa dan humran ta fito tana tashin Kamshi. Babu kunya Jidda ta shige dakin mijinta, ta bar Nasreen da dogon tunani. A lokacin ne kuma Naufal ya shigo hannunsa dauke da waya ya miKawa Nasreen ya ce, “Ki yi magana Dee ne yake kan layi.� Shi ma ya fice abinsa harabar Hotel din yana kallon yadda tsarin su yake abin akwai sha’awa da sanya nishadi. Yana sanya masoya a cikin wani hali na samun natsuwa.
Nasreen ta lume akan gadonta tana jin sany1 yana ratsata, ta fara magana cikin sanyi da ruda dukkan wanda ya _ saurari wannan murya, “Amincin Allah ya tabbata a gareka uban marayu. Da fatan zuciyar da na bari a cikin shauki cike da soyayyata tana cikin kwanciyar hankali da natsuwa?��
Sassanyar murmushi ya saki sannan ya bata amsa cike da kewarta da ke nuKurKusansa, “Wannan zuciya da kika tafi kika bari, kin barta ne cikin sonki da kewarki hakan ya taimaka wajen Kuntatawa wannan zuciyar. Me yasa ma bature bai fitar mana da yadda zaka zama tsuntsu ka je dukkan garin da ka gadama a lokacin da ka. so ba? Ai da yanzu na iso bisa gadonki na tayaki barci irin na Lagos.�
Murmushi ya subuce mata, ta sake jawo filon ta KanKame. “Anan wurin haka tawa zuciyar take ciki. Sai dai jin muryarka ya kore dukkan wani Kishirwa da ke cikin maKoshina, hakan ke nuna min ruwan da yake nema ne aka kawo akan lokaci kuma aka shayar da makoshin har ya gamsu.�
Ya gamsu da bayanan matarsa akansa, ya gamsu soyayya tana matuKar riKe aure, musamman ma idan ladabi yana ciki. Domin ladabin aure shi ne magin cikin aure, soyayya kuma ya goya masa baya ya zama gishirin da ke cikin aure. Haka suka ci gaba da hira cike da annashuwa, haka kamar ba kudi ake cirewa ba. Ya ce mata ta riKe wayar zai dinga kiranta. Ta yi godiya ta ajiye wayar tana jin natsuwa tana shigarta. Jidda ce ta shigo tana murmushi, sai dai Nasreen ba ganinta take yi ba, don haka ta yi shiru.
Jidda ta ce, “Wallahi muna dawowa Najeriya zan ziyarci shagon Jafar dinnan da kaina ba sako ba. Kai amma dai Yumnah ta ci amanar zaman tare, shegiya sai shige-shige ka rasa wa yake gaya mata irin wadannan sirrikan.� Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Wa zai gaya mata idan banda ‘yar mutan Borno? Ita ta gaya mata komai. Shiyasa na gama kula kamar ta fi son Yumnah akan mu.�
Jidda ta girgiza kai, “Ke kike ganin hakan, amma ni nasan ta fi sona akan kowa.� Nasreen ta gyada kai “Zai iya yiwuwa. Yanzu na gama waya da Dee, ya ce yana gaida ku.�
6/29/22, 12:42 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4
CHAPTER 4
BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
MUN TSAYA
soyayya tana matuKar riKe aure, musamman ma idan ladabi yana ciki. Domin ladabin aure shi ne magin cikin aure, soyayya kuma ya goya masa baya ya zama gishirin da ke cikin aure. Haka suka ci gaba da hira cike da annashuwa, haka kamar ba kudi ake cirewa ba. Ya ce mata ta riKe wayar zai dinga kiranta. Ta yi godiya ta ajiye wayar tana jin natsuwa tana shigarta. Jidda ce ta shigo tana murmushi, sai dai Nasreen ba ganinta take yi ba, don haka ta yi shiru.
Jidda ta ce, “Wallahi muna dawowa Najeriya zan ziyarci shagon Jafar dinnan da kaina ba sako ba. Kai amma dai Yumnah ta ci amanar zaman tare, shegiya sai shige-shige ka rasa wa yake gaya mata irin wadannan sirrikan.� Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Wa zai gaya mata idan banda ‘yar mutan Borno? Ita ta gaya mata komai. Shiyasa na gama kula kamar ta fi son Yumnah akan mu.�
Jidda ta girgiza kai, “Ke kike ganin hakan, amma ni nasan ta fi sona akan kowa.� Nasreen ta gyada kai “Zai iya yiwuwa. Yanzu na gama waya da Dee, ya ce yana gaida ku.�
ZAMU TASHI
Ta nufi bandaki tana cewa, “Shi ya sa na ga fuskarki fes babu damuwa, sai fara’a kike yi, ashe soyayya kika sha.� Nasreen ta dan muskuta ta ce, “Ke kuma ruwa kika je kika ba shi kenan.� Jidda ta KyalKyace da dariya ta shige abinta.
Cikin dare Sultan ya kasa barci, yana kallon yadda Zakiyya take shakan barcinta minshari yana biyo baya. Gaba daya idan tana barci sai muninta ya sake fitowa. A cikin natsuwarsa ya mike ya fito
falonsa yana kaiwa da komowa, gaba daya ya rasa meke masa dadi? Yana son sake jin kalaman Nasreen, wanda yake masa kama da wacce take busan sarewa.
Wayarsa ya zaro ya danna layin da ya gaya mata ta rike wayar, yana addu’ar Allah yasa ta amsa ko a cikin magagin barci ne. Tunda yasan awa daya ne a tsakanin su da London. Ita kanta bata yi barcin ba, ta kasa samun natsuwa. Jidda kuwa tuni ta gudu wurin mijinta, daga cewa tana zuwa. Nasreen ta Kosa idanunta su bude tana son ganin Sultan, tana da burin ganin yadda Naufal dinta ya koma. Farin ciki ya Kara kamata, ta y! juyi ta sake Kankame filonta. Karar wayar ya ankarar da ita, ba tare da dogon tunani ba, ta lalubi madannin wayar ta danna ta kara a kunne. Kafin ta yi magana ta ji saukan ajiyar zuciyarsa. Ita ma bayansa ta bi da ajiyar zuciyar tana jin tarin natsuwa yana sake ziyartarta. “Na yi kewar muryarka. Na Kosa inganka na kasa mance zaman mu a Lagos na kwana daya tak! Sai nake jin kamar shekara muka yi.� Lumshe idanunsa ya yi yana sake cusa kansa a windo yana Karewa tsakar gidansa kallo da ya wadatu da Kwayaye masu haske. “Na fi ki tunawa da kwanan mu a Lagos, domin kina ta guduna, hakan ya rage mana jin dadin mu. Kina zaton zan yi maki wani abu ne? Babu abinda zan maki, ina sane da Kasar da za ki je, idan nayi maki hakan waye zai taimaka ya lallaba min ke kina narkewa ina lallabaki? Nasan abinda nake yi Nasreen, ina tattalin lafiyarki fiye da nawa. Bani labarin yadda kuka sami London.�
Ta dan shagwabe ta ce, “Ba na gani Dee, bana iya tantance fari da baki a cikin Kwayar idanun nan nawa. Amma naji Naufal da Jidda suna ta kururuta Kasar. Ka bani labarin Kasata Najeriya su Umma suna lafiya ko?� Idanunsa Kyar akan windo yana mamakin ganin kamar ‘yan sandan nan dukkan su barci suke yi. Kuma barci irin wanda ba Karamin nisa suka yi ba. Sai dai bai kawo komai a zuciyarsa ba ya ci gaba da cewa, “Kasarmu akwai dadi sai dai kwanciyar hankali da sakin jiki kayi barci sai turai. Gidan ya yi mana fadi saboda babu majidadin cikin gidan.�
Murmushi ya Kwace mata, “Irin sarautar da ka bani kenan? Zan fi kyau da sarauniyar zuciyar mijinta.� “Uhm! Babu sarautar da ban baki ba, ni da na baki sarautar Naufal gaba daya?�
Nasreen ta tuntsure da dariya, hakan ba Karamin faranta masa ya yi ba, ya jima bai ji dariyarta haka ba. Sultan ya shaki numfashi ya fesar a cikin wayar, wannan numfashi shi ya yi sanadiyyar mutuwar duk wani abu da ke jikinta, ya saukar mata da wani irin kasala. Itama ta sakar masa nata, a lokacin da bata zaci fitowarsa ba. Hakan yasa dukkansu suka yi shiru na wasu lokuta, wanda da ba dan saukar ajiyar zuciyarta ba, da zai iya cewa babu ita akan layin. A wannan lokacin ne kuma ya ware idanunsa masu tsananin haske ya watso a waje yana sake nazarin gidan. Motsi ya ji a in da bai kamata ba, hakan ya gane an shirya masa wani abu a cikin gidansa, cikin gaggawa ya koma ya dauko
bindigarsa ya fice a hankali. Shi kansa bai san bai kashe wayar ba, kawai mayar da wayar ya yi a cikin aljihu ya labe sosai, ta in da babu wanda ya isa ya ganshi. Ta nan ne yake hango mutane masu bakaken kaya, mamaki ya kama shi, ya kafe su da ido.
Yau lalacewa ta yi lalacewar da barayi za su tako su shigo har gidan AIG? Ta ya ya suka ci nasarar sanya masu gadinsa barci?
Baya buKatar kira a zo daga office shi kadai zai iya da su. Tuni zuciyarsa ta gaya masa daga inda suka fito, don haka ya sake samun Karfin guiwa. Kafafun daya daga cikin su ya saita a lokacin da suke KoKarin neman hanyar da za su shiga cikin gidan, ya danna masa harbi. Hakan ya gigita su, har suka yi zaton tabbas akwai wadanda maganin barcin bai yi masu amfani ba, sai dai idan suka tuna Karfin farin hodan da suka watsa suna da tabbacin ba tashin yanzu ba, sai dai idan akwai wasu a cikin gidansa. Amma kuma yawan ‘yan sandan da ke gidan an gaya masu ko su nawa ne, kuma gasu reras a kwance. Tunawa da Sultan din jan wuya ne ya sa duk suka sake gigicewa, suna KoKarin dauke wanda aka harba, suka sake jin harbi. Gashi ko ma waye
mai harbin ya Kware a saiti, indai ya harba sai ya sami mutum. Su Umma suka ji Karar bindiga don haka suka fito falon a gigice. Zakiyya ma jikinta yana rawa ta fito. Sultan ya dan waiwaya yaga Umma da Hafsat suna doso shi suna kuka, ya dan walwaya yana girgiza masu kai, “Umma ku koma ciki ku rufe Kofa insha Allahu babu abinda zai same ni.�
Hafsat ta fasa kuka ta yi bayan Sultan ta KanKame shi, Umma ma ta kama dayan hannunsa tana KoKarin jansa suna kuka, “Yaya ka taimake mu ka zo mu je mu Boye kada su kashe mana kai. Yaya ka zo mu je, ba zamu iya tafiya mu barka ba.�
Umma ta sake rike shi sosai tana fadin ‘‘Wallahi sai dai a kashe mu tare, ba zamu barka ka tafi ba, sai dai a kashemu.� .
Sultan yasan halin mata da gigicewa shiyasa bai so da suka tashi ba. Zakiyya kuwa tuni ta yi cikin daki da gudu ta rufe Kofa tana fadin wani miji ba za ta kashe kanta ba, su dai da suka ga za su iya su tsaya. Sultan ya juya da su Umma suka shiga daki ya yi masu dabara ya rufe su ya fice tsakar gidan gaba daya. Nasreen ta fasa Kara tana Salati, fadi take yi “Shi kenan sun kashe min shi, ankashe Deeedi wayyo! Ashe turo ni kayi nan Kasar saboda akasheka? Naufal! Na shiga uku bani da idanu ina